Sashe 12
Tsuron Tsirin Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ya kwasheshi. Ajjiyar zuchiya mai nauyi na sauke. A lokacin na samu zarafin yin sallah, na jima a sujjada ina kai kukanmu zuwa ga sarkin sarakuna, sarkin adalci, sarkin da babu sarki kamarshi. Ana kiran sallar isha, na miƙe na gabatar, ina yin Azkhar mijinyawa ya ɗan farka. Zaka iya zuwa banɗaki ka ɗauro alwala kayi sallah ko a zaune ne? Ɗan guntun murmushi yayi mun, wallahi sai naji sanyi da duk damuwar data dunƙule a ƙirjina. Ku fahimci wani abu guda ɗaya. Soyayya fa gaskiya ce, so kuma hana ganin laifi ne. Manzon Allah S A W da aka tambayeshi duk duniya wa yake so, sai yace Ummuna Aisha. Akace a maza fa, yace Abubakar Assiddiq. Wannan kaɗai ya ishemu mu san cewar soyayya ba ƙarya bace. Kuma ita Ummuna Aisha bata taɓa haihuwa da manzonmu Arrasul S A W ba. Amman munji irin son da yake mata. "Zan iya, jikin ai da sauƙi. Kina shagwaɓani fa" Hmm ai dole. Kaima ai kana da raki, baka da juriyar ciwo. Amman ni nafi kyautata zaton maganinnan da kasha ne ya turo zazzaɓin naka fa. Ina da fanado in kaci abinci sai in baka kasha" Miƙewa yayi yaje ya ɗauro alwala yazo ya gabatar da sallah, ni kuma kafin ya idar na kawo abincin da ɗazu Baraka ta aikoshi. Tuwon dawane da miyar lalo taji wake da daddawa, kuma ganyen lalo ɗinma yaji sosai sai ta tubke bata yi irin tsinkewarnan ba. A baki naita bashi yana karɓa. Tausayinshi na neman halakani (umminmama kina dai ji, da Maman Jaririya, da Mamanzee, da Jamilatsafe) "Ya isheni, bani maganin in haɗiya da tuwo" Maganin na saka mai a tuwo ya haɗiye. Saida naga ya kwanta kafin na soma cin tuwon. Duk gishiri miyar amman a haka na tuttura na kora da ruwa. Kusan dare na raba ina sallah, ina karatun Qur'ani. Hakanne yasa mijinyawa ya farka, shima auwalar ya ɗauro yazo ya tada kabbara, a lokacin ina miƙa godiyata ga Allah ne, tare da roƙon Allah ya bamu ikon cinye jarabawarnan. Bayan mijinyawa ya idar sai ya zubamun idanu, ɗakin babu haske saina acibalbal ɗin da ta kusan macewa sakamakon kalanzir da yayi ƙasa. "Mun tsallake ruwa, mun faɗa ruwa Tutar so. Ba abinda likita yace bane ya kwantar dani ba. Tausayinki, da yadda zan rasaki, da tausayin nawa kan su suka kaini ƙasa. Ciwonnan da Allah ya ɗauramun Allah shine shaidana wallahi ko da likitan ya faɗamun banji wata damuwa ba ta ƙashin kaina ba. Damuwata a kanki take. Ina sonki wallahi, inna rasaki shikenan" Sai ga hawaye Mijinyawa yanayi, hakan bai mishi ba sai kawai ya fashe da kuka yana shessheƙa. Shiru nayi ina kallonshi yana kukanshi. Zuchiyata nima suya take yi mun, idanuna a bushe tamkar zasu dare. Hannayenshi na riƙe gam, sai ya zubamun fararen idanunshi masu kwalli, da ƙyalli, da tasiri. 🤣 Kana tunanin zan rabu dakai, sabida ance baka haihuwane wai. Ashe kai bakasan girman sonka da nake yi bama ashe. Ruwa da iska ba zasu rabamu ba. Banyi tunanin akwai abinda zai taso maka na wata lalura da zata iya rabamu ba. Kaima baka gujeni ba a lokacin da danginka suke zargin rashin haihuwar daga gareni ne. Babu gori, ko canji dana samu a gareka, Ka bani kariya, har aure aka baka umarnin yi amman baka yi ba, duk dan ka bani kariya. Sai nice zan tafi in barka sabida baka haihuwa. Shin ƴa ko ɗan da zamu karɓo a gidan marayu bai ishemu rayuwar duniya ba ashe? Mijinyawa ka kwantar da hankalinka, akan rashin haihuwa bazan gujeka ba abadan wallahi ka rubuta a ajjiye. Kuma kaimun alƙawarin wannan sirrin namu ne mu kaɗai mu ya shafa. Bana son jin wannan sirrin a wajen kowa hatta Nanno bana so taji, har Qasimu da Abdulƙadiri nake nufi. Mu burne abinmu sabida kaga in muka tona muma mun ɗauki wuƙa mun daɓama cikinmu ne. Sabida yaron da zamu ɗakko da sunan namu. Ka kuma godema Allah a duk halin da kake ciki. Sannan ka dena tunanin zamu rabu, mutuwa ita kaɗaice ta isa raba wannan soyayyar." Hannayenshi ya zame a nawa yace. "Aa Hindu ni bazan zalunceki in tauyeki ba. Kina da damar da zaki iya auren wani mijin ki hayayyafa, me yasa zaki zauna dani da yaron da zamu ɗakko? Ai ni da cewa nayi zamu ce ma Nanno cikin ya zube kawai. Ko kuma mu faɗa musu babu cikin ƙaryace kawai muka yi, rabamu da take so ayi sai ya tafi akan wannan dalilin, kiyi haƙuri Hindu na roƙeki. Bazan iya cutar dake ba. Kina da damarki fa. Ina ina Hindu. Ban isa kashe miki rayuwa ba. Son da zan nuna miki wannan shine dasaukarwa mafi girma, kije ki yi aurenki ki ga jininki a duniya" Idanunshi sun kaɗa sun yi jawur dasu, jijiyoyin kanshi duk sun firfito, ga hawaye, harda majina. Ni mamakin kalamanshi ma nake yi sosai. Kawai saina kwanta a ƙasa na rabu dashi, yaita kuka yana mayawa. Sautin kukanshi na sawa inji kamar zan mutu. Shima filo ya kada ya kwanta a bayana. Idanunmu biyu har fa akayi kiran sallar asuba, sai dai makarai sun ziyarceni tabbas naji a jikina, ga kumburin fuska inaji. A hankali muka miƙe. Alwala ya sabumta ya fita, nima na sako alwala nazo na gabatar da sallah. Ina zaune a kan sallaya sai gashi ya shigo ba kuzari a jikinshi sam. Kwanciya ya kuma yi yana dafe da kanshi, idanunshi jawur. Na yinƙura zan tashi sai ya riƙe hannayena. Bakin gadon na dawo na zauna. "Hindu ya zanyi. Ki amince da abinda nace shine mafitarmu mai kyau. Ina miki irin son da zatonki bai zata ba. Na yarda na gamsu sonki yafi nawa yawa tun fari. Amman ki.... " Hannu nasa na rufe mishi bakinshi, sai yai shiru. Hindu takace abadan. Wallahi Allah akan wannan abun banga ranar da zan gujeka ba, ban ganta ba ban ganta ba. Muna tare har cikin aljannah, ni ɗinnan nice shugaban matanka na aljannah. Ni abinda nake so dakai kaji taoron Allah, ka godema Allah da abinda yayi maka. Musa hannu bibbiyu mu amshi ƙaddararmu, kuma in sha Allah zan ɗauki ɗan kunnena da sarƙana in siyar mu samu aima allurannan da magunguna da likita yace, sai kaga an dace bana so kana karaya dan Allah." Kamar ba namiji ba, sai ga hawaye na bin gefen kuncinshi yana zuba akan fulo. Tunda ya lumshe idanunshi, ya riƙe saitin zuchiyarshi bai sake cemun komai ba. Mun share kusan minti goma, ni ina mishi kallon tausayi, inaji dama ace ina da ikon yaye mishi damuwarshi, ko dawo da ciwon jikina, ace matsalar daga nice wallahi da nayi yanzu take. Sai dai kash, Allah shi yake yi, shi yake zaɓan wanda yaso, ba domin ƙiyayyaba sai domin jarraba imanin bayinshi. Haƙuri da rungumar ƙaddarar da Ubangiji ya ɗauroma ka iya sanyawa Allah yasa bawa a aljannah. Zan tattaleshi mu burne wannan sirri, walwalarmu da farin cikinmu nasan zasu dawo da zaran mun samu jinjiri a gabanmu da sunan ɗanmu. Bayan ya buɗe idanunshi naga sunyi wani irin ja mai ban tsoro. "Hindu me yasa kike sona haka, me yasa kike ta shan wahala sabida ni, wai me kike gani tattare dani ne haka? Naga ni bani da komai, ni ba kyau ba, ni ba likima mai zurfi ba, ni ba kuɗi ba. Ɗan ƙauye bagidaje dani" Soyayya ai gaskiya ce, in inason abu, ina sonshi ne da dukkan rayuwata, haka in naƙi abu haka nake, haka Allah ya halicceni. Babu irin sadaukarwar da bazan iya maka ba. Amman bana son cin amana daga wajen wanda na yarda dashi." "Nagode sosai da wannan soyayyar. Amman ban yarda ki saida ko da barimar hancinki ba da sunan wai ki biyamun kuɗin maganguna ba. Sannan ko ma kin siyar ba zasu isa kuɗin alluran har a gama ba. Sannan bani da amsar da zan ba su Innarmu a lokacin da zasu ankara babu wannan ɗan kunne da sarƙan. Kiyi haƙuri Hindu. Na miki alƙawarin duk inda maganin gargajiya yake zanje in nema, kuma in sha Allah zamu dace, ba sai kin mun wata hidima ba gaskiya, wacce kike yi ma ta'isa" Ajjiyar zuchiya na sauke kafin nace. Kayi haƙuri, babu wanda zai san na siyar. In haka kake gudu zan siyar da ƙananan ɗan kunnayena biyu, shi ɗan kunne da sarƙan sai in barshi. Amman batun maganin gargajiya ai bazan hana ba, sabida bansan ina za'a dace ba. Na asibitinma zamu soma. Da zaran naje gida na dawo. Ka amince dan Allah, domin Allah nayi maka bana neman komai a gareka" Tasowa yayi ya zauna da kyau muka fuskanci juna sosai yace dani. "To ni bansan me zance miki ba, bani da kalmar da zan iya gode miki, ko nuna miki farin cikina. Amman ga wani alƙawari ni mijinyawa zan miki. Ke da zama da kishiya har gaba da abada. Ke kaɗai zaki rayu a zuchiyata, rayuwata, gidana, daga ke babu ƙari in sha Allah. Babu abinda zan samu daga wata ɗiya macen wanda ban samu a wajenki ba. Hindu kin zamemun huɗu a ɗaya, ko mata huɗu ba lallai su kamo ki ba jarumata. Mijinyawa naki ne kiyi yadda kike so dashi, sai yadda kika ce. Na miki wannan alƙawarin ba dan tuwuici ba, sai dan dama a zuchiyata tun kafin wannan lamarin kinsan ina faɗa miki hakan. Duk da naga baki taɓa yadda ba. Amman a yanzu zaki yadda ai. Babu yadda za'ayima in Auro ƴar mutane alhalin nasan bana haihuwa " Laa ka adana wannan alƙawarin, zaka warke in sha Allah. Sannan kar kayi alƙawarin abinda ba zaka iyaba. Ai ba sabida haihuwa kaɗai ake yin aure ba. Nasan ribar soyayya Aure, rubar aure haihuwane. Amman ai Allah shi yayi masu haihuwa yayi marasa haihuwa. Suma marasa haihuwan sun ci ribar kasancewa a inuwar aure, kuma in suka riƙe aurensu da kyau zasu samu rabo mai kyau. Kar kasa in saka a raina wataran ina zaune inji ana shigo da Amarya kayo Aure." Jin kishi ya tsirgamun yasa na haɗiye wani yawu wanda da kanshi ya tsinko mun, duk na kishine. Mun daɗe dai muna tattaunawa, dake asabarne ba makaranta sai kawai muka kwanta tunda dama bamu samu bacci ba jiya. Ai kuwa sai