Sashe 67
Tsuron Tsirin Part 3 Complete Hausa Novel · about 5 min read
Gidan NagoÉ—i.:.
"Sabida Allah sai ka kamasu kaita lafta, nima gashi na samu tsarabata. Yarannan sun wuce duka, kaima ka sassautama kanka, girma yana ta hawanka. Tunda ka dawo da'ita gida shikenan sai ka zuba idanu aga zuwa da dawowan. Ni a wajena dakkotan baimun ba, nayi _nayi ka ƙi yaddane shi yasa na barka. Wannan dagiya taku daka gado, itama Hindu ta gado a wajenku, ku sassautata. Yanzu jibi Ruwayya duk yadda aka taru ana wannan dambarwar, mulkinta dake yana kanta ai bata ma leƙo ba fa."
Qazzafi ne ya leƙo.
"Baba Sojanmu zo kaga abinda Innarmu da Hindu suke yi"
Yana zazzare idanu yace.
"Me suke yi, ta kyale Hindu inma tafiya da'ita zasu yi sai dai su tafi da'ita. Babu abinda zanyi akai ni. Makaranta ne dole ta koma. In kuma basa ƙaunarta shikenan sai su ɗauketa suje can su rayu da'ita a duniyarsu"
Baba NagoÉ—i ya girgiza kai.
"Kai me yake faruwa? "
"Baba Innarmu ce ta shiga wani hali, sai jijjiga kanta take yi, ga Hindu sai wani irin abu take yi"
Baba Sojanmu da jin haka ya miƙe sai gashi a tsaye a ɗakin. In ya kalli Hindu, sai ya kalli Innah.
Baba NagoÉ—i ne yayi sallama ya shigo.
Innarmu na riƙe da kanta, sai jijjigashi take yi, idanunta tamkar zasu zazzago mata.
"Jeka Janaral adda'a za'ayi musu. Kai Qazzafi zo kayi ma Ruwayya. Ni bari in ma Hindu"
Baba Sojanmu yana tsaye ƙiƙam idanunshi akan Innah Ruwayya.
Qazzafi yaita ragargazo karatu, Baba Nagoɗi nayi. Duk da ƙarfi suke yi.
Hindu ta shiga kurma wani ihu ƙasusuwanta suna wani irin ƙara.
Take gidan ya kuma birkicewa, aka cika falonnan har ƙofar shigowa.
Karatunsu kawai kake ji da ƙarfi yana tashi.
Warware Hindu suka yi, ta sauke ajjiyar zuchiya a jajjere, sai numfashinta ya daidaita a hankali.
Innarmu kuwa ta dena jijjiga kan nata tayi shiru tana kallon Qazzafi.
Baba Sojane ya riƙo hannunta ya ɗagata.
Baice komai ba ya fito da'ita ƙofar ɗakin a cike dam da mata, harda Innah Abidah data cika ta batse. Ganin Baba Soja ya riƙo hannun Innah.
Baba sojanmu bai dureta ko'inaba sai turakarshi, ya zaunar da'ita. Ya tsiyaya mata ruwa a kofi ta karɓa tasha.
Zama yayi yana fuskantarta da kyau.
"Ma lob ɗago ki kalleni ko zanji daɗi. Ki faɗamun menene, na ɓata miki raine akan abinda nayi ma Hindu, ko kina ganin bai dace in tsaya rayuwarta ta inganta ba? Nine nan mai tsayama yaran maƙota, marayu, da zawarawa, da yaran ƴan uwa fa"
Kallonshi Innah Ruwayya tayi da kyau. Bata ce komai ba, amman yaga komai a cikin ƙwayar idanunta. Murmurshi ta sakar mishi.
Sai yayi ajjiyar zuchiya, tare da yin wata ƴar dariyar basawa amman can ƙasa_ƙasa.
"Ai baka laifi gogan Ruwayya jarumin maza, maza gumbar dutse. Lallai naji kana ba gidan labarin irin soyayyar da muka buga. Wannan yanayin kuma yana da nasaba da su Hindun, amman bai shafi hukuncin da kayi mata ba.
Taruwan ƴan gidannan, da maƙota_maƙota shi ya hautsinani kasan dama so akeyi a gansu a ƙasa.
Amman duk da haka basa ƙasa, yaron zai share hawayenta. Ina da yaƙini a kanshi."
ÆŠan juya idanu yayi yana girgiza kai halamun tunani kafin yace.
"Nayi farin ciki da ba nine silar shiganki wannan halin ba.
Kiyi kwanciyarki anan, kafin su NagoÉ—i su gama abinda suke yi. Akwai abinda kike sha'awar ci ko sha da daddare in kawo miki? "
"To kaza gashasshiya nake so, da nono mai sanyi in zan samu"
"Me zai hana Gimbiya zaki samu, ai ko babu ko rugane zanje in nemo miki. Matar janaral tauraruwar zuchiyar Janaral"
Murmusawa tayi.
Nan sukaita tattaunawa, Innah Ruwayya ta dinga tausarshi tana bashi kalma har ya huce. Amman yace baya ma son ganin Hindu ko jin halin da take ciki.
A haka aka samu nasara wannan allura ta lafa.
Innah Abidah kuwa a wannan ranar kusan alƙiyamarta ce ta tsaya. Ganin irin yadda Baba Soja yake ta ririta Innah Ruwayya. Da kuma maganar daya faɗa ɗazu wacce take ta mata ƙaiƙayi a ruhi. Kazarma a mota ya sakata suka je suka siyo. Itama ya siyo mata nata, amman ita a wajenta da kazar, gara ma kunu maras sikari.
Hindu kuma tunda dai ta samu wannan bacci fa, bata farka ba. Har washegari babu labari. An yi tunanin tashinta ma sabida sallah, amman gaskiya bata tashi ba.
Asama'u sai hayewa jikinta take yi tana kuka. Azgar shi baya kukan amman du yaran haka suke manne da Hindun. Abu fa har magriba. Hindu ga numfashi dai tana yi, amman taƙi tashi jijjigawar duniya.
Innah Ruwayya tayi ma Baba Soja magana akan halin da Hindu take ciki. Tana so suje Durumin iya da'ita wajen wani malami mai ruƙiya. Yace shi babu ruwanshi, in sun ga dama suje, in aljanun sun so su saceta ma uban kowa ya huta.
Haka dai Qazzafi ya tuƙasu zuwa Durumin iya, da rakiyar Saratu da Zubaina.
A gidan maganinne aka samu ta farka bayan adda'a da ya dinga yi, yana yarfa mata tuwan tofi.
Ta farka, amman babu baki, sai idanu. Ga jikinta yayi tsami sabida makarai, da kuma yadda ta sha nannaɗa. Ta miƙe ma ta kasa miƙewa sai su Yaya Saratune suka taimaka mata ta miƙe, aka kaita mota.
Ko da suka dawo. Innah Abidah na falo ranar kwananta ne, ta kallesu ta watsar, a cikin gidannan babu wanda ya tako yaji jikin Hindu, ta farfaɗo ko bata farfaɗo ba. A maza mazan kuwa harda samarin gidan saida duk suka shigo. Da yaran maƙota da suke kwana a shagunan gidan, tare da mazan gidan duk sun shigo. Qazzafi kuwa sai da aka tilasta mishi, aka guyabeshi kana ya tafi. Amman yana kiran lanlin yaji ya jikin nata.
Yaya Saratu bayan sun dawo ta samu tawul duk ta goge ma Hindu jiki da ruwa mai zafi, bayanta daya fashe ma ta gasa mata, Innah ta ba da man zafi aka shafa mata. Sallolinta tayi abunta a zaune, ba baki dai, sai magana ƴan uwanta suke yi, duk sun ruɗe, Innah ce take ta ƙarfafasu.
A baki Innah ta ba Hindu kunu, yaranta suna jikinta, annuri fal fuskarsu ganin uwarsu ido biyu. Azgar sai magana yake yi mata, amman ina ba bakin magana. Innah sai girgiza kai tayi yi. Tausayin yaran duk ya cikata.
Hankula sosai suka tashi gaskiya.:.