← Book details Tsuron Tsirin Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 70 OF 84

Sashe 70

Tsuron Tsirin Part 3 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Hindu:.
Komawa gado nayi na kwanta tare da lumshe idanuna.
Ina maƙale a jikin labule naji duk abinda aka tattauna.
A daren ranar a sallaya na kwana ina roƙon Allah ya buɗe mun bakina, ya sassautamun nauyin da zuchiyata take yi mini.
Innarmu na gefena ta idar da nata sallar tana karatun Qur'ani ne cikin ƙira'a mai daɗin amo.
Baba Sojanmu ne ya turo ƙofar ya shigo, dake ba sakata ake sakama ƙofofin ba. Ƙofar babban falo kaɗai ake sakama sakata, sai turakar Baba sojanmu.
Shigowa yayi da jallabiyya a jikinshi.
"Da daddarennan ina ka baro Abidah Uwargida sarautar mata? "
"Tana bacci. Ƙira'arnan taki da take ƙara mun sonki ita ke tashina a duk daren duniya. Inma muna tare, inma bama tare. Alwala zan ɗaura in yi sallah nima huɗu saura yanzu, bacci yayi mun nauyi. Gaki ga ɗiyarki kuna raya dare. Ubangiji Allah ya ɗaga darajarku, ya haskaka sadarinku, ya baku abinda kuke so fid duniya wal akira. Masu tsayuwar dare Ubangiji yana haska musu gabansu sosai, yana cikin lamuransu face_face. Ko da wannan kaɗai kinyi zarra. Balle kyawawan, natijajjun halayenki yawa garesu.
Dubanshi ya dawo dashu gareni. Ya É—an murmusamun, nima na mayar mishi da murmushin. Kaina ya É—an bubbuga halamun rarrashi, jin daÉ—i.
Miƙewa yayi ya fita, yana murmushi.
Ai ko sai muka jiyo muryar Innah Abida har da kukanta wallahi.
Kai kawai Innarmu ta girgiza taci gaba da karatunta. Kishi masifa ne wallahi mata. Tsawon waɗannan shekarun gidanmu yaƙi samun zaman lafiya, da haɗin kai. Tsawon wannan lokacin an kasa sanyama zuchiya risilama. Shin sai yaushe kenan komai zai ƙare kenan?
Wani ɓangare na zuchiyata yaimun matashiya da cewa.
Dukkan abun duniya yana da iyakarshi. Ita wannan iyakar zata zo, ko da shiri, ko babu shiri. Watarana za'a wayi gari ɗaya ya mutu, ƙura ta lafa. Ko a wayi gari ɗaya ba lafiya cikin rashin zato da tsammani. Komai ya lafa. Inma ba haka ba. Akwai ranar da sai dai a kalli juna kawai, an kai matakin tsufan da kowa nafsi_nafsi ne kawai.
Ajjiyar zuchiya na sauke. Jama'a ina tsoron Allah, ina tsoron ranar mutuwata, ina kuma tsoron day wan a kabari. Allah alhakim.
Bani na kwanta ba sai da nayi sallar asuba.
Ban samu farkawa ba har sai da luba ta zo, lokacin Innarmu ta tafi aiki ne inaga.
"Hindu! Hindu!! bacci kike yi"
Kamar almara bayan na buÉ—e idanuna, dana motsa harshena da zummar amsawa, kamar yadda nake yi kullum bana gajiyawa. Sai kawai naji na haÉ—a kalma.
Na'am Luba.
Ihu Luba tayi ta rungumeni, ni kuma saina kama dariya inata ambaton sunanta.
"Alhamdulillahi naji daÉ—i dana kasance wacce taji muryarki a fari.
Kafin nan mijinyawa ya aikoni da takadda, ki karanta kafin a shigo ki bani amsa in kai mishi yana bakin titi maza_maza."
Wasiƙar ta zaro ta banin
Cikin gaggawa na warwareta.
*Zan soma da sallama irinta addinin musulunci. Amincin Allah ya tabbata a gareki.*
*Dama ace ina da damar dawo da lokaci baya, da banzo na zama silar shiganmu mawuyacin hali irin wannan ba.*
*Inama ina da dama dana riƙeki a jikina na rarrashi abuna.*
*Hindu babu wanda yake da damar rabamu tunda Allah shi ya haÉ—amu.*
*Mun zame musu tsuron tsirin tsandauri kafin Allah, bana mutum ba.*
*Naji irin halin da kika tsinci kanki na ɗaukewar murya, irin wanda kika taɓa yi a baya.*
*Kiyi haƙuri, ki yi haƙuri, kiyi murmushi, mijinki na miki adda'ar samun lafiya a kullum.*
*Ina mai baki haƙuri, kinga na kwana har biyar banzo ba ko?*
*Nasan baki yi wannan tsammanin ba, bani da lafiya tun ranar dana bar gida, har zuwa yanzu da nake gidan Luba ina rubuta miki wannan takadda.*
*Na kawo kuÉ—in fom É—inki, a zuwa na biyu in sha Allah zan zone in É—aukeki mu koma gidan mu anan Kano.* *Naje na samu Kawu munyi magana muna jiran Nanno....* "
Sallamar Yaya Saratu ne yasa nayi saurin ɓoye takaddar a ƙasan filo.
"Luba kece kika zo duba jikin ƙawa? Nima aiki zan wuce nace bari inzo in dubata.
Asama'u ba lafiya harma an kwantar dasu Innarmu ma tana can ita da Baba Sojanmu.
Me ya sameta Yaya? '
Jin muryata yasa itama tayi hamdala tana ta murna. Nima murmushi kawai nayi mata.
"Ban dai san meke damunta ba. Dama tunda na tafi dasu take ta laulayinta, tunma dai ban ɗaukesu ba. Sannu kema Allah ya ƙara sauƙi. Ga farfesu na kawo miki kici. Ni zan tafi aiki, inna dawo zan biyo"
Nan tai mana sallama ta fita.
Luba muje ki kaini inga mijinyawa "
"Wa wallahi baki isaba, ƴar mai taurin tsiya. Dan wallahi masifa kike shirin ja mana mai tsayi. Ki yi gagawar rubuta mishi amsarshi in kai mishi, tun kafin Baba Sojanmu yazo ya rutsamu. Ke da yasan an kawo takaddarnan har zan mayar da amsa ke ya kike ganin abubuwa zasu kasance ne. Zaneni zaiyi ƙila harda Sunusi"
Luba duk ta rikice. Takadda da biro na nema nayi rubutu na naɗe. Jakata na buɗe na zaro kuɗaɗen dana nannaɗe a zani, na ɗiba na mayar cikin ƙasan kaya, mai yawan kuma na nannaɗe a zanin ba tare da Luba tasan menene ba. Na nemi leda na jefa zanin.
Na bata.
"Bari in kai mishi in dawo mu sha farfesunnan. Yaushe rabon mu gamu."
Tayi sauri ta fice.
Ajjiyar zuchiya na sauke. Sai nake jina tamkar wata sabuwar halitta. Sai na shiga tausayin bayin Allahn da Ubangiji ya haliccesu ba Magana. Allah buwayi gagara misali. Mai yin yarda yaso da bawanshi.
Allah Ubangiji ya bamu ikon tsarkake harsunan namu. Domin akwai tarin tulin al'ummar da harshe zai halakasu, ya jasu izuwa wuta.
Luba taje ta dawo muka sha farfesunmu, mukaita hirarmu, aikinma bata je ba. Hankalina ya dawo kan yarana kuma.
Da yamma sai ga Innarmu an sallamo Asama'u a Asibiti, tana goye da'ita Azgar kuma ta riƙeshi a hannunta.
Ba Innarmu ba, hatta su Azgar sun yi farin cikin jin amona. Duk da kasancewarsu yara.
Sukaita wasa a jikina, Asama'u babu kuzari a jikinta sam sam. Ita kuma haka Allah yayita laulayi ne da'ita sosai, wannan laulayi yasa bata girma sam, kamar yarinya ƴar watanni, hatta ƙafafunta basu da ƙwari sosai, data miƙe saita faɗi. Sai ta ɗan soma tafiya ƙafar ta ɗanyi ƙwari. Sai ciwo ya kwantar da'ita, shikenan sai ta dawo ba.
Gaga_gaga_gaga_gaga.
Haka abubuwan suka ci gaba da cukumurÉ—awa.
An siyo mun fom na jamb na cike, tare da manna fasfo É—ina. Mijinyawa kawai nake jira, inji inda zancanmu ya kwana.
Gulma da tsigudidi fa sai wanda Æ´an gidanmu suka manta.
A cikin Æ´an gida, duk wacce ta kawo ziyara sai labari ya dawo sabo.
Akaita caccanja labari, tare da ƙawatashi dan yafi armashi, kai subhanallahi, tur_tur da wasu gidajen yawan.

Mijinyawa.:.
Chapter 70 · 0% Book details