← Book details Tsuron Tsirin Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 84

Sashe 8

Tsuron Tsirin Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"A sanin kanku ne samun ɗan mutum musamman jariri abune mai wuyar gaske a gaskiya. Wani lokacin kuma mu kan same su ma a kusa_kusa, kuga mun haɗa biyu uku ma. Amman ku zuwa nan da wata nawa kuke da buƙata? " Mijinyawane yace. "Wata bakwai, ko shida haka, imma ta kama wata takwas ko tara muna so, tunda ana haihuwar shekararren ɗa, ko mu shekara guda muka yi a cikin ummanmu kafin ta haifemu, harma anata zargin asiri akai mata" Sai da ta nisa kafin ta soma magana, ni dai gabana ma sai faɗuwa yake yi. "Hanyoyin da ake bi domin ɗaukar yaro (adoption) a gidan marayu a Jihar Bauchi, dama ko'ina a Najeriya, suna tafiya ne ƙarƙashin dokokin ƙasa da na ma'aikatun walwalar jama'a na jiha. Babban mataki na farko shi ne tuntuɓar Ma'aikatar Shari'a da Walwalar Jama'a (Ministry of Women Affairs and Social Development) ta Jihar Bauchi, domin su ne ke da alhakin amincewa da tsarin bisa doka. Kuma fa tsarukane masu yawa dake sa da dama sarewa, koma haƙura da abun baki ɗaya. Ɗan mutum ba wasa bane sam. Tsarin ya kasu kashi da kashi kamar haka: Sharuɗɗan Da Ake Bukata Ga Mai Neman Ɗaukar Yaro Dole ne mai neman ɗaukar yaro ya kasance yana da aƙalla shekaru 25, kuma ya girmi yaron da yake son ɗauka da aƙalla shekaru 21,. Idan Ma'aurata, kamar ku haka ne, Dole ne miji da mata su amince, kuma su haɗu tare su nemi ɗaukar yaron. Idan mutum ɗaya ne (maras aure), yawanci doka ta fi amincewa mace ta ɗauki yarinya mace, muddin ta cika sharuɗɗa. Tabbatar da Samun Kudin Shiga, Dole ne a nuna shaidar samun kuɗi ko sana'a tabbatacciya da zata ba da damar kula da lafiya, ilimi, da kuma ci gaban yaron. Matakan Da Ake Bi Wajen Aiwatar Da Tsarin. Shine Sayan Fom da Neman Izini. Zaku ziyarci Ma'aikatar Harkokin Mata da Walwalar Jama'a ta Jihar Bauchi, don bayyana aniyarku tare da cike fomin neman ɗaukar yaro na hukuma. Tantancewa da Binciken Gida (Home Assessment): Jami'an walwalar jama'a (Social Workers) za su ziyarci gidanku, don ganin yanayin wurin da yaron zai zauna, da kuma tabbatar da cewa kuna da halayya ta gari da kuma ikon kula da yaro ta fannin tunani da lafiya. Tattaunawa (Interview) Hukumar zata zauna da ku (idan ma'aurata ne) domin tattaunawa ta musamman don gano manufarku ta gaske. Ziyartar Gidan Marayu. Idan hukuma ta gamsu, za a ba ku izinin zuwa babban gidan marayu na gwamnati, ko wanda ke da rajista a Bauchi domin duba yaran da suka cancanci a ɗauke su, Lokacin Gwaji (Fostering/Attachment Period) Yawanci ana bayar da kwanaki ko watanni uku (3 months) domin ku zauna da yaron a gidanku karkashin sanya idon jami'an gwamnati, don ganin yadda zaku saba da juna, amman wannan sai in babba zaku ɗauka, ba wai jariri sabuwar haihuwa ba. Matakin Ƙarshe na Kotu (Legalization) Bayan cikar lokacin gwaji kuma, jami'an walwalar jama'a sun kawo rahoton cewa komai yana tafiya daidai, za a shigar da maganar gaban Kotun Iyali (Family Court / Juvenile Court) a Bauchi. Alƙali zai duba dukkan takardun, idan ya gamsu, zai bayar da takardar umarni ta ƙarshe (Adoption Order) wadda ke tabbatar da cewa yaron ya zama naku, na shari'a guda ɗaya da halataccen ɗan da kuka haifa. Mataki na Farko, da zaku bi, Idan kun shiga Ma'aikatar Harkokin Mata ta Jihar Bauchi, ku nemi Sashen Walwalar Jama'a (Department of Social Welfare). Neman Darakta ko Jami'i, Za ku nemi ganin Darakta mai kula da walwalar jama'a (Director of Social Welfare) ko kuma jami’in da ke kula da shirin Adoption/Fostering. Aikin Jami'an Su ne za su saurare ku, su ba ku fomi, su bayyana muku dukkan takardun da za ku kawo, kuma su ne za su gudanar da binciken gida (home assessment) don tabbatar da kun cancanci daukar yaron. Sanya Hannun Kwamishina, Neman amincewar Kwamishina ko sanya hannunta yana zuwa ne a matsayin mataki na karshe na gudanarwa (administrative approval) bayan ma'aikatanta na karkashinsa sun tantance ku, kuma sun gamsu da buƙatarku. Dakta Aisha usman Mahmood itace kwamishiniyar harkokin mata da walwalarsu, macece mai kirki da sanin makamar aiki. Na sanda sanadiyyar ƙawar Yayata ce, tare suka yi makaranta. Zan taimaka muku dan ganin tsarin ya tafi yadda suke so. Kana kafin a mika muku jariri sabuwar haihuwa, ma'aikatar walwalar jama'a tare da hadin giwar asibitin gwamnati za su gudanar da cikakkun gwaje-gwaje na lafiya (medical check-ups) ga jaririn. Wannan ya hada da duba lafiyarsa ta asali, gwajin jini, cututtuka masu yaduwa (kamar HIV, Hepatitis), da sauran matsalolin lafiya na gado, domin ku san ainihin yanayin lafiyar jaririn da kuke shirin riƙawa. Shikenan aiki ya kammalu in sha Allah. Amman fa samun jaririn shima wani hot kek ne, amman iyakar bakin ƙoƙarina a gaskiya zan yi muku in sha Allah, sabida Harira. Zan kuma taimaka muku wajen bin dokokin domin abun yazo muku da sauƙi. Amman zaku sha dai zurga_zurgane dai, da fatan ba zaku gajiya ba dai. Sabida akwai da dama da suke somawa su kakare su haƙura, furoses ɗin da yawane. Allah yasa mu dace, in kuna da rabon haihuwar Allah ya baku, in babu kuma ya sanya haƙuri da dangana a zukatanku, yasa ku samu mai share muku hawaye. Shi ɗa muddin yana jinjiri kuka ɗauka mancewa akeyi da ba'a haihuwa, ko baku kuka haifeshi ba ma. Nima ɗana na fari tsintarshi akayi, a lokacin an kai gidan mai unguwar ƙauyenmu ne, kafin a damƙashi ga gidan marayu na buƙaci inaso. Aka bani shi, bayan dana ɗaukeshi saida na shekara ashirin kafin na samu haihuwa, lokacin na girma al'adatama daf take da tsaiwa. Yana daga cikin dalilan da yasa na nace saida na samu aiki a gidan marayu. Kana na daga cikin dalilina, na yin iyakar iyawata, akan matan da suka zo gareni da nufin ɗaukar yaro." Jikin mijinyawa yayi wani irin sanyi gaya, ga karaya nan a idanunshi linkib. Ni kaina bawai ban sare bane, amman na danne kuma ina da yaƙinin inna miƙa lamarin ga Allah zan samu dacewa, Allah zai mana mafitar da bamu yi tunani ba. Nasan dai za'a sha fama da Nanno ne kawai, domin zata ga sunturin yayi yawa, amman inaga hutun makaranta zan ɗauka muyi amfani da lokacin wajen duk zurga_zurgar daya dace kawai, shine abu mafi sauƙi daya dace. Wannan Hajiya mukai ma sallama Harira ta rakamu har inda zamu shiga mota, mun yi da'ita akan sati mai zuwa zamu dawo mu soma wannan aiki da muka saka a gaba. Dafani tayi muna zaune a mota ana lodi tace. "Adda'a zaki dage dayi. In sha Allah zaki samu salama. Mijinyawa sai ka kula da'ita sosai dan Allah. Ina fatan in da rabonku zaku haihu watarana zaku riƙe ɗanku ko ƴarku a hannunku in sha Allah" In sha Allah Harira. Ina ƙara jaddada ki zama mai alƙawari, da riƙon sirri dan Allah. Yadda da aminci yasa nayi wannan maganar dake, domin kuma samun mafita. Bani da wani sirri daya wuce wannan a duniya" Murmushi tayi mun tace. "Ki ɗauka tamkar baki sanar ma kowa ba. Ki ɗauka Harira ta mutune an birneta da sirrinki Hindu" Sallama muka yi ta wuce. Mijinyawa ya dubeni da kyau yace. "Kawo kuɗi in siyo mana masar Bauchi gashi nan anata tallansu sai ƙamshi take zubawa." Kuɗin na zaro na miƙa mishi, ya dure zuwa waje, dake motar bata cika ba. Masa harda tsire mai zafi ya siyo mun da ruwan swan na gora. Motarmu ta tashi, muna tafe na ɗaura kaina a kusa da kafaɗarshi ina murmusawa harna hangoni da goyo a bayana ina jijjigawa, ko kuma yaro ya hanamu bacci munata rarrashinshi. Ko kuma yayi fitsari, ko bayan gida a cikin ruwan wankanshi, kamar yadda naga yaran uwatale, da su Shafa suna yi. Murmushi mai sauti nayi, wanda hakan ya jawo hankalin mijinyawa ya taɓani nayi saurin ɗagowa, muka zuba ma juna idanu, cike da soyayya da tsantsar nuna kulawa." "Hankalinki ya kwanta kema zaki mallaki ɗanki na kanki ko? " Yayi mun maganar kusa da kunnena. Kai na gyaɗa mishi halamun eh. "Farin cikinki shine farin cikina. Nayi murna dana amince miki kika samu farinciki. Ina fatan yaron da zamu ɗauka ko yarinya ya zame mana abun alfahari, ya tallafemu a yayin rauninmu, mu bashi tarbiyyar da ko wata rana lokaci yayi halinshi yasan bamu bane iyayenshi na asaliba. Ya zamto yana alfahari damu in sha Allah" Da waɗannan maganganun muka isa jama'are, daga tashar muka hau acaɓa har zuwa ƙofar gida. Shi ya tsaya a wajen su Abdulƙadiri. Ni kuma na shige gida, ledar masata tana cikin mayafi. Ina ajjiye mayafi Uwatale ta shigo da kwano a hannunta. Miƙewa nayi muka haɗa idanu, na ƙanƙance idanuna na tsantsar ɓacin rai. Kafin ince wani abun tace. "Yi haƙuri naga ranki ya ɓaci, dama ɗan wake ne na kawo miki ko zaki ci. Amman naji ma ƙamshin kamar masa ko tsirene kike yi." Bana cin ɗan wake, sannan in zaki shigo ɓarayin mutum a ƙa'ida sai kayi sallama an baka izini kafin ka shigo. Babu mamaki ma baki san anayin hakan ba ko?" "Me kike nufi Hindu? " Abinda kike nufi shi nima nake nufi." Wucewata ciki nayi da laidata na barta nan a tsaye tana sababi. Mijinyawa na shigowa ciki ya zauna kenan. Sai ga sallamar Nanno, tare da kwaɗamun kira. A guje mijinyawa ya fito, ni ko da ƙyar na fito ma. Ɗan wake na gani zube a ƙasa yasha ƙasa. "Yayi kyau hamshaƙiya mandiya ɗiyar ƙaruna. Sannu nace ɗiyar sarki fir'auna sarkin da yace da kanshi shine Allah ma baki ɗaya, sabida yadda duniya tayi mai daɗi. Yau kinci albarkacin cikin dake jikinki, wallahi da kinga abinda zan miki akan wannan almubassazancin da kika yi akan ɗan wakennan" Mijinyawa ne yace.. "Nanno wai me ke faruwane dan Allah, aimun bayani mana? " "Ga matarka nan zata yi maka bayani. Ina laifin uwatale dan kawai ta nuna kulawarta gareta. Karfa ka mance uwatale matar wanka ce, ɗan uwan tagwaitakarka, kuma ƙanwarkace Uwatale. Kaga matarka so take ta rabaka da uban kowa. Sai dai danginta kawai, dasu zata fi so ka samu kusanci. Inta haihu bansan wanne irin mulkarka zata yi ba. Ina tausayama a hannun wayayyar mace wallahi. Ke Uwatale ki fita sabgarta
Chapter 8 · 0% Book details