← Book details Tsuron Tsirin Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 84

Sashe 16

Tsuron Tsirin Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

goma sha biyu na zuba, na kwarara miya akai na koma ciki. Kaza na tadda Salamatu tana ci, ga kular Alala da kunun gyaɗa a gabanta kuma. "Hinduwa ashe wai kin samu ƙaruwa ɗan da ƙyar kenan " Allah ya nufa" Iyakar abinda nace kenan. "To Allah ya raba lafiya. Ba ranar komawa karatu kenan, sai lokacin reno" Saida na zauna kana nace. Ai banyi tunanin reno yana hana karatu ba, da yana hanawa da Yaya Saratu bata yi ba, dasu Khadijan lungun Baba Nagoɗi ba. Kuma ke kanki ai da baki yi aikin ba, tunda kema kin haihu. Lokaci in yayi zan koma karatu in sha Allah" Bakinta ta taɓe, Baba Sojanmu kuma yana shan wannan farfesu yana kallonmu. "Ai Salamatu zai zo ne ya sameni a wannan karon tabbas sai an tsaida mun lokaci kafinma in barta ta koma. Naga abun nashi tamkar raini ne ko menene dai oho. Amman duk abinda ke kanshi saina sauke mishi. Ba lallai ta koma wannan ƙauyen ƙayau ɗin ba" Ni dai nayi shiru ina cin masa har lumshe idanu nake yi sabida tsabaragen daɗin masar. Salamatu kuwa, sai zaro magana take yi, da misalai domin sake harzuƙa Baba Sojanmu. Ina kammalawa sai ga Qazzafi ya shigo falon, ya nemi waje ya zauna. Innarmu kuma tana daga falonta tana aikin kasafta tsarabar da nayo mai yawan gaske. Yadda nake samun damar kawo tsaraba mai yawa, tanadi nake yi duk ɗan abinda yake arha sai in siya in adana, da haka haka har in cika buhu da tsaraba. Nan kuma Innarmu tasa aka soma zagaye da tsarabarnan lungu_lungu harma da maƙota. "Abidah ga naku da Salamatu." "Aa ni kam sai dai Innah ki haɗa da nawa ni kam nagode" Cewar Salamatu kenan. Ni hankalina ma yana kan Baba Sojanmu da Qazzafi muna ta hirarmu. Zuwa sha ɗayan rana gida ya soma ɗinkewa da jama'ar taro. Bayan azahar su Zubaina suka dawo wajen aiki. Nan muka sanya kayan fitar suna, ni dai lace na saka su Yaya Saratu da su Rayya kuma Atampa ce suka saka, amman ba anko ba dai. Ƴan gidanmu sabida gulma fa, wallahi kowa sai zuwa ganina yake yi ana ta yi mun barka da arziki, kona gulmane, kona gaskiya ne ohon musu dai. Sai kusan magriba muka samu kammu ƴan ɗakinmu mu ka ɗan keɓe. "To ke Hindu wanne tanadin kika yi tun da kafin samun cikinnan. Sannan menene shirinku. Masu kurmin idanu da wuri suke soma kuka. Kinsan dai za'ayi gayya ta mamaki, kuma kowa yaje yana son ganin me za'ayi me akayi. Ko ba haka ba Saratu? " "Hakane Innarmu nima dai hankalina duk kuma sai ya koma kan yadda za'a ƙarke. Sabida muna da ƴan baƙin gida, ga ƴan uba dake son ganin faɗuwarka. Musamman faɗuwar ita Hindun. To ya kamata a san abun yi. Tunda ba lallai ta sake zuwa ba sai dai ƙila saƙon takadda. Batun wankan gida shima za'a tattauna muji yadda zata kaya" Yaya Zubaina tace. "Gaskiya kam ni tunda aka sanarmun wallahi harna soma ajjiye atampa, da kayan yara wanda maza da mata zasu iya amfani dashi ma. Innarmu duk ta koya mana tsimi." To ni dai kam muna yin namu shirye_shiryen daidai da ƙarfinmu, ta namu ɓangaren Innarmu. Danginshi ma suna yin nasu, gaku kuma dai. Ni dai Allah ma ya saukeni lafiya ji nake yi kamar ma mutuwa zanyi ba lallai in haihu ba" Nayi hakanne sabida in rage ƙarfin maganar tasu, sabida bani da abun cewa amman dai in sha Allah ba zamu ji kunya ba, zanyi iyakar iyawar abinda zan iya. Ga ɗan adashen makaranta ma na shiga. Kuma inaso in sake labule da kafet ɗin falo, kujerunma so samu in sauyasu, amman bana jin zai yiwu gaskiya" "Babu komai a bar maganar Ubangiji Allah zai saukeki lami lafiya Hinduna. Ki ta adda'a Allah zai saukeki lafiya. Akwai kayan jira jirai na fitar suna da setin jinjirare zaki haɗa ki tafi dasu. Sannan in cikin ki fa ya tsufa ki sashi ya dinga fita dake kina tattaki Hindu. Allah ya saukeki lafiya ai zanji daɗin ganin abinda zaki haifa" "Kuma Innarmu ai ya kamata ace kafin suna, a sauyama Hindu kayan ɗaki, ko da ba sababbi dadal bane, amman me kika gani shekara shida fa?" Cewar Yaya Saratu. "Eh to wannan gaskiya ne. Sai dai kuma wannan aikin naki ne. Abinda yasa nace haka, nafi son a sai kayan a Kano nan, a kai sai a kwaso natan a siyar. Zan mata ciko ko ba sababbi bane a sauya ɗin yana da kyau." Da haka zancan ya ƙare dai. Washegari da safe na shirya Qazzafi ya kaini gidan Luba. Tana tsakar gida, wanki ta tara mai yawan gaske ta duƙufa tana ta fama, ga igoyoyin gidan cike_cike fam da kayan shanya. Matan gidan kuwa Facalolinta ko wacce aikinta take yi. Masu girki nayi, masu kitso nayi, masu wankin ma dai duk suna yi ko wacce tana ƙofar ɗakinta. Luba na ganina tazo da gudu ta rungumeni sai kawai ta saki kukan farin ciki. Wani sanyi naji a raina. Ita hanyar nuna ƙaunarta da kewarta kukane, ni kuma sanyi nake ji a cikin zuchiyata annuri ya bayyana a fuskata. Jama'a ina son Luba sosai, kuma inai muku adda'a Ubangiji Allah ya haɗaku da ƙawaye na amana, ƙawancen gaskiya da gaskiya akwai daɗi sosai. "Hindu kinsan Allah jiya nayi mafarkinki wai kin haihu munje suna anata rikici da Yaya Jamila" Dariya muka saka ta jawo hannuna muka wuce. Cikin jam'u na gaishe da matan gidan. Duk suka washe baki cike da fara'a suka amsa gaisuwata. Ciki muka shige ni da Luba, ni a ƙasan ledar tsakar ɗakin da duk ta yage anbi da baƙin salateb na zauna. Wash Allah Luba ciki akwai wuya" Ihu Luba ta saka tare da godema Allah. "Hindu cikine dake, abun nema ya samu kenan? Kai na taya ki murna gaskiya na ganki kin yi ƙiba fuskarki ta ciko to ya kika ji laulayin daɗi ko? " Harararta nayi ta miƙo mun hannu muka kashe. "Mafarkina ya tabbata ashe, Allah ne yaso ya nuna mun. Kin ganni nima cikinne dani amman nawa ƙaramine sosai gaskiya, ga makaranta Hindu na koma rayuwar dai sai adda'a abubuwa sun sake damewa baki gani ba." Kin samu komawa makaranta Luba? Na taya ki murna. Ai in sha Allah in kika kammala karatun abubuwan zasu zo muku da sauƙi, da zaran an samu aiki koma wanne irine. Wuyarta a koma makarantar ai. Sunusi fa yayi ƙoƙari ni kin ganni har yanzu dai shiru. Baba Sojanmu ma wallahi cewa yayi bazan koma ba har sai mijinyawa yazo sun zauna akan batun komawata makaranta. Kinga lokaci nata ƙurewa, amman wallahi da abun yake kwana yake tashi Luba, babu halin komawa karatunne a halin yanzu. To kinsan Baba sojanmu shi babu ruwanshi da wannan labarin ma" Luba ta sauke ajjiyar zuchiya tace. "Ni kaina dafa ƙyar ake ta turawa Hindu. Bama lallai inci gaba da karatun ba. Kona abun hawa bana samu fa, to Sunusi bashi dashi, Mamanmu ce ma take yawan taimaka mana. Ɗan abinda ta tattaro saita aiko su Aisha su kawo mana. Ga wanki can na tara kuɗin omonne babu shi yasa suka taru haka. Abincin da zanci babu ko karyawa ban ba Hindu. Sunusin dai yaje ya dawo naji shiru, to fa tunda naji shiru baifa samo bane. Niyata wallahi inna kammala wankin, da aikace_aikacen gida zani. Inna ciyo na rana, na dare zan tawo mana da dafaffe." Luba ga ɗari biyu ki aiki yaro ya siyo mana taliyar murji ki ɓararraka mana muci, wannan ɗari ukun ya siyo mai da magi, ganyen shayi da sikari. Kina da itace ne? " "Ina kuwa naga itace. Ai ko wanka kin ganmu bamu yi ba. Wai kinsan Hindu rabi da kusan kwatan kayan akwatina, da wasu ƴan kayan kicin ɗina duk na siyar da wasu anci abinci da kuɗin kuwa? Hmmm. Sai idanunta yayi ƙwal ƙwal tana shirin yin kuka nera hamsin na saka kuɗin itace. Luba ashe da kanta ta je cefanen. Fitarta ke da wahala sai ga Sunusi. Da ƴar ledarshi baƙa a hannu. "Laa Hindu kece a garin. Yaushe kika shigo? Wallahi nice Sunusi shekaranjiya na shigo. Na same ku lafiya, ya aikin? " "Lafiya lau. Aiki gashinan anata lallaɓawa, yanzu haka ma daga wajen aiki nake nace bari in kawo mata abun kari, yau mun wayi gari sai godiyar Ubangiji. Ina abokina Gawata tare kuka tawo ne?" Aa yana jama'are ba tare muka tawo ba. Zai dai zo sai mu koma tare." Muna ɗan taɓa hira sai muka ji Luba ta watsar da itace sharab a bakin ƙofa, shigowa tayi da cefane a hannunta. "Sunusi ka dawo ashe? Ka ganni cefane naje yowa." Sunusi yace. "Cefane da wanne kuɗin Luba, bashi kika ciyo ne?" Luba tayi dariya tace. "Ko kaɗan Hindu ce ta bada kuɗin. Shiru shiru kai baka dawo ba to" Sai ya ɗan sosa kai ya shiga godiya. Ledar hannunshi ya miƙa mata, ya ce damu. "To ni kam na tafin ku. Hindu zaki kwana a wajen Luba ne, ni aikin kwana yau zanyi mai taimaka mun ɗin baya nan dole kwana zanyi" To babu damuwa sai mu kwanan ai hirarmu dama bata ƙare bace" Ficewa yayi Luba tabi bayanshi. Bata jima ba sai gata ta dawo da nera ɗari biyu. Ledar da Sunusi ya miƙa mata kuma Alala ce guda huɗu na gongoni an zazzage shi a leda an zuba mai da yajin akai, sai kunun gyaɗa shima a ledar. Jujjuyewa tayi ta duremun. "Cinye Hindu bari in hura wuta inzo" Ta miƙe tana murmushi. Illahirin jikina sai naji ya mutu murus _murus wallahi. Har Luba ta hura itace ta ɗaura tukunna tayi jajjage, ta tsayar da sanwa, ta shigo ta zauna kusa dani. Inata faman tubkewa da warwarewa akan wannan lamari "Hindu baki taɓa komai ba to? " Luba ke dai zauna ki karya, ni na karya ai in taliyar ta dahu naci, ki karya ga juna biyu a jikinki kina zama da yinwa" Jan kwanon tayi tace. "Ko ɗayane kici ko zanji daɗi" Hannu nasa na soma ci, kafin ta soma cin nata itama, muna ta zuba hira ba ƙaƙƙautawa nayi rashe_rashe a falo. Bayan mun ci abinci mun yi sallah, saina
Chapter 16 · 0% Book details