← Book details Tsuron Tsirin Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 66 OF 84

Sashe 66

Tsuron Tsirin Part 3 Complete Hausa Novel · about 10 min read

ÆŠaga bel Baba Sojanmu yayi ya sake sakar musu du su biyun. Ita dai dama Hindu ta sandare tamkar itace.
An rasa wanda zai iya matsowa gudun ta ɓare dashi. Sai sake dai taruwa akeyi, abun nema to ya samu.
Qazzafi ne yazo da sauri, yana son zare Asama'u wacce ta shiÉ—e da kuka, ga tsoro.
Aiko ji kake tabbb saukan bel a gadon bayanshi. Baba Soja ya zuba mishi.
A haka ya ɓanɓare Asama'u a hannun Hindu, da ƙyar sabida tayi wani irin sandarewa na ban mamaki.
Ya miƙata ga Luba, Luba ta shige ciki da'ita a guje. Sai hawaye take sharɓewa.
Aka cika maƙil kab matan gidan, sai ƙus_ƙus akeyi.
Su Innah Abidah da Innah Yabine ma suka samu ƙarfin guiwar ba da haƙuri. Sauran kam sai dai kallo kawai. Masu jin daɗi nayi, waɗanda abin bai musu daɗi ba ma, gasunan dai.
Mijinyawa kanshi a ƙasa kawai hawaye na ɗiga yana ƙoƙarin makanta ganinshi.
Ba kukan dukan yake yi ba. Jin zafin fulalar ne ya gigitashi daya tuno cewar irin yadda yake jin raɗaɗi, Hindu dake a matsayin mace zata iya jin fin nashi. Gashi duk yadda Hindu ta kai da son rufin asirinsu. Yau gashi an tozartasu a idanun maƙiyansu, masu burin son ganin faɗuwarsu. Wannan shine manyan dalilan zubar hawayenshi.
Gashi su Baba Nagoɗi basa cikin gidan, balle su kawo ɗauki. Su Qazzafi sun yi kaɗan su yi wani agaji. In ana babbakar giwa ba'a jiyo ƙaurin zomo.
"Ai musu Afuwa wani abunne ya kuma faruwane?
" Heyyyyyyyyy Aje waya"
Ya daka ma Innah Mairamu tsawa, jikinshi fa rawa yake yi. Wata faɗuwa da ƙara Hindu ta kuma yi. Ji kake tum ta faɗi.
Da mijinyawa da Qazzafi har suna gwara kai wajen ceton Hindu.
Zubb Baba Sojanmu ya kuma zuba musu bel É—innan tare. Saida yawu mai yawa ya zubo a bakin Mijinyawa, ya zuba a jikin Hindu bai yi aune ba.
Shigowar Baba NagoÉ—i a guje ne yasa aka daddare.
"Yauwa Alhamdulillahi gara da kuka dawo"
A lokacin wani irin ƙara Hindu take yi, kamar irin na mage haka abun tsoro. Tana wani irin kanannaɗewa.
Amman a hakan Baba Sojanmu ya kuma zuba mata bel ɗinnan, ai sai suka nannaɗeta suka cureta waje ɗaya tamkar babu ƙashi a jikinta. Allah al hakim, babu wanda bai tsorata da yanayin halittar Hindu yadda ta nannaɗe a wannan rana ba. Take ƴan cikin falon suka soma matsawa, harda masu zuba ihu. Iyayene kusan suka cika falon dama.
An cika sosai, harma mahaifiyar Luba tayi ƙarfin halin shigowa. Dake ba yau ake tare ba, kuma ta jima tana shigowa ceton su Qazzafi, da ragowar yaran maƙota.
Baba Nagoɗi ya matso yana ƙoƙarin ƙwace bel ɗinnan amman ya kasa sam, ƙarfin soja da farar hula bazai zama ɗaya ba.
"Ka kyaleni in kashesu in huta NagoÉ—i. Let mi fut him in his fi-les.
Laifinka nake gani akan komai da yake faruwa anan.
Ni yaronnan zai kwaso jiki wai shi loba boi yazo babu tartibiyar magana hi tink am sutufib o wat? Don eba disresfet mi lik dis agen. E militiri haushold is not e filegiraunt. If yu don hab news abaut de sukul, don sho yo fes hiya agen.
Ni zaku nuna ma soyayya. Ni zaka nuna ma kai jarmai ne a soyayya? Je ka tambayi Moda É—inku kai da'ita Hindun, i min yo inlo. Zata baku labarin irin soyayya da muka buga. Da irin yadda jarumtata take.
Soja ba gidan wasa bane. Ashe kazo ka ganta ne kawai ya kawoka. A tunaninka ku saurayi da budurwane oh wat.?"
Ai sai ya ɗaga bel ɗinnan ya nufi Mijinyawa dake ƙoƙarin soma karatun Qur'ani ma Hindu, ya tsorata ganin yadda kanta ya shige tsakiya tamkar macijiya. Gashi an rasa wanda zai ma iya matsowa inda take, daga shi sai Qazzafi kawai.
Ai kuwa sai jin saukar bel yayi, a mazaunanshi kaÉ—ai ta sameshi harshen bel É—inne, Baba nagoÉ—i shi aka zugama jikin bel É—in.
Idanu mijinyawa ya runtse da ƙarfi, tare da girgiza kai irin na wanda zafi ke ratsa ɓargonshi.
Baba NagoÉ—i kuwa ihu yasa.
"Ahhhh wayyo Allah na"
Jirine yake shirin kayar dashi to jikin tsufa. Ya haÉ—u da bel É—in soja.
Baba Dogara da Qazzafi, da Yahuza da suka shigo yanzune suka riƙe Baba Nagoɗi. Aka zaunar dashi a doguwar kujera. Baba Soja na tsaye yana tsuma.
" Qazzafi, Yahuza ku mai yaren sojoji ko zai huce.
Janaral kashemu zaka yi ne. Ku bani ruwa. Kaima Allah ka ƙyale yarannan haka koma me suka yi maka"
Baba Lukumanu ne da yazo, suka ruƙunƙume Baba Sojanmu da shi da Baba Dogara, akasa Qazzafi da Yahuza su karɓe bel ɗin. A lokacin mijinyawa ya soma ma Hindu karatu ga kuka yanayi wiwi yana jin danshin jini a bayanshi.
Baba Sojanmu ya dinga kawo ma su Qazzafi naushi da ƙafa suna kaucewa. Sun kasa ƙwace bel ɗinnan.
Ƴan gidan an nutsu anata naɗe labari. Suna ta kallon Mijinyawa da Hindu, ga kuma kallo a wajen Baba Soja.
Yaya Saratu dai kuka kawai take É—irka. Luba ma kuka take yi mai gunji sosai. Su Salamatu sai murmushi suke sakarma juna ita da Innah Abidah uwarta. Su hakan yayi musu fari sosai. Da abun zaifi haka ma suna maraba dashi.
Hindu da mijinyawa sun matuƙar ba Saratu tausayi wallahi.
"Janaral kaima Allah ka sassautama kanka. Kayi haƙuri wannan yaron sirikinka ne fa. Ka daure. Ya'isa haka wannan ai dole ya koma gida yayi jinyar jikinshi. Ni kaina Yahuza sai kun kaini asibiti, babu yawu sam a bakina. Ga jiri daga zaune ɗibata yake yi. Wajen fa ya ɗaye ko Yahuza? "
Cewar Baba Nagoɗi da yake ta faman haki, Baba sojanmu na kallonshi yana ƙanƙance idanu na masifa.
Baba NagoÉ—i ya kuma cewa.
"Saratu tawo ki taimaka mun in miƙe, dena kukan, ya zamu yi da janaral. Yaranne ma abun a duba. Janaral yau allurarnan tunda ta tashi yau sai Allah kuma. Kuma nima nayi tunanin in yaronnan yace zai zo cikin gidannan ba za'a kwashe lafiya ba."
Saratu tayi sauri ta taimaki Baba nagoɗi ya miƙe tsaye.
"Duk kowa ya watse bana son ganin kowa a falonnan, ko bakin ƙofar falonnan. Hindu ku kinkimeta ku shiga da'ita ciki, wajen gyatumarta. Tananan ma kuwa? "
"Tana ciki Baba"
Cewar Saratu dake riƙe dashi.
"Ruwayya manyan ƙasa, ta janaral ikon Allah.
Kai Magawata kaje kaji. Kayi haƙuri kuma, na roƙeka kayi haƙuri dan girman Allah. Duk da janaral ubane, ko baka auren Hindu zai iya maka hukunci. Kuma ka cika mai biyayya daka nuna shi asalin ubane gareka, kamar yadda Qazzafi da Yahuza basu isa yin tari in yana dukansu ba. Allurarshi ce ta tashi. Kaje in ka shirya batun makarantar, da batun dawowa birnin ka neme ni dani zaka yi magana daga yau"
"Hel no dani zai yi magana ba da kai ba. Bazan kuma yadda ba ehe wallahi bazan yadda ba. Ai duk kai kaja har aka kai wannan shekarun."
"Ai ni na bashi auren É—iyar ba kai ba. In iyakata zaka nuna mun sai in zare hanuna."
"Go ahed an rumub yur han an so wat?"
Kuma harzuƙa ma yayi.
Yayi kica_kica zai ƙwace suka kuma cabkeshi gam.
Mijinyawa, da Qazzafi ne suka kinkimi Hindu a cure suka shiga da'ita ciki. Innarmu tana zaune shayi take sha, ga Azgar a cinyarta Asama'u kuma tayi bacci, sai ajjiyar zuchiya na wahala take yi.
"Ku shinfiÉ—eta a gado Qazzafi".
A gado suka shinfiÉ—eta, mijinyawa yana waige har ya fita, sai ya dawo ya tsaya a gaban Hindu. Hawaye kawai yake zubarwa.
Innah ta miƙe taje ta tsaya kusa dashi.
" Kaje kaji, kayi abinda NagoÉ—i yace maka. Jeka abunka. Ka bari in ka shirya sai ka dawo"
"Innah dan girman Allah kar a rabani da Hindu. Bazan iya É—auka ba. Zan dawo mu sai fom É—in a bani ita, zan je nan da kwana biyu zan dawo"
Fita yayi da saurinshi. Innarmu ta girgiza kanta. Ta dubi Qazzafi dake ma Hindu adda'a ƙur tayi mai da idanunshi. Taga irin ruɗu da ɗimuwar da yake ciki.
Kanta ne ya soma yamutsewa tana ganin jiri jiri. Ga ƙara mai kama dana mage da Hindu take yi, da ƙaran haɗuwar haƙoranta suna sake sosa mata ƙwaƙwalwarta.
"Innarmu lafiya. Naga kina ta kallona. Kinga halinda Hindu take ciki?"
"Babu komai. Bari in yi tofi a ruwa ka shasshafa mata. Zasu tafi. Dama Janaral a kusa yake hmmm, tun jiya yake son dukanta bai samu zarafin bane, sai yanzu"
Zama tayi tana dafe kanta da takeji kamar rabewa yake yi.
Mijinyawa ya fito falon ya samu anci nasara Baba Sojanmu ya miƙa bel ɗin, amman fa jikinshi sai rawa yake yi idanunshi yayi ja sosai.
Sum _sum _sum mijinyawa yazo wucewa Baba Sojanmu ya zabura, kica_kica.
A guje mijinyawa ya fice har yana bigewa.
Yana ratsa gidansu Hindu, ana kallonshi, harda masu dariya da ƙyar ya fita a cikin gidan.
Ji yake yi inama ƙasa ta buɗe ya afka. Har cikin ranshi baya jin zai iya jin zafin abinda Baba Soja yayi mishi. Kamar yadda Nanno ke tozarta. Kuma tayi haƙuri ba tare da ta taɓa yin ƙorafi ba. Shima yayi biyayya. Ko yankashi Baba Soja zai yi, yana tare da Hindu iyakar runtsi.
Shiru yayi tare da kallon saman layin, ya kalli ƙasan layin sai ya lumshe idanunshi.
A hankali yake tafiya tamkar majinuni. Bai san me yake ciki ba, babu tsimi babu dabara. Allah ne yasan karatun kurma.
"Malam rayuwarka eh ta isheka ne eh? In eh ta isheka, ba ga babban hanya ba, ka hau tirelar eh lemo ta take ka mana"
Cewar wani mai acaɓa mashayine mai jan ido.
Ashe mijinyawa hanya ya shiga gadan _gadan bai sani ba, harma Acaɓa ta kusan bigeshi.
"Kayi haƙuri dan Allah"
"Kai kauce eh dallah"
Yai saurin matsawa, tare da É—an seseta kanshi amman dai ina.
Da taimakon Allah ya isa wajen Abokinshi Auwali mai gwanda. Ganinshi kawai Auwali yayi ya zauna a benji yana haki, wani irin tiririn zafin zazzaɓine ke damunshi gaya.
"Ahh wa nake gani kamar Mijinyawa mai Lemo? Ko da yake ganinka babu mamaki cikinshi, tunda dai matarka da kake Aure tananan."
Zama yayi kusa dashi bayan ya sallami wani mai siyan ayaba.
"Ai jiya ma Nawata muna tare dashi anan, Uwar haka.
Harda Shehulle an haɗu anyi zumunci wallahi. Kaima zaka dawone ka kafa teburin lemunka a titi ko yaya? Shi Nawata ya samu aiki a tasha yana gurgurawa, Shehulle ne yai mai hanya. Ai ya kamata kuma ku baro ƙauyannan haka"
Idanu mijinyawa ya lumshe kawai.
Cikin dauriya suka gaisa.
"Baka da lafiyane naga idanunka kamar ma fa kuka kayi. Laa kaga ai jinine a rigarka fa. Kaga zo zo muje"
Auwali ya ja hannunshi zuwa shagon da anan suke kwana. Ga tarin buhunhunan kaya, kaca kaca É—akin dai babu kyan gani.
"Zauna in kawo maka tuwo da magani"
Shi dai baice uffan ba, Auwali na fita ya ɗauki buta ya leƙo ya ɗaura alwala ya koma ciki, tare da tutture kaya. Nan ya shiga sallah inya yi sujada sai yayi kamar bazai ɗago ba. Haka ya dinga yi.
Har isha tayi.
Tuwon Auwali ya tursasa mishi, loma biyar yayi, ya watsa magani bakinshi yabi da ruwan shayi mai madara, da Auwali ya kawo mishi.
Kafin kace me, zazzaɓi ya lulluɓeshi mai zafin gaske jikinshi babu ta inda baya rawa, hawaye sai bin gefen idanshi yake yi yana sauka a fulon tsumman da Auwali yai mishi matashin kai.
"Ko dai inje in kirawo Nawata ne yazo yaga halin da kake ciki ne. Naga kamar hatsari fa kayi ai ya kamata aje asibiti.
Da ƙyar ya tashi zaune yana jin ciwon zanannan yanzune ma yake shigarshi, sabida tsamin da yayi.
" Aa ba sai ka kirashi ba. Gobe da asussuba zan koma garinmu hatsari nayi Auwali. Babu damuwa ba sai naje asibiti ba.
Asibiti basu da maganin da zasu bani. Sannan wannan ya tsaya a tsakaninmu. Kar ka faÉ—ama Shehulle, ko Nawata nazo. Basu san ma nazo ba. Dan Allah abokina.:.
Chapter 66 · 0% Book details