Sashe 31
Tsuron Tsirin Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
In miƙe tsaye mu fita na kasa, tun ina ganinshi bibiyu, uku_uku har na dena ganin hasken duniya baki ɗaya. Irin tashin hankalin da muke ciki yafi gaban misali jama'a. Ni dai buɗar idanuna nayi kawai na ganni a mota, ga Harira ga Mijinyawa, harma da Hajiya Bara. "Alhamdulillahi ta buɗe idon nata. Sannu Hindu Ubangiji Allah ya yaye miki, ya kuma kawo mafitar wancan abun. Mijinyawa ni ko akwai gidan wata mai magani a can wani ƙauye mai nisa a Katsina. Ina ganin in bayan wannan lamarin an gamashi akwai buƙatar ka ɗauki Hindu ka kaita wajen. Ana dacewa sosai, kaga yanzu haihuwa zaku yi ace tana shiga cikin irin wannan halin tana da ƙaramin goyo ɗanye abun fa bazai zama mai kyau ba. Kuma ana dacewa sosai, sai dai da nisa sosai kamar zaku shiga nijar haka wajen yake, inma ta kama ta riƙeku ne zata riƙeku har Allah ya bata lafiya. Har mahaukata matar take karɓa. Ta jibiya akwai hanyar shiga ƙauyen" Cewar Hajiya Bara. "To ai ko Hajiya mun gode sosai. Ai ko cikin nijar ɗinne zamu je, lafiya ai tafi gaban wasa. Kuma anan ɗinma duk wajen da naji magani ina zuwa in karɓo mata, zamu je in sha Allahu. Bari dai mu gama da wannan lamarin tukunna." "Wannan dole sai taga maras lafiya kafin ta ba da magani gaskiya. Amman ana dacewa, ko sulhune sai ayi musu, su shafa mata lafiya, uwa zata zama. Da ba dan na tausaya ba ma, wannan safgar ba zata yiwu da irin mai lalurarta ba. Tarbiyyar yaron abun dubawace sosai da sosai" Ni dai ina jinsu bance komai ba, harshena yayi nauyi ko motsi baya iya yi. Mun sauka a inda mota take saukewa bus sitop kenan. Daga nan muka hau acaɓa har ƙwar gida, inda majalisar matasan unguwar suke zama. Tare dukka muka shiga gidan, da sallama a bakinsu. Nan hankalin kowa ya dawo bisa kanmu suka shiga ware idanu, sabida ganin baƙuwar fuska, dan ko Harira basu sani ba. Muna shiga mijinyawa ya zari kula babba ya fita. Nasan abinci zai siyo musu. Ku shigo Hajiya Bara" Na faɗa a sanyaye jikina babu laka. Shigowa suka yi duk suka zauna. Hajiya Bara sai ƙarema ɗakin kallo take yi. Mijinyawane ya leƙo ya miƙo kularnan shaƙe dam da dambu yaji man shanu da yaji. A gabansu na dire, na ɗebo musu ruwan sanyi. Ga abinci kuci, ni zan yi sallah kafin ku gama. "Sannu Hindu, mungode sosai. Harira zuba mana muci, muma sai muyi sallah kafin mu kama hanya ai, kinga uku saura. Ta dubi agogon dake tsintsiyar hannunta. Alwala na ɗauro na fito na gabatar da sallah, na ɗaga hannu nace. Allah ga kayanka nan, kai kasan yadda zaka yi dashi." Shikenan na sauke hannuna na fito, sai na jiyo maganar su Hajiya Bara a tsakar gida kamar alwala suke yi, inajin motsin ruwa da buta. Da sallama suka shigo. "Wato Hindu ɓarayinki ya ban sha'awa ko'ina a tsabtace, kuma a killace, ɗakinki tamkar a birni, gashi ko ina sai ƙamshin turare, hatta butocinki ƙamshin turaren wuta suke yi, ni har ruwan alwalarma ƙamshi yake mun" ( kina da turaren mrs Bukhari ko kema ƙarnin kifi komai na gidanki yake yi? Ko turaren wuta mai warin sigari kema kike iya siyane Hajiya. Maza ga lambar wayata ki mun magana in baki ingantattun turaruka 08179523215) Murmushin dole nayi. Sallamar Nanno muka jiyo, tare da ɗaga labulen ɗakin, duk muka juyo muka kalleta. "Au baƙi kika yi daga birni ne?" Eh baƙi nayi?" Gaggaisawa suka yi, Nanno sai fara'a take yi. Tayi tunanin daga Kano ne tabbas. Harma data fita ta aiko yara da fura cikin kwanon sha mai murtala. Bayan sun idar da sallah Harira ta miƙomun ƙunshin leda. Na karɓa, ta soma mun bayanin magungunan. "Ganyen nonon kurciyane, ki dinga damawa da nono kina sha harna tsawon sati biyu, ruwan ummanki zai kawo lafiyayye da izinin Allah da zaran yaro ya kama. Nima dashi nayi amfani, sannan ki dinga yawan shan ruwa, ki yawaita tafasa hulba kina shan ruwan da zuma kamar shayi, ummanki zai kawo lafiyayyen madarar da zaki shayar da yaronki ko yarinyarki cikin aminci. Sannan ki dinga matsa kan umman a hankali a hankali ki ɗan dinga mishi tausa. Kuma ko jaririn yazo ko umman bai zo ba, ki dinga bashi zai zo. Wannan kuma na koriyar ledar da ruwan zafi zaki kaɗa, ko ki kaɗa a cikin kunu zazzafa ki sha. Shi wannan jini yake ɓallowa. Amman baya wuce sati biyu zai tsaya, ya danganta. In kuma da kika sha jinin ya ɓalle ya wuce ƙa'ida, sai ki kaɗa manda gatanan a kofi ki shanye ruwan, jinin zai dakata in sha Allah. A wajen wata wanzamiya ƴar na gada, ba haye ba na karɓo miki. Magungunanta suna da kyau. Hajiya mu sha furarnan mu kama hanya kuma" Godiya nayi mata, suka kammala shan furarsu suka fito na rakasu, lokacin ana masallaci an shiga sallar la'asar ne. Dawowar da zanyi Nanno ta tareni. "Su ɗin daga ina suke, ai nayi zaton ƴan uwanki ne daga Kano. Sai gashi sun tafi. Ke ƴannan wai lafiya kuwa, kwanaki can har sau biyu a jere wasu sun shigo gidannan kamar duba gari, harda namiji a ƙofar gida, sau biyu suka zo, kuma uwatale ta tabbatarmun dube dube taga suna ta yi. Yau ga wasu sun zo me kuke ƙullawa? " Babu abinda muke ƙullawa dukkansu abokan aikinane kamar yadda na faɗa miki tun lokacin. Waɗannan ma ɗaya abokiyar aikinace itama malamace, ɗayar kuma ƴar uwartace ni ban ma santa ba. Kuma ai bance miki daga kano suka zo ba ko?" Na gama kaiwa iyakar wuya har tsuma jikina yake yi ina tsaye. Da ba dan addini, da tarbiyya bata ba da damar a raina babba, ko a lailayo ashariya a ƙundumama mutum ba, ko a tsinka mishi mari ba, da Nanno yau taga tsiya. Amman kash, ina da tartibiyar tarbiyya, iyayena sun ɗaurani bisa gwadabe mai tsafta. Itama tana tsaye ƙiƙam tana zazzaremun idanu, a haka Mijinyawa ya shigo ya taddamu, kai tsaye wajenmu ya nufo. "Nanno lafiya meke faruwa? " "Akan baƙin da suka fita yanzu ne. Daga tambayarta su waye, shine fa take zazzagina ita ga sallamammiya" Murmushine ya suɓucemun na takaici da baƙin ciki. Jan sawuna nayi da ƙyar na koma ciki. Kabbarar sallar la'asar na tayar harna idar Mijinyawa bai shigo ba. Kular dambunnan na jawo in duba ko sun rage, dan raina ya biya gaskiya. Aiko baifi rabi suka ci ba, cokali na ɗakko, na dawo na jujjuya dambunnan. Loma ɗaya loma biyu sai ga Mijinyawa ya shigo. Zama yayi a gabana tare da yin tagumi hankalinshi baya jikinshi, gangar jikinne kawai anan. Idanu na ƙura mishi a gaskiya domin Allah Mijinyawa ya rame sosai, yayi duhu kuma. Juyowa yayi muka haɗa idanu. "Akwai abinda kike sone, ko jikinne? " A lokacin raina fansane ga Mijinyawa maganganun bakinshi sun shigeni sosai da sosai. Babu komai, ga dambu kazo mu ci basu ci da yawa ba" Lokali na miƙa mishi, in yayi loma ɗaya sai ya ban loma biyu, yana yi yana bani ruwan rubutu ina sha har muka gama. "To Nanno ta soma tambayata batun haihuwa, tana lissafe wallahi da komai cib da kika sani. To tace za'ayo miki rubutun naƙuda kisha zuwa sati na gaba in baki sauka ba. Ni gobe zamu wuce Bauchi sati ɗaya kacal zanyi, zan biya can wajen Hajiya Bara. Kusanma shine ƙarfin zuwan nawa. Ga damuna tana ta kawo kai, wannan karon zamu dai yi noma na faɗa miki Abdulƙadiri ya yankamun gona ni da Qasimu zamu noma, shi zai yi amfani da gonar Yayansu mai rasuwa. Ki samu a adda'a noma tayi kyau, harma munje jiya mun yi sharar gona lokaci kawai ake jira, gero da gyaɗa zan noma in sha Allah. Qasimu kuma masarar zallah yake tunanin nomawa dai ƙila da wake dai." To Ubangiji Allah ya baku sa'a Allah yasa yabanya tayi kyau. Nima da ace akwai waje ai da nayi nomannan nima. Baraka tace duk shekara ita ke noma musu shinkafar da zasu ci ko?" "Ƙwarai kuwa. Amman ke kam ban isa in barki kiyi noma ba. Ke da a lokacin kina jego ma. Kuma ko babu jego kalarki batai kalar noma ba. In shinkafar kike son in noma sai in noma ai Giwa. Amman ita sai ruwa ya daki ƙasa sosai, sannan ƙasar garinnan bata fiye yin shinkafa me kyau ba." Dariya muka yi baki ɗayanmu. Ai gyaɗarma abune mai kyau sosai, tana da daraja" "Ƙwarai kuwa tana da daraja sosai ma kuwa. Yanzu in Allah ya taimaka sai kiga mun samu gyaɗa fin buhu goma sha biyar fa, gero buhu goma kinga ina lefi zamu shekara ba yinwa" Hayaniyar oyoyo_oyoyoce tasa mukai shiru. Nawatane ya dawo, sai bayan damina kuma, an nome amfanin gona, hatsi ya koma rumbu tukunnah. Gaskiya naga Uwatale ta sha lalle, ga cikinta har yafi nawa girma ta shiga na wata bakwai kenan. Kafin Magriba sai ga tsaraba Uwatale ta leƙo ta miƙo mana a bokiti. Hmmm shinkafa ce mudu guda, sai magi, da bushasshen tattasai da tumaturi bushasshe. Sai mangwaro, uku, lemo uku. Tunda na ajjiye bokitin a cikin ɗakin ajjiye abinci ban sake bi ta kanshi ba. Ina kan sallaya na idar da sallah, ga turaren wuta na tashi a kasko, na ɗanyi wanka nasa riga doguwa zafi akeyi kamar me ruwan sama ya kusan sauka, sai ga Baraka. A tsakar gida ta zauna a tabarma dana shinfiɗa mana. Saina fito na taddata da kular abinci. Yau ke da kanki ina Ya'u da bai kawo ba? " Na faɗa da fara'a ina zama. "Maman biyu kenan. Babu mamaki biyune a cikinnan. Wai nace ashe lokacin haihuwar taki tayi, naji Uwatale sai surutu take a gari. Tana ta roƙon Allah yasa kar ki haifi ƴan biyu sai ta haifa" Bakina na taɓe kawai. Haihuwa kam ko yanzu, ko anjima an shiga watan har ya ɗan gota. Fatan shine mu samu mai albarka da jin ƙai, ba biyu ko uku ba dai." Tana kallon rago dake ta zaƙar harawa ya sake girma, dan gaskiya abinci Mijinyawa yake bashi haiƙan. "Hakane kam. Nima dai nayi mamaki nace in banda uwatale ai ba'a jayayye da ƙudurar Allah