Sashe 42
Tsuron Tsirin Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
SIRRIN GYARAN FATA. HAƊIN SABULUN SALO NA MUSAMMAN DOMIN HASKASUWA DA SULBƊIN JIKIN MAI JEGO. Wannan haɗin sabulun salo na musamman ne ga macen da ke son fatarta ta yi sumul, ta yi sheƙi, kuma ta yi sulɓi ba tare da ta yi bilicin ba. Yana da matukar kyau wurin kwashe tsofaffin ƙofofin fata da dawo da ainihin kyawun kalar chocolate ko wankan tarwada. ( BANDA FARAREN MATA DAN ALLAH) Abubuwan da Za a Buƙata, Sabulun Salo, A daka shi a turmi, a samu zuma mai kyau, Rabin kofi. Don ba da damshi da laushin fata) Manori / Man Kaɗanya (Shea Butter) Cokali 3 na girki (Don maganin bushewar fata da kariya). Man Kwakwa, Cokali 2 (Don ƙarin kumfa da sulɓi) Girislin, na Ruwa: Cokali 2. Kurkum na gari Cokali 1 (Wurin goge tabo da fito da hasken fata). Garin Jan Itace (Camwood/Majigi) cokali 2 Sandalwood.Cokali huɗu (Sirrin sulɓi da sili-sili na jikin mace, da sirrin riƙe ƙamshi). Dilkha haɗaɗɗiya ta mutan kanuri, dunƙule huɗu, ko uku. Domin sake murje fata, da dauwamammen ƙamshi. Sai madarar turare mai daɗin ƙamshi gaya. Matakan Haɗawa Daki-Daki Mataki na Farko, Fasa sabulun salon na Gana kashi-kashi, sannan a zuba shi a cikin babban turmi ko kwanon roba mai faɗi.Mataki na Biyu. A narke Shea Butter da Man Kwakwa a kan wuta mai ɗumi (kar a bar su su ƙone), sannan a juye ruwan man a kan sabulun salon da aka daka. Mataki na Uku. A zuba Zuma da Glycerin a kai. A zuba dilkha. Waɗannan sinadaran su ne za su tabbatar sabulun bai busar da fatar mace ba.Mataki na Faɗu. A zuba garin Kurkum da kuma Camwood (Majigi) da Sandalwood a saman haɗin.Mataki na Biyar, A zuba turaren mai irin ƙamshin da yayi miki, amman ba mai yawa ba, wannan basarakiyar Dilkha itace gamawan da zata riƙe miki ƙamshi a jikinki, sabida anyi mata dukkan haɗin gargajiya ( kizo in baki Basarakiyar Dilkha ɗin mrs Bukhari ta haɗa miki a kan farashi mai rahusa) Mataki na shida A daka su duka a cikin turmi ko a juya su da muciya sosai. A tabbatar komai ya gauraye har sabulun ya zama da laushi sumul (kamar dambu ko ɗanƙo) Mataki na Ƙarshe. A kwashe sabulun a zuba shi a cikin mazubi mai kyau da ke da murfi A bar shi ya zauna na tsawon wata guda, kafin a fara amfani da shi, domin sinadaran su haɗe da kyau. Hanyar Amfani da wannan sabulu. Lokacin wanka, a jika jiki da ruwa, sannan a shafa sabulun ta amfani da soso mai laushi. A goge jiki duka a hankali, musamman wuraren da suka fi fuskantar dukan rana kamar hannaye da ƙafafu. Bayan an gama murzawa, a wanke da ruwa nan da nan (kar a bar shi ya daɗe a jiki). Bayan an fito wanka, a shafa kulaccam mai danƙo bata loshon ba. mai kyau don kiyaye sulɓin fatar Da adana ƙamshi. Matan Kanuri suna yin wannan sirrinne domin goge datti da kanɓori_kamɓorin baƙi da mai ciki take fuskanta a yayin juna biyu, da irin duhun da bayanta da wuyanta yake yi. Kafin ranar suna sai mai jego ta fito tana wani irin haskawa da sheƙi ruwan zafin da Innah ta ajjiyemun ban shiga a haka ba zubar da rabi nayi, na zuba wannan na babban bawo wanda taimun wanka dashi dake ya huce, nayi zamana. Ya ko sha magani, harda itacen dorot a ciki😉 Sai naji daɗin jikina sosai da sosai. Ina fitowa tun kafinma in shiga ɗaki aka ɓalle da ruwan sama, dama garin yayi kamar irin jefin asubannan yayi duhu. Baraka na gaban gaushi tana gashin cibi da cokali, ni dai ji nake tamkar a jikina ake ɗana cokalin, tsigar jikina har tashi take yi. Sababbin kaya na atampa mai kyau ɗinkin zamani na gani akan gado innah ta ajjiyemun. Ina ɗaga rigar na tabbatar ni ta ajjiyema. Ohh gata mai daɗi. Kulaccam mai danƙo ta wajen Mrs Bukhari na mulke jikina dashi. Saka rigar nayi, na ɗaura zanin rigar, na yi ɗaurin ɗankwali, na saka kwalli, da ɗan mai mai gurguwa dana shafa a leɓena Humra na shafa a jikina, da kayana. Saina haye gado. Innah ta shigo da sallama hannunta da kwano, da kofin silba. Ta miƙo mun. Tare da jawo babbar kwalbar turaren gabgab ta zuba a gaushi, take ɗakin ya kaure da ƙamshin al'adarmu. Ta ɗebi gaushi guda ɗaya ɗan ƙarami ta zuba wani haɗin turaren tsugunno mai gyara dausayi ta saka kaskon a ƙasan kujerar da aka fafe samanta. "Zo ki zauna maza akai na minti biyar ma ya isheki. (Kema kina da buƙatar turaren Dausayi Hajiya. Mrs Bukhari tana dashi gangariyan asalin na matan kanurin. Wannan haɗin na kwana bakwai ake buƙatar mai jego, uwargida ta zauna akai. Banda Amare na macen data taɓa haihuwane. Kizo in baki zaki ba da labari). Minti biyar nayi, na sauka na koma gado. Kwanon dai farfesun bushasshen kifine manyan nannaɗe uku, sun kwanta a kwanononnan ga wani ƙamshin kayan ƙamshi, kofin kuma kunun gyerone na marɗon yaji nonon da dama dashi ta tawo. Ina zaune dirshan a kan gado, sai ga sallamar Uwatale a cikin ruwa, gulma na cizonta dole haka ta shigo, ga balangon jiyanan da kaza Innah na juyewa a faranti, zata sake sarrafashi nasu bai yi daɗi ba. Ga farfesu nayi zaman masu jego a tsakiyar gado ina sha. "Uwatale mai jego, ke da jikinki yake ɗanye, ina ke ina fitowa kinji irin ruwan da ake zugawa kuwa? " Cewar Baraka wacce ta gama gashin cibin Azgar tana sauke mai rigarshi. Idanun uwatale akan farfesun dake gabana, ga nama tana gani innah ta juye. "Wallahi nazo ganin baƙon duniyane. Hinduwa ashe kin sauka, ikon Allah ashe asibiti ya kaiki, ga yaronan tittiƙeƙe abunshi, shekarau kenan. Dake ya shekara a ciki yafi na wajena girma sosai." Murmushi kawai nayi mata, uffan bance ba. Tama rasa me zata kalla, gata a uwarɗakina tana ƙarema sababbin kaya kallo, da yadda na canja fasalin zaman komai. Gashi ta ganni da sabuwar atamfa. Abubuwa goma da ashirin. "Ga yaron ki ganshi, ki zauna ga kujera nan" Uwatale bata sanma Baraka nayi ba. Sai da Innah tace. "Dake fa ake magana, ga jaririn ana miƙo miki" Sai tayi firgigit ta amsa, tare da zama a kujera wan sita dake cikin ɗakin. "Innah bamu gaisaba. Kinzo lafiya, ya aka baro birni kuma? " "Lafiya lau, da fatan kema kin sauka lafiya, ance rana ɗaya kuka haihu" Sai tayi dariya. "Wallahi rana ɗaya fa, shikenan suna za'a haɗe duk an huta. Ga yaro tiƙeƙe dashi wallahi" Nan dai tai ta zarar zance, ni tunda na duƙufa cin kifinnan banma bi ta kanta ba. Hindu bari in shiga daga bayan gidanki in wanke wannan kayan jaririn da naki wanda kika cire" Haba Baraka shiga mana. Akwai omo a ciki, sabulunma akwai a banɗakin" "Ahh su Baraka an yi ɗa shekara ta bakwai, ai dole kya yi. Bari in tafi kar Baban masu gida ya nemi umma. Gashi Hindu Allah ya raya mana su baki ɗaya" Hannu nasa na amshi ɗana. Ameen nagode" Ai saita riƙe haɓa. "Na shiga uku ni uwatale, ai ba'a amsawa da ameen haihuwar fari. Shiru akeyi" Wani kallo da nayi mata babu shiri ta fice a ɗakin tana dariya ƙasa _ƙasa ta tantiran munafukai. Ai in kowa baizo ba, dole uwatale saita zo, wai danma haihuwa tayi ƙila dan munafurci da a nan zata tare. Ni dana gama shan farfesunnan da kunun baccina nayi, tunda dai na samu Azgar yana ta baccinshi ya sha gashi. A wannan bacci nawa ashe Innah Yahanasu taje ɓarayin Nanno, jin ba'asi anko yi ɗauki babu daɗi rikici sosai suka gwabza. Ance Nanno sai ɗaki aka shige da'ita tana kuka wiwi akan anzo har fadarta ana ci mata mutumci. Innah dai sai da taima duk matan gidan tatas, ƙofa ƙofa ta dinga zuwa cikin ruwa fa, duk ta sille kowa ta kuma ɗaura da cewa. Bata son ganin ƙafar uban kowa yazo mata da zummar ganin ɗa. Hayaniyar matan maƙota masu shigowa barkane ya tasheni. Nan suka shiga gaisheni da jiki, tare da taya ni barka. A lokacin azahar ta kusan kawowa, amman har lokacin babu a maza, balle a mata na dangin mijinyawa da suka zo barka, harfa da Nanno. Ni bansan anyi wannan gurmin ba lokacin. Yinƙurawa nayi na fito, ruwan zafi nake so zan kama ruwa. "Koma garin da sanyi, me kike so? " Innah ke tambayata, tana bakin magudana tana wanke ƙafar saniya, da jela. wanda mijinyawa ya jido, ga naman ƙaurinan har ya hau kaskon gashima. Shima ƙafar saniyar ta ɗaura wani sai dahuwa yake yi ƙamshi duk ya kaure gidan. Ruwan zafi nake so zan kama ruwa" "Jeki zan kawo miki maza" Farin cikine ya lulluɓeni, nice harda ajjiyar zuchiya da ganin irin bajintar da mijinyawa ya nuna, ya fiddani gagarumin kunya, Allah yaci gaba da rufa mana wannan asirin, har a gama a watse. Ruwan zafi ta bani a butar ƙarfe na shiga na kamo ruwa. Fitowar da zanyi sai naji kamar muryar Innarmu, kamar harda Baba Sojanmu. Kafinma in fita saiga Mijinyawa ya shigo. Ganina yasa yayi turus yana bina da kallo. "Kinyi kyau sosai Tutar so, kin fito a amaryar ƙarni sak. Kizo su Baba Sojanmune suka iso." Azgar ya ɗauka, nabi bayanshi zuwa falo. Su kuma sai lokacin suke shigowa. Baba sojanmu ne, da Yaya Sojanmu, sai Innarmu, da Luba. Baba Sojanmu yana saye da riga da wando na ƙananun kaya, rigar mai dogon hannu mai kwala, sai zanzaro da yayi, harda hular fosinkab a kanshi, da hula da bel duk na sojojine. "Ahhh kawo shi ni zan soma ɗauka, rabu da Ruwayya ta huta" Cewar Baba Sojanmu dake ta murmushi. Gabanshi Mijinyawa ya koma ya miƙa mishi Azgar ya karɓa. Gabansu na koma na zauna sai baki nake washema Innarmu. Itama tana ta murmusawa, harma ta shafi kaina.. "Sannu Hindu, bakya jin ciwon komai ko? " Aa bana ji Innarmu, Yaya Sojanmu barka da zuwa. Baba Sojanmu maraba." Na dubi Luba da ƙaton cikinta nai mata sigina, itama tayi mun. "Hindu, yaronnan kamar fa dani yake kama, baki ga hancinshi dogo kamar nawa ba, kuma kinga yana da haske" Dariya muka yi dukka, tunda cikin sigar zolaya yayi. "Oh