← Book details Tsuron Tsirin Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 84

Sashe 49

Tsuron Tsirin Part 3 Complete Hausa Novel · about 11 min read

Ta ɓangaren Nanno a tsaye take a tsakar ɗakinta ta goya hannayenta a bayanta, tana ji damuwa, baƙin ciki na neman rayuwarta.
"Rago fa mijinyawa ya ba ƴan uwan matarshi suka ƙaro mai, banda wanda ya siyo tiƙeƙe. Ga buhun kayan cefane da suka shigo dashi fa"
Innah Kulu tace.
"Yaya tun jiya ake wucewa da buhunhuna.
Kina gani bus biyu ƴan uwanta suka kwaso suka zo, suna cikin bus ɗinma ruwa ya hanasu fitowa. Yaronnan an gama asurceshi nace ko a ina yake samo kuɗinma oho Yaya. Amman lallai saikin tashi tsaye. Kuma muddin kika bar yarinyarnan ta tafi wankan gida, to fa an dinga tatsarshi kenan. Babu mamaki har gidannan ya siyar ya mallaka mata kuɗi, ga ɗan gwal wanda ba'a taɓa haihuwar irinshi ba an haifo"
Nanno ta juyo a fusace tace.
"Ruwa na tsagaitawa aje a kwaso ragunannan dukka biyu, da cefanen da suka shige dashi a ruwannan É—azu. Ke Zakiya a ruwannan kije ki nemo mun Magawata yazo yanzu yanzunnan. Zan iya mai baki in bai yi wasa ba"

To jama'a da alkhairi.
Sai mun haɗa ranar litinin in muna cikin masu rai da lafiya son so💪🏼💪🏼💪🏼💪🏼💪🏼

Mrs BukhariMRS BUKHARI

.............

*Wai kina da labarin Gidauniya ta mata, farin cikinsu, da walwalarsu, mai suna *MURYAR MATA (FARIN CIKIN AL'UMMA)*🧕🏻👩🏻‍🎓
*Wanda ni Mrs BUKHARI muka yi haÉ—in guiwa wajen buÉ—ewa, tare da sauran shuwagabannin Taskar Badiat Ibrahim?*
*ku matso kusa ki kasance a cikin wannan tafiyar ta Alkhairi, tafiyar da zata gyara rayuwar Aurenki, tafiyar da zata gyara miki tunaninki, tafiyar da mace zata gane ni'imominta, tasan kima da darajar kanta, gidauniyar da zata koya miki sana'ar da zaki dogara da kanki, gidauniyar da zata koya miki tattalin uwar kuɗin kasuwancinki, da yadda zaki tattali ribarki ta yadda zaki ƙarfafa kasuwancinki, sha'awar son komawa makarantar addini, ko na boko kike so? To biyomu muje wannan gidauniyar taku ce mata, gidauniyar ta ƙunshi abubuwan da zatonku ma bai zata ba.*
*Ga lambar wayata ga matan da basa cikin Taskar Badiat group 1 group 2 group 3 sai kui mun magana in sha Allah zaki kasance a cikin wannan tafiyar ta manyan mata*
(08179523215)
*Ƴan taska kuma zaku iya tuntuɓar Admins ɗinmu ta pc domin kuji yadda tsari da dokokin kasancewa memba a cikin wannan shahsrarriyar, garnaƙaƙar gidauniya wacce ta haɗa manyan masana zamantakewar aure, malamai, manazarta, mahukunta, ƴan gwagwarmaya, masana ta ɓangaren gyaran aure, ƙwararrun ƴan kasuwa, da gogaggun ƴan boko, wanda ya haɗa matan arewanmu da kudunma baki ɗaya, zamu kasance a duk faɗin Najeriya da izinin Allah*
*Hindu ma tace mata mu farka, musan menene yake mana ciwo, kuma tana sa ran za'ayi wannan tafiyar tare da'ita*💪🏼💪🏼💪🏼💪🏼💪🏼💪🏼

Zakiya ta miƙe a ruwannan ta tafi kiran Magawata.
Fitarta ke da wuya, ta tarar dangin Hindu sun soma shigewa ciki a guje, ga kaya niƙi_niƙi sunata shiga dashi.
A madadin ta wuce aiken da akayi mata, saita ja tunga har saida taga sun wuce kaf É—insu, ga kayayyaki sosai wanda suka tawo dashi. Gasu da yawa sunfi su ashirin, ko wacce kuma cikin shiga ta kece raini. Sai ta gansu kyawawa dasu tamkar wasu halittune daban.
Tana tafe tana girgiza kai.
A zauren samari na ƙofar gidansu Qasimu Yaya Zakiya ta tsaya. Aiko alai mijinyawa yana ciki, kiranshi tayi suka fito tare jikinshi a mace.
Suna zuwa ƙofar gidansu Innah Abidah tace.
"Yauwa Magawata ga buhunhunan kayan abincinnan shige mana dasu, mai motan sai ya taya ka"
"To Innah. Yaya Zakiya kije ganinan zuwa"
Ya saɓi buhun shinkafa irin mai mudu tamanin ɗinnan yayi ciki, mai mota ya biyoshi da wani irinshi a kafaɗa.
Nan fa kallo ya koma Sama, sai ga Uwatale tsulum_tsulum a cikin ruwa ta fito ganin abinda a rayuwa basu taɓa gani ba. Manja wannan babban galan mai ashirin aka kawo mata, haka ma mangyada, maggi mai tauraro katan guda.
Haka akaita shigewa da kaya, saida aka gama mijinyawa ya shiga ɓarayin Nanno.
"Wallahi Nanno ke kinga kayan garar da suke ta shigewa dashi kuwa? Ahh dole Hindu ta raina mutane ta dinga musu kallon waÉ—anda basu san abinda suke yi ba.
Gaskiya iyayenta haƙiƙa suna da arziki, shi yasa gaskiya girman kanta yayi yawa. Maganar gaskiya Aurennan nasu bama su dace da juna ba sam.
Shima Mijinyawa dole ya liƙe musu suna nuna mai gadara, shi yasa ma ya kuma siyo musu rago sabida ya nuna kalar tashi gwanintar"
Kanshi kawai ya girgiza, Uwatale kenan bata so aso Hindu kona misƙala zarratin, ya rasa a duniya mai Hindu ta tare mata. Kishi take yi da'itane. Ko ko dai a yanzu tana sonshi ne ba Nawata take so ba? Shi ya kasa gane irin wannan bita da ƙullin da Uwatale take ma Aurensu, da irin yadda take yi mai wani kallo in suka haɗu, shine ma yake dakewa in ya ganta, baya sa fuskar wasa sam.
Da sallama ya shiga É—akin Nanno na tsaye ta kasa zama sam.
"Kaje yannzunnan dukka raguna biyunnan ka kawomun su da hannunka. Da cefanen da kaba ma ƴar gwal ɗiyar ƙaruna ƴan uwanta suka je suka yo, sabida ka nuna musu ni bani da darajar da zan hanaka, ko in sakaka.
Yara nawa ta haifa da zaka siyo raguna har biyu gabza_ gabza. Sannan nace maka abincinnan Yayunkane zasu yi dukka dana Uwatale. Yayan naka ma Nawata, kaga nashi cefanen ya dure mun ka gansu nan, tunda shi ai ya auro matar da yafi ƙarfinta ba ita tafi ƙarfinta ba"
Ya juya ya kalli cefanen.
"To ragon da za'a yanka ma gashinan a ɗaure a ƙofata nan ya kawo, ya gwadama a aikace ya fika sanin darajata. Kayan suna da za'a kaima uwatale na ɓangaren miji. Ka gansu a leda ya kawo mana, zamu gagganda da abinda maƙota, da ƴan uwa suka kawo asa a bawo akai, ashiri duka ya rufu.
Amman kai da ka kake komanka tamkar baka da iyaye, wallahi ragunannan dukka biyu sai an kawosu, da duk abinda kasan ka kaima Hindu na suna, kuɗi ko sutura saika karɓosu.
Ai dole kasha wahalar aure, ganin uban Hindu ya tabbatarmun bata fito gidan tarbiyya ba.
Ni dai hana ƙarya lokacin da turawa suke ɗaukar yaranmu su sasu a makaranta, na taɓa ganin turawa da irin hularshi da wannan zanzaron. Ya dattijon mutumci zai sayo ƙananun kaya, da hula irin wannan da zanzoro ya fuskanci surukai.
Banma taɓa ganin uba yazo barkar ɗiyarshi ba, ai ko uwa in ido da kunya bata zuwa, sai dai kishiyoyinta suje.
Sai turanci yake yi shi ga É—an boko ko ince É—an duniya, dan yafi kama da baduniye"
Kallon Nanno kawai yake yi, yana tunanin shi yaushe zai taɓa iya burgeta. Me zai yi ta soshi, menene laifinshi ya roƙa a yafe mishi. Mai Hindu tayi musu, laifinta shine tana sonshi, tana tattalinshi ta yadda ta rayu dashi duk runtsi?
Kawai sai yaji damshi a kumatunshi.
"Kinga wai kuka yake yi. Ai wallahi in kukan jini zaka yi sai an karɓo komai, ni da kaina zan karɓo bama sai yaje ba. Babu mamaki sabida kin sako uban Hindune yake wannan kukan. Tunda kowa tsoronshi yake ji, shima jikinshi ai har rawa yake yi daya ganshi. Kai dai baka san darajarmu ba sam"
Cewar Yaya Jamila fa kenan.
Innah Kulu tace.
"Abi a hankali dai. Kai kaje ka kwaso komai kamar yadda kyatumarka ta faÉ—ama shine kawai"
Kafin yace wani abun sai ga Nawata da nama cikin leda mai zane.
"Ga nama na ƙaro sabida naga dangin matar Magawata yawane dasu kamar tsaki, su kuma ƴan birnine yanzu sai su raina duk abinda za'ayi na ƙoƙari"
Da idanu Mijinyawa yabi abokin tagwaitakar tashi yana mai kallon tsam ko zaiga wani abu daya rabasu domin ya ƙaryata su ƴan biyu ne, ya kuma ƙaryata ɗan ɗakin Nanno ne shi. Sai dai kash basu da wata maraba saita hasken fata shima kaɗanne, sai ƙirji him daya fishi, shima ba haihuwarshi akayi dashi ba, shi ya gadarma kanshi a sakamakon yawan karance_ karance littatafan Hausa, musamman na soyayya.
"Kagani ko, kai kana nan ka siyo nama dan ka rufama ɗan uwanka asiri. Shi kuma rago ya kuma basu kuɗi suka siyo. Dana karɓi cefanen nace ayi girkin tare, sai ya basu suka siyo wani baka ga kaya ba him"
BuÉ—ar bakin Nawata yace.
"Sabida baka da hankali rago fa. Kai wai me Hindu tayi ma ne? "
"Sabida bani da hankalin. Kai wa ya tambayeka mai uwatale tayi ma. Uwatalen da kowa juyawa take yi a cikin gidannan. Take mulkarka, sai Hindu itace karkatacciyar kukarku. Me muka yi muku ne, in bakwa son ganinmu ku bamu dama mu bar muku gidan mu huta ku huta na roƙeku. Tura tana neman ta kaini bango. Nanno ya kamata a dinga tausayamun, kuma a dinga bari anajin ta bakina koma yayane. Wallahi ni yanzune dana shiga naga ragon. Bani na basu kuɗin ba, kuma bani na ba da kuɗin cefane ba, wallahi bani da ko sisi. Ina naga kuɗin wannan hidimar, yaushe na soma fita aikinma da har zan samu kuɗi haka. Ko cefanen da kika karɓa, su Qasimu ne ƙarfin siyayyar"
Uwatale sai baki take buÉ—ewa, itace harda salati da tafa hannaye.
Mari yaji tau a fuskarshi. Yana juyowa yaga jamila ce ta mareshi. Ai sai kawai yasa hannu ya rama. Itama taji tas a kumatunta.
Da mamaki ta dubeshi, Nanno ta fashe da kuka wiwi. Nawata kuma ya rungumeshi da dambe, ya dira a wuyanshi.
Ai kuwa dambe gagarumi ya kaure a tsakaninsu, dake dama ran mijinyawa a tunzure yake, Mijinyawa ya dinga naushin Nawata iyakar ƙarfinshi harda fasa baki.
Ruƙunƙumeshi Nawata yayi ya runtumashi da ƙasa rim, nan suka hau birgima yana koƙarin cirema Mijinyawa kunne. Dan kunnenshi ya riƙe yake fisga.
Yaya Salihu da Qasimu ne suka shigo a guje, Nanno kuwa Zakiya ta riƙeta tana ta kuka harda doka ƙafa kamar yarinya. Innah Kulu sai bari_bari take ma su Magawata., Innah Dubu ba shiri ta saki abunda take yi ta garzayo.
"Haba nagaji ya isheni. Cikinku babu wanda zai iya haƙurin da nayi da irin abubuwan da akemun nifa kullum mai laifine fa"
Marinshi Yaya Salihu yayi. Nanno tace.
"Ka ƙara mishi"
Ya ƙara mishi,
"Ka kuma ƙara mishi nace, dan abu ta kazan...."
Ya ɗaga hannu zai ƙaramai dashi da Qasimu suka riƙe hannun carab. Idanun mijinyawa ya tara jini sakamakon naushin da Nawata yayi mishi a ido, kanshi ma ta gefen wajen ciwo yake yi.
Hannunshi ya zare, ya bar Qasimu riƙe da hannun Yaya Salihu, wanda yayi saurin fincikewa.
"Kai Qasimu fice ka bamu waje, ashe kaima baka da mutumci. In Bala ne zaka riƙe mishi hannu in yana dukanka ne? "
"Aa bazan riƙe mai ba. Sabida bazai mun dukan zalunci irin wannan ba. Magawata wuce muje, ka barsu suje su ɗakko, tunda kai basu yadda da gaskiyarka ba. In sun basu shikenan. In basu basu ba shikenan"
"Amman Qasimu danme za'aje a tsinkata a gaban danginta alhalin bani na siya musu komai ba, wanda na siyo an kwace. An taru fa danginta bus biyu rigimace kawai dai za'a ɓalle ba za'a bar zuchiyata ni ta huta ba"
"Wallahi sai mun karɓo. Kuma sai kayi nadamar wannan marin da kayi mun"
"In baki yafe mishi ba, nima ban yafe mishi ba"
Jin wannan furuci na nanno ya kassara mijinyawa sosai. Babu shiri ya zube a guiwa yana roƙon gafarar Yaya Jamila. Aka kaɗa, aka raya, da ƙyar tace ta yafe mai.
Qasimu da yazo har wuya ya finciki hannunshi suka fice.
Suna fitowa motar ƴan Maiduguri na ƙarasowa suma a cikin wannan ruwan.
"Qasimu yanzu haka zasu je su tsinkamu Hinduna a cikin taron dangi irin wannan. Ya kake tunanin zata ji? "
"Ai bazai kwatantu ba yadda zata ji. Nasan rikici har maƙota tsakaninsu, amman da Innah Yahanasu kaima ka san bama zaka ji muryar Hindu ba, sai dai a assasa mata wani baƙin cikin, da makarai zasu doketa ƙilama ayi sunan bata ma san inda kanta yake ba.
Zan baka shawara duk runtsi muddin Nawata yasa ƙafa ya ɗauki tsinanniyar Uwatalennan suka koma birni, to tabbas kaima ka kama hannun Hindu da ɗanku ku ƙara gaba. In sama da ƙasa zata haɗe. Nasan haka Allah ya halicceka da sanyin hali, rauninka yana da yawa. Da rauninka Nanno take amfani tana sa ƴan uwanka su tozartaka. Kayi haƙuri watarana sai labari. Muje ƙarƙashin bishiyarcan mu jira zuwa da dawowan yau ruwannan a kanmu nasan zai ƙare. Yaƙin duniya dai suke son tayarwa. Ji irin rikicin da akayi akan wankan jariri ma. Wai kasan yadda na tsani Uwatale haka na tsani mutuwata. Ni zarginta nake yi ƙila yanzu tana sonka ne, sakamakon yadda kake kyautatama Hindu, da soyayyarku. Ada tayi tunanin ba lallai ka samu kamarta ba, sai gashi Allah ya musanyama da Hindu mace wayayya, ƴar birni, mai ilimi. Shine cutar hassadarta ta tashi, ta lashi takobi akanku"
Hannunshi ya ja zuwa wannan bishiya, ruwa akeyi a jiƙe suke kashirɓan, yadin jikinsu duk ya maƙalƙale a jikinsu dama ba nauyi ba.
"Wai sun san da sunan da akaima yaro huÉ—uba?"
Qasimu ya tambayeshi.
Yana goge idanunshi wanda ya tara jini dan sai ruwa yake yi yace.
"Ai Nanno ta mance bata tambaya ba. Babu wanda ya tuno. Itama Uwatale bata tuno ba, data tuna musu tunda itace annamimiyar da take son tarwatsamun gidana. Nasan akan sunanma sai Nanno taji dalili. Balle wancan yaso mu sama yaran sunanmu"
"Wanene wancan kuma?
Qasimu ya tambayeshi.
" Wa kuwa In ba Nawata ba"
Dariya Qasimu yasa yace.
"Ja'iri ai ya daku. Gara daka turmusheshi wallahi, ni wallahi naso kaita dukan hancinshi da bakinshi, kai mishi irin jina jinannan"
Dariya suka yi, amman fa zuchiyarsu cike fal da damuwa ainun.
Chapter 49 · 0% Book details