← Book details Tsuron Tsirin Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 76 OF 84

Sashe 76

Tsuron Tsirin Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ina jin sallamarnan, na fito a tsanake daga uwarɗaki babu ko ɗan kwali a kaina, yara na biye dani. Mijinyawa yana tsaye a falo muka fito. Illahirin mamakine ya kamashi, yara suka nufeshi suna kiran Abba Abba. Abba hankalinshi na kaina, tsugunnawa yayi ya ɗauki yaran dukansu, miƙewar da zaiyi ya haɗa dani yai mana riƙon alawar yara. Ajjiyar zuchiya muka sauke, ya shafi ƙananun kitsona, ni dashi muka soma kallon ƙuda, har saida yara suka gaji suka shiga mutsu_mutsu kafin ya dawo hayyacinshi. Duresu yayi yana ta fara'a. "Yaushe kuka dawo, ashe yau zaki dawo? Jina nake yi tamkar maraya, kullum cikin tunaninku nake. Gashi bana so inje gida ya zame mana matsala dukanmu. Alhamdulillahi komai aka sa mai lokaci zai zo Tutar so." Kaji kiran sallah, ka samu kayi alwala ka tafi masallaci, in ka dawo ma zauna. Ai da labari" "Yau kam kwana zamu yi muna hira ai gaskiya." Muna dariya ya fice a ɗakin. Yana fita aka kawo wuta ya haske ko'ina. Ɗakin na kuma kallo, na juya na kalli uwarɗakina. Yanzu shikenan na baro jama'are. Zaman ƙauye ya zama tarihi. Haƙiƙa Allah shine abun godiya, Allah kasa mun dawo a sa'a, ka bamu rufin asirin da zamu fi ƙarfin tozarci. Allah mun faɗi rub da ciki a gaban maƙiyanmu, sunga wallanmu. Ya Allah ka ɗagamu suna gani, mu tsaya da ƙafafunmu irin tsaiwar tsirin tsandauri, ta yadda babu mai iya tugemu. Kai Azgar kuzo muje mu yi alwala ko? " Jaye su nayi muka fito tsakar gidan, ga hasken wuta nan tantar. Alwala. Muka yi ni da yara, a wani waje da tabbas an tanadeshine domin wanke_wanke, wanki, da duk abinda dai ya danganci ruwa. Sallah muka yi, ina ta zaune har nayi isha Mijinyawa bai shigo ba, harma na soma jin yinwa, danma farinciki na ɗauke mun hankali. Sai can ya shigo da ledoji cike _cike fa. Yana direwa ya fito, sai gashi da tire. Kajine biyu manya_manya ya saka a tire. Carab na karɓi ledar a hannunshi na ciro gurasa, harda lemun kwalba guda huɗu. Ɗayar ledar kayan shayine da biredi harda ƙwai. "To wannan daren amarcine zamu maimaita. Inaso wannan daren ya kasance a cikin darare mafiya tarihi a rayuwarmu." Ilai hakane ya tabbata. Wannan daren darene wanda yake tsaye ƙyam a raina, babu daren da zai iya kankare wannan, sai dai wani daren shima ya kafa nashi tarihin. Sai bayan mun nutsa, sai nace dashi. Kayan kicin ɗina ban gansu ba. Naga babu kicin a ciki, hala na tsskar gidane ko?" "Ga kicinnan na buga miki na langa_langa komai yana ciki. Akwai kalanzirma dana siyo yana ciki, ina ɗan tafasa ruwan bunu, da ruwan wanka. Kinga kaya, kinga wajen ko da fatan yayi miki? " Idanuna na kaɗa cikin sigar soyayya. Kuma tabbas saƙo yaje. Nagani, kaya sun yi kyau sosai, banyi zatonsu haka da kyau ba, ai kayane masu kyau. Lallai kayi ƙoƙari sosai. Ɗakunan gasu manya_manya sunyi kyau sosai, nagode, Allah ya saka da alkhairi. Yanzu dai muje ka rakani in kunna risho in ɗaura ruwan wanka." "Naƙi ɗin. Da izinin wa zaki je ɗaura ruwan"? Daga haka shikenan kuma ni Hindu. Washegari sassafe misalin shidan safe, harna dafa ruwan shayi, na soya ƙwai, na ajjiye a teburin tsakiyar falon. Saina koma na gyara Uwarɗakina na share duka ɗakin. Gashi ni bani da gaushi inason turara turaren wuta, dama ina da gawayinne sai in karashi a risho ya ruru. Shida da arba'in Mijinyawa ya shigo. Ganin ko'ina fes_fes, ga yara nayi ma Azgar wanka, Asama'u kam harna shiryata. "Har kin soma aiyukanne Amarya? " Ai dolena zani makaranta ina da lakca tara da rabi, ga yara zan kaisu gidan Yaya Zubaina in ajjiyesu" "Aa yau kam ki barsu, babu inda zanje. Sai jibi in sha Allah zan kafa teburin lemona, na tambaya to shi Alhajin dana tambayeshi bai ce mun komai ba tukunna. Kinga tunda ƙofar gidanshine sai abinda yace. Amman in har zuwa jibi baice mun komai ba, sai in nemi wani abun da zanyi, ko in sake gwada wani wajen" Shiru nayi, can nace. To shikenan Ubangiji Allah yasa a dace. Bari in kammala sai in tafi, dan saina biya ta gidan Yaya na faɗa mata yau bazan kawosu ba." Shiryawa nayi, muka karya gabaki ɗaya, ƙarfe takwas da rabi daidai, harmun ƙarasa titi zan hau abun hawa, sabida da ɗan tafiya daga Kurna zuwa Buk tsohon shashi. Gashi zan tsaya a gidan Yaya Zubaina dake Kabuga. Inda a ƙofar Kabuga motoci suke ajjiyemu, kuma gidanta a kan titi yake sauƙin dana samu kenan. Bani da wata matsala da yara. Ita tana da mai aikinta dake kula mata da yara, ko da batanan. Ƴan gwangwani bus na hau zuwa ƙofar ruwa, wasu a Bata suke tsaiwa. Daga nan ƙofar ruwa kuma, na sake hawa kai tsaye inda zan sauka a Kabuga anan motocin suke tsayawa, wasu suna shiga har cikin buk tsohon shashi, a lokacin babu mota ta kai tsaye daga Kurna zuwa Buk. Ganin tara saura yasa ban tsaya gidan Yaya Zubaina ba. Ina sauka na shiga ɗaga ƙafata kawai. Tara da minti biyar ina cikin aji. Ƙarfe biyu na gama da makaranta. Kai tsaye gidan Yaya Zubaina na nufa, anko ci sa'a ashe bata je wajen aiki ba, kanta na ciwo a kwance a ɗakinta na isketa. "Tun safe nake ta zuba idanu inga kin kawo yara naji shiru. Nayi tunanin ma ko baki shiga makaranta ba" Ai ko dai na shiga, dake Mijinyawa bai fita aikin ba, yace sai jibi shine na barsu tare a gida. Baki je aikin ba yau?" Na tambaya ina miƙewa, yinwa nake ji sosai tunda nayi sallah a makaranta ai gara inci abinci kafin in tafi. "Ciwon kannan ne dai ya uzzuramun, tun safe ni ko falo ban fita ba. Bansan ma wainar da ake toyawa ba. Ni dai naji ɗuriyar yara sun dawo boko, sunci abinci Islamiyya tayi kira" Ladi na kira ta zubo mun abinci, shinkafa ce ds miya da kifi, inaci muna hira. Biyu da arba'in nai mata sallama na fita. Bani na shiga gida ba sai la'asar. Na shiga gidan na tadda anata shigowa da kayan ɗaki, da dukkan alamu dawowa akayi ɗaya daga cikin ɗakunan. Ga mata a tsakar gidan anata aiki. Sallama nayi, muka gaggaisa da matan da na gani a tsakar gidan. A kicin naji ɓuruntun mijinyawa, Asama'u na zaune a dokin ƙofata, Azgar na tsaye a bakin kicin. Gyaran kicin ɗin kake ta yi ne, me yasa baka jira na dawo nayi ba?" Murmushi kawai yayi mun. Asama'u data matso na ɗauketa, Azgar kuma inata shafa kanshi. Ka shiga ciki, kaga gidan cike da mata k0? " "To gimbiya sarautar mata. Ku shiga da yaran ganinan zuwa" Hannun Azgar na ja muka shiga, na gaji sosai kuwa. Amman hakan na tashi na fita na ɗauro alwala, mijinyawa kuma ya tafi masallaci. Ina zaune ina ɗan nazarin karatunmu na yau, mijinyawa ya shigo da sallamarshi, ga cefanen kayan miya a hannunshi. Kayan miyan na karɓa muka gaisa. Nan muka shiga hirar makaranta, da bayan rabuwa halin da kowannenmu ya tsinci kanshi a ciki. Na tambayeshi mai suka ci da rana, yace dani ragowar kazar jiya da daddare suka ci da biredi. Hirar dai taƙi ƙarewa muka koma kicin, shi yana zaune a kujera daga waje. Ni ina daga cikin kicin ɗin, na kunna risho. Ya gyara kicin ɗin fes, ya jera komai, a kantocin sama da aka kewaye kicin ɗin dashi, ƙasa kuma kayan abincine, da risho, sai kwandon kwanuka. Shinkafa na dafa mana fara, na juye miyar dana tawo dashi a tukunya na ɗumama. Sai na tafasa ruwan zafi na cika filas. Dake zafi akeyi da ruwan sanyi, da magriba nayi wankana a bayangida, ina fitowa na ɗaura alwala saina shige. Mijinyawa na ƙoƙarin fita na shigo. Inason gawayi zan samu nan kusa, inason in turara ɗakinne ya ɗauki ƙamshi" "To in zan shigo daga masallaci sai in tawo miki dashi." To shikenan adawo lafiya, Allah ya tsare" Da "ameen" Ya amsa tare da ficewa. Saida nayi kwalliya na kintsa. Wani yadi nasa mai taushi ɗinkin riga da zani, rigar iyakar guiwa, na karya ɗankwali, nabi jikina da humrori kafin na ta da kabbatar sallah a uwarɗaki. Ina kan sallah na dinga jiyo sallama, can kuma sai naji shiru. Bayan na idarma saida na kuma gyara tsaiwar ɗankwalina. Hmm ina fita mutuniyarku tana zaune dafa'an a kujera ta yi tagumi wallahi kunji na rantse. Ta yi mugu_mugun zurfi a tunani. Ni ko raina fa yayi maƙurar ɓaci. Zama nayi a kujerar dake fuskantarta, bata ma san na fito ba, bance mata uffan ba. Fitowar yara da gudune ya dawo da'ita hayyacinta. Tana ganina kuma sai ta shiga washe baki tana wayancewa. "Ashe kin fito ban sani ba. Ikon Allah wannan sababbin kaya haka Hindu? Gaskiya waje yayi kyau. Iyayenki suna da kuɗi gaskiya. Wai nace Hindu ni kam inaso in zaki gidanku in biki aje a gaggaisa" Ni dariya ma ta bani da ƙyar na dake. Abinda zan soma miki dashi shine. Ba'a shigowa ɗakin mutum a zauna ba izininshi, kinyi sallama ba'a amsa ba sai ki haƙura. Amman kin shigo kin yi zamanki, kuma kika yi shiru? Bari kiji kada ki sake" Sai tayi dariya. "Laa to shikenan dama tunanina ko kina sallah ne. Kin dawo lafiya. Ohhh Asama'u yarinyar Hindu. Kin samu yarinya a ɓagas wallahi. Yanzu shikenan an rabata da gyatumarta ana haka in ba mutuwa ba kuwa" Sai kuma ta ɗan yi dariya kamar taɓaɓɓa. "Ammi abinci zanci" Azgar ya katseta. "Kinji yaronnan baki raɗau, ko da yake Ɗan safiyo ma abokin tagwaitakarshi yaro baki ji surutu ba. Ni banma taɓa jin muryar yaronnan ba, dake baya fitowa tsakar gida." Ta ƙarashe da dariya. Miƙewa nayi, na nufi kicin Uwatale ta biyoni fa "Ay wannan madafine ashe. Kai amman yayi kyau ga kayan alatu rigis" Tana yi tana kallon miyata mai cike da zuƙu_ zuƙun nama. Azgar na zuba ma abincin na bashi, Asama'u ma na zuba mata nata na bata. Sai na zuba ma Uwatale data bisu suka shiga ciki. Ga abinci fa" "Laaa sai dai in tafi dashi na ƙoshi, na ci tuwo kamar cikina zai fashe. Gashi miyar jawur da'ita ta bani sha'awa, ji
Chapter 76 · 0% Book details