Sashe 11
Tsuron Tsirin Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ni dai da shigarmu akace nawa sakamakon tukunna, suna buƙatar mataki na gaba wato gwaje_gwajen jini kuma. Da zaran na soma al'ada a kwanaki biyu zuwa uku na al'ada akwai gwaji. Za'a sake neman wani jinin na sinadarin Progesterone a kwana na 21 na al'ada (don gani ko ƙwai ya fita) A baya can duk an yi mun wannan gwaje_gwajen, dasu hoton mahaifa, dana toshewar bakin mahaifa, duk nayi su. Nayi tunanin tunda zuwa na biyune ba sai anyi duk wannan ba, tunda yana rubuce. Amman likitana tace dole akwai buƙatar sake sabon gwaje_gwajen. Sunturin asibiti ya ganmu. Shima Mijinyawa wai za'ayi mishi gwajin jini tukunna, kafin muji sakamakon, amman dai yace tabbas yasan da matsala kawai dai likitan yace babu komai ne, amman jikinshi yana bashi tabbas akwai matsala babba. Muna barin asibiti muka shiga bin diddigin hanyoyin daya dace abi dangane da neman yaro. Gaga_gaga haka abubuwan sukaita tafiya, sunturi kam mun shashi, na asibiti da ƙa'idojin ɗaukar yaro. Kusan tare aka gama da batun asibiti, shi wancan na neman yaro mun gama na ɓangarenmu, muna dai jiran sakamakon daya kamata, kafin umarnin zuwa gidan marayu, duk da mu jariri zamu ɗauka. A ranar sakamakon duk gwaje_gwajenmu ya kammala. Kamar na baya, ni bani da matsalar komai. Muna murna muka nufi likitan mijinyawa bayan bin layi muka samu shiga, yana zaune, muma munyi shiru sakamakon muke son a bamu muji. "Magawata sakamakon gwaje_gwajen da duk muka yi maka sun fito. Nace ko madam zata iya jiranmu a waje in da hali?" Ai sai nayi saurin riƙe ma Mijinyawa hannu, shikenan nasan ma matsala zai faɗa. Murmushi yayi yace. "Aa madam ba zata yadda ba, kaga yadda ta riƙeni ai. Dakta ai babu komai matatace, zaka iya faɗan komai" Kuma mu musulmaine, mun yadda da Allah, mun yarda da ranar sakamako. Dukkan abinda Allah ya nufa shike wanzuwa, shike da tasarrafi da isa, da buwaya." "To shikenan, a sakamakon gwaji na farko ya nuna mana Magawata bashi da kwayoyin Halitta. A gwaji na biyu ya sake tabbatar mana da bashi dasu, ba'a halicceshi dasu ba. Amman nace a sunanka naga kamar ku ƴan biyu ne ko? " Jiki a saɓule mijinyawa yace. "Tabbas mu ƴan biyu ne dakta" Shiru likitan yayi can sai yace. "Kunyi kama matsananciya, ko irin ƴan biyunnanne da basu da kama? " "Munyi kama sosai, komai namu iri ɗayane, girma kawai nafi ɗan uwane, shine kaɗai bambancinmu" "To shi yayi Aure ya haihu kuma?" Saida mijinyawa ya lunshe idanu kana yace. "Tabbas yana haihuwa, yanzu haka matarshi juna gareta." Ajjiyar zuchiya wannan dakta yayi, sai yayi rubutu yayi rubutu kafin yace. "Ba'a fiye samun haka ga ƴan biyun da suka yi kama ba sam. Anfi samu ga tagwayen da basu da kama. A yawan lokuta, matsalar tana faruwa ne saboda lalura bayan an haife ƴan biyu, ana iya haifar ƴan biyu ɗaya kwata-kwata ba shi da kwayoyin halittar haihuwa tun daga ranar haihuwarsa, yayin da ɗan uwansa kuma aka haife shi lafiya lau. A fannin kimiyya da likitanci, akwai dalilai guda biyu na musamman da ke sa ɗaya ya zo duniya ba shi da kwayoyin haihuwa, ko masana'antar kera su, ko da sun yi kamanni da juna su ƴan biyun 1. Rashin Sauko da Maraina Tun a Ciki (Cryptorchidism/Anorchia) Yayin da jariri namiji yake girma a cikin cikin mahaifiyarsa, marainansa suna samuwa ne a cikin cikinsa daf da koda, sannan kafin a haife shi su sauko su daidaita (scrotum). 2. Me ke faruwa da ƴan biyu ɗayan? Ana samun yanayin da jinin da ke kai wa marainan ɗaya daga cikin tagwayen abinci ya toshe, ko ya murɗe tun suna cikin ciki (Testicular Regression Syndrome). 3. Wannan matsalar tana sa marainan yaron ta narke ta ɓace gaba ɗaya, kafin a haife shi (wato an haife shi kwata-kwata ba shi da maraina, ko kuma an haifeshi kwata kwata bashi da kwayoyin halittar haihuwa). 4. ɗan uwansa kuma yana saukowa lafiya lau. Canjin Kwayoyin Halitta na Mosaicism,Wannan yana faruwa ne da zaran ƙwan da ya rabe ya zama tagwaye masu kama ya fara rarrabuwa a farkon ciki. Yayin rarrabuwar kwayoyin halitta, ɗaya daga cikin tagwayen yana iya samun matsala inda kwayoyin halittarsa na maza (XY chromosomes) suke canzawa, ko kuma kwayar halittar 'Y' ɗin ta ɓace a sassan da ke kera maraina. Wannan yaron za a haife shi da matsalar Gonadal Dysgenesis, wato an haife shi da masana'antar haihuwa da ba ta nuna ba, kuma ba ta da kwayoyin kera maniyyi ko guda ɗaya tun asali. Ɗan uwansa kuma kwayoyinsa suna tafiya daidai. Tabbas bincike ya tabbatar ana samu. Sannan akwai lalurori da ake samu a yayin girma zuwa balagar yara, nan ma ɗaya zai iya samun matsala a marainanshi wanda ka iya kashe ƙwayoyin halittar. Shin kayi irin wasan rafinnan lokacin da kake tasawa?" Jikin mijinyawa yana rawa yace. "Nayi wankan rafi sosai. A cikin abokaina nafi kowa ƙwarewa" "To kaga shima yana haifar da cutar tsargiya, a sakamakon wasu ƙananun halittun ruwa dake samun damar shigewa jikin yara. Su shiga su zuba ƙwayayensu a jikin mutum, sai kaga yana haifar da zafin fitsari, ko in an gama fitsarin kaga ɗan jinin da baifi ɗigo ba. Tabbas shima wannan yana haifar da matsalar rashin haihuwa, koma ya raunata al'aurar baki ɗaya. Cikin wannan misalan ka taɓa fuskantar ɗaya a ciki?" "Likita na fuskanci duka, musamman na jini a ƙarshen fitsarin. Nayi hira da abokina Qasimu sai yace mun wai na balaga ne shi yasa" Likita yayi rubutu, yayi rubutu kafin ya ɗago ya zuba mana idanu. Can sai yace. "Babu damuwa in sha Allah. Sai dai akwai maganguna da allurai da zan ɗaurashi akai, na tsawon watanni shida, zuwa shekara guda. Ina mai tabbatar muku in sha Allah zasu farfaɗo da waɗannan sunadaran. Wannan ba matsala bace kuma ba wani abun bane. Baya ga haka kana da cikakkiyar lafiyarka ta jiki, data al'aura. Sannan kar ka ɗauki damuwa ka saka ma kanka, babu komai in dai kabi abinda zan ɗauraka akai za'a dace, harma ya zama tarihi." Allah mun gode maka, Allah mun karɓa, Allah ka fimu sanin dalili. In haihuwa alkhairice a garemu, Allah ka bamu ƴaƴan da duniya zata yi alfahari dasu, in babu alkhairi Allah mun karɓa a haka, ka fimu son kanmu, kai kake tsara komai, kuma komai yana da dalilinshi" Wannan maganganu nawa, su suka ƙwarara mijinyawa daya karaya har jikinshi na rawa inaji, hannayenshi dake cikin nawa tuni suka jiƙe. "Madam madallah dake. Irinku akeso masu bama mazajensu nutsuwa akan duk abinda zai firgitar dasu. Ku daure abi hanyar shan maganin da alluran za'a dace. Duk mako sau biyu za'ayi mishi a ƙalla. Wanda a wata za'ayi mai allura takwas. Ko wacce allura ɗaya kuɗinta zai kai dubu biyu da ɗari biyar. Zamu yi na wata uku, zuwa shida, sannan akwai magunguna da zai dinga sha. Su kuma bana tunanin zasu wuce dubu bakwai zuwa takwas dai. ( a lokacin kuɗine masu yawa gaskiya tunda a yanzu wannan zamanin allurar ko wanne ɗaya tana kaiwa dubu ashirin da biyar a wata guda kuma kuɗin kusan dubu ɗari da sittin zuwa dubu ɗari biyune) Kainane naji ya sara, kuɗaɗe ake buƙata mazajen kuɗi ba matan kuɗi ba. Mijinyawa yace. "Mungode dakta. Hindu tashi mu tafi kinji?" Ajjiyar zuchiya na sauke, jikina a mace na miƙe. Dakta zamu dawo in kuɗaɗen sun kammala in sha Allah" Tunda muka shiga mota, ni dashi babu wanda ya tanka har muka isa tasha inda zamu sauka. Shi ya biya kuɗin, ya riƙo hannuna munata tafiya, bamu hau abun hawa ba. Sai adda'a da ambaton Allah nake yi. Munyi tafiya mai nisa kafin na dawo hayyacina, harma na taran mana acaɓa muka hau. Mijinyawa baya cewa komai, sukuku ya shiga gida, wannan ganin da Uwatale tayi mishi ai saita garzaya ta je ta kirawo nanno. Ina can gaban sib ina ɓoye takaddun asibitinnan, na jiyo Nanno tana tambayarshi ko lafiya? Sannan ance kwanana nawa bana zuwa makaranta, to ina nake zuwa. Ƙin fitowa nayi, na nemi gado na kwanta shiru kawai, zuchiyata da ƙwaƙwalwata aiki kawai take yi. Kaina ya kulle, zuchiyata nauyi tayi mun sosai. Nanno ce ta kwaɗo mun kira, na amsa a hankali tare da fitowa. Mijinyawa yana kwance a doguwar kujera da gani zazzaɓine ya rufan mishi sosai. "Meke damunshi ya shigo a cikin wannan yanayin. Gashi jikinshi fa da zafi sosai, nace ko wani abunne ya samu yaron cikin naki ne? " Aa zazzaɓine kawai yake damunshi, zai sha magani yansu" "To naji zurga_zurgar duk da kuke yi, ina kuke zuwa? Ance kin kwana biyu bakya zuwa makaranta, to ina kuke zuwa tabbas wancan satin an tabbatar mun Bauchi kuka je. Me akeyi a Bauchin har haka" Uwatale na kalla, idanunta a kaina. Na juyo da dubana wajen mijinyawa wanda ya miƙe zaune. "Nine bani da lafiya asibiti muke zuwa, wannan satin kuma itace bata ji daɗi ba shine na kaita." "Amman baka da lafiya baka iya faɗama kowa ba, sai matarka ko? Ga jikinka da zafi, da sanarmun kayi nasa aka dafa maka saƙesaƙi ka sha da tuni ka warke. Me akeyi da ƙwayar bature da har zaka je asibiti. Ke ba'a zuwa asibiti a cikin gidannan kiji da kyau. Duk abinda kuma yake damunshi a tabbatar an sanar mun. Ke dai ƙoƙarin ki na raba kan dangine kawai. In ba haka ba ya yaro ba lafiya ba zaki sanar mun ba" Hmm kunji wai yaro. Mijinyawa fa take nufi, ba yaro mai shan nono ba. Na kasa buɗe baki ma ince uffan, firejar dake kaina a lokacin ta wuce gaban misali. Shima da yaso sake wata maganar hanashi tayi kawai. Ba'afi minti talatin da fitar ta ba, sai ga Shafa an aiko da magani cikin ƙaramin bokitin fenti ta dure mana. Abu kamar wasa kafin dare Mijinyawa baya gani, sai sunana kawai yake ambato. Ni dai inata tofa mishi adda'a, ban sanar da kowa halin da ake ciki ba sam. Ga jikin ina ganin yayi tsanani, har sau biyu ya suma, ina yayyafa mishi ruwa. Ruwa na ɗebo nayi mishi tofi, na bashi yasha, ragowar na shafe mishi jikinshi dashi. Naita jiƙa tsumma ina goge mishi jiki da ruwan sanyi. Sai ajjiyar zuchiya yake saukewa. Can sai bacci mai nauyi