← Book details Tsuron Tsirin Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 84

Sashe 17

Tsuron Tsirin Part 3 Complete Hausa Novel · about 4 min read

taya ta muka game wankin da sai da muka kai kusan magriba kafin muka gama. Wanke tsakar gidan tayi da ruwan wankin tas, muka ɗaura alwala muka shiga ciki. Shinkafa da wake da manja da yaji na wuta ta kusan nuna, daf la'asar Sunusi ya leƙo ya kawo mata. Ina sallah yaro ya shigo wai Hindu ta fito inji Qazzafi su tafi. Luba ce ta fita, ina sallamewa Qazzafi da Luba suna shigowa. "Qazzafi yau gashi naci albarkacin Hindu kazo gidana. Ina wuni ya gidan ya iyalin? " "Luba kenan iyayen baki ai kin dace da aikin jaridan da kuke da buri sosai. Ke kuma taso mu tafi sauri nake yi" Anan zan kwana Qazzafi, Sunusi bayanan gobe in Allah ya kaimu zamu tawo gida da Luban. In kaje ka faɗama Innarmu" Qazzafi bai bar gidan luba ba saida yaci abinci, gashi babu abincin da yawa shinkafa ce gongoni uku wake gongoni ɗaya rak. Sai dai da zai tafi sai ya ajjiye ma Luba dubu uku. Ya turo yaro da biredi, da kayan shayi harda tsire cikin takadda. Muka baje tsiren a saman shinkafa da wakennan muna ci muna tattaunawa dangane da batun masu zuwa jama'are in haihuwar tazo. A wannan rana mun tattauna abubuwa da yawa da Luba. Washegari bayan mun karya kuma muka nufi gida nanma wunin ne cur. Sai kuma aka shiga hidimar biki, dangi duk sun hallara, ƴan Kwantagora ma duk gasunan. Akayi biki lafiya, aka gama lafiya, sai ɗan rikicin daya kusan ɓallewa tsakanin Zubaina da Matar Yahuza, da Yaya Saratu da Salamatu. Amman Iyaye maza saida suka shiga, sabida rikicin ya yi ƙarfi sosai. Ni wallahi saida ƙurar ta lafa kana naji, ashe wai a kainane Yaya Saratu suka yi da Salamatu. Bayan kwana biyu na soma zagayen gidajen ƴan uwa, inanan Khadijan su Qazzafi ta haihu. Ranar suna sai gani ga matar Qazzafi sai wani fiskewa take yi, tana wani turanci da su Lamin su Qazzafi. Ni ko banza na ba ajjiyarta gaisuwa wannan bata shiga tsakaninmu ba. Hirarmu kawai muke yi dasu Luba da ƴan lungun Baba Alƙali. Sai dab magriba muka kama hanyar gida. Ni dai haka na share wata guda a gida, danma na nemi Inda Shehulle yake lodi na bashi wasiƙa ya kaima mijinyawa. Gashi asirina yana shirin tonuwa, yau da gobe ina mance ya kamata in ɗan dinga son jiki, da ɗan kwaɗayi haka, sannan sai inga Innarmu nata kallona haka dai. To ranar litinin muna dawowa daga kasuwa da yamma da Luba. Mun je wata ƙawarta ta fasa dilar kayan jira jirai muka je muka tsinto masu yawa gaskiya, dan tayi mana sauƙi ni kuma a lokacin da ɗan kuɗaɗe a hannuna da Akarami ya bani, Yaya Soja ma da yazo ya bani, Qazzafi ma haka. Kuma dama mun shiga kasuwa mun siyo safuna, da huluna, da wandunan jarirai abun gwanin sha'awa, har labule irin gumamannan na siya, masu kyau baku gansu ba. Inama ace da gaske haihuwar zanyi da ba haka ba. Sai dai kash. Muna shigowa na tadda mijinyawa a falo a zaune yana jiran Baba Sojanmu. Innarmu ta ajjiye mishi abinci da ruwa, da filas ɗin shayinmu na Kanurai. Idanu muka haɗa na sakar mishi murmushi, shima murmushin nayi kewarki yayi mun. Gyaran muryar Baba Sojanmu ne yasa na dawo hayyacina. Innah Abidah sai ƙarema ledojin hannayenmu ni da Luba da suke gaisawa da mijinyawa kallo take yi. "Hindu siyayyar haihuwar kike yi a nan kafin ki wuce ko? Ai yafi miki ki sai duk abinda ya dace. Wallahi kinsan fa ƙauye ba lallai ki samu irin kayan daya dace ba" Kallonta kawai nayi, bance uffan ba naja hannun Luba muka shige. Meya faru me ya faru kawai muka soma jiyo turanci na tashi a falo, Baba Sojanmu naji yana bazan koma ba, nazo kenan, sai dai shi ya koma shi kaɗai. Duk fa da turanci. Ni dai ina zaune jigum nasan dama za'a rina. Innarmu ce ta leƙo. "Ke Hindu kizo inji Baba Sojanku maza" Miƙewa nayi nabi bayanta zuwa falon. Innah Abida sai zurga_zurga take yi. Tana ganin na fito ta nemi waje ta zauna, sabida jin ƙwaƙwaf. Mijinyawa kanshi a sauke baya ko iya ɗagowa. Ga Baba Nagoɗi, ga Baba Alƙali duk Baba Soja ya kirawosu su zame mishi shaidar gani da idanu. Ga takaddar yarjejeniya a hannun Baba Sojanmu harda biro. Yaufa ake yinta. Me za'ayi da biro ni Hindu? Mrs Bukhari Sai mun haɗu zuwa gobe in Ubangiji ya amince. 💪🏼MRS BUKHARI
Chapter 17 · 0% Book details