← Book details Tsuron Tsirin Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 84

Sashe 44

Tsuron Tsirin Part 3 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Sha Da Nono/Madara. Zuba cokali 2 na gumban nan a cikin madara mai kyau ko nono, ki juya sosai ki sha. Ana iya mulmulata a dinga taunawa kamar alewa lokaci zuwa lokaci hmmm. A riƙa sha da safe kafin karyawa da kuma da daddare kafin barci. Yana da kyau sosai wajen sa damshin dausayi da dawo da martabar mace. "Wannan tsumine na ƴar gata. Shima da madara kar ki yi wasa da komai anan Hindu, Yaha ke kinsan komai." Ga haɗin tsuminnan. TSUMIN MAI JEGO MAI KAURI DA INGANCI (Gyaran dausayi mai ingamci) Wannan tsumi ne na musamman wanda ke ƙara wa mace kyan dausayi, yana kwashe sanyin dausayi, kuma yana sa mace ta dawo fafur kamar ba ta taɓa haihuwa ba. Abubuwan da Zaki Buƙata. Ganyen Magarya da Ganyen Sidir – Shi ne asalin ginin tsumin (ganyen magarya cokali 3 na garinsa, ko ɗanyen busasshe cokali 3). Kanunfari, da Citta Suna sa kauri da daɗi kuma suna dumama mahaifa.Habatussauda, Cokali 2 (yana warkar da duk wata cuta da sanyi). Namijin Goro – Guda 3 (a daka shi, yana da kyau sosai wajen matse dausayi da dawo da ƙarfin dausayi). Dabino, da Ɓaure, Shi dabinon (kofi 1) shi ke kawo kaurin tsumi, ɓaure kuma yana matsin dausayi, Garin Jirjir, ko Bagaruwa cokali 1, tana busar da jiƙan dausayi. Zuma ko Mazarkwaila Shi ne sirrin kaurin! Zaki buƙaci zuma mai kyau cokali 5 ko mazarkwaila guda 2. Yadda Ake Haɗawa yayi kauri. Wanke ganyen magarya, dabino (wanda aka cire ƙwallo), namijin goro, kanunfari, citta, da ɓaure. Zuba su a tukunya. Zuba ruwa dai-dai gwargwado (kamar kofuna 3 zuwa 4). Bar shi ya tafasa sosai a wuta marar ƙarfi, na tsayin minti 20 zuwa 30 har sai dabinon ya farfashe a cikin ruwan. Ruwan kuma ya ragu ya yi duhu sosai. Tace ruwan da kyau ta amfani da rariya mai laushi ko tsumman tata, duka raguwar kayan su fita. Zuma/Mazarkwaila Mayar da ruwan tsumin da kika tace a kan wuta, sannan ki zuba zuma mai yawa ko mazarkwaila da kika daka. Dahuwar Ƙarshe. Bar shi a kan wuta yana dahuwa a hankali Zakii ga ruwan yana ƙara yin kauri sosai yana kumfa kamar zum. Da zaran ya yi kauri yadda kike so, ki sauke ki bar shi ya huce. Juye shi a jarka mai kyau. Yadda Ake Sha. Ana shan cokali 2 zuwa 3 na wannan tsumi a cikin babban kofi na shayi ko madara mai zafi. Safe da daddare kafin barci. Yana sa jikin mace ya haɗe, dausayi ya matse, tana jin dumi kuma yana wanke dattin mara duka. Sai turaren tsugunno na musamman, ingsntacce, mai gyara dausayi, ya dawo da martabarshi. (Wannan ki cire nerarki dubu goma in baki Hajiya, harda kyautar kwalbar farin miski ɗan asali ƙarami yake zuwa) Zaro wata robar tayi basarakiyar daka ne a ciki shi kuma, sha da nono, ko madara. Cikui ne da dabino, sai geron mata, da garin idanun zakara. Dakesu zaki yi su zama gari, a dinga damawa da madara, ko nono, wannan dakan gamawane kat. (Mata na baku wannan sirrine domin gyaran gidajen Aure. A yanzu siyen maganin mata barkate ba naki bane. Mu kula da lafiyarmu, da abinda zamu dinga ɗibgama kanmu in di nam ob maganin mata😆. Lafiyarmu abar kiyayewace. Wannan haɗin in kika daure kika haɗa abunki, bakya buƙatar ko wanne irin maganin mata na siyarwa. Da wanda zan kakkawo muku a gaba in sha Allah. Saura kuma kuce yau na cika musu fejinne da sharhin magunguna nasan zaku aika🤣 to da Innah Yaha zan haɗaku ehe son so domin Allah. Burina inga na taɓa rayuwar auren mata da yawa kuma na gyara musu zamantakewarsu. Mata mu san kanmu, mu kula da kanmu, mu mutumta kanmu, musan girma da darajar da Allah yai mana. Mu yi karatu, mu kama sana'a., mu yi aiki in mazajenmu sun bamu damu. Mu tsare mutumcinmu a wajen aiki, mu tsabtace sana'armu mu sa gaskiya. Mu riƙe adda'a tare da miƙama Allah lamuranmu tare da yaƙini. Sai mun haɗu gobe)
Chapter 44 · 0% Book details