← Book details Tsuron Tsirin Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 60 OF 84

Sashe 60

Tsuron Tsirin Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yau wacce rana mun tadda wutar nefa kuwa. "Bari inje ko wajen Baraka ne in karɓoma Innah Abinci" "Laa barshi, aini da nayi sallah tafiya zamu yi. Akwai biredi da miya a mota ya ishemu, kaje ka samu furob. Ke kuma bara in yi sallah" Ta miƙe ta shige ciki. Kallona mijinyawa yayi ya saki murmushi. Kana yasa kai ya fice, sai zumuɗi yake yi. Bayan Innah Yahanasu ta rama sallolinta tace. "Ni kam Hindu da alkhairi, nan da wata takwas akwai biki na gidanku. Sai mun haɗu acan. Duk wacce ta miki, ki mata kar ki sake ki ɗagama ko wacce ƴar abu ta kazan uba ƙafa, na faɗa miki kenan. To kinji, Azgar zamu yi kewarka yaro mai shiga rai." Har waje na rakata, saida motarsu ta yi nisa muka shigo gidan. Uwatale na cikin tsakar gidanmu da kwano a hannunta muka shigo, tayi saurin zabura. Leda ce baƙa a hannunta ina ganin sanda ta tura a mararta jikina ya riga ya bani bata da gaskiya wallahi. Kada ki sake ƙafarki ta sake shigomun cikin gidana, tsakar gidana ba tare da nice nan na baki izini ba. Ɓacemun da gani, dake da ƙazamin abincinki, ni kin taɓa gani naci abincin ƙazantarki ne? Ki fita nace" Na daka mata wata tsawa, uwatale ta isheni na gaji da iskancinta. Ina da yaro yanzu bazai yiwu uwatale ta dinga shigomun haka sasakai ba, dan ni bamma yadda da'ita ba. Sum _sum ta fice Mijinyawa ya jani muka shiga ciki. Azgar ya ajjiye a doguwar kujera, nasan kun biya karatun da kyau kuma. Mun yi nisa a karatu, yana nuna mun darasin kewa. Kawai muka ga labulenmu a sama. Juyowar da zamu yi, mukai idanu huɗu da Nanno da Uwatale. Wallahi alamu ya nuna, ya tabbatar,sun jima a tsaye a wajen. Babu mamaki tun karfon karatun har zuwa inda karatun yayi zafi, kaina ma baya ɗauka sabida nauyin baƙin, wasu wasalinsu a sama, wasu wasalin na ƙasa, ƙila suke tsaye suma suna jin karatun. Rigata na gyara, na ɗauki ɗankwalina a ƙasa, nayi shigewata ciki. "Babu shakka tabbatacce. Kananan ana maka zizizi da zazaza. Ta ya wannan makirar zata barka kaga mutumcina Magawata hiye" Ta dai yi mai faɗa tai ta zazzaga, tamkar ta kamashi yana saɓon Allah. Aka dawo batun zuwa Maiduguri shi dai haƙuri kawai ya bata, dole ya karɓi laifin da Innah yahanasu ta ƙaƙaba mishi. Ta gama ta tafi. A wannan dare, mun yi karatu masu wasali, sosai nake fahimta ta dalilin magangunan washin ƙwaƙwalwa dana shassha😉. Rayuwa taci gaba da cukumurɗawa, abubuwan suka ci gaba da faruwa, masu daɗi da marasa daɗin ma. Na kunce gara na ba Nanno rabin buhun shinkafa, komai saida na ɗiban mata, na bata atampa, sabulu, omo duka. Kuma ranar dana dafa naman kai saida na ba kowa ma a cikin gidan. Gaga gaga gaga Abubuwa suka ci gaba da garawa, mu jiƙa mu matse dai. Bamu da matsalar abinci sam, daga nan har shekara biyu ma inaga koma fi, tunda jalauta abunmu muke yi, gani da bushasshen kifi mai yawan gaske. Mijinyawa suna tafiya aiki wannan gidan gona, ko su tsaya a Gombe, ko a Bauchi. Mafi ƙaranci sati biyu yake yi in a Bauchi suke, in a Gombe ne kuma wata guda, shi zai yi ya yawo. A nanne na fahimci Nanno kasancewarmu tare ne sam bata so, taga Mijinyawa a gida ni dashi muna nishaɗi, shine bata ƙauna. Da zaran ya dawo take kafa ƙahon zuƙa. Daya sa ƙafa ya koma take sakarmun marata in yi fitsari, sai ƙorafe_ƙorafen da ba'a rasasu. Tunda Uwatale na kai rahoto, bata sauya zane ba, sai ƙiyayya data ƙara a sanadiyar fita da Mijinyawa yake yi, da yadda taga hatsi ya wadacemu, abinci sai da kifi, in Mijinyawa zai dawo kuma in saka nama. Kar ku mance kuɗaɗen dana samu na suna, sunanan a adane nayi musu kyakkyawan ajiya gaya, kuma ina ƙarawa akai duk randa na ɗauki albashina, tunda abubuwa da yawa sun warware mana, Azgar ya shigo rayuwarmu da alkhairi gaya. Azgar yana samun kulawa sosai, kuma har Nanno na turawa a ɗaukeshi, shi da yaron Uwatale da suke kira da Baba. An mammai mugunta sosai, sai dai in kauda kaina. Daga ranar dana zo mai wanka zamu tafi makaranta koyarwa, sai naga tabo kamar na cizone ga haƙora reras a cinyarshi wallahi. To ban kuma ba da shi ba ko an aiko. Haka daya soma rarrafenshi iyakarshi tsakar gidana bai taɓa fita babban tsakar gida ba. Azgar na da wata tara muka je biki gida, a lokacin dabo ma yake yi, in yayi ɗaya biyu sai ya faɗi. Da taro yai taro a gida jama'a aka cika, ƴan kwantagora ma duk sun zo. Sai hirar dambarwar sunan Azgar ya tashi. Harda masu miƙewa su kwatanta yadda akayi, da irin rikicin Nanno da Innah yahanasu. Ni ko ko in kula, to me zaice da gaskiyarsu su yi abinda suke so. Naji daɗin zuwa bikinnan sabida yadda na fito ba damane a cikin dangina, haka yarona kowa na son ɗaukarshi ƙato dashi yaro mai cikar lafiya da kuzari. Sati uku nayi na koma, Baba sojanmu baya nan yayi tafiya wannan dai karon bamu haɗu ba, sabida shi na ƙara sati ɗaya, amman dake Allah bai nufa da rabon ganawar ba, bamu gana ba. Na koma jama'are da kwana biyu Mijinyawa ya dawo daga nema. Azgar daya ganshi sai murna da zabure_zabure. Haka muke ta gudanar da lamuranmu. Ina ya Allah babu ya Allah Kwanaki, satika, watanni sukaita matsawa. Har bakin Azgar ya soma buɗewa, yana cemun Maa, a lokacin Mijinyawa kuma yana iya ce mai Babba. Bari in dawo daku baya a farko nayi magana cewar tsawon shekaru shidda nayi a Jama'are. Mantuwace sakamakon abun ya jima amman nafi wannan shekarun Afwan masoyan Hindu, duk da ma Magawata a halin yanzu ya fini fada. Wannan kenan. Sannan Asam'u bata yi shekara biyu a hannun mahaifiyarta ba afwan shima duhu ya shige mun, a yanzu abubuwan da suke kaina suna da yawa ne ( inji Hindu ne da fatan kun gane?) A cikin wannan kwacuɓen da Azgar yake yi Halima ta haihu ɗiyarta mace fara kyakkyawar yarinya santala. Kullum ina zuwa inna gama da makaranta. A wannan zuwanne na tabbatar da irin babbar matsalar da Abdulƙadiri ke ciki da Halima. Dama Mijinyawa na labartamun wasu. Bata mishi biyayya, a gaban kowa yaɓa mai magana take yi. Ya rame, ya lalace, cikin ƙanƙanin lokaci kamar ba Abdulƙadirin da muka sani ba. "Ai da ba dan mu ba da tuni Abdulƙadiri ya saki Halima, kinga wannan cikin data haifeshi shi ya tseratar da igiyoyin aurensu gaskiya. Amman har cukumeshi Halima take yi. Ita bariki take son komawa ma gaskiya. A hakanma yana zarginta da wani tsohon bazawari da suke zaune a maƙota, ga gida ga gida. Rannan da muka dawo Gombe, mun soma biyawa ta gidanshi. Hmmm wannan ƙaton ɗan iskan a falonshi fa wai hirace kawai suke yi. Shine dalilin wannan damben dana baki labarin sunyi, ta ɗauki tukunya ta danƙara mishi a kanshi wallahi. Abdulƙadiri yana cikin jarabawa mai girma. Har kuka yake yi inya tuno da irin baƙin cikin da Halima ke ƙunsa mishi a wajen aiki fa. Illar auren ƴar bariki yana da yawa. Ba duka bane suke tuba na gaskiya ba. Kuma kinsan basu ɗauki maza da daraja bane, wannnan yana ƙara assasa wutar rikicinsu Ta saba da zaman daduro. Duk baƙin cikin da zaisa magidanci kuka akan iyalinshi, Tutar so abun da girma to yake." Mun jima sosai muna tattaunawa, washegari ma da naje gaskiya saida nayi mata nasiha, wani ashar data lailayo ta danƙarama Abdulƙadiri, kawai dan ƙanwarshi tace a bata kanwa zata saka a miya. Shikenan ta dinga zagin Abdulƙadiri. Danginshi sai muƙus suka yi, a lokacin ne na dinga nuna mata ba daidai bane. Tunda tana mugun ganin mutumcina sosai, kuma sosai take son ƙawance dani. Shi yasa ma tace ma Abdulƙadiri ita a bani kuɗin kayan yara in siyo mata a Kano lokacin zanje. Ai ko ilai ni na siyo mata duk kayan da ake buƙata nice harda ciko. Shi kuma Abdulƙadiri sabida yadda yake martaba amininshi Mijinyawa ne yaima ɗiyar huɗuba amman dai su suka zaɓi sunan da zasu saka ma ƴarsu. Ranar suna yarinya ta amsa suna Asama'u. Akayi taron suna lami lafiya, aka kammala. Harda su Uwatale a wajen suna. Lokacin tana fama da laulayin ciki, ga goyo, ga shayarwa. Sai duk ta canja kamanninta ma sai da suka sauya. Duk da dai tana ji da wannan ciki. A gidan sunanne naji tana faɗin tana haihuwa zasu koma birni, cikin data samune ma ya kawo tsaikon komawar. Amman tana haihuwa, akayi bayan suna zasu tattara yanasu_yanasu su koma birni. Nan na soma farin ciki, muma lokacinmu ya kusa kenan, dama bana fata ko kusa ace Azgar ya soma karatu a wannan ƙauye. Kuma duk sanda za'a turo wasiƙa, Baba Sojanmu na jaddada mana batun komowarmu birni, sannan yana jaddada a kiyayi ranar da turarmu zata kaishi bango. Duk sanda aka turo wasiƙarnan bana iya rutsawa sam. Nasan Baba Sojanmu, nasan fishinshi babu kyau. Sannan ni kaina hankalina kacokam ya koma kan karatu. Ga Luba ta gama karatunta harma ta samu gidan rediyo ta maƙale tana aikinta. Ga irin ci gaban da ƴan uwana suke ta samu, da ƙarin matsayi duk ta dalilin karatu. Matar Akarami, matar Qazzafi, da Anti matar Yaya Sojanmu. Duk fa sun koma makaranta dukkansu mastas garesu, dake suma tamkar wata gasace a tsakankanin mazan. Na cewar matar wane bazan bari tafi matata ilimi, ko wayewa, ko kyan gani ba. Wannan yaja matan yayinmu maza suna fitowa sosai, kece raini suke yi gaya. Kuma sun samu guraben aiki mai kyau. Matan suma gasace lafiyayya a tsakaninsu, a zahiri basu da matsala za'a haɗu ayi hira. Amman a baɗini gaskiya kowa cikinsu bata son ace ai a sunan wance, ko a bikin wane matar wane ce ta cinye taron a surukan gida kenan. Matan da iyakarsu digiri, dasu akafi gabzawa da masu mastas, duk da dai anata musu ɗauki ɗai_ɗai wajen jefasu a makaranta. In naje biki ko suna gida na kallesu, ko inji suna hirar ai ofishinmu kaza ne ya faru, aa masana'antarmu kaza. Sai inji tamkar allura suke
Chapter 60 · 0% Book details