Sashe 35
Tsuron Tsirin Part 3 Complete Hausa Novel · about 4 min read
"To kinji dai an dudduba gidajen abokanshi ko sunje, amman ba'a samesu ba. Amman duk inda suka je zasu dawo. Kiyi haƙuri ala bashi ko zuwa gobe da safene za'a san inda suke, tunda ba ɓata suka yi ba. Abokinshi Abdulƙadiri ma yace ya gansu da yamma lis. Har bayan la'asar tana cikin gidannan dake bama mai yawan fitowa bace, dama haka take yi."
Innah Dubu ce ke magana da Innah Yahanasu, wacce take zaune tana cin alkakin da ta tawo dashi, dan anyi juyin duniya taci abinci taƙi ci. Hatta maƙota an kawo kusan kwano huɗu na mabanbantan abinci, bata ci ba. Kasancewarta macece mai ƙyama sosai, a birninma ita ba abincin kowa take iya ci ba, balle a nan ƙauye.
Nanno ce ta shigo tana cewa.
"Kinga fa abu kamar wasa Dubu babu Hindu babu Mijinyawa ko ina suka je baza su sanar ma mutane ba sai Allah. Duk sai naci mutumcinsu in suka dawo marasa hankali. Kuma nasan aikin Hindune itace zata jashi su kama hanya. Tunda nake yarana basu taɓa zuwa wani wajen ba izinina ba sai gashi yau Hindu ta zama sila"
"Tunda shi wawane ai dole kice Hindu ce sila. Wato ke dai har kullum son kanki ne dake. Kina nan amman kin yanke hukunci. Madadin ki musu fatan alkhairi, sai cewa kike yi zasu dawo su sameki mutanen banza. Ke wacce iriyar uwace ke haka ne? Kai Allah ya sauwaƙe"
"Kinga baiwar Allah bafa zaki zo har gidan mijina ki nemi farfaɗamun maganganu ba ehe. In ba Hindu bace zata ja shi, da can yayi hakan mana. Kinzo sai wani daɗɗagama mutane kai kike yi. Duk abinda aka baki kinƙi ci, ku ga zuriyar ƙaruna ko?"
Innah Yahanasu ai saita miƙe tsaye, gata doguwar kanuri ingarma. Innah Dubu tace.
"Bafa za'ayi haka ba. Dan Allah ku sakama zuchiyoyinku risilama. Muyi fatan Allah ya dawo mana dasu lafiya tukunna. Ke Yaya ki tafi abunki"
Ai ina wuta Nanno tasa Innah Dubu tunda dama tsoronta suke ji, maraina wayonta ne. Danma ruwane a haka ya doki babban zakara, in da canne tama isa ta shiga safgar Nanno ne, balle har ta shigar mata magana.
Innah Yahanasu kuwa ta dinga zazzagoma Nanno baƙaƙen maganganu masu zafi, da ƙyar husumarnan ta lafa. Dan da kuka wiwi Nanno ta wuce, a hakanma saida Yaya Salihu yazo ya dinga ba da haƙuri, ya kuma sa aka jaye Nanno.
Su Qasimu da Abdulƙadiri sukaita sunturi a jama'are ko Allah zai sa su ci karo dasu amman ina, dole sukai haƙuri akan a barma gobe ko asibitinne sai su leƙa tunda dai Abdulƙadiri ya faɗama Qasimu shi kaɗai cewar ai Magawata yace Asibiti zai kai Hindu ɗazu da suka zo. Amman bai sanarma su Innah Dubu ba, yasan akwai gagarumin rikici muddin suka ji inda Magawata ya kai Hindu.
Akwai narkakken rikici.
Asibiti.
Mijinyawa Harira tayi juyin duniya ya zauna yaci abinci, amman ina yaƙi yadda yaci.
Yana ƙofar ɗakin da Hindu take, lokaci zuwa lokaci yana shiga ya dubasu, bacci Hindu da yaronta suke yi, sai wani sa'in inya leƙa ya tadda Harira tana gyangyaɗi.
"Ka daure ka yi kwanciyarka ba sai kana leƙowa ba. Allurarran fa da akayi mata, sai ta kai gobe zata saketa. Sai zurga_zurga kake yi. Gashi cikinka babu komai"
Murmushi mijinyawa yayi.
"Ai babu komai Harira, ba ma zan iya wani bacci ba gaskiya"
Daya fitane baiwar Allahn dake jinyar wacce ta haifi Æ´an biyu tace.
"Inama Alhaji Dauda zai zo yayi koyi daga wajen bawan Allah'nnan. Yazo yaga yadda maza suke damuwa, da nuna kulawa da matansu. Shi ya É—auka namiji babu abinda zaizo yayi a asibiti dan matarshi zata haihu, ko ta haihun. A cewarshi aikin namiji shine kawai ya biya dukkan kuÉ—in É—awainiyar asibitin, wanzuwarshi bata da mahimmanci. Kaico"
Harira tayi shiru tana nazari kafin ta san me zata furta.
"Ai kulawama wani abunne sosai. Kuma wannan kulawar, da damuwar. Halamun soyayya, da tausayine a zuchiyar namiji. Amman shima Dauda bashi da laifi. Babu mamaki haka ya taso yaga ana kulawa da mace, ta hanyar bata kuɗi ta magance matsalolinta, lokacinshi ba nata bane, na kuɗine da kasuwancinshi, ko aikinshi kaɗai. Ita mace ɓangarentane dole ta kula da namiji, tai mai gadin gida, ta ɗau ciki, ta haihu, taci gaba da kulawa da yaran, mijin, gidan. Ita bata buƙatar kulawa, da lokaci sam."
Shirune ya wanzu a tsakankaninsu kawai. Ji kake kurum.
Wajajen asubane jaririnnan ya soma kuka kamar ranshine zai fita. Yana hannun mijinyawa yana aikin jijjigashi, idanunshi akan yaronnan.
Wannan kuka shine ya zama wasila na farkawar Hindu daga nannauyan baccin data tafi, na allurai.
Allah take ambato tunma kafin ta buÉ—e idanunta.
"Harira Hindu ta farka, naji muryarta"
Hindu:.