← Book details Tsuron Tsirin Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 84

Sashe 28

Tsuron Tsirin Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

kikace? " Kusan dukkanmu ukun muka haɗe baki wajen faɗin haka, saini daga ƙara da cabɗijan" Sumi_sumi ta fice sai gata da buhun ta jawo kiiii zuwa inda ta ɗauka. Turke Qasimu yaima ragonnan a rumfa, ya taya shi suka shigar da kaya cikin ɗakin da muke adana hatsi. Nayi nayi ya tsaya suci abincin Qasimu yaƙi fur. Sallama yayi mana ya ƙara gaba abunshi. Ni kuma naja hannun Mijinyawa zuwa ciki. Saida yayo wanka kafin muka zauna zaman cin taliyarnan, tako yi daɗi, kifinne baimun laushi yadda nake sonshi ba gaskiya, sai manja daya gaza. "Hindu makaranne suka mayar mun dake haka wai? Ni kam wannan makarai suna cutarmun da mata. Wallahi gabaki ɗaya kamanninki duk sun sauya, sai naga kamar kanki ma fa ya ƙaru sosai hakane? " Hakane, nima ina jinshi gingiringin dashi, sai dai haƙuri. Ya aikin naga dawa tayi mai har rago ka siyo? " "Dawa tayi mai. Ga Hatsinan shinkafa mai kyau marar ƙuƙus kusan kwatan buhu, wake mudu bakwai, garin tuwoma wani dana gani mai tsabta na cikin leda na siyo, tuwonshi da daɗi ga danƙo. Sai ƴan abubuwan da baza'a rasaba dai inmun gama sai mu duba. Wannan rago a can gidan Gonar da muka je kulawa dashi yake. Alhajinne ya ware ragunan da shanun da zai siyar. Fin guda ɗari, Kamar wasa nace inason wannan, a dubu bakwai ya barmun, amman fa sai nayi aikin kuɗin ragon kusan a bashi ya fito, sai dai aikin wata guda zai biya wannan bashi. Bana son abinda ƴan uwanki zasu zo suyi ƙorafi akaine, kinga ai babbane sosai. Shinkafa ma zamu ƙaro a gulmare ranar kasuwa, da mai da maggi duk zamu ƙaro da ragowar canjin hannuna. Fatanmu shine Allah ya dubemu ya ji ƙanmu, game da abinda muka saka a gaba." Mukaita tattaunawa, muna ni shaɗinmu. Bayan la'asar muka bubbuɗa kayan abincinnan duk muka juye komai a inda ya dace, muka adana komai. Alhamdulillahi kayan abinci kam muna dashi, ga itacen wanka shima akwaishi mai kyau faskare bushasshe. Gaga_gaga_gaga _gaga Muka shiga hidimar bikin Abdulƙadiri. Wajen Harira nasa Mijinyawa ya kai mun ɗinkin kaya kala biyu, da atampa mai kyau da Abdulƙadiri ya bani, wai tukuicin riƙe kaya, kuma haka suke yi dole yasa na karɓa. Harira tasa akaimun ɗinki mai kyau. Ni da Baraka a haka ina tutturawa, ni aka ba kwangilar girkin maza ƴan ɗaurin Aure. Dafadukan shinkafa, da soyayyun kaji muka yi, sai soɓo da kunun zaƙi da muka yi musu. Soɓo robar fenti ɗaya, kunun zaƙinma robar fenti ɗaya. Baraka ita kaɗai duk ta ƙuƙƙulla a leda. Abincin na juye a manyan kuloli biyu, matan gidan duk na basu nasu. Nayo wanka kenan, na sa sabon ɗinkina riga da zani. Saiga Mijinyawa an sha ankon yadi mai ruwan jinin kare. Ya shigo a hanzarce shi da Balele, da Qasimu ɗaukar abinci. "An ɗaura auren kenan Qasimu har kun dawo?" Cewar Baraka dake zaune tana zura abinci, kwanonnan yayi tsoro. "An ɗaura, sai da yamma kuma zaku je ɗakko Amarya. Hindu kam ba sai taje ba, gobe wuni ta leƙa dai ayi da'ita" Ai kuwa hakan akayi, bayan la'asar sakaliya suka tafi ɗakko Amarya. Basu suka dawo ba sai wajajen taran dare. Mijinyawa bashi ya shigo gidaba sai goman dare, amari ƙirjin biki ake faɗa muku. Washegari da yamma na biya ma Baraka muka je wunin biki. Lasiri na saka ja, mai adon baƙi mai tsadane sosai yana daga cikin anko ankon gidanmu. Na sa baƙin takalmin da innarmu ta sai mun, shi nake fita dashi unguwa bama ni da wani, na ɗakko mayafina baƙi na saka. A gidan wuninnan muka tadda su Shafa, da Uwatale dai. Kutsawa muka yi wajen Amarya. "Amarya sunana Baraka matar Qasimu, wannan kuma Hindu ce matar Magawata" Da fara'arta ta tarbemu. Idanunta tsabar yagewa har ɗayan ya haɗe da ɗayan. Ga wani kitson gashin doki da tayi, ga ƙawayenta karuwai nan duk sun halarci wannan biki. Ni dai sai jinjinawa nake yi dai. Shinkafa da miya, da alala aka bamu, sai kunun zaƙi yako ji sikarin. A haka dai taron biki ya ƙare. Gaga_gaga_gaga_gaga. Ciki yana shiga wata tara, a ranar da lissafinmu ciki ya cika wata tara. Ina zaune a ƙofar ɗakina ina karanta littafin hausa, da yammane, mijinyawa suna Bauchi na samu na lallaɓashi ya koma, wannan shine tafiyarsu ta uku, kuma Alhamdulillahi ana samu. Kwatsam sai na jiyo muryar Yaya Saratu a tsakar gidan har tana cewa "Ga can kwanar da zaku yi? " Ai ba shiri na fito da saurina, in rungumeta na kasa asiri zai tonu taji ƙqarya, ganin Akarami da Qazzafi ya sake faɗaɗa murnata gaya. Kayan kujeru suka kawo mun sababbi dal wallahi, waɗanda suka fi nawa kyauma. Ai fa Jama'are ta ɗauka, kafin kuce kwabo ɓarayina ya cika da mata, harda Nanno saida ta shigo ganin ƙwaƙwaf. Uwatale kuwa mai zata yi in ba habaice _habaice da ƙunci ba. Ai kuwa a tsakar gida aka dire kayayyakin, wasu kuma duk aka ɗaura wasu kan wasu. Nan suka shiga aikin fitar da tsofaffin kayan nawa, na riƙe kafet ɗin falona inaso a kaima Luba da labulayena dan Allah. "Karki damu, ai gidana kai tsaye za'a kai kayan zan cire mata ni da kaina zan kai mata. Amman kayannan sai zuwa gobe gaskiya zamu jera miki, kafin mu kama hanyar garinmu kuma. Amman su Akarami zasu samu wajen kwana a gidannan Hindu? " To bazai gagaraba ko a gidan maƙota zasu kwana. Zanje inma maman Qasimun Baraka magana za'a samu. Inaso Yaya inba Baraka labulayen uwarɗakina akwai wanda na siyo a kano na gumama suna da kyau sai in sakasu a uwarɗakin" "Ai babu komai zaki iya cirewa ki bata. Abinci fa, shayi zaki dafa mana mun siyo kajinmu da masar Bauchi" Akarami yace. "Ina mai gidanne Hindu?" Ai ya tafi nema Yana Bauchi, gata muke sa ran dawowar tasu. Qazzafi ga filas ɗin ruwan zafi nan ɗan miƙo bari in kawo kofuna da sikari, da ganyen shayin." "Wato nine marenin wayonki ko Duwab, me yasa baki ce Akarami ya miƙo miki ba. Yana ƙanina" "Kai waye ƙanin naka, wata takwas fa kawai ka bani" Dariya dukkanmu muka saka, ƴan uwa abun wuya. Miƙewa nayi da ƙyar na kawo musu kofuna, sikari, ganyen shayi, da babban tire. Tabarmace babba na shinkafa mana akai duk muke zaune, mukai da'ira muna cin masa da kazarnan Qazzafi dai sai kallona kawai yake yi. "Wannan irin kumburi haka, amman dai a asibiti zaki haihu ko? Sabida bana lafiya bane wannan kumburin ba" A can zan haihu ai koma ban kumburan ba gaskiya, haihuwar fari yaushe zan yadda in haihu a ƙauyennan." Haka dai mukaita tattaunawa, muna hirarmu ta zumunci, Akarami da Qazzafi sai zolayata suke yi. Da daddare bayan munci tuwo miyar kuka, yaji bushasshen kifi da daddawa , Yaya Saratu ce ta girka mana, Baraka ta kawo ma baƙi dafadukan shinkafar manja da ganye. Wajen nanno naje na tambayi batun kwanansu Akarami. Da naci sa'a sai tace a buɗe ɗakin samartakan Mijinyawa tunda su Lauwali basanan sun tafi cirani. Ilai anan suka kwana. Mun yi hira sosai da Yaya Saratu. Harma take sanar dani irin ɗinke_ɗinken fitar sunan da Innarmu tayi mun, har Baba Sojanmu ya siyo mun kayayyaki. Washegari sassafe, koma ince asussuba suka soma mun aikace aikace, ni kuma ina gaban murhu ina tuyar doyar da suka kawo mun tsaraba, jiya na aika aka siyomun ƙwan kazar hausa a wajen Shafa guda huɗu. A wannan lokacin huɗun du nera sittin in manyane, in ƙananane hamsin. Kafin takwas na safe kuma ɗaki ya kammala sun gamamun komai da komai, komai ya fito shar dashi sosai, damma ba'ai fenti ba. Komai na kalar kayan ɗakin mai ruwan ƙasane, da ruwan madara. Bayan sun kammala na zuba mana doya da toyayyen ƙoyi, da shayi muka karya. "To Hindu, mu kam zamu koma, sai munga wasiƙa daga Shehulle ƙila ma gobe mu sake juyowa kin haihu, Ubangiji Allah ya raba lafiya? " Ameen Yaya nagode sosai. Akarami Qazzafi, nagode sosai Allah ya bar zumunci" Akarami ya bani dubu biyar, Qazzafi ya bani dubu goma. Na rakasu har ƙofar gida inda motar Qazzafi take, saida suka ɓacema ganina kana na dawo. Ga durowar turarukan wutana an kuma batsemun ita da turarukan wuta na jego. Hmmm nan kuma aka soma zuruftun zuwa ganin waje. Allah ya soni Nanno bata ce Mijinyawa bane yayi mun wannan kayan ba, tana gani daga gidanmu yayuna suka kawo. Mutuniyarku gunɗu kuwa ko a cikin gayyar masu shigowa ganin ɗaki bata zo ba. Ni dai bama na cikin haiyacina, tafiyar su Yaya da kwana bakwai saiga Mijinyawa. Wannan karon kam tsaraba Nanno ce ta raba ta bamu, sai kayan jira jirai daya siyo, shima ta raba ta ba Uwatale rabi. Na shaƙa na shaƙa dan har cewa nayi ya ɗauka ya haɗama Uwatalen baki ɗaya tukunna. Saida yace in yi haƙuri zamu je ni da kaina in siyo kafin na haƙura. "Wannan kaya da aka kuma narka miki tubarkallah. Gaskiya su Innarmu suna sonmu babu laifi. Jibi gadonnan mai kyau." Murmushi kawai nayi mishi. Ni kam kaga ya fa kamata gobe sasafe muje wajen Hajiya Bara tun wuri kafin hankalinsu Nanno ya dawo kanmu. Wata tara da kwana tara yau cikinnan cif, ya kamata mu san me muke ciki kar asirinmu ya tonu, duk da ina ta faɗama Allah" "Hmmm Tutar so, ai ni wasu mafarkai dana dingayi a Bauchi a jejjere nama gama sarewa. Yaromnan abune mai wuya mu samesu fa. Mafarkin ba kyau nake faɗa miki" Haba mijinyawa, sai kace wani mai fassarar mafarki, kuma mafarki ai ba ko wannene yake zama gaskiya ba. Ni ina ganin muje kawai goben muji me ake ciki. Daga nan sai mu siyo setin bowon wanka, dama kace saika dawo tukunna" Kai ya girgiza yace. "To shikenan Allah ya kaimun Tutar so. Allah yasa mu dace. Ya kamata ki tafi ma da Harira kayan da za'a ajjiye a wajenta na batun haihuwar, in muka siyo riyo sai a cire a haɗa mata dashi ko kuwa? In Allah yaso ma sai kiga mun dawo da jariri, ko jaririyarmu a hannun?" Allah yasa, amman ka mance yadda aka tsara kaine zaka koma ka faɗa musu ina asibiti, saima na kwana? " Kanshi ya shafa
Chapter 28 · 0% Book details