← Book details Tsuron Tsirin Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 84

Sashe 23

Tsuron Tsirin Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Baba Alƙaline yayi sallama ya shigo, tare da neman wajen zama ya zauna. Tabb abunnan babbane kam. "Inason Abidah ta bamu waje in da hali, tunda dukkan abinda ya shafi yaran ɗakinta bana kutse, bare katsalandan akai. Ko kuma in da hali mu je ɓarayin Babansu Alƙali nanne babu yawaitar mata da hayaniya." Cewar Innarmu wacce ta haɗe girarta ta sama data ƙasa ta ɗaure. "In banda abinki Ruwayya da Hindu da su Salamatu ai duk ƴaƴanane. Miji ɗaya fa muke aure, menene danna zauna an tattauna matsalar Auren Duwab dani? " Har tana ƙarashewa da murmushi, ta ƙwantar da murya lunbu_ lunbu. "Ba ɗaya bane o_o kema kuma kin sani ai. Yanzu irin hidimar da kike ma Salamatu in zata koma irinta kike ma Hindu ashe?" Baba Nagoɗi yace. "To abinda za'ayi dai shine ita Abidah ta shiga ɗaki to. Ni banga wani abu a cikin wannan lamarin ba dan ta zauna. Batune na karatun Hindu ina ya kwana kawai, ba saɓani ko yaji tayo ba. Yaro ma ai yayi bazata, ita kanta Hindu ai ta ba da mamaki an fa shiga shekaru na shida da aure." Innarmu naga ta ma Baba Sojanmu wani kallo, tare da mai nuni da Baba Alƙali. Bafa cikin raini ba sam. Cikin sanin girma da mutumcin kai ga matar da take jan zarenta, kuma tasan mijinta da logonshi. Da yawa ana ganin tamkar Baba sojanmu tsoron Innarmu yake yi. Sam ba haka bane, ko wacce mace da irin baiwarta, da kuma irin matsayinta a wajen mijinta, a yadda kika ɗauki kanki, a haka kike a zuchiyar mijinki. Masu cewa Innarmu ta samu waje, su waya hanasu samun nasu wajen a wajen mazajensu? Ni dai nasan burin ko wacce mace ace mijinta yafi kusanci da'ita koda kuwa su ɗarine matanshi. Ke dai ki zauna a yadda kike so ki zauna, zaɓinki ne. Sai kawai Baba Sojanmu ya gyara murya. "Wel inaga muje lungun Alƙali ɗin tunda Ruwayya ta insistin. Acan za'afi sakewa ai" Baba Nagoɗi ya girgiza kai yace. "Ni na rasa dalilin da yasa faɗanka da tsaurinka baya taɓa hawa kan Ruwayya. Ai shikenan sai mu jenku gimbiya ta canja shirin." Baba Sojanmu da Innarmu sai suka mayar da abun wasan da dolensu suma suka ɗaukeshi a hakan. Ɗunguma muka yi zuwa falon Baba Alƙali dake shi matarshi ɗaya ce aina faɗa muku dama. Bayan mun zauna sai Baba Sojanmu ya buɗe takadda yace. "Hindu karanta mishi takaddarnan, a tunasar dashi yarjejeniyar dake tsakaninmu. Ko a addinance yarjejeniya gaskiya ce, rubutu gaskiya ne. Danme zai saɓa yarjejeniyar dake tsakaninmu? Ni nasan shine dalilin da yasa baya iya rakoki duk sanda zaki zo gida, baya so in ganshi balle in tuno. To yanzu haihuwa zaki yi a wannan ƙauyen in ban tashi tsaye ba shikenan zaki tara yara, batun karatunki ya sha ruwa. Amman kafinnan maza maza kije ki dirje wannan kwallin dake fuskarki, kaima ka dena sayo kwallinnan in zaka zo gidannan." "Aimun afuwa bazan sake ba" Mijinyawa ya faɗa muryarshi na rawa. Ni dai fita nayi ƙofar babban falon, na zare ɗankwalin atampar kaina, na goge kwallin kafin na dawo. Miƙe mun takaddar ya kuma yi, nasa hannu na karɓa. Zan soma karatun manyan turancin da akayi rubutun dasu, Baba Nagoɗi ya ɗaga mun hannu saina dakata. "Duk ba wannan ba. Yaro ai yasan da wannan yarjejeniya janaral baya musu a kanta. Al muhim shine mu tuntuɓeshi muji ta bakinshi. Janaral ka dinga sassautama boko haka nan" "Akanme, boko kam ai shima a wannan zamanin dole ne ko Nagoɗi. Yanzu yarinyar maƙotanmu yamma damu da auren ya mutu, na mayar da'ita karatu ta haɗa digiri. Kana ganin irin babban mai ɗamarar daya Aureta fa. Aurenta na farko ai maras ilimi ta aura yara nawa ta kwankwasa mishi. To sai akan Hindu ne zanyi shiru, duk irin ɗaga ƙafar da nayi. Alƙali kana jin mutuninka ko? Shifa dashi aka biye boko ma a gidannan ba yi za'ayi ha sam, sai dai a gani a maƙota. Ai yana da kyau ilimi ko sannan wannan yarjejeniya ce wacce a gabanku duk aka yita, na fa yi haƙuri ku duba" Baba Alƙali yace. "Nagoɗi a wannan gaɓar Janaral daidai ya faɗa. A tuntuɓi yaro aji inda yarjejeniya ta kwana shine kawai. Shi alƙawari girma gareshi. Ni sam banga wani laifinshi ba, in aka yi lakwa_lakwa da wannan ishu ɗin to Hindu ba zata yi karatun ba, dan babu wata alama data nuna zata yi. Da yaso tayi da yanzu ta gama, ko tana fainal ya ɗinta o somtin lik dat. Kai Magawata a ina zancen karatu ya kwana shekara an shiga na bakwai, dan an wuce shida? Muna son ji daga gareka" Mijinyawa ya ɗago muka haɗa idanu, na ɗan mai nuni da yayi magana kuma ya ƙwarara kanshi. Ai kuwa sai naga ya samu ƴar nutsuwa. Domin maganar gaskiya Baba sojanmu mutummne mai kwarjini da haiba, kwarjininshi muka ɗakko sosai. "Ayi haƙuri wallahi daidai da sakan ban taɓa mancewa da batun wannan alƙawari da yarjejeniya ba. Yanayin al'amurane da sukaita jujjuyawa damu, shine babban abinda ya kawo tsaiko a batun karatun. Amman yanzu aimun afuwa inasone in ɗan uwana ya ƙarashe gininshi daya soma anan kano ɗinnan. Zai dawo da iyalinshi, to inaso nima in roƙi mahaifiyarmu in biyoshi mu dawo nan Kano sai ta soma karatun anan Kano. Dan Allah a ƙaramun lokaci aimun afuwa, nasan an ɗagamun ƙafa sosai, amman dan Allah a ƙara" Baba sojanmu da yayi ƙur yana kallonshi yana nazari, sai can Baba Nagoɗi yace. "Zuwa shekaru nawa kenan tunda kaga gini yake yi ai ko? Kuma kasan gini ba abu bane mai sauƙi ba, shin sai yaushe kasa lokacin da kanka, sabida babu ɗaga ƙafa tsakaninmu." "To bana ce ba. Baba Nagoɗi aimun alfarma har zuwa a gama ginin mu dawo in sha Allah da zaran mun dawo zata soma makaranta. Ayi haƙuri bana son saka lokacine ya zamana kuma lokacin yayi bai gama ginin ba. Dan Allah a bani lokaci" Baba Sojanmu zai yi magana. Baba Nagoɗi ya dakatar dashi da hannun. Amman ina sai takadda ya miƙo da biro. "Amshi ka rubuta mata takaddarta. Iskancine a kanka na fahimceka. Infosibul ace wai sai an gama gini, o somtin lik dat, sannan ku dawo, a lokacin ne zata shiga makaranta. Lissafin hau meni ya kenan kake mun. Yaro kasan a inda kake, da waɗanda kake magana dasu kuwa? Sallamarmun ɗiyata ka kama hanyarka kawai" Da sauri duk muka ɗago muna kallonshi da biro da takadda. "In hankali ya gushe, hankali ake turawa ya nemo shi. Ai daɗina da gobe saurin zuwa, duk fa abinda aka saka mishi rana zai zo janaral. Inaso ka dinga sassautama zuchiyarka akan batun karatun yarannan. Akan karatu aure bai kamata ya mutu ba? " Cewar Baba Nagoɗi kenan. Baba Lukumanu yayi gyaran murya yace. "Kai Magawata wannan lissafin naka yayi nisa, gini ba abun wasa bane. Me zai hana ku kama haya, kafin shi ɗan uwan naka ya kammala ginin nashi. Sai kaga harta gama makarantar ba lallai ya kammala ginin ba. Ai ina ganin haka zaifi ko? Sannan mu zamu ɗauki nauyin makarantar tata" "Neba, infosibul mu ɗauki nauyinta. Ka mance a rubuce shi zai ɗauki nauyinta. Sannan ni na tura moda ɗinta har jama'are akan zan ɗauki nauyin karatun wai bikos na tausaya. Cewa yayi ya gode, amman zai iya ɗaukar nauyin matarshi. Sabida haka ya rubuta takaddarnan kawai" Hawayene naga yana bin kuncin Mijinyawa, baki Baba Sojanmu ya buɗe kawai. Aka buga, shima ya buga akan saifa an sakeni. Mijinyawa yaita magiya, hawaye shaɓe_shaɓe akan bazai iya rayuwa babu ni ba dai. Ni ko ji nayi alƙiyamata tamkar ta tsaya. "Shikenan Ubangiji Allah ya amince Magawata. Allah ya nuna mana lokacin da ranmu da lafiyarmu. Kai janaral haƙurin da kayi a baya har aka kai wannan matakin, ka ƙarashi akai. A bashi dama tunda ba mancewa yayi ba, ba kuma ƙin cika sharaɗin yayi ba. Ɗaga ƙafar yana da kyau sosai. Ko me kace Alƙalin alƙalai iyayen boko?" "To Yaya Nagoɗi tunda haka kace shikenan ba zamu yi jayayya ba. Amman ace sai an kammala gini abune babba fa. Gini a wannan marrar masu kuɗinma jjigasu gini yake yi. Balle wanda bai tara ba. Amman in akayi la'akari da irin yadda ya riƙe Hindu. Babu rashin sha, babu naci, babu rashin sutura, ga ƙoƙarin shi akan lafiyarta sai dai ace son barka. Amman muddin aka gama gini basu dawo birni ba, kuma ba'a ta da zancan karatun ba. To ta ɓangarena kaɗai zan iya datse igoyiyon auren ba sai janaral ba, ka amince?" "In sha Allah ma ba zamu kai ga wannan jallin ba. Zan yi iyakacin iyawata" "To shikenan ke Hindu ki kaishi ɗakin samarin gidan ya huta, a kai mishi abinci. Yaushe zaku koma kuma?" Mijinyawa ya dubi Innarmu yace. "Gobe sassafe zamu juya in sha Allah. Nanno bata da lafiya wanda yake kanta ma bata ganewa" Innarmu tace. "Ashsha Allah Ubangiji ya bata lafiya" Baba Sojanmu sai rubutu yake ta faman yi. "Ungo yasa hannu, kema ki saka, sai ki ba Nagoɗi, da Lukumanu su saka hannu suma." Sharaɗine akan batun gini da yace da an gama zamu dawo, da mun dawo zan shiga makaranta. Hannu nasa, na ba Mijinyawa shima ya saka, saina miƙama Baba Nagoɗi. "To ayi mutum komai sai yace a saka hannu, yanzu wata takaddar ka sake rubutawa, wannan uban rubutun, kaddai duk abinda aka tauna ka rubuta? " Obkos shi na rubuta, ma firen sain" Nan taron ya ƙare, muka fita tare. Baba Sojanmu ko magana ya dena yi, sai harɗe hannayenshi kawai da yayi ƙirjinshi yana ta jijjiga. Mukaita ratsa gidanmu domin zuwa shagon samarin gidan namu. Wallahi duk inda muka gilma sai kallo ya dawo garemu, har sai sai da muka fita, kafin hankalinsu ya kwanta. Kai subhanallahi tur da gidan yawa irin namu, da wanda ma yafi namu. Shagon su Akarami na da na kaishi, sai tulin tarin tsummokarai a hanga irin ta bangonnan, ko wacce katifa da hangarta a gefen gadonta. Kaya kuwa ba damane, katifun duk a tuɓe babu zannuwan gado. A ɗaya daga cikin katifun nai mishi nuni ya zauna. Komawa ciki nayi na tadda Innarmu na harhaɗamun komatsaina buhu guda. Luba na taya ta. "Ga
Chapter 23 · 0% Book details