Sashe 75
Tsuron Tsirin Part 3 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Hindu;.
Innarmu ce ta shigo da yaran a hannunta, ta nemi waje ta zauna.
"Hindu hoo wato harma kin shirya, tafiya kawai kike jira Æ´ar nema. To Janaral yace sai admishon ya fito, an biya kuÉ—in rijistireshon kafin ki koma"
Murmushi nayi nace.
Babu komai Innarmu Allah ya kaimu"
"To ameen. Hindu nasan janaral yana da zafi da kuma tsauri. Amman kinga duk wannan abun da yake yi?
Ba wai so yake aurenki ya mutu, ko ya samu tangarÉ—a bane. Ba kuma yana nufin saida ilimi mutum ke samun É—aukaka, ko daraja ba. In Allah yaso É—aga bawanshi, yana É—agashine a duk sanda yaso, ko wannan bawan yana da ilimi ko bashi dashi.
Darajar amman mai ilimi daban take, musamman ilimin addini, shi wannan daidai gwargwado nasan kina dashi, kuma kina ƙoƙarinki wajen bin dokokin mahaliccinmu, ga tsayuwar dare da kike yi, wanda shima wannan mai tsayuwar daren in domin Allah yake yi, dan neman yardarshi darajarshi daban take a wajen Allah.
Na horeki da haƙuri, ki koya daga gareni Hindu.
Ki jira lokaci alƙali tamkar yaune"
In sha Allah Innarmu. Nagode, kuma wallahi nasan Baba Sojanmu ba ƙin Mijinyawa yake yi ba, nima ba ƙina yake yi ba. Kuma tunda har yace haka, nasan babu mai mishi dole. Mijinyawa kuwa nasan bazai dawo ba har sai lokacin da wa'adi ya cika."
Innarmu ta gyaÉ—a kanta, halamun ta gamsu da abinda nace.
Gaga_gaga haka akaci gaba da cukumurÉ—awa. An yi jarabawar Jamb a ranar ashirin da takwas ga Afirilu.
Cikakken sakamakon hukumar jami'ar BUK ta zauna don tantance maki ( cut off maks) na kowanne kwas da sashe, inda aka fara kafe sunayen É—alibain da suka samu nasara a jikin allon sanarwa na makaranta.
A tsakankanin watan satumba, Nuwamba, na wannan shekarar.
Ina gada cikin waÉ—anda suka samu gurbin karatuu
Sai dai mu ce alhamdulillahi.
Duk wani cike cike, da duk abinda ya dace Baba Sojanmu shi ya shige mun gaba, tare dashi muke zuwa duk inda ya dace aje.
Har dai lokacin biyan rijistireshon yayi.
A nanne ya sanarma Baba NagoÉ—i ya nemi mijinyawa.
Baba NagoÉ—i.
Baba NagoÉ—i da magriba yasa samarin gidanmu suka kaishi Kurna, cikin ikon Allah sun haÉ—u da Mijinyawa ya fito masallaci kenan.
Nan suka gaggaisa.
"Lokacin biyan kuɗin rijistireshon yayi. Kamar yadda na ɗauki alƙawarin nemanka shine nasa yaro ya kawoni.
Inaga ka bani kuÉ—in bama sai kazo ba.
Sannan ka bani ɗan mabuɗin gidan, da ɗan mabuɗin ɗakin ita Hindun. Da kaina zan kawo maka ita. Sai haƙuri Baban naku akwaishi da zafi"
Mijinyawa yaita goÉ—iya.
Tambayar kuɗin rijistireshon ɗin yayi, a take ya shiga ya ƙirgo kuɗin, da ɗan mabuɗin ya bashi.
Suka yi sallama Baba NagoÉ—i ya kamo hanyarshi suka dawo.
Ya danƙama Baba soja wannan kuɗi.
Hindu:.
Yau cike nake da farin ciki marar abun misali.
Yau itace ranata ta farko a cikin ajin ɗaukar darasi, tare da ƴan uwana sababbin ɗalibai. Galibi ƴan matane, matan auren a wannan lokacin bamu da yawa, bamu wuce ace ɗaya, biyu, uku ba an gama ƙirgamu.
Kuma ayau zan koma É—akina Baba NagoÉ—i yace ina dawowa in jirashi zai dawo daga kasuwa ya maidani da kanshi.
Nayi lalle, na yi ƙunshi, nayi dilka duka, magungunan ta da komaɗa ma duk nasha, kafin in tafi makaranta na gama kammala kayana tas.
Ina dawowa Baba Sojanmu ya tareni.
"Ya lakca Hinduna? Sai yanzune na samu nutsuwa da kwanciyar hankali. Ina miki fatan alkhairi, tare da adda'ar gamawa lafiya. NagoÉ—i tun tuni ya dawo yana ta so kizo ya kai ki gidanki. Amman nace dani za'aje da Innarku"
Ameen Baba Sojanmu nagode ƙwarai da jajircewarka."
Tashi nayi na shiga ciki, innarmu na tarar ta shirye tsab, yaranma ta saka musu kaya sababbi siya musu tayi gaskiya.
Ban ko zauna ba akace in fito.
Jakata na ɗauka kawai su Azgar na tafe da ƙafafunsu.
Matan gidan duk sun fito rakiyata har gaban mota.
Ni dai motarmu na hawa titi na lumshe idanuna kawai.
Tafe tafe sai gamu a ƙofar gidan.
"Ga gidannan ka ganshi tsaya gefe Tasi'u"
Yaya Tasi'u ya kyara tsaiwa duk muka sakko a tsanake.
ÆŠan mabuÉ—i Yaya Tasi'u ya saka ya buÉ—e gidan, muka shiga da sallama. Tsakar gidan lallai akwai yalwa.
Sai dai ashe Tasi'u bai shigo ya ga inane É—akina ba ranar da yazo sauke Mijinyawa ba.
Muna wannan tsaiwar cirko_cirko a yayin da Baba Sojanmu yake ta ma Yaya Tasi'u turanci na faÉ—a.
Sai ga uwar Gulma Uwatale da alayyawo cikin leda ta shigo, kwaram_kwaram. Yatsunta sun fito har suna taɓa ƙasa ta gaban takalmin. Ga mayafi an yafa.
"Ashe dai ke É—in na gani Hindu? Ai ina wajen Shitu mai kayan miya, kawai naga tsayuwar mota. Sannunku ina wuninku?"
Su duk sun amsa, ni kuwa sai ido.
"Ga É—akin can ai, ba nan inda kuke tsaye bane"
"Ayya to mun gode ko?"
Cewar Innarmu, data amshi ɗan mabuɗi a hannun Yaya Tasi'u, ta nufi ƙofar ɗakin ta buɗe.
Uwatale dai taƙi tafiya. Ganin na haɗe raina ne yasa tace wai zata je ta dawo.
Ni dai jakata na É—auka nabi bayansu muka shiga.
Masha Allah falo yayi kyau, kujeru sun haska gaskiya.
Innarmu sai ƙarema falon kallo take yi.
Ni dai waje na samu na zauna.
"To Hindu mu kam za kuma mu koma, mun dawo dake É—akin mijinki, zai dawo ya taddaki. Allah ya ba da sa'a akan karatunki. Ubangiji Allah ya sanya albarka a ciki"
Cewar Baba NagoÉ—i kenan.
Baba sojanmu shima ya sanya albarka, tare da Yaya Tasi'u da sai tattaɓe bakinshi yake yi.
Innarmu dai ganin iskancin da Tasi'u yake yi ni nasan shi ya hanata magana, kusan tama riga kowa ficewa. Bayan ta ajjiyemun soyayyar situ É—in da tayi mun mai cike da nama.
Har saida motarsu ta tafi na koma ciki.
Ina shiga falon na sauke ajjiyar zuchiya wani irin farin ciki marar musaltuwa nake ji.
Saida nayi sallar la'asar na soma gyaran sib, ya ci mun lokaci sosai, sai daf magriba na gama.
Inata mamakin banga kayan kicin É—ina ba.
Kwatsam sai na jiyo sallama.
Mrs BUKHARIMRS BUKHARI
....................
*Wai kina da labarin Gidauniya ta mata, farin cikinsu, da walwalarsu, mai suna *MURYAR MATA (FARIN CIKIN AL'UMMA)*🧕ðŸ»ðŸ‘©ðŸ»â€ðŸŽ“
*Wanda ni Mrs BUKHARI muka yi haÉ—in guiwa wajen buÉ—ewa, tare da sauran shuwagabannin Taskar Badiat Ibrahim?*
*ku matso kusa ki kasance a cikin wannan tafiyar ta Alkhairi, tafiyar da zata gyara rayuwar Aurenki, tafiyar da zata gyara miki tunaninki, tafiyar da mace zata gane ni'imominta, tasan kima da darajar kanta, gidauniyar da zata koya miki sana'ar da zaki dogara da kanki, gidauniyar da zata koya miki tattalin uwar kuɗin kasuwancinki, da yadda zaki tattali ribarki ta yadda zaki ƙarfafa kasuwancinki, sha'awar son komawa makarantar addini, ko na boko kike so? To biyomu muje wannan gidauniyar taku ce mata, gidauniyar ta ƙunshi abubuwan da zatonku ma bai zata ba.*
*Ga lambar wayata ga matan da basa cikin Taskar Badiat group 1 group 2 group 3 sai kui mun magana in sha Allah zaki kasance a cikin wannan tafiyar ta manyan mata*
(08179523215)
*Ƴan taska kuma zaku iya tuntuɓar Admins ɗinmu ta pc domin kuji yadda tsari da dokokin kasancewa memba a cikin wannan shahsrarriyar, garnaƙaƙar gidauniya wacce ta haɗa manyan masana zamantakewar aure, malamai, manazarta, mahukunta, ƴan gwagwarmaya, masana ta ɓangaren gyaran aure, ƙwararrun ƴan kasuwa, da gogaggun ƴan boko, wanda ya haɗa matan arewanmu da kudunma baki ɗaya, zamu kasance a duk faɗin Najeriya da izinin Allah*