Sashe 5
Tsuron Tsirin Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sojanmu. Nace Innarmu ta sako mun man shanu in Baba sojanmu ya kawo. Duk dai abinda ya dace na rubuta, mijinyawa yasa a ajjihunshi zai kaima Shehulle in ya fita da yamma. Da taimakonshi nayi mana tuwonmu na gari, da miyar kuɓewa ɗanya. Naman gida biyu na raba, rabin na barshi a tukunya. Ina kammala girkin na kulle ɓangarena muka shige wanka tare da mijinyawa, abinda yafi so kenan. Muna fitowa ya wuce sallar magriba. Kasancewar yanayine na zafi sosai ɗinnan a tsakar gida na shinfiɗa mana daddaruma ƙatuwa, na jera mana kayan abincin namu. Wani sa'inma a wajen muke kwana gidan sauro kawai muke ɗaurawa, a gefe kuma nayi sallah ta. Ina raka'ar ƙarshe naji anata bubbuga ƙofar, kafin in sallame aka dena bugawa, ina durƙushe ina ɗiban rushi a kasko zan zuba turaren wuta naji yo muryar mijinyawa yana ambaton. "Ahh Baraka sallah inaga take yi fa. Kin bubbuga bata buɗe ba ko? " Da sauri na zuba turaren wutan, nazo na buɗe ina murmushi. "Ahh Malama Hindu kai Alhamdulillahi nayi murna da jin wannan kyakkyawan labarin." Hannunta na jawo muka shigo daga ciki. Mijinyawa ya shige falo mu kuma ya barmu a tsakar gidan. "Wannan turaren wuta naki wallahi ba dai ƙamshi ba. Ɗakina duk ya kama ƙamshi tun wannan da kika kawo mun tsarabarshi fa, inata cancanawa wallahi." Ohh na wajen Mrs Bukhari kenan, gaskiya kayan ƙamshinta ƙarshene. Wannan ma na wajenta ne ai" Kula mai hannu ta roba ta dure mun a kan kafet. "Ga abinci ƙila kiji sha'awarshi. Kuma Qasimu yace a dinga zuba miki abinci kullum dare daga nan har zuwa ranar da zaki sauka. In kika ji kina sha'awar wani abunma zaki iya faɗamun zan girka miki. Kinsan tsarabe _tsaraben ciki da yawa yake." Ahhh wannan nauyi da Qasimu ya ɗaura miki haka Baraka?" "Oo_oo ba nauyi bane. Tsakanin Qasimu da mijinyawa babu wani bambamci wallahi. Ɗazu da rana ma ai nazo na riƙo miki kwaɗon zogale Uwatale bata faɗa miki nazo bane?" Murmurewa nayi, ai ba zata taɓa faɗa ba. Na buɗe tuwo, ina kan zuba mata ne nace. Babu mamaki ta mance bata faɗamun ba. Ga tuwo da zafinshi kici" "Ahh zanci gaskiya irin yadda naga miyarnan da ƙamshinta dole tayi daɗi. Ni kam akwai wani ƙamshi da miyarki take yi na musamman dan Allah menene sirrin a sammun mana" Dariya muka yi. Ta ja kwanon tuwon ta soma yanka tana lumshe idanu. Sirrin kayan ƙamshine namu dai na gargajiya. Mu kanuri bama girki ba tare da mun sa tafarnuwa, citta, kanunfari, ɗiyan miya, masoro ba. Kinga masoro yana da wani irin ƙamshi na musamman wanda gaskiya ba duk mata bane suka san da wannan sirrin ba. To shine sirrina, sai barin miya ta dahu a nutsuwa. Tayi magana ta kasa, sai loma kawai take zubawa har saida ta gama kafin tace. "To kingani nima na dinga yin miyarku ta birni mai ƙamshi, duk da muma muna sa citta, amman tafarnuwa kam bama sawa. Itama ɗiyar miyar kam gefi_ gefi muke sawa, barinma ni ban taɓa amfani da'ita ba gaskiya. Amman kinga ita citta ai muna dakawa tare da daddawa, har a jalof inasa citta. Muna wannan hirar muka jiyo sallamar Qasimu da Abdulƙadiri. Da sauri miinyawa ya fito, ni kuma na sake gyara mayafina. Na koma gefe na shimfiɗa mana tabarma. Sai ko gasu sun shigo niƙi_niƙi da tsaraba. "Ga Tutar so ta Magawata ba da kanshi a sare yaje gida yace ya faɗi. Barka barka munji abun arziki Alhamdulillahi za'a haifo mana ɗan so, ko ƴar so" Abdulƙadiri yayi carab yace. "Mu dai koma me aka haifo na kama zan haɗasu auratayya da yarana" Ai sai wajen ya ɓalle da dariya, ni dai na dara kaɗanne. Amman zo kuga dariyar Baraka ɓaratatata. "Kai dallah. Aurenma da ko haramar yi baka yi ba. Zaka wani ce ka kama abunda za'a haifa. Ai ka bar mana dai kawai" Murmusawa yayi yace. "To zan iya bar maka. Amman nima inason haɗa jinina sosai da Mijinyawa kasan gudane da ɓari. Amman batun aure yana kusa kusa Allah na kusan fito muku da matar Aure. Hindu zan kawo miki kayan tarin nawa ma ki ajjiye a wajenki. Sabida Baba tafiya zata yi, kuma bata rufe ƙofa, kwanakin baya data tafi ganin gida kusan atampa uku aka sace mun datsa_ datsa." To shikenan Abdulƙadiri babu damuwa sai ka kawo. Bamu gaisa ba ma, ina wuninku, Abdulƙadiri ka dawo lafiya? " Nan gaisuwa ta gudana a tsakaninmu dai. Ledojin gabanshi ya turo mun wai tsarabace, Qasimu ya miƙo mun lemu da gwaiba cikin leda. Godiya nayi mishi, na ja hannun Baraka muka shiga ciki na basu waje suka ci tuwonsu. Turarukan wuta na mata haɗin gambiza dashi. A kwalbar man shafawa mai gurguwa. Saina bata jan bakin majigi ina dasu da yawa. Godiya tayi mun, tare muka yi isha da'ita a ɗaki su kuma mijinyawa suka fita zuwa masallaci. Baraka ita ta wanke mun kwanakun da su mijinyawa suka ci abinci, tayi mun shara kafin tamun sallama ta tafi. Kular da Baraka ta kawo mun abinci na buɗe. Shinkaface da miya, aka jangaɓa miyar akai ga dai nama zuƙu zuƙu. Ɗiba nayi inaci ina korawa da ruwa, a gaskiya bata wani iya girki ba, tsabta gareta sosai irin masu aljanun tsabtarnanne shi yasa ma nake cin abuncinta. Miyarnan janƙwab da ruwa a ƙasanta. Ina kan ci Mijinyawa ya shigo yana fara'a. "Uwar biyu kenan abincin akeci, kina ɗan jin daɗin bakin naki yanzu ko?" Zama yayi daf dani ya raɗamun cewar Uwatale na zaune a dokin ƙofar ɓarayinta. Bakina na taɓe kawai, yasa hannu tare muka ci abincinnan, a tsakar gida muka kwana. Washegari na kintsa bakwai da rabi na fito da zummar tafiya makaranta, Mijinyawa na rataye da jakata ciki da takaddun ƴan makaranta. Ai daga zuwa gaishe da Nanno ta dira tijara akan na bar zuwa karatu, nace mata aa fa zani makaranta ko dan rufa mana asiri. Nan ta dura tijara aka kaɗa aka raya, na kafe na ƙeƙashe wallahi bamu muka baro gidannan ba sai takwas na safe. Haka ya kaini makaranta na shiga aji, zuchiyata cike tab da saƙe _saƙen wannan lamarin. Gaga gaga gaga haka akaita tafiya, da daddare Baraka zata aiko mana da wadataccen abinci muci da daddare mu ɗumama da safe abincin rana kawai nake girkawa an rage mana wahala. Bayan kwana biyu da tafiyar Shehulle sai gashi da yamma sakaliya ɗauke da jakar bakko shaƙe da kaya, da zungurereyiyar wasiƙa. Ranar nayi murna sosai. Ina ciccira kaya, mijinyawa na karanta mun takaddar. Gaisuwace da taya murnar samun juna biyu, da kuma batun nan da watanni biyu zuwa uku tana son inzo akwai biki, sannan lallai tana son ganina kafin ace na haihu. Harda miya Innarmu tayo mun miyar jirgi, wato soyayyar miyar sutu wacce babu ruwa a cikinta, wannan wacce zaku ga har duhu tayi sabida suya, tana shan mai sosai kuma bata lalacewa ko wata zata yi ba'a ɗumama ba, muddin a tukunya take ba a robaba. Tako ji soyayyun naman saniya harda awarar nono a ciki wagashi in ji mutan togo. Ga bushasshen kifi him, gasu yajin daddawa, jan yaji, maggi mai sita da reko, da farin maggi, sai kayan ƙamshi tafarnuwa, masoro, citta, ɗiyan miya harda man shanu cikin babbar gora mai girman wan lita. Naga madara da furanto, da sikari masu yawa suma. Sai wani ƙyalle da aka nannaɗe ina buɗewa a hankali dubu talatin rafa uku ƴan ishirin ishirin sababbi miƙaƙƙu suka zubo. Daidai Shigowar Uwatale. Mayafina nasa na rufe duka kayan. Ai mun saba a gidama Innah Abida haka take ma Innarmu, muddin taga an shige da leda to sha Allahu saita bankaɗo labule ko sokiburutsune saifa tayi. Sai ta soma shirmen gangan tana yi tana sosa kai, tana dariya wai tazo ganin jikin nawa ne, haka ta fita ba guiwa. Mijinyawa ne ma ya samu zarafin mata magana, amman ni da idanu kawai na kakkafeta. Tana fita ya bita ya maida sakata. A tsakiyar wannan kuɗi sai ga wasiƙar Baba Sojanmu da turanci manya manya ya rubuta. Tabb daga layin farko zazzagane na faɗa. Akan batun makarantata, yanzu ance cikine dani tun bani da nauyin kowa mijinyawa ya ƙi cika alƙawarin da ya ɗauka. To wallahi ya rantse mun muddin na haihu Mijinyawa bai maidani karatu kamar yadda yake a sharaɗi ba, zan dawo gida in zauna har sai ya tara kuɗin makaranta kafin zai amince. Baba sojanmu yayi maganganu masu zafi da kaifi sosai dangane da yanayin yadda Mijinyawa ya saɓa mishi alƙawari. Ga ƴan uwana duk suna aikinsu, suna da albashinsu. Ni dai kasa fassarama Mijinyawa nayi wannan takadda, amman duk da haka yaga sauyi a yanayina bayyananne, sai bai tanka ba, shima illahirin jikinshi ya mutu. Rafa ɗaya na miƙa mishi a cikin kuɗin. Kai mana cefane zuwa gobe, wannan kuma sai mu adana, ga maganar jigilar zuwa Bauchi kaga Alhamdulillahi." Karɓa yayi yana murmursawa. Haka kuwa akayi washegari kafin in dawo makaranta mijinyawa ya siyo mana cefanen duk kayan buƙata, ya siyo itace da yawa wai ya samu wani abokinsune shi ne ya jibga mishi wannan itace. Nako ji daɗin itacennan gashi bushasshe. Da hakan dabara ta faɗomun akan in dinga siye ina tarawa kafin lokacin batun haihuwarnan, kuma a damuna tsakiya haihuwa zata zo. Haka dai sati ya zagayo sassafe wannan karon ko Nanno a gaskiya bamu yi ma sallama ba muka wuce. Ƙarfe takwas a ƙofar gidan Harira tayi mana, sai dai yaronta yace ta fita zata dawo daga wajen aiki zuwa azahar. Sai muka zarce asibiti kawai domin mu rage lokaci. Jikina a sanyaye yake gaya, mijinyawa ma sai naga duk ya karaya harma gara ni. Muna ta zaune har dai aka soma kiraye kirayen sunaye, layi dai yazo kanmu. Duk da haka wani ɓangaren ni aka turani wajen likitan mata, mijinyawa ma aka dai haɗashi da wani likitan maza ( (Urologist) Ni kam na sha tambayoyi bila adadin gaskiya. Nan ɗinma fa cewa akayi sati mai zuwa mu dawo zamu samu sakamako komai a ranar. Haka muka fito wajajen bayan azahar. A bakin asibiti na siya mana cincin, da doya da ƙwai a bakin titi, muka hau abun hawa zuwa gidan Harira. Mun ko taki sa'a shigowarta kenan itama, ta haɗa