← Book details Tsuron Tsirin Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 65 OF 84

Sashe 65

Tsuron Tsirin Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Hindu:.
Tattaunawa muke yi ni da Luba, Yaya Saratu tana gado sai bacci take yi. Daga wajen aiki yau kam ta gudo, shine take ta wannan baccin sabida ciwon kai. Innarmu kuma bata nan
To ke Luba ai koma yayane kina aikinki, ba albashi ake dubawa ba. Ilimin da gogewar da zaki samu. Sannan in kika horu kinanan wata rana Bbc hausa zata kiraki. Kinsan dai ko wanne matashi, da babban ɗan jarida burinshi Bbc Hausa ne, sabida sha ƙungum ce"
"Hmmm Hindu hakane maganarki. Amman aikin kam gaskiya ba sauƙi albashin babu yawa, amman Alhamdulillahi ana gurgurawa. Kuɗin motane da yake cinye kuɗin albashin. Wallahi da fa harda bashi ma nake haɗawa. Sunusi ne yace in dinga tafiya a ƙafa shine ma kuɗin yake ɗan afki. Adashen wata nera ɗari biyar nake yi. Dashi kaɗai nake tsira Hindu. Kuɗaɗen duka a cefane yake tafiya. Takalmana duk sun suɗe, amman a hakan dai aketa gurgurawa"
To amfanin neman kenan ka taimaki iyalinka. Allah dai yasa mu dace. Hankalina yana kan mijinyawa ko a wanne halin yake sai Allah Luba. Amman lallai inason karatu ko dan inganta rayuwar yarannan namu Luba. Inaso su yi karatu mai kyau. Karatun Qur'ani nake son su soma kamar yadda Baba Nagoɗi yayi mana. Kai ai yafi jan karatu sosai sabida Qur'ani ya huda ƙwaƙwalwar sosai"
Sallamar Innarmu ce ta katse mana hirarmu.
"Luba manya har kin garzayo kenan wannan yaran"
"Innarmu danma dai shekaranjiya na zo naci abinci nayi bacci"
Dariya Innarmu tayi. Ta warware lafayarta.
"Ita kuma wannan gajiyar aikine yasa take bacci, ko ciwon kanne?"
"Ciwon kanne amman gajiyar aikice. Aiki akwai wahala akwai daÉ—i Innarmu"
"Gaskiya ne Luba. Ga wannan yaran suma sai baccinsu suke yi abinsu"
Baba Sojanmu ne ya leƙo, Qazzafi na biye dashi.
"Kizo ga mijinki yazo yana so kuyi magana."
Cewar Baba Sojanmu, wanda sai yanzu ne ya kulani tun jiyannan.
Miƙewa nayi ina murna a cikin zuchiyata.
Lafaya na naÉ—a na É—an murza humra na fice.
Mijinyawa yana zaune a ƙasan kafet. Baba Sojanmu yana zaune a kan kujera ya harɗe ga jarida a hannunshi, halamun babu inda zaije ya bamu waje.
Zama nayi daga É—an nesa muka gaisa.
A tsorace ya kalleni, murmushinma ya kasa sam.
Yara dai ya tambayesu nace sun yi bacci.
Sai muka yi shiru. Juyowa nayi muka haɗa idanu da Baba Sojanmu idanunshi ƙir a kanmu, ba karatun jaridar yake yi ba tsaronmu yake yi.
Shiru falon yayi, fitowar Innah Abida, da Luba ne ya É—an motsa falon ta hanyar gaggaisawa.
"Fom É—in kazo siya mata ne Mijinyawa?"
"Aa Innah tukunna dai, amman za'a siya in sha Allah ayi haƙuri zan siya"
Hmmm Innah Abidah kenan. Sai murna take yi wallahi ta kasa ɓoye farin cikinta ma.
"To Allah ya yassare. Amman daga baya ma ance maka za'a ɗauki nauyinta tayi karatun, tunda ka kasa ka nuna gazawa, kuma ansan baka da ƙarfi. Sai kaƙi gashi dai har yanzu anata abu ɗaya ai gara ka bari mahaifinta ya ɗauki nauyinta. Kaima a ƙalla ka samu sauƙi, kuma wannan dai alƙawarin ya cika a samu a baka matarka"
Ɗagowa nayi na dubi Baba Sojanmu mu dai yake kallo, jaridarshi a sama tamkar karatun yake yi. Amman baice uffan ba. Innarmu ce ta leƙo tace.
"Ko kusa baice miki ya kasa ba, ba gazawa bace tasa bai cika alƙawarin nashi ba. Kuma tunda yace zai cika alƙawari Abidah ai sai a barshi. Batun a mayar mishi da mata wannan ba huruminki bane, tunda ai ba ke kika ɗaukota ba"
"To hakane Ruwayya. Allah ya kyauta zamu ce. Allah yasa a soma karatun a sa'a"
"To ameen Abidah"
Luba ta miƙe ta shiga ciki, Innah Abidah ma ta fice a lungun ma.
Mijinyawa na kalla kawai, idanunshi yayi jawur sosai.
"Kizo Hindu ga abinci ki ba Mijinki yaci, wannan yarinyar ta tashi fa".
Miƙewa nayi na shiga ciki, idanun Baba Sojanmu a kaina..
Asama'u na É—akko na kawoma mijinyawa. Na koma ciki na É—akko tire nazo na dure a gaban mijinyawa, na koma na É—akko langar dake kan gaushi cike da nama a kakide na dawo.
Shinkafa da miya na zuba mishi, na tsami namannan guda huɗu tuƙu_tuƙu na zuba mishi.
Baba Sojanmu yake kallo shima idanunshi a kanmu yake.
"Naƙoshi"
Ya faÉ—a gabaki É—aya ya kasa sakewa, sai É—ari_É—ari yake yi.
Komawa ciki nayi.
Innarmu ki ce ma Baba Sojanmu ya shiga ciki dan Allah"
"Ke ki raba kanki da tsokano tsuliyar dodo. Kinga a ciki yake daku. In ba so kuke yi ya zaneku, ko yasa a banƙareku ba. To wallahi yaci abincinshi kawai ya kama hanyarshi, in dai ba fom yazo siya miki ba ato. Zuchiyarshi a kusa take, dan ya amayar muku ba komai bane. Babu ruwana. Jiya kina jin yadda ya kusan kwana yana turanci, da safe kinji Baba sojanku yayi hausa yau? To ki kiyaye. Anfa ƙureshi dan ƙurewa"
Luba dariya harda faÉ—owa a gado.
"Wayyo dariya zata halakani. Harna tuno sanda ake banƙare su Qazzafi in suka yi wani laifi. A barsu a rana kamar an gasa kilishi suita gumi."
Qazzafi ya tuntsure da dariya kawai.
"Luba bakya ji wallahi. Lokacin haka zaku zo kuita tsokanarmu, harda mintsini fa. Muma in aka sakemu muita dukan yara, duk wanda ya kulani ranar saina fasa bakinshi. Hindu ce kaÉ—ai zata kulani in amsa. Itafa har ruwa take kawomun. Gashi sai ta hau turmi take iya bani ruwan in sha. Rayuwa kenan"
Ni dai komawa nayi na barsu sunata hirarsu.
Mijinyawa ya kasa cin abinci.
Sai cewa yayi fa.
"Zan tafi zan dawo nan da kwana uku, sai ayi batun fom É—in. Banga Azgar É—ina ba.
" Yana ta bacci yaci tuwon matarshi. Ka daure kaci abincin mana"
Baba Sojanmu ya kuma kallo. Da sauri ya sauke kanshi, ganin yadda yake muzurai.
Miƙewa yayi ya miƙomun Asama'u, na karɓeta.
"Baba Sojanmu zan koma. Kayi haƙuri nan da kwana uku zan dawo, sai ayi batun fom ɗin in sha Allah. Dan Allah kayi haƙuri."
In kun tanka, to ya tanka.
Idanunshi rarrabasu yake yi a tsakanin mu biyun. Inya kalleni, sai ya kalli Mijinyawa.
Yaƙi cewa uffan, tunda muka ga yana hura hanci babu shiri ya miƙe ya fita babu guiwa.
Miƙewar da zanyi, naga Baba Sojanmu yana jijjiga ƙafarshi.
Duk da haka na dake na nufi fita da zummar raka mijinyawa.
Ai wallahi sai jin ihun Baba Sojanmu muka yi,
Irin ihun sojaji da suke yi, in rayukansu ya kai bango.
Ya miƙe ya nufo kanmu a guje wallahi.
Yana zuwa ya ruƙunƙumeni ni da Asama'u.
Ai sai ya zare bell ya zuba mun a gadon bayana. Yana ruƙunƙume dani.
Mijinyawa ya shigo da sauri, dan da harya ruga da gudu, dawowa yayi, da yaji saukar bell a bayana.
Aiko ya É—aga bell É—innan ya sauke mishi a kafaÉ—arshi shima.
Ka gudu, ka gudu, ka gudu mijinyawa kaje"
Na faɗa da ƙarfi, idanuna a rufe jikina yana wani irin kaɗawa kar_kar_kar.
"Aa Hindu bazan iyaba"
Bell ya kuma ɗagawa yana shaƙe dani, Asama'u sai ihu take yi.
Innarmu taƙi fitowa, sai Qazzafi, Luba, Yaya Saratu, da Innah Abidah, suka tawo a guje, harda Salamatu ashe tana ciki.
Aiko ya kuma sauke mana bell É—innan du mu biyun.
Mijinyawa saida ya gantsare.
Wani irin ihu na saka ihun da ba gidanba, ungywarmu kab saida akaji wannan ihun nawa.
Mrs Bukhari ce.
To sai Allah ya sake sadamu ranar litinin kuma
Son so💪🏼💪🏼MRS BUKHARI

*Wai kina da labarin Gidauniya ta mata, farin cikinsu, da walwalarsu, mai suna *MURYAR MATA (FARIN CIKIN AL'UMMA)*🧕🏻👩🏻‍🎓
*Wanda ni Mrs BUKHARI muka yi haÉ—in guiwa wajen buÉ—ewa, tare da sauran shuwagabannin Taskar Badiat Ibrahim?*
*ku matso kusa ki kasance a cikin wannan tafiyar ta Alkhairi, tafiyar da zata gyara rayuwar Aurenki, tafiyar da zata gyara miki tunaninki, tafiyar da mace zata gane ni'imominta, tasan kima da darajar kanta, gidauniyar da zata koya miki sana'ar da zaki dogara da kanki, gidauniyar da zata koya miki tattalin uwar kuɗin kasuwancinki, da yadda zaki tattali ribarki ta yadda zaki ƙarfafa kasuwancinki, sha'awar son komawa makarantar addini, ko na boko kike so? To biyomu muje wannan gidauniyar taku ce mata, gidauniyar ta ƙunshi abubuwan da zatonku ma bai zata ba.*
*Ga lambar wayata ga matan da basa cikin Taskar Badiat group 1 group 2 group 3 sai kui mun magana in sha Allah zaki kasance a cikin wannan tafiyar ta manyan mata*
(08179523215)
*Ƴan taska kuma zaku iya tuntuɓar Admins ɗinmu ta pc domin kuji yadda tsari da dokokin kasancewa memba a cikin wannan shahsrarriyar, garnaƙaƙar gidauniya wacce ta haɗa manyan masana zamantakewar aure, malamai, manazarta, mahukunta, ƴan gwagwarmaya, masana ta ɓangaren gyaran aure, ƙwararrun ƴan kasuwa, da gogaggun ƴan boko, wanda ya haɗa matan arewanmu da kudunma baki ɗaya, zamu kasance a duk faɗin Najeriya da izinin Allah*

Tun daga wannan ihun da na jishi a saman kaina tare da saukar bel, ban sake sanin me ake ciki ba. ÆŠib na dena ji, ko ganin komai ma.

Gidansu Hindu:.
Chapter 65 · 0% Book details