← Book details Tsuron Tsirin Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 77 OF 84

Sashe 77

Tsuron Tsirin Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

nama wani babban yanka." To shikenan " Iyakata da'ita kenan, sai ga Mijinyawa ya shigo da sallama. "Shigo mana Nawata bismillah" Nawata ya biyo bayanshi suka shigo. Ni dai tunda muka gaisa ban kuma cewa komai ba. Kwano da cokali na ƙaro musu, mijinyawa ya zuba musu abincinnan. "Azgar ana cin shinkafa da miya?" Cewar Nawata, saida ya cika bakinshi dam da abinci ya soma ɓarin zance. "Yanzu mijinyawa shikenan an raba Halima da Asama'u kenan, ko kuwa dai zaka mayar mata da ƴarta in ta tasa? " Ya kuma cikowa ya kai baki. Mutuniyarku itama saita soma cin nata kawai. Suna hirarsu tana saka baki, ni dai idanune nawa kawai, hirace da bata shafi Hindu ba. Dana miƙe ma sai na nufi kicin. Gawayi na gani ƙulli ɗaya, na ko karashi a risho ya ruru kana na dawo ciki na ɗauki kasko na koma. Tunda na shige ciki, ni kam ban sake bi ta kansu ba. Daga uwarɗaki nayi musu sallama tare da godiya. "To sai kin shigo mana. Daga wannan gidan naku gida goma sha huɗu ne, da babban layi a tsakani" Sai mijinyawa Babba yace. "To in banda ke Uwatale ai Mijinyawa zai kawota in ta huta kema dai" Ya fita rakasu, ni kuma na fito na gyara wajen da suka ci abinci. Asama'u na tarar tana amai. Da sauri nayi kanta jikinta sai zazzaɓi kau. Asama'u akwai laulayi ƙarshe akan saman ƙirjina ta kwana, ni kam baccina rabi da rabi, gashi dama ban kwanta da wuri ba, ina karatu mijinyawa na sanar dani mai gidan daya tambaya zai dinga saida lemo a ƙofar gidanshi, yau yayi mai magana bai amince ba. Dan haka gobe zai fita buga_ buga. To amman yanzu yaushe kasan gari da har zaka shiga buga_buga?" "Tutar so ho. Ga Nawata da bai ma taɓa shigowa birni irin na Kano ba. Amman yana fita buga_bugarshi. Ai binni ba kamar ƙauye bane kingani, akwai sana'o'i iri da kala, aikin ƙarfinnan gasunan suma. Kinga batun karatunki bana son a samu wata matsala, ga hayar gida, ga Nanno dole in zamu je da sallah mutum zai riƙe wani abu. Ga yara a gabanmu" Hakane Ubangiji Allah ya sauƙaƙe maka ya buɗa maka" Washegari da yaran na tafi na saukesu a gidan Yaya, ni na wuce makaranta. Uku na shiga gidan Yaya, bata ma dawo ba. Na tadda wai su Nana sun tafi islamiyya dasu Azgar. Ladi ya jikin Asama'u kin bata maganin kuwa na rana, sannan taci abinci?" "Jikin da sauƙi taga yara ta ware sosai. Sai dai abincin da taci ta dawo dashi gaskiya. Amman na dama mata kunu da ta ƙoshi saina bata maganin" Wannan shine mafarin shigan su Azgar islamiyya Tare da su Nana. Mijinyawa kuma a fitar farko dako yayi a kasuwa, fita ta biyu shugaban leburori yace ya sake kasuwa ya kauce ƙa'ida dokarsu. Sai ya shiga buga_bugar duk abinda ya samu zai yi. Yayi wannan buga_buga kusan na watanni shidda. Kafin ya samu aikin kwandastan Bus, kuma babu laifi ana sallamarshi da kyau. Sai dai kuma sai wajen sha ɗayan dare yake shigowa. A gajiye tulus kullum, kafin ya dawo na tanadar mishi ruwan zafi, zan gargasa mishi jikinshi da kaina, yaci abinci mu ɗan taɓa hira sai bacci, wataran ma hirar sam bata samuwa. Ranar lahadi ne kaɗai muke samun lokaci kanmu. Ɗakunan hayan gidan duk mata sun shiga, amarya guda ɗaya, sai masu yara kamata haka dai. In mun haɗu a tsakar gida, muna gaisawa, ni dake ba zama sosai nake yi ba ma, bama haɗuwa. Ranar wankin bayangida in ya zagayo kaina, zan wanke kafin in tafi aiki, haka ma sharar tsakar gida. Wajen da muke wanki, wanke_wanke ni ce kaɗai nake sa tsintsiya da ruwan kumfa in zirje tas bayan na gama wankin da nake yi duk ranar lahadi. Uwatale dai kullum da yamma saita shigo, in tazo siyan kayan miya. Hana ƙarya na shiga sau biyu gidansu. Na farko tare da Mijinyawa. Na biyu ni kaɗai bata ji daɗi ba, na shiga na sameta ta na ta zuga amai. Ƴan gidanmu sun zazzo da yawan, sau uku suka zo, sun rarraba tafiyar. Ƴan kuɗaɗen hannuna duk saida suka ƙare ayi musu hidimar girkin fita kunya. Kuma alhamdulillahi an fita kunyar. Gida kuma ina zuwa dubo su Baba sojanmu, musamman daga makaranta nake wucewa. Sai da uwatale duk yadda zata yi ta naniƙi matar gidanmu, Maman Zailani. To shikenan a lokacinne tasan kullum ina fita, Maman Zailani ta faɗa mata. Itama ta gani da idanunta, na dawo makaranta da yara nazo na sameta a zaune a tsakar gidanmu. Tana ma Maman Zailani wanke_wanke fa. Daga ita sai ɗaurin ƙirji, ga hijabinta rataye bisa igiyar shanya. Matan gidan duk suna tsakar gidan suna shirye_shiryen sanwar dare, kamar yadda kusan kullum a haka nake samunsu. Sai Amarya da take kicin ɗinta, tunda ni da'itane masu kicin ɗin langa_langa. Su a ƙofar ɗakunansu suke girkin, ga kicin shirgege na tsakar gida, shirginsu kawai suke sanyawa. "Ahh Hindu kin dawo, ai na shigo wajen ƙawata ban sameki ba. Ashe kin kuma samun koyarwa ananma? " Ƴar dariya nayi mata kawai. "Kin dawo maman Asama'u?" Su haka suke ce mun. Nadawo Maman Fatu sannunku da gidan" Na wuce tare da buɗe ƙofata na shiga. Nagaji sosai, ga yinwa inaji. Faten doya Yaya suka yi, ni kuma lalatamun ciki yake musamman mai wake da ganye a ciki. Gashi bana siyan komai a makaranta, abinci nake dafawa in tafi dashi, in zan kai yamma a makaranta. In nasan bazan wuce biyu ba nasan zanci a gidan Yaya. Sai da na huta kana na fito, na saka ɗan mabuɗi na buɗe kicin ɗina. Sai naga cefane a cikin bokiti mijinyawa ya ajjiyemun, Allah sarki ya zagayo kenan, dake yasan babu kuɗi a hannuna, kuma ba cefane. Kuɓewa ɗanya nagani, sai attahuru, albasa, tumaturi, tattasai, sai ɗanyen kifi jela ɗaya, da maggi, ina da mai. Risho na kunna na ɗaura ruwan tuwon nawa. Sai nayi zaman gyara kayan miyana ina jefawa a turmi. Jajjagawa nayi na juye a tukunya, na zuba maggi, manja ina da daddawata da kayan ƙamshi a cikinta aka haɗa aka daka, sai kawai ɗiba. Na yanka kifinnan na zuba. Sai na juye ruwa a bokiti naima yara wanka, na sauya musu kaya, suna wasansu daga ƙofar ɗaki cikin barandata. Su Zainab kuwa sai uban guje_guje da ihu suke yi. Tamkar ana kaɗasu da ruwan hanji. Azgar sai karatu yake yi, sai Asama'u itama ta soma karatun, suna yi suna nishaɗinsu. Ƴaƴa rahamane wallahi jinsu nake a cikin rayuwata tamkar ni na haifi abuna. Ita Asama'u dake mai laulayice dole zata fi shiga raina, zanfi damuwa da'ita. Amman son da Azgar yake mun gurbin yaron na musamman ne. Murmushi nayi na tuno sanda Baba Sojanmu yake kawo musu tsaraba, yaita rungumarsu Asama'u tai ta birgimarta a jikinshi. Uwatale sai labarin jama'are take basu, muryarta kuwa nayi imani har maƙota. Naga a gidanmu tayi jajjayen kayan miyanta ta zuba a leda dan jar jarsba. Sai da taga duhu fa ya soma rufawa, a lokacin harna sauke tuwo na maida miya, na ja ruwa na tafi wanka. Kafin Uwatale kuma ta kwasa a guje wai ta shiga uku bata san yamma tayi ba. Kai kawai na girgiza, na yi wankana, ina fitowa nayo alwala. Kalanzir ɗina na fita na tadda ya ƙare miyar ko tafasa bata yi ba. Ina da gawayina, saina janye kurfotina na ƙasa laka nake nufi, banma taɓa amfani dashi ba, sabida rami biyu gareshi ma'ana yananan kamar irin risho mai kai biyu. Gashi da nauyi. Fito dashi nayi baranda na kunna da leda. Kafin na shiga ciki na shafa mai, na zura doguwar rigar yadi dinkin umburela amman doguwa. Saida muka yi sallah da yara na fito.. Na tadda murhun ya ruru sosai garin sai iska ba_ba-ba_ba ga hadari har walƙiya akeyi. Mun shigo watan damuna Allah yasa mu samu ruwan dare. Ai kafin in idasa tunanin, sai ruwa mai iska aka soma shi. Haka na ɗauki kurfotinnan na mayar kicin, ɗayan gefen ruwan wankan mijinyawa na saka, na zuba gaushi a kasko na turare ɗakin nawa, ga yinwa, gashi bani da komai na taɓin gishiri, sai bayan isha na kammala miyarnan. Nako ci tuwo sosai, yau dai ban jira mijinyawa ba. A cikin ruwannan ya dawo ya jiƙe sharab. Kai tsaye ma ruwan wanka na juye mai yaje yayo. Yana cin abinci, muna taɓa hirar karatu. Ga kuɗaɗen aikinshi da kullum yake zubemun su, ni zan bubbuɗasu in jejjerasu, sai yace in adana in ya ɗan ɗauki wani abun, watarana ma baya ɗauka. Muna ta hirarmu ta karatu, wuyarshi da daɗinshi, da wuyar neman kuɗi da daɗinshi. Nan nake sanar mushi Uwatale tasan ina fita gashi_gashi. "To ai sai mu barsu a hakan. Ai duk sun san dama kina koyarwa a barshi a hakan. Allah ya taimakemu" Murmushi kawai nayi mishi. Haka dai gidanmu shikenan ya zama gidan zuwan Uwatale wuni zuryan fa, daga haka Uwatale sai tasa mata ke zuwa su saka kujera aita hira. Ta fa baro gidanta, ta tare a nan gidanmu. Ni yau dana shigo hirar takin dausayi suke ta yi, ko wacce na faɗin irin nata takin, suna ta shewa. Muryar uwatale wallahi har waje. Ina shiga sai suka ɗan daburce basu zaci ni bace. "Hindu to kuma da yaran duk kike zuwa koyarwan, ki dinga kawosu mana ai ba sai kin sha wahala ba. Ni kullum ma inanan" Aa nagode, babu wahala a cikin tafiya dasu ai Uwatale. Bana ɗaurama kowa nauyi." Yau dai harna gama dafa dukata ta bushasshen kifin da aka aiko mun da tsarabarshi, Uwatale tana gidan. Nayi wanka, naima yara, na bulale ɗakina da ƙamshin turaren wuta. Ina zaune ina nazarin karatu. Amman uwatatale manya tananan ana zuba. Ko sai yaushe take kammala girki oho. Asabar data zagayone na gane lallai wuni uwatale take yi a gidan tun safe take zuwa, tun kafin fitar Mijin Maman Zailani, dake Nawata sassafe yake fita, inaji tace wai ya samu wani babban aiki. Jarabawa mu kam ma mukeyi na samestan farko, duk na rame sabida karatu, da wuri nake shiga makatanta mu zauna da abokan difatiment muita karatu, zuwa wannan lokacin an shaidani wajen naci da ƙwaƙwar karatu, ga tambayoyi da nake
Chapter 77 · 0% Book details