Sashe 73
Tsuron Tsirin Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
...................
*Wai kina da labarin Gidauniya ta mata, farin cikinsu, da walwalarsu, mai suna *MURYAR MATA (FARIN CIKIN AL'UMMA)*🧕ðŸ»ðŸ‘©ðŸ»â€ðŸŽ“
*Wanda ni Mrs BUKHARI muka yi haÉ—in guiwa wajen buÉ—ewa, tare da sauran shuwagabannin Taskar Badiat Ibrahim?*
*ku matso kusa ki kasance a cikin wannan tafiyar ta Alkhairi, tafiyar da zata gyara rayuwar Aurenki, tafiyar da zata gyara miki tunaninki, tafiyar da mace zata gane ni'imominta, tasan kima da darajar kanta, gidauniyar da zata koya miki sana'ar da zaki dogara da kanki, gidauniyar da zata koya miki tattalin uwar kuɗin kasuwancinki, da yadda zaki tattali ribarki ta yadda zaki ƙarfafa kasuwancinki, sha'awar son komawa makarantar addini, ko na boko kike so? To biyomu muje wannan gidauniyar taku ce mata, gidauniyar ta ƙunshi abubuwan da zatonku ma bai zata ba.*
*Ga lambar wayata ga matan da basa cikin Taskar Badiat group 1 group 2 group 3 sai kui mun magana in sha Allah zaki kasance a cikin wannan tafiyar ta manyan mata*
(08179523215)
*Ƴan taska kuma zaku iya tuntuɓar Admins ɗinmu ta pc domin kuji yadda tsari da dokokin kasancewa memba a cikin wannan shahsrarriyar, garnaƙaƙar gidauniya wacce ta haɗa manyan masana zamantakewar aure, malamai, manazarta, mahukunta, ƴan gwagwarmaya, masana ta ɓangaren gyaran aure, ƙwararrun ƴan kasuwa, da gogaggun ƴan boko, wanda ya haɗa matan arewanmu da kudunma baki ɗaya, zamu kasance a duk faɗin Najeriya da izinin Allah*
Washegari sassafe su Mijinyawa suka tashi.
A rijiyar gidan suka ja ruwa, Qasimu ya siyo soso da Sabulu, kafin ya dawo Mijinyawa shi yayi nashi wankan, da nasu soso da sabulun.
Suna shiryawa kai tsaye suka nufi wajen Nawata.
Ɗumamen tuwo miyar kuɓewa ɗanya Uwatale ta saka musu, sai ruwan kokko.
Sai kuɗin mummuƙi Nawata ya bata, yace su sha sha shayi da mummuƙi tunda ɗumamen ya ƙare ba'asan da zuwansu ba.
"Jiya kuka shigone? Dan jiyan ma naso in kai Uwatale taga gidan. To a rufe yake shi yasa dai bamu shiga ba."
"Jiya da daddare muka shigo ai shi yasa. In Hindu ta tare ta shigo ai taga wajen. Yanzu kam ai babu komai a ciki."
Nawata yace.
"To ita Hindun ka sanar mata cewar kayan jerenta an barsu acan kamar yadda muma namu yake can, sabida in munje ya zamana muna da masauki? "
"Na sanar mata. Babu matsala zata sai wasu kayan É—akin tace"
"Iyayenta ne kenan zasu yi mata, babu matsalar da kai ka hanga akan hakan? "
Qasimu yayi carab yace.
"Su zasu yi mata mana. Kuma tace ai babu matsala, to babu matsalarne."
Dole zancan ya tsaya a haka.
Uwatale dai sai barbaza kunnuwa take yi, ta kasa zaune balle tsaye. Sai zurga_zurga kawai take yi.
Suna gama karyawa, su Mijinyawa suka nufi wajen Auwali mai gwanda, Nawata kuma ya nufi tasha wajen aikinshi.
Auwali ya ba da jiran kayan sana'arshi, ya rakasu inda ake saida kujeru, da gadaje sababbi, dama na hannu waÉ—anda basu sha jiki ba.
A zahirin gaskiya sababbin kujerun basu yi mai kyau da ma halamun ƙarko ba. Amman yaga wasu setin kujeru, da gado, da sib, masu kyau sosai, kuma basu sha jiki ba, da gani masu tsadane. Su dannma ance musu na hannune suka gane tsabar yadda suka nuna sabunta.
Mijinyawa yaji su yake so, sune suka dace da irin zaɓin Hindu. Waɗannan sababbin basu da ƙarko, kuma yadunansu gasunan burwatsai dai haka.
Cinikinne ya ɗaukesu lokaci mai tsayi. Ta yarda har Auwali ya barsu a wajen ya koma bakin sana'arshi. Da ƙyar suka ƙarƙare a kuɗin da mai kayan ya kafe akai, bayan ya ɗan yi ragin kaɗan.
"Kayannan masu kyaune, kuma aurene na wata shidda ya mutu. Shine iyayen yarinyar suka siyar dan dole, sabida basu da wajen ajjiya, ga takaici.
Da ace munso ma a sababbi zaku siyesu gaskiya. Dan dai gaskiya da gaskiya muke komai ne"
"To shikenan babu damuwa mun siya a hakan. Za'a samu mota da zata kai mana kayan ko?"
"Kyauta kuwa, bari in kira wannan. Kai mu'azu zo ka kai musu wannan kayan can kurna."
A wajen Mijinyawa ya sai kafet babba na falo sabo, duk da kuɗin da nauyi, amman a haka ya siya. Aka lode komai a mota, suna gaban mota har Kurna. Da ƙyar suka gane layin ma, mai mota yana ta rantsuwar shi sai sun ƙaramai wani abun, shi wallahi, shi tallahi dai.
Bayan ya taimaka musu wajen shigar da kayanne, mijinyawa ya É—auki É—ari biyar ya bashi, sai lokacin yayi dariya, gami da godiya ya ja motarshi kuma.
Sallah suka yi a tsakar gida, kana suka fita nemo abinci. Duk wannan aikin Qasimu bai nuna gajiyawarshi ba sam.
Kunji abota abun a yaba, ba irin abota ta yanzu da hassada ta cika mana ciki ba ko.
A ranar suka kafa gado, suka ajjiye sib inda ta dace, suka ajjiye dires miro.
Falo ma suka jera kujeru, suka saka kayan kallo.
Komai fes sai dai babu labule a tagogin falo, ya mance shab. Amman tunda Qasimu shi gobe yake son komawa, satinsu kusan biyu suna kai kawo. Ko shi kaÉ—aine kafin yaje É—akko Hindun ya siyo ya saka. Kicin kuma ya barta da aikinta in ta dawo ita tasan yadda zata jera, a yadda take so. Suturuma duk a saman gadon ya jibge mata.
Washegari sassafe sai ga su Mijinyawa a tashi Qasimu zai tafi.
KuÉ—i Mijinyawa ya saka ma Qasimu a ajjihu, baisan kuÉ—i bane shi yasa ya barshi.
Komawa sabon gidansu yayi sai ƙarema falon kallo yake yi. Yana mai farin cikin dawowarsu birni.
Zuchiyar tashi cike da zabarin son ganawa da Hindunshi.
Wasa, ne gaskene, sun doshi wata biyu basu sa juna a ido ba.
Shi tun sanda suka kai kuÉ—in fom basu sake zuwa ba, yadda suka yi da Baba nagoÉ—i shine sai randa ya shirya tariya sai yaje ya sameshi. Dan haka ana magriba zai fita yaje.
Murmushi yake yi, yana hasaso irin tarbar da zaima Tutar so da yaran baki É—aya.
Har kaza ma zai siyo musu gashasshiya a sabunta amarci. Tunda dama a darensu na farko Hindu ce ta siya musu, wannan karon zai siya duk kayan da ake buƙata na siyan bakin amarya ya tanadar mata.
Kafin magriba ya shirya cikin wagambari shadda, wacce Hindu ta ɗinka mishi bayan sunan Azgar. A cikin kayan suna ta sassamesu, sai ta bashi kala huɗu duk aka ɗinko mishi, biyu ya taɓa sakawa suma da sallah ne kawai.
Mai ruwan ƙasan ya saka, ya tsaida jar dara, ya shafe jikinshi da Alhaji Abdullahi, yabi da kulaccam ɗin Hindu.
A masallaci suka haÉ—u da Nawata, saida aka idar sun fito ya tareshi da zuba.
"Na ganka kamar ango gidansu Hindu zaka je ne, tariyarce tazo?"
"Eh zan je in tawo dasu, tunda an zuba mata kayan har an jejjera dawowane kawai."
Baki Nawata ya buÉ—e.
"Au har an zo an mata jere, shine baka sanar dani Uwatale ta musu girki ba? Yanzu ma da zaka je ɗakkota sabida Allah ba sai ka sanarmun muje tare ba. Kuma ko naman miyane a siyo a haɗe sanwar dare daku. Nace ko zumuncinmu ya samu tangarɗane? Kaifa ɗan uwanane bani da tamkarka. Abubuwan da duk kaga sun faru a gida can, naƙi goyon bayanka akan abubuwa da yawa, sabida Nanno taji cewar muna bayanta, ba dan bana jin zafi, ko ko tausayin abinda akeyi maka ba. Kayi haƙuri ɗan uwana ka watsar da komai mu yi rayuwarmu mai kyau, mu rungumi junanmu. Baka da kamata, bani da kamarka. Kuma kada mu bari mata su gilma tsakaninmu"
Mijinyawa yayi shiru yana nazari.
Take yaji wani sanyi a ranshi, ya kuma gamsu da bayanin biyunshi, kuma yayi mishi uziri. Ya tabbatar tabbas yana sonshi, baya nufinshi da sharri, uwatale ce ke neman farraƙa kansu.
Amman bazai iya zuwa dashi tawo da Hindu ba. Wannan ranar tasu ce, Hindu ma ba zata zo azo mata da kowa ba.
"Na fahimceku daga kai har su Yaya Jamilan. Na kuma yi ma kowa uziri akan abunda yake yi. Ni bazan so ace duk kuna bayana, ita ana kallonta a matsayin ba daidai take yi mun ba.
Nanno uwace, soyayyace tabbas yasa take nuna mun haka. Kaza na take É—anta ba dan bata sinshi bane. Kuma, kuma babu yadda za'ayi ace kullum kareni kuke yi."
"Hakane nagode da fahimta. To muje in watsa ruwa sai mu tafi ai ko? "
"Aa babu damuwa tunda ba dakai aka shirya tafiyar ba, ka bari inje ni kaÉ—ai É—in. Ai bama shiga ciki zanyi ba. Yaro zan tura ta fito mu dawo. Gobe dai kwa zo a gaggaisa ku ga waje.'
Da haka ya lallaɓashi suka rabu salamun_salamun.
Ko da yaje ƙofar gidansu Hindu lokacin sallah gashi yayi, sai kawai ya zarce masallaci. Sahunsu ɗaya da Qazzafi ma, ga Azgar a gefenshi sai riga yake ja yana nishi. Su Baba Nagoɗi sune a gaba gaba.
Bayan an idar, masu yin nafila sun yi, marasa yi sun fita, masu karatun Qar, ani sun soma.
Mijinyawa ya miƙama Qazzafi suka yi musabaha. Azgar yana ɗago kai ya ga Babanshi.
"Abba Abba Abba."
Ya miƙe a guje tare da faɗawa jikin Mijinyawa.
Tsam yayi mishi a jikinshi, sai ƙamshi turaren wuta yake ta faman yi.
Sanyi da tsantsar son yaronne yaji yana hudashi. Shi ko yayi lub a jikinshi.
Miƙewa yayi da yarin a hannunshi suka fita.
Baba NagoÉ—i yabi a baya a hankali.
Su Baba soja, dasu Baba Lukumanu suna gaba.
Saida akaje ƙofar gidan Mijinyawa yace.
"Barka da dare Baba'
Da sauri ya juyi.
" Mijinyawa kaine Ka dawo kenan?
To bismillah muje falona.
Hindu:.