Sashe 63
Tsuron Tsirin Part 3 Complete Hausa Novel · about 10 min read
................
*Wai kina da labarin Gidauniya ta mata, farin cikinsu, da walwalarsu da ni Mrs BUKHARI muka buÉ—e tare da sauran shuwagabannin Taskar Badiat Ibrahim?*
*ku matso kusa ki kasance a cikin wannan tafiyar ta Alkhairi, tafiyar da zata gyara rayuwar Aurenki, tafiyar da zata gyara miki tunaninki, tafiyar da mace zata gane ni'imominta, tasan kima da darajar kanta, gidauniyar da zata koya miki sana'ar da zaki dogara da kanki, gidauniyar da zata koya miki tattalin uwar kuɗin kasuwancinki, da yadda zaki tattali ribarki ta yadda zaki ƙarfafa kasuwancinki, sha'awar son komawa makarantar addini, ko na boko kike so? To biyomu muje wannan gidauniyar taku ce mata, gidauniyar ta ƙunshi abubuwan da zatonku ma bai zata ba.*
*Ga lambar wayata ga matan da basa cikin Taskar Badiat group 1 group 2 group 3 sai kui mun magana in sha Allah zaki kasance a cikin wannan tafiyar ta manyan mata*
(08179523215)
*Ƴan taska kuma zaku iya tuntuɓar Admins ɗinmu ta pc domin kuji yadda tsari da dokokin kasancewa memba a cikin wannan shahsrarriyar, garnaƙaƙar gidauniya wacce ta haɗa manyan masana zamantakewar aure, malamai, manazarta, mahukunta, ƴan gwagwarmaya, masana ta ɓangaren gyaran aure, ƙwararrun ƴan kasuwa, da gogaggun ƴan boko, wanda ya haɗa matan arewanmu da kudunma baki ɗaya, zamu kasance a duk faɗin Najeriya da izinin Allah*
Tunda muka ɗauki hanya Baba sojanmu yake faɗa babu ƙaƙƙautawa. Yayi hausa ma yaƙi fur, yana ta rantsuwar matsawar bamu dawo birni da zama ba, ko da aljanu zasu saceni suƙi dawo dani, a wannan karon babu ɗaga ƙafa. Ko dawowa birni, da ci gaban karatuna, ko takaddar saki.
Qazzafi ya kalleni da kyau ta madubin mota, yai mun lallausan murmushin da kai tsaye na fassarashi a matsayin na farin ciki.
Na sani Qazzafi yana sona fiye da tunani. Amman baimun ba, namiji mara faɗi da damatsa bana mishi ma kallon namiji. Kuyi haƙuri ra'ayinane wannnan tunma kafin in san ciwon kaina, har nazo na sani.
Na biyu Innah Mairamu bata ƙaunata, ta kuma kirani gajerar da bata san mai Qazzafi zai yi dani ba.
Innarmu kuma a lokacin tace.
"Allah ya É—aura mishi son wannan gajerar da bata yi kanta ba, gajerar da take hamdala ga Allahn da yaji yana son kallonta a gajera. Sannan kuma ya rasata, kuma sonta ya guyabeshi.
Ke da kike da tsayi, sai dai kash tunaninki gajerene"
Ranar munga jarfa ganin idanunmu.
Idanuna na lumshe, tare da gyarama Asama'u kwanciya akan ƙirjina.
"Allah ya kyauta. Ni naso abi a hankali ta yadda ba sai an kai ga zuwa gida ba. Kaga fa in muka je gida da Hindu haka za'aita gutsira ana tsomawa"
"An so? Ai ta gutsura mana. Ai kema kinsan nayi haƙurin da wama yayi zaton zan iya irinshi ne?
A wannan karon ƙorafinki bazai taɓa samun gurbiba dole a cika wannan sharaɗin, ko a rabu shikenan. Akanme zai mayar mun da yarinya ƴar ƙauye. Ki duba Hindu yadda ta koma. Ibin do i no shis tirayin ha bes taga ta lulluɓe wannan ƙauyancin. Amman ya bayyana sosai a jikinta. Yanzu shima Azgar inya taso anan ke kina ganin zai shiga ajinne ma? Sannan tunda ɗan uwanshi ya ɗakko ƴar ƙauyen matarshi da yaranshi suka dawo ƙwaryar kano, sai shine sabida raini zai zauna bayan ga rubutun da muka yi. Sa'a yaci ma ban zanesu ba"
Ya nuno mata takaddar.
A nanne ya ƙilla idanunshi akan Asama'u dake ta ja mun mayafina tana kirana Amma, daga baya ne ta dawo cewa Ammi, Ammin ake cemun kenan.
"Wannan kuma fa, haihuwa Hindun ta kuma yi, sabida kar in yi magana aka kasa sanarmun?" Nan ya sake buÉ—e wuta, idanunshi sun rufe baki É—aya, baya ko buÉ—esu.
Qazzafi ya É—an yi dariya.
Tsawa ya daka mishi, cikin yaren Sojoji yace dashi.
"Aje waya"
Qazzafi ya ɗan ƙame tare da sara mai.
"Ba haihuwa tayi ba. Yarinyace akayi mata kyautarta. Marainiyace mahaifinta ya rasu. Ka dinga sassautawa."
Baice komai ba, ya koma ya zauna. Tare da É—aurawa daga inda ya tsaya.
Bamu muka shiga Kano ba sai ƙarfe bakwai na dare. Motarmu ta tsaya a ƙofar gidanmu.
Idanu na kuma lumshewa.
Shikenan hankalin kowa sai ya kwanta, wallen mijinyawa ake son gani, to shikenan su sa ruwa a ƙasa su sha.
Da ƙarfin guiwata na taka ƙofar gidanmu.
Asama'u na É—afe a jikina, Azgar na wajen Innarmu.
Da Innah Mairamu muka soma karo, tunda sune Æ´an farko.
"Ga Hindu ga Hindu. Ga kuma maigida Azgar. Aa Hindu É—iya kika yi ne, naga mace a hannunki?
Eh wallahi É—iya nayi. Bani ita akayi"
"To to muje ciki, kya zo ku gaggaisa daga baya, lokacin sallah harya wuce. Mairamu NagoÉ—i ya dawo kuwa? "
Cewar Baba sojanmu. Ni kam gaba nayi, bansan ko me tace mishi ba.
Ina shiga falo na tadda Salamatu ita da Dakta. Ga kuloli masu kyau an mishi girki, dan wannan bama abincin gida bane. Salamatu ta zuba mishi yana ci, tana ta narkewa.
"Mutan jama'are kune a tafe da yammannan, ko ince darennan maraba"
Cewar Salamatu harda dariyarta ƙaƙas sabida tana gaban Dakta.
Dariyar nima nayi mata, na tsaya muka gaisa da Dakta, itama muka gaisa sosai kafin na shige, sai kallon Asama'u take yi.
Innah Abidah dake suruki na falo, bata fito ganin ƙwaƙwab ba.
Nima ina ajjiye Asama'u a kan gadon Innarmu saina fito na leƙa muka gaisa.
"Lafiya kuwa Hindu, ni dai nasan kinfi zuwa a yanayi na biki, ko suna duk da sunan ma baki fiye zuwa ba. To na ganki yanzu ko wani abunne? "
Lami tana zaune tana cin abinci.
"Innah to menene dan tazo gida haka kurum dan Allah. Nasiru maza cinye Abbanka ya kirani yana hanyar zuwa É—aukermu, ya je gareji dubomun motatane shi yasa bai zo da wuri ba."
Murmushi kawai nayi, tare da miƙewa Lami kenan saƙon ya iso. Na furta a zuchiyata.
A falo na tadda Baba Sojanmu tare da Dakta suna tattaunawa, ni kuma na shiga na tadda Innarmu tana wasa dasu Asama'u.
"Wajen Abidah kika shiga ko, nasan dole saita tsareki da tambayoyi danma Dakta yananan. Hmmm ai abun nema ya samu a gidannan Hindu. Amman babu komai rayuwarki muke dubawa, ina daidai da ko wacce Æ´ar... "
Hmm tambaya take yi ta ganni ba suna ba, ba biki ba, kuma ko lafiya. Na dai ce mata lafiya. Sai Lami dake sanarmun tayi mota. Mota Jamilun ya sai mata kenan?
"Mota ya danƙaro mata babba sosai, an kawo mana ma mun sanya albarka. Kinsan ta sake aiki, yanzu aikin kamfani take yi albashinta babba sosai, shine ya siya mata wai ta dinga hawa taje aiki kada a rainata. Tunda wajen aikin nasu duk masu motane. Wai inji Abidah fa"
Ficewa tayi abunta, ni kuma na maida hankali ga yaran. Ga tunanin halin da Mijinyawa yake ciki a halin yanzu.
Innarmu na shigowa nima na fita na É—auro alwala, na rama sallolina.
"Bari in ma yarannan wanka ko zasu ji daÉ—in bacci.
Kema kije ki É—ebi ruwa ki gargasa jikinki sai kizo kici abinci ki bi iyayenki da gaisuwa, kafin Janaral ya haÉ—a miki mitin. Duk da ya sanar ma Æ´an uwan nashi batun É—akkokin tunma kafin mu tafin. Allah dai ya kyauta.
Ni fatana mijinki yazo ayi magana ga fom na jam ana ta siyarwa, kema ya siya miki. Janaral ya samu ya sallameku"
To ai Innarmu Nanno ce bata amince da dawowar tamu birni ba. Bawai daga mijinyawa bane, kuma ba makarantar bane bazai sani ba fa.
Amman nasan in sha Allah zai shawo kanta, in dai ta amince shikenan faÉ—uwa tazo daidai da zama, sai ya siya mun fom É—in. Sai dai in bata amince ba to bansan yadda za'ayi ba"
"Kin sani mana takaddarki zai baki, a siya miki fom ki zana jam, ki koma karatu kema ai kin sani.
Wallahi in bata yadda da zaman ku birni ba sai dai a rabu. Kuma ko ta amince da zamanku, karatuma shima wani rikicin zata saka. Balle danme ma zata hanaku dawowa birni, alhalin ga ɗan uwanshi, da matarshi, da yaranshi a birni? Ko kune dai take so ta kashema rayuwa, ta dankwafar daku? To ke in baki da hankali, mu da hankalinmu. Hindu banso duka wannnan abun ya zama haka ba. Sabida Abidah tayi rantsuwa da maganganu, akan Mijinki bazai taɓa iya dawowa birni ba yadda ta san uwarmijinki, sannan ba zaki yi wannnan karatun da aketa burin kiyi ba. Maganganun rikicin sunan Azgar kuwa, hatta baƙi in akayi da, sai ta zauna tai ta basu labari suna la'antar surukarki da dangin mijinki. Alhalin ba daidai bane haka, ita kashin bayanta ta zauna akai dan gudun kar ta tashi aji ɗoyinshi. Amman shawarar da zan baki kibi Baba Sojanku a hankali in kina son zaman lafiya.
Hmmm kije ki yi wankan"
Fita nayi kai tsaye zuwa kicin na É—ebi ruwan wanka, na sirka da ruwan randa na gargaso jikina, na fito.
Na gama shafa mai kenan, sai ga Innah Mairamu ta yo sallama.
"Shigo Bismillah Mairamu"
Da sauri ta shigo ta nemi gefe ta zauna.
"Ashe sabida wannnan dai alƙawarin makatanta ne Hindu kuka je kuka ɗakkota? Ai ban sani ba da ba'ayi hakan ba"
"Au haba sabida kece mai iko da'ita ko Mairamu? "
Innarmu tayi saurin katseta, ko kallonta bata yi Azgar take shafa ma mai, ta gama da Asama'u har ta sa mata wando.
"Aa sabida dai ai auren yafi karatun Ruwayya. Babansu ma sai faÉ—a yake yi baiji daÉ—in abun ba. Amman nace in bai cika sharaÉ—in ba, da gaske sakin nata za'ayi tazo tayi zawarci kenan fa? Itace zata kasance bazawara ta farko a cikin gidannan kenan? "
"Me yasa shi NagoÉ—in baki tambayeshi wannnan ba. Tunda naga ai acan bakinshi kika ji wannan ma.
Har a ranku kunsa makarantar ma ba zata yi ba, shi yasa har ake lissafin ta zama bazawara ta farko? To saime a tunaninku zawarci ai ƙarshen rayuwane ko?
Kinga Mairamu tashi kiyi tafiyarki. Hindu dai ba zata rabu da mijinta ba. Karatu kuma ko bakya so zata yi, aka biyama wasu ma suka yi har suke ƙafafa dashi balle Hindu"
Ai itama saita fusata.
"Kamar su wa kenan kike nufi.?
" Ai kema kinsan kamar waÉ—anda nake nufi, tunda kinsan bana tsoronki ko? Kamar Æ´aÆ´an cikin É—akin ki, dama sauran kab É—akunan gidan.
Dan haka jeki tun kafin raina ya ɓaci in faɗa miki mutuwa"
Ta miƙe tana son yin zazzaga.
Sai ga Qazzafi ya shigo, ga ledar nama a hannunshi sai maiƙo take yi.
Harararshi tayi ta fita tana jan tsaki.
"Aikin banza, kai dai anya ba canjamun kai akayi ba kuwa?
Innarmu tayi tsakin itama.
"Aikin banza. Ke saka musu kaya kinji. Kai kuma nemi waje dallah ka zauna, kai mun tsaye a kai. Ni nagaji da halin Mairamu irin wannan bin diddigin da me to yayi kama?"
Qazzafi dai ya zauna yana zare idanu. Ba yau farau ba. Duk faÉ—an bala'in da za'ayi Qazzafi yana É—akinmu, dokace Baba NagoÉ—i yayi ma Innah Mairamu akan babu ruwanta da son raba Qazzafi damu, ko hanashi yin alkhairin da yaso.
Dan akwai rikicin da aka taɓa yi. Qazzafi fa da girmanshi Innarmu taje har ɗaki ta damƙo hannunshi ta dawo dashi ɗakinta. Sabida Innah Mairamu tace in ya kuma shiga saita ɗaga mishi umma.
Innah Mairamu tazo da rikici akan dole sai ya fito an asirceshi. Tace in ta isa ta shigo tace zata rabasu ta gani. Sannan umma ta daÉ—e bata É—aga ba. Da ummanta dana Akuya duk É—aya.
Kai ranar munga abinda yafi zare tsayi, saida man kanmu yai ta tsiyaya.
A ranarne Baba NagoÉ—i yayi wannnan togacciyar, shine dalilin da yasa ta sarara mai.
Ni anan na bar Qazzafi da Innarmu, da yara.
Na dinga bi lungu, lungu zuwa gaisuwa. Duk labarin dalilin dawowata yana bakunansu, sun haddace sai biyamun suke yi, masu jimami nayi, masu cewa daidai ne hakan nayi. Ni dai da idanu kawai nake binsu. Dama an sanni in magana bata gameni ba, duk girmanta bana tankawa, ko da an so in tanka É—in bana yi.
Haka aka kwana aka hantse. Baba Sojanmu fur yaƙi amsa gaisuwata, sai ƙur yake mun da idanu.
Wannan kenan