Sashe 57
Tsuron Tsirin Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yaya Jamila da sauran mata _mata na cikin gida suka tafi suma. Da izinina zasu tafi Nanno, kiyi haƙuri kinga baki da lafiya ma" Ai sai ta saka salati. Innah ta fincikeni ta dannani a mota. Furob ya fito yace. "Ma lob akwai furobilem ne. Ba da yardar mijinta dama za'a tafi da'ita ba? Kinsan ba kowa ke son wannan al'adun ba. Ibin mi to i dont lik it." "Aa furob shiga mota abunka, zanma bayani a mota. Rigimace irin ta matan karkara" Har motarmu tayi nisa, su mijinyawa na ba Nanno haƙuri. Ajjiyar zuchiya na sauke a yayin da muka hau kan titin Bauchi. Zuchiyata cike fal da tunane _tunanen abubuwan masu daman gaske. Zuchiyata tayi tauri sosai, ina girmama ƙiyayyar da dangin mijinyawa suke yi mun, ina kuma yawan hasashen abinda ya assasa tsanar, wanda a wajena sam ba dalilin da za'ayi riƙo dashi, aita cusgunamun sama da shekaru shida bane. Motarnan na garawa, daidai da yadda ƙwaƙwalwata take ta lissafe_ lissafen rayuwar baya, da wacce kuma zamu fuskanta a gaba. Har bacci yayi awon gaba dani. Awanmu Takwas da minti arba'in cur a hanya, kafin muka isa maiduguri, da gidansu mai kyau na ƴan boko, wanda babu hayaniya sam. Wannan rashin hayaniyar ya bani damar samun hutu sosai, daga ni har Azgar bamu da aiki sai bacci, da safe Innah da furob suke fita aiki. Daga ni sai Furera mai aikin Innah dattijuwar data saba da mitar Innah shekaru sama da goma suna tare, da duk wannan faɗan na Innah, dake ta kasance mai tausayi da yawan kyauta, da son shiga lamuran mutane. Saida na huta gaya, dangi suka soma tururuwar zuwa dubani, tare da yi mun barka. Duk wanda zai zo da abun hannunshi, waɗanda basu dashi sai su ƙullomun turaren wuta a kwalba su kawo mun ko humra. Nanma fa haka na tara kayan barka. Ga daɗi da ake sa Furera ta dafamun, magungunan gyaran jikina ina shansu sosai, kuma ina jin kyansu a jikina. Cikin kwana goma nayi ƙiba ni da Azgar mukai ɓulɓul. Azgar irin yarannanne da gani masu ƙiba, girmanshi sai mamaki yake bamu, lokaci guda ya soma haɗa kumatu fa. Na murje nayi wani irin kyau sosai. Furob ya kwashi manyan atampopina tela namiji akaba ya zubomun ɗunkunan da suka sake fito da martabar kayan. Tun lokacin ma teloli maza ɗinki maza suke yi banda na mata, sai ɗaiɗaiku dake ɗinkin mata. Shi wannan ma ɗan sinigal ne, kun sansu dai da iya sarrafa sutura. Saida aka ɗinka mun kala sama da goma, kuma a cikin kwanaki bakwai dake yana da yaran ɗinki, kamar kamfanine haka da suke yin ɗinkunan manyan matan masu muƙami matan ƴan siyasa, ana siya a ɗinke, akwai wani ɗinkin shadda mai haɗe da lesiri ma da Furob ya siyo mana ni da Innah Yahanasu daga zuwa karɓomun ɗinki yace ya gansu sunyi mai kyau. Muna cika kwana sha takwas sai ga mijinyawa kwatsam da yamma daf magriba. Da adireshin da Innah ta rubuta mishi, dake a maidugurinma gidanta sanannene sabida furob sanannen mutum ne sosai, kuma lekcarane a jami'ar Maiduguri, kuma yana harkar siyasa sosai fuskarshi sananniyace ga al'umma. Innah na zaune tana karanta littafin Hausa, dan tana karatu sosai, litattafanta waje ta ware musu a sib ɗinta zan iya cewa basu da iyaka. Anan na karanta wazai auri jahila, allura cikin ruwa, mata da miji, Da sauran littattafai masu koyar da ɗunbun ilimi gaya. A lokacin su Anty Bilkisu Funtua ke tashe, Ado Ahmad gidan dabino, Nazir Adam Salih, Bala Ahmad Babinlata, Balaraba Ramat, Kamilu Ladan koki. Sai ga maigadi ya doko sallama wai anyi baƙone yace Mijinyawane daga Jama'are. "Kace ya shigo, mijin Ƴatane Maman Azgar" Naji irin daɗin da bashi da abun kwatance, wannan kalmar Maman Azgar ta faranta, ta wanke, ta haskaka mun zuchiyata ƙwarai. "Maza wuce ki murzo Humra ki gyara fuskarki kafin ya shigo" Miƙewa nayi, na ɗaura mata Azgar a jikinta na wuce ciki. Humrarta mai rikita furob na murzo, na gyara ɗaurin ɗankwalina, na murza kwalli, amman ba cikawaba irin yadda Innah Yahanasu take zizarawa. A wannan kwanakin ni da kaina wallahi na sauya, kuma tabbas ashe na canja kaɗan a ƙauye. Zaman Maiduguri, da samun sababbin littattafai na marubuta masu raya Aure a Ƙasar Hausa, yasa na sake gyagijewa. Zamana nayi har saida Furare tazo ta kirawoni kana na fito. Wannan shaddar ta ranar suna, ita mijinyawa ya sako, da hular yayi shar dashi, sutura na gyara mutum sosai gaya. Sai satar kallona yake yi. Ga Innah Yahanasu na shirin miƙewa, Azgar na hannunshi. "Ki kaishi masauki, wancan ɗakin na hagu, yayi wanka, yayi sallah. Ki sameni a kicin" Tana gama faɗar haka ta wuce. Sai lokacin ya samu damar ɗagowa muka haɗa idanu. Zukatanmu fal farin ciki, sai kallonmu yake yi ni da Azgar. To taso mu shiga daga ciki, wannan bakin akwai magana tabbas" Dariya kawai yayi mun, na ɗauki buhun kayanshi, zan ɗauki babbar ledar yace ai tsarabace da yayo ma Innah Yahanasu. Furare na kira ta shiga dashi. Ɗakin da muka shiga gadone, sai kafet malala da har da talabijin da bidiyo. Muna shiga ya haɗani ni da Azgar ɗin. Dariya yayi yana kallon tsakiyar idanuna. "Rayuwata lamice tamkar miyar da babu ɗanɗano, matsawar bakya cikinta. Jina nake yi tamkar kin mun tazarar shekaru masu yawa. Gaku kun yi kyau, kun sake haske da kumari. Menene wannan sirrin? " Zamewa nayi na zaunar dashi akan gado, na zauna gefenshi. Sirrin jegone kawai. Ina samu cikakken gata sosai. Kuma kasan ma ko baka zo ba jibi zamu dawo. Sabida Innah Yahanasu zasu tafi umarah ita da Baba Furob. Shine tace zata dawo dani kafin su tafi" Ai wannan maganar ta sashi farin ciki sosai. Banɗaki na shiga na haɗa mishi ruwa a bokiti zafi akeyi sosai ruwan sanyine na tara mishi. Saida na tabbatar ya shiga banɗakin kana na fito, da Furare naci karo zata kawo kaskon turaren wuta. Karɓa nayi na shigar mishi dashi. Saina wuce ciki, Furare ta riƙe Azgar, ni kuma nayo wanka tare da alwala. Saida nayi sallah na ɗauki riga da zani na materiyar lokacin ana yin zani, da wani irin hannu mai tsayi har guiwa. Humra na kuma shafawa na yi kwalliya sama sama,na fito kai tsaye zuwa Kitchen, acanne na tadda Innah Yahanasu tana jera tuwon Ndalayi a fulas. A tire ta zuzzuba daya sha iska shine take maidashi filas. "Zuba miya a waccan kular maza ki kaima mijinki abinci, yaci kafin furob ya shigo" Miyar margi ce wacce tun safe aka ɗaura a gaushi kaɗan sai bayan la'asar aka sauke. A babban tire na jera komai na tafi na kaima mijinyawa. Na kunna tibi na saka mishi bidiyo kaset na shirin IN DA SO DA ƘAUNA shirin Ado Ahmad gidan Dabino uban marubuta ba. Na zuba mishi abincin, yana ci muna hirarmu cike da farin ciki. Lokacin sallar isha da yayi saina tafi ɗaki naje nayi sallah. Muka ci abinci da Innarmu. Muna kan ci ma furob ya shigo Shima saida yaci ya ƙoshi kafin Innah tasa nai kiran mijinyawa muka shiga falon furob yana shan shayi. Nan suka gaggaisa. "Ai dama jibi suke shirin komawa, mu zamu je Umarah. To faɗuwa tazo daidai da zama sai ku tafi tare kawai. Gimbiya gobe sai ki shiga mata kasuwa ayi mata siyayya, a siyo mata bushasshen kifi ma" Godiya nayi mishi sosai, muka fito Azgar na hannun furob ya shaƙu da yaron sosai. Nima shigewarmu muka yi ciki mukaita hirarmu ta soyayya mai daɗi, sai wajen taran dare nayi mai sallama na dawo ɗaki na kwanta. Innah Allah ya soni bata ɗakin tana wajen Furob Ko da ta kawo Azgar tayi ƙwafa. "Ai na ɗauka kina canne ince futsararriyar kawai. Ga shi shinfiɗeshi ki kashe wutar sai da safe. Gobe zamu fita da sassafe a zazzagaya dangi, ki musu sallama, sai mu shiga kasuwa" Ai kuwa haka akayi , bamu shigo gida ba sai wajajen sha ɗayan darema duniya na kwance abunta. A wannan daren Innah Yahanasu tai mun kwalimar suturunta masu riga da zani, dake rigunan irin dogayennanne zuwa cinya. Dana gwada wata ni ta wuce mun guiwa sosai, dake doguwace, sun mun yawa amman dama su a haka ake sakasu. Sai rigunan bacci, da wasu turarukan wutan, banda wanda duk gidan da muka shiga ake bani ko kifi ko turaren wuta, da kayan shayi. A wannan dare ta tayani muka haɗe duk kayanmu. Ta kuma yi mun lalle, dama an mun kitso kwananshi biyar. Washegari ana fitowa sallar Asuba muka kama hanyar jama'are. Na sha sabon ɗinki, sabuwar lafaya mai tsada, ta Innah Yahanasu ce na sanyo bata ce mun uffan ba. Ta samu irinsu har uku kalane ya bambantasu, ga sabon takalmi mai jaka, ko yau ace za'ayi bikin gida na mallaki abubuwa da yawa na ado. Hatta ɗan kunnena da sarƙa na gwal Innah Yahanasu ta karɓa ta canjomun, nayi ciko na ƙara gram uku akan na da. Ni kam ma tafiya na nisawa nayi bacci, sabida jiya bamu yi baccin kirki ba. Wuni muka yi cur a hanya, da yamma sakaliya irin dab magriba muka isa jama'are kuma a hakan Furob yace yau zasu wuce Bauchi su kwana a zangon baƙi, gobe sassafe su juya. Matasan dake ƙofar gidane suka taimaka wajen shigar da kaya. Mu kuma muka shiga da sallama. Gidan ko damƙam da mata, wai Zainab ɗin Uwatale ce ta faɗa rijiya an dai ci sa'a an cirota kuma da ranta. Shine aketa maida zance. Haka suka saba barin yarannan suna wasa a bakin rijiyarnan, ko a jikinsu. Ai muna sallama kallo ya dawo kanmu. Uwatale ta shaƙi numfashi ta cika, Nanno tayi ma Mijinyawa ƙur da idanu cike da tuhuma. "Hindu kece kika dawo, har an gama wankan ba dai arba'in ba dai ko?" Cewar Tsahare kenan. "Haba ƴarnan ba dai arba'in ba. Kwananta ashirin cib. Mijinta ne ya matsa, yaje har Maiduguri. Shine dai nace bari in kawo mishi matarshi." Inji Innah Yahanasu ranta ɗaya harda dariya. "Au dama Maiduguri ya tafi mijinyawan kenan? " "Au ke baki da labari ashe? Ai zuwanshi biyu, sunturin ya isheni, wannan soyayya daga Allah ne Da fatan mun sameku lafiya" Shafa ce tayi wannan tambayar Nanno tayi ƙwafa tare da barin