← Book details Tsuron Tsirin Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 84

Sashe 39

Tsuron Tsirin Part 3 Complete Hausa Novel · about 9 min read

"Subhanallahi Hindu, ke Hindu"
Cewar Innah Yahanasu kenan, wuf ta zare yaron daga jikin Hindu. Mijinyawane dai ya daddage ya cire kunya ya leƙo Innah na riƙe da Hindu sai dariya da guɗa take yi.
"Kaga zo maza ka taya ni. Farin ciki su ka zo nunawa, yaro na tsaka da shan umma"
Nan ya ƙaraso ya zauna, tare da soma karatu yana tufa mata.
Kan yaron suka shafa, suka shafa fuskarshi sai murmushi kuma. Shikenan iyakar abinda suka yi sai bacci ya É—ebeta. Mijinyawa ya shinfiÉ—eta.
"Shikenan Innah sun tafi, bacci take yi da zaran ta tashi shikenan"
Bata ce mai uffan ba. Shima É—ari _É—ari yake yi da'ita dan babu ko É—igon wasa a fuskarta.
Yana juyawa ta saki tsaki.
"Aikin banza da wofi kenan. In banda ƙaddara da rabon wannan yaron me zai kawo ni wannan ƙauyen da sunan wai wajen ɗiyata nazo. Kai wannan ƙaddarar tana da girma. Hindu Allah ya kawo miki silar barin wannan ƙauye"
Sum_sum_sum ya fita zuwa É—akin kayan abincinsu, nan ya shiga zurga_zurga goye da hannayenshi a bayanshi.
Dukkan maganganun Innah Yahanasu a kunnenshi tayi su. Yana tsoron ranar da dangin Hindu zasu rabashi da Hindu. Duk da yayi imanin yadda ya tsaya ya kasa barin danginshi su rabasu, itama yasan zata yi abinda yafi nashi dan ganin sun rayu tare.
Bashi da wani buri a yanzu daya wuce burin ganin ya ɗauki Hindu da ɗansu zuwa birni. Daga ranar da Mijinyawa ya sa ƙafarshi ya ɗauki iyalanshi zuwa birni. Daga lokacin zai ta da nashi tafiyar ko da sama da ƙasa haɗewa zata yi, dan yasan yaƙin basasa za'ayi da Nanno. Amman in adalci zata yi mai, babu dalilin da zaisa ta bar Mijinyawa babba ya koma birni da iyalinshi, ace shi ta hanasu komawa da nashi iyalin, Yana roƙon Allah ya dafa mishi, kuma ya kawo mishi lamarin a cikin sauƙi in lokacin ya gabata. Yana so ma ya tuntuɓi mijinyawa yaji a ina zancen ginin ya kwana.
Yana kuma so yaji, shin zai iya samu waje shi da matarshi, tun wuri gara yaji, in babu waje sai ya tanadi kuɗin haya, domin cika sharaɗin aurensu na mayar da Hindu makaranta. Ya yaya Nanno zata ɗauki wannan lamarin oho. Amman yasan ba abune mai sauƙi ba, yana jin bama abune wanda zai yiwu cikin daɗi ba. Ajjiyar zuchiya ya sauke kawai.
Muryar Yaya Jamila yaji tana rakaÉ—a mishi kira.
Da sauri ya fito, Baraka na tuƙa tuwo, Innah Yahanasu na zuba ruwan wankan jariri a bawo.
"Kai nace gyatumarka da sauran matan Babanka, da duk jama'ar gidannan basu san mun dawo daga asibiti bane? Naga babu wanda yaje asibitine, mun dawo ma babu me zuwane, koko basa farin ciki da zuwan wannan bawan Allahn ne, ko kuma al'adarkuce ta shar'anta hakan inason ji tun wuri kafin danginka da kai kanka ku ƙarashe kaini bango"
A mugun É—aure take magana, bama ka isa ka kawo ma Innah Yahanasu wani wargi bane, ba wajen bane. Gata da kwarjini.
"Basu sani ba. Yanzune dai zan je in sanar musu da dawowar tamu, sabida mun shigo ana ruwane sosai. Zasu shigo Innah kiyi haƙuri"
Ci gaba da ɗiban ruwan zafinta tayi, Shi kuma ya fita gabanshi na dokawa. Ruwafa akeyi kashirɓan saima abinda ya ƙaru, koshi mijinyawan a jiƙe yake sharkab. Haka ya shiga ɗakin Nanno, ya tadda Yaya Jamila, Yaya Salihu, da mijinyawa Babba.
"Yayi hamshaƙi tabbatacce. Inaso a gaban yayunka ka faɗamun menene dalilin da yasa ka ɗauki Hindu ka kaita ta haihu a asibiti. Ina unguwar zoman da duk wata haihuwa kusan ni na karɓeta sai Deluwa da itama ta kasance daɗaɗɗiyar unguwar zoma. Shin in ni bakwa so in karɓi haihuwar me yasa baka kira mata Deluwa ba. Wato kai komai saika nuna ita wannan matar taka tafi uban kowa kenan. Duk surukan gidannan babu wacce ranta bai sosu ba akan abinda ka aikata. Dama ai ita waccan maras kunyar ƙanwar gyatumar tata tace ko naƙi ko naso sai ta ɗauketa ta kaita asibiti. Ashe haka suka maka huɗuba shi yasa ko? Sannan ina mabiyar yaron take, ai ya kamata a birne a wajen da taku take, kusa da yaran ɗan uwanka, da kuka haifa rana ɗaya ko?"
Nanno ke magana da faɗa, ɗaga murya, da fishi duk a lokaci guda. Ɗakin yayi shiru. Mijinyawa dai baima san me zaice ba. Da Nanno ta cika, sai Yaya jamila ta caɓe itama, tana gamawa Yaya Salihu ya ɗaura, shine harda zagin Hindu da cewa gajeriya da'ita, mahaukaciya mai makarai da'ita.
"Babu mamaki ma makaran nata ne suka aureshi suke juyashi yadda suke so. Wai haukane auren mace a burni. Ko kuma a kanka aka soma ne. Naga ga yaran birninnan an aurosu sun saki rayuwarsu ta birni, sun rungumi yadda Allah yayi dasu. Ita matarka wacce irice da ba zata bari kayi komai irin yadda akeyi ba?"
Shi dai baice uffan ba. Bai kuma shirya cewa ba, to me zaice musu.
"Ni dai a madadinshi nace kuyi haƙuri ba dan naji daɗin abinda yayi ba, ba kuma dan ina goyon bayanshi bane. Zai kiyaye gaba. Amman in kuka duba itafa Hindu daga babban gida ta fito ko da a birninne. Mahaifinta da yayyunta duk sojojine. Hatta mahaifiyarta malamace ta makarantar sakandare, kamar dai ita Hindun. Ita wannan ƙanwar gyatumar tata fa ance babban hamshaƙi take aure a maiduguri. Kuyi haƙuri tunda Allah ya sauketa lafiya sai a gode. Batun mahaifa, ya riga yayi kasadar birnewa a asibiti, wai sabida kar ta kwana tayi wari. Ni shine ma babban abinda yafi damuna".
Ai Nanno sai ta tarwatse da kuka, har tana bubbuga ƙafafunta.
Yanda du suke jaddada batun mahaifarnan, zaku É—auka Azgar É—inne akace an birne da ranshi.
Wato ƙauye suma suna da nasu al'adun masu wahalarwa, yanzu menene laifi dan an burne mahaifa a asibiti, da har zai zama babbar matsala irin wannan.
"Shikenan yaro ya zama ba jikin gidan ba. Dama ita Hindu burinta shine ta rabaka da danginka. Bazan taɓa yafema wannan yarinyar ba, akan saka da tayi ka burne mahaifar jikina a asibiti ba, abadan bazan yafe ba"
Nanno ta ƙarashe da ƙyar kuka yaci ƙarfinta. Innah Dubu ce ta leƙo jin kukan Nannon yayi yawa.
Jamila ta labarta mata halin da ake ciki.
"Tabb amman wannan yaro ya faɗa hannun ƴan asiri. Yaya ai wannan asirceshi akayi. Ina mai tabbatar miki ya kamata a mai hayaƙi da rubutun da zai dinga sha. Ina wannan ba lafiya ba. Ya burne mahaifa a asibiti fa.
Kai nace zaka gane wajen daka burne, aje a tono a dawo da'ita muhallinta? Wannan da kake ji da gani umarnin mahaifinku ne fa. Mu so kake mu tsallake umarnin malam kenan?"
"Kiyi Haƙuri Innah. Bazan iya ganewa ba, da daddare na burne, kuma asibiti ba zasu yadda a musu tono a ciro wani abu da aka burne ba"
Ai ina wuta Nanno, da Jamila su saka mijinyawa.
Kallonsu kawai yake yi, yana sake ƙarfafa zargin anya shi kuwa ɗan wannan gidanne, Nanno ce da gaske ta haifeshi. Ko dai kamace kawai yayi da Mijinyawa Babba?
To ina asalin mahaifanshi suke?
Tunowa da mahaifinsu, da irin ƙaunar da yake nuna musu, shi ke kore mai zargin ba Nanno ta haifeshi ba.
Idanunshi sun kaÉ—a sun yi jawur.
Mijinyawa Babba ne yake ta ban haƙuri, da bayani.
Yaya Jamila ce ta katse mijinyawa Babba da cewa.
"Gafara dallah shashasha Hindu ta maida mutane banzaye, amman kana sake jaddada mana cewar ta fito babban gida. Ku ba daga babban gida kuka fito ba kenan. Kasan waye mahaifinmu a ƙauyennan kuwa, kana da tarihin mahaifin Nanno kakanku kuwa, har an isa a nuna mana asali, mu da sarauta ce kakanninmu. Mahaifin mahaifin Nanno mai garine kakanta. Mahaifinta mai garine, kakanmu, Babban wanta mai garine, ita kanta da Namijice da zata yi sarautar"
Kuka Nanno ta saka ta nuna Mijinyawa tace.
"Ka tashi ka fice mun daga ɗaki, kaje ni na barma Hindu, da danginta kai. Kuje ku ƙarata taci gaba da juyaka. Yaro kuma Allah ya rayashi, amman bazan ma iya zuwa barka ba"
Baki ya buɗe da zummar bata haƙuri, ta ɗaga hannunta ta kwaɗa mishi mari, tare da nuna mishi ƙofa. Babu shiri ya fita jikinshi duk a sanyaye.
A cikin ruwan ya fita har waje, kai tsaye gidansu Baraka ya wuce, Qasimu yana bakin ƙofa yana juye ruwan sama a babban duro ya hangi Mijinyawa ya shigo zauren.
"Lafiya kake tafe haka a jiƙe. Batun asibitinne ko? Ai nasan wallahi ba zaka samu sauƙi a ko inaba. Babanmu ma baka ji yadda take ta mun faɗa ba, yadda kasan nine na ɗauki Hindu na kaita asibitinnan. Cewa tayi zaka zo ka sameta ne."
A zauren ya ɗakko mishi kujera ya zauna, shima ya zauna daga dokin ƙofar Baraka sukai shiru, sai ƙaran saukar ruwa kawai ke tashi a garin baki ɗaya.
Idanu Mijinyawa ya lumshe kawai, zuchiyarshi na mishi suya, tuno farin cikin dake shinfiÉ—e a fuskar Hindu, da kuma tuno fuskar Azgar, ya tilasta mishi yin murmushin da bai shirya zuwanshi ba. Qasimu dai yana ta kallon shekara.
Ajjiyar zuchiya ya sauke, sai yaji duk damuwar ma ta kau, fuskar Hindu kaÉ—ai ta wadatar da zuchiyarshi.
"Babu komai Qasimu, duk suyi haƙuri aikin gama ya gama."
"Ni inaga ka bar musu gidan kawai, ga É—akinmu na samartaka kazo ka buÉ—e ka shiga babu kowa a ciki"
"Aa dole ana buƙatata, kasan jinjiraye da kukan dare, dole in dinga taimaka musu"
Idanu Qasimu ya zare yace.
"Wallahi ka kula, littattafan hausa da kake karantawa zasu kaika su baro, a ƙauyennan ba zasu ɗauki wannan ba"
Murmushi mijinyawa yayi yace.
"Ai addininmu ma ya riga ya koya mana yadda zamu rayu da iyalanmu. In muka duba gidan ma'aiki arrasul SAW ai kaga zance ya ƙare. Duk wani soyayya da tattalin iyali a nan ya ƙare. Kaga ba a littattafan hausa na soma karantawa ba, dan dai kai baka tsaya ka mayar da hankali a karatun bane. Kuma zan taimaki Hindu iyakar ƙarfina, wanda yake da abun faɗe Qasimu ya faɗa. Da kasan kalar cin kashin da yanzu aka gama mun, bama zaka ce komai ba.
Ni mu bar wannan zancan Qasimu. Yau yanda ake Ruwannan Balele zai yi gashin balangu da tsire kuwa?"
"Mai zai hana. Ai kasan a yanayi irin haka na damuna anfi cinikin nama da zafi zafinshi. Rumfarshi tana da kyau ko yanzu kaje zaka tadda yana gashinshi gaskiya, dan ɗazu ma na wuce ta rumfar yana ta aikin nama. Zaka siya ma maijegone kafin gobe a siyo naman ƙauri ba?"
Nan sukaita hirarsu dai magriba na kawo kai cikin ƙudurar Ubangiji sai ruwannan ya sassauta sai yayyafi, amman sabon hadarine ganga_ganga sosai a garin yau da alamu za'a sha ruwan dare.
Chapter 39 · 0% Book details