Sashe 78
Tsuron Tsirin Part 3 Complete Hausa Novel · about 5 min read
damun lakcarorin dashi, wasu su yaba da ƙwazon, yayin da wasu suke ganin iyayin nawa ai ai yawa. Hakama a ajinmu kowanne da fassararshi. Ni bana bi ma takan kowa, ni ai karatune ya kawoni, in banyi tambaya ba me zanyi to?. Gaga gaga gaga, aka shiga azumi, muka gabatar da ibadarmu cikin nutsuwa, kwanciyar hankali, abu mafi daɗi lokacin buɗe baki yadda iyali ke haɗuwa ayi buɗa baki, da kuma yadda ake tafiyar sallah a masalci maza da mata. Ana jibi sallah muka wuce Jama'are, su Uwatale ai tuni su azumi na ashirin suka tafi, kamar masu zuwa umara. Da yamma lis sai gamu a jama'are, su Shafa ana tsakar gida, naci adona da kaya na alfarma, haka ma yarana. Nan akaita kururuwan murnar zuwanmu. Bayan mun ajjiye kayanmu, muka nufi ɓarayin Nanno. Hmm Uwatale tana can ɓarayin tana damama Nanno kunu. Ni ko sau ɗaya ta amsa gaisuwata, ta kawar da kanta. Tashi nayi bayan na ajjiye mata tsarabarta, harda kayan sallah, da hijabi, da takalmi da muka yi mata. Na wuce shashena. A daren sai ga Baraka da abinci, dariya mukaima juna, mun taɓa hira babu laifi gaskiya. Washegari sai ga Halima tazo ganin Asama'u. Tayi farin cikin ganin yadda Asama'u ta koma sosai, itama muna ta hirarmu tunda mun saba sosai, kuma yanzu shaƙuwar ta ƙaru sakamakon riƙon Asama'u. Ashe ita, Tata manufar zuwan dabanne. A daranne tace ma mijinyawa tana sonshi, tunda yana riƙe da ƴarta, mai zai hana ya aureta sai riƙon yarinyar ya dawo hannunta? A daren take faɗa mai ita da auren Abdulƙadiri ma tana jin motsin son Mijinyawa duk ranar data ganshi, kuma tana so ta kasance a inuwar aurenshi. Cike da mamaki yazo yake sanar dani yadda suka yi da Halima. Murmusawa kawai nayi, to me zance ni kaza? Mijinyawa yaita faɗa fa, yanata ɓaɓatu. Daga lokacin ban kuma sake ma Halima fuska ba, har akayi sallah aka gama muka tattare yanamu_yanamu muka koma. Gashi sai ta caɓo ado tazo, ta barbaza kitson ƙari, sabida a tunaninta ai bansan mijinyawa take farauta ba. Na muku tsallake, ai saida Nanno ta titsiyeshi akan batun koyarwar da nake yi, da sunturi da yara da nake yi kullum wai ita bata so, kar mu zo da babbar sallah ace mata naci gaba da zuwa koyarwannan. To ashe tsugunne bata ƙareba. Da babbar sallah tazo banje Jama'are ba, shi dasu Uwatale suka je. Yace ƙaramar sallah kawai zan dinga binshi, babbar sallah nima inyi tare da dangina yana ganin zaifi, tunda suma suna da buƙatata. Nace mishi to, ai kuwa hakan akayi. Nanno kashe mijinyawa ta dawo dashine kawai bata yi ba, faɗa kam tayi_tayi shi babu iyaka. Wallahi ya dawomun idanunshi duk ya faɗa. Gaga gaga kamar wasa har na shiga lebul na biyu a jami'a. Baba Sojanmu sai jin daɗi yake yi, musamman in naje gida sai yace. "Hinduna ta farfaɗo, ta dawo ƴar gayenta, ƴar birni ke da ƙauye har abada, sai dai ziyara" In sha Allah Baba Sojanmu" Abunda nake cewa dashi kenan. Kuma muddin naje gida dubu biyar ɗinnan alƙawarine sai ya bani, to da naga bani dana mota, naje makaranta a ƙafa, na dawo a ƙafa sai in kai musu ziyara. Innarmu kuma tana bani dubu biyu da tarkacen kayan alawa, da biskiti na ƴan makaranta. Ana tsaka da zafin karatu Luba ta haihu. Sunturi salamu alaikum, ga babu kuɗi a hannunmu, mun biya haya a lokacin. A ƙafa da kuka sani wallahi nake niƙan gari inje duk inda zani. Tunda Luba ta haihu a ƙafa nake zuwa kusan kwana nawa. Sai ranar sunane dake na biya gida na samo wannan nera dubu bakwai da nake samowa. Ranar suna nakai mata atampopi biyu, na siya mata omo da sabulu na dubu biyu. Ina ya Allah, babu ya Allah. Ranar da Uwatale zata gane ashe jami'a nake zuwa ranar asabar da yamma, ina jan ruwa a rijiya ga hadari baƙiƙƙirin a garin. Kwatsam sai ga Alawiyya wata abokiyar karatuna kilas mait ɗina ce ma ƙarewarta. "Hindu Nagoɗi dama ashe gidanku ɗaya da Maman Zailani? Ikon Allah" Ai kuwa Alawiyya mai Rago gidanmu ɗaya, ƴar uwarkice?" Hankalin Uwatale na kaimu. "Ƙanwar mijinace ai. To ya karatun, karatu yanata zafi. Ko da yake kune gurayen aji ai gaskiya ai kanki yana ja" Dariya kawai nayi mata. "Anti Alawiyya ina kikasan Maman Asama'u?" "Ai makarantarmu ɗaya, ajinmu ɗaya muna karanta kwas ɗaya" Uwatale na kalla, sai zazzare idanu da susar kai take yi. Ina aikin girki inata tunane_tunanen abinda zai je ya dawo dan nasan akan wannan al'amari tsab Uwatale zata ko shirya zuwa Jama'are. Ai kuwa kamar da ƙasa. Anyi haka da kamar wata guda kenan. Lokacin babu mota a hannun ogan mijinyawa, bige_bige kawai yake yi. Yau tun daga Kurna har zuwa makaranta da ƙafata na dawo, bani da kuɗin motar, ni kuma bazan iya ɗaukar huƙa in huda cikina ba, shi yasa ban tambayi Yaya Zubaina ba. Abubuwan sun yi mana yawane su Azgar ma an sasu a makaranta, ga Islamiyya sun ma dena zuwa an ɗakkoma su Nana malamai har gida suke zuwa su karantar dasu, karatu mai kyau hadda suke yi na Qur'ani sosai, inajin daɗin yadda bakin Asama'u ya buɗe da karatu, Azgar kam ba'a magana in yana karatun Qur'ani muna mamaki wallahi, dake ƙwaƙwalwar da Qur'ani aka buɗeta. Ina shigowa cikin gidan da sallamata, muka haɗa idanu da Uwatale, in waiga Gefen kicin ɗina naga Nanno a zaune da jakarta ta buhu. "Ba shakka shanshani. Wata baki dena zuwa makarantar ba ashe? To ƙarshenki yazo wallahi wallahi, yau zaki sha mamaki" Na kalleta, na kalli matan gida duk mu suke kallo, Uwatale kuwa fara'a sosai a fuskarta. Mrs Bukhari.MRS BUKHARI