Sashe 1
Tsuron Tsirin Part 3 Complete Hausa Novel · about 10 min read
TSURON TSIRIN...
TSANDAURI..
HARƘA TA UKU
LITTAFIN BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI GIDAN ƘAMSHI
JAMA'A BARKANMU DA DAWOWA BAKIN DAGA💪ðŸ¼ðŸ’ªðŸ¼
Ina so nayi amfani da wannan damar wajen miƙa saƙon gaisuwa, da godiya a gareku masoyana na haƙiƙa.
Ƴan bati ban barku a baya ba, kuna Æ™ure kwament sosai, ina yinku, tabbas na san soyayya ce har ta jaku zuwa bibiyar aikin ina godiya son so💪ðŸ¼
Hindu
Suna kwance a tsakar gida magashiyyan, cikin neman agajin al'umma.
Sun shallake lokaci mai tsayi, irin lokacin da bazai kwatantu ba. Amman dai sun daÉ—e sosai kafin Allah yayi ikonshi akansu.
GIDANSU HINDU:.
Baba Sojanmu ne ya fito cikin riga da wando, yayi zanzaro, ga hula mai fesinkab ya saka, ya nufi É—akin Innah Ruwayya yana É—aura agogo a hannunshi, Innah Abida na kallonshi dan tasan kwananta ne.
Cikin shirin fita ya tadda Innah Ruwayya.
"Sai ina naganki cikin shirin fita? "
"Wallahi kuwa, akwai wani taron mata ƴan kasuwa, ƴan gwagwarmaya da zan halarta, ina daga cikin baƙin da aka gayyata, zan yi magana akan yadda ake tattala uwarkuɗi har a kai matakin nasara, mancewa kayi kafin in fita girki ai na shaida maka. Qazzafine zai kaini, motata tana gajeri har yanzu. Ina tunanin saida motarnan zanyi, Akarami yai mun ciko in sauya wata."
Kai ya girgiza yayi jim, can yace.
"Abinda za'ayi shine, muje ki rakani gidan Hindu Yahuza tunda yazo sai ya kaimu, Qazzafinma zai bi bayanmu, in muka gama abinda muke yi sai ya wuce dake shi Qazzafin, Yahuza kuma ya zai wuce dani wani taron tsofaffin sojoji. Kawai naji inason in kai mata ziyara, nayi mafarki mara kyau a kanta gaskiya da iyalanta, jiya ban yi baccin kirki ba, mafarkin yana da sarƙaƙiya"
Shiru Innah Ruwayya tayi sai kuma tace.
"To muje daga can Qazzafi ya kaini wajen taron ba damuwa"
ÆŠakinta ta rufo suka fito, daidai shigowar Yahuza. Qazzafi yana zaune abunshi a falo yana jiran Innah Ruwayya.
Innah Abida na zaune tana shan kunu ga masa taji miya shane_shane a gabanta. Innah Turai ma tana falon tanai ma Tahira kitso.
"Sannu da fitowa Janaral"
Cewar Innah Turai kenan.
"Yauwa Turai mu zamu fita. Kai Yahuza muje ka kaimu gidan Hindu ni da Innarku, Qazzafi ka biyo mu a baya kai"
Uhum Innah Abida bata ce ba, kallo wannan basu isheta ba sam.
"Tahira Æ´ar Fulani kitso akeyi kenan, ya karatun naki dai"
"Karatu Alhamdulillahi Baba Sojanmu, karatu kam yazo ƙarshe sai batun bautar ƙasa kuma, bamu san inda za'a turamu ba"
Yahuza yace.
"Gashi duk ma inda aka turaki Baba Sojanmu ba ɗaga ƙafa sai kinje, shima ilimine ni a Taraba nayi nawa, kuma na haɗu da mutanen arziki acan sosai, shima ilimine mai zaman kanshi, bawai mutum ya ƙunshe kanshi yace sai a garinsu shi zai yi bautar ƙasa ba. Qazzafi a Fatakwal yayi nashi, shima haka yaje ya gamo ya dawo"
Dariya Baba Sojanmu yayi kawai, tare da sa kanshi bai ko kalli Innah Abida ba, rikici take ji, jiya saida allurarshi ta sojoji ta motsa ya kusan raba dare yana turanci ma manya_manya, fitina take ji ƙaƙas.
Innah Ruwayya da Baba Sojanmu duk motar Yahuza suka shiga, Qazzafi na biye dasu a baya, ya dai fahimci gidan Hindu za'aje.
Suna tafe a hanya Baba Sojanmu na hirar barikin sojoji da Yahuza, yana shaida musu a shekarun baya lokacin mulkin soja irin daɗin da akaji, da irin aikin da su suka yi haiƙan, da kuma irin kwantar da tarzoma da aka tutturasu har zuwa wasu ƙasashen ma, ya zaga Najeriya sosai da sosai shi yasa yake da wayewa mai yawan gaske.
Da wannan hirar har suka isa ƙofar gidan Hindu. Babban abinda ya basu mamaki ganin get ɗin gidan a buɗe shine abu na farko na al'ajabin da suka soma karo dashi.
Na biyu kuwa shine suna danna hancin motarsu suka hango Hindu da Azgar a yashe a ƙofar shiga cikin gidan, ga akwati babba da jaka yashe shima.
Motar Qazzafi bata samu shiga ba, a waje ya ajjiyeta ya fito da sauri.
A guje suka fito a motar, Innah Ruwayya ta shiga jijjiga Hindu wacce bata ko motsi, jikinta ya sandare sosai ta zama kamar itace. Qazzafi yayi kan Azgar shima a sanƙamen yake, yana jijjiga yaron, yana kallon Hindu Innarmu na jijjigata.
"Yahuza a sasu a mota mu wuce asibiti kawai dasu maza. Maza mu wuce asibitin cikin barikin Bukavu (Armed forces Specialist Hospital Kano)
Cikin gaggawa asa kasa su Hindu a mota. Azgar na cikin motar Qazzafi, Hindu na cikin ta Yahuza.
Innah Ruwayya ta shiga cikin gidan tana kwaÉ—ama Sabira kira jin shiru, ba Sabira ba Mijinyawa ya tilasta mata fitowa, tare da kulle gidan suka fice Yahuza ya dawo ya rufe get É—in gidan suka wuce kai tsaye asibiti.
Dama asibitin cikin bariki suke amfani dashi a gidan, duk da ritayar Baba Sojanmu, kuma yaran sun yi girman da babu inshorar lafiya a kansu. Amman ana samun lukawa ta musamman, da magunguna masu kyau a asibitocin sojoji.
"Kinga inata neman wayar Mijinyawa bata shiga kwata_kwata, kuma basa ce mun suwich ob. Allah yasa lafiya, duk da bai yi kama da lafiyar ba. To ita Sabira ko tana tare da ubanne oho"
Innarmu tace da Baba Sojanmu.
"Kaci gaba da gwadawa ko Allah zaisa a dace. In bata shiga ba, zuwa anjima sai a kira abokin tagwaitakarshi ai."
Dukkaninsu hankalinsu baya tare dasu sam, a haka suka isa Asibitin Innarmu na bayan mota tare da Hindu. Qazzafi shi kaÉ—ai aka bari da Azgar tsabar ruÉ—ewane kawai.
Nan da nan aka basu gado tare da cike_ciken duk daya dace ace anyi. Suna zaune a falon jira basa iya cewa uffan, sai Yahuza dake ta faman waye_wayenshi da jama'arshi.
"Baba Sojanmu nace akwai wani abun da za'a kawo muku daga gidane? Dan da dukkan halamu yadda muka kawo su Hindu asibitinnan dole gadone ma za'a basu gaskiya. Kuma da gani ba lafiya, kai ina babu lafiya wani babban abu ya faru. Innarmu wai baki lura da akwatuna a tsakar gidan Hindu ba, gashi ba Mijinyawa, babu motarshi, Sabira ma bata ciki. Kuma yaran Hindu daga gida sai makaranta, ko can gida kaÉ—ai suke zuwa"
"In naga Akwati sai me Yahuza? Ya yarinya tana halin rai kwakwai mutu kwakwai amman kana kawo mun wasu irin maganganu marasa kan gado, ko dan dai ita Hindu burin kowane yaji matsala a gidanta. Abu shekara sama da ashirin an kasa zubar da makaman yaƙin haka? Ka fita idanuna na faɗama"
Cikin fishi take maganar, a fuskarta babu wargi. Amman a hakan Yahuza yace.
"Wallahi ba haka bane ba. Hindu ai ƙanwatace ta jini, abinda duk ya sameta ni ya sama fa. Ba abinda kike tunani bane"
Ya ƙarashe murya ba kuzari.
Baba sojanmu dai sai kallonsu yake yi, ya harɗe hannayenshi du biyun a ƙirjinshi yayi kurum. Qazzafi shima yayi shiru baya iya cewa uffan, zuchiyarshi sai zillo take yi mishi.
Yahuza yace da Baba Sojanmu.
"Ni zan tafi, ko abincine sai a kawo, zan sanarma su Innah"
"A, a da dai ka barshi, Hindu ai tana da miji shine a haƙƙu ya sa a kawo mata abinci. Jeka uzirinka Yahuza shikenan"
Cewar Baba Sojanmu da yake sake kwada lambar mijinyawa. Innarmu kuma tana waya da Saratu ne akan dai batun Hindu da Azgar, tana sanar mata ta faÉ—ama sauran Æ´an uwan nata. Kuma ta tawo musu da dadduma, da abinci, da ruwan zafi.
Yahuza ya saka kai ya fita, yana ma Innarmu magana tayi biris dashi. Baba sojanmu yayi mata murmushi na ƙauna tare da ci gaba da gwada lambar mijinyawa.
Har su Saratu da Rayya suka iso, lambar mijinyawa bata shiga. Har likita ya kirasu Baba Sojanmu, da Yaya Saratu, da Qazzafi ne suka shiga.
Ananne yai musu bayanin dukkansu suna cikin wani hali gaskiya.
Shi dai Azgar hawan jinine ya kamashi kuma jinin nashi ya hau sosai. Ita kuma Hindu ana kan bincike tukunna. Amman duk an musu allura suna bacci, kuma ana ƙara musu ruwa.
"To shikenan likita mun gode sosai. Da fatan dai babu damuwa zamu iya shiga duk mu gansu? "
"Eh sir. Zaku iya shiga ku gansu, amman kar ayi wata hayaniya a kansu, ko doguwar magana haka"
Tunda suka fito suka sanarma Innarmu, tasan akwai matsala jikinta tabbas ya bata matsala. Kuma tabbas ita Hindu ciwonta bana asibiti bane duka, dole akwai buƙatar a karɓo mata rubutu a shasshafa mata.
To amman abinda duk ya ɗaure ma kowa kai menene haɗin saurayin mai shirin zuwa bautar ƙasa da hawan jini, tunda shi galibi ciwone da damuwa, da tashin hankali ke haifar dashi. Tambayar da dukkanninsu suke ma kayukansu kenan, gasu a tsaye a gaban gadon Azgar, wanda lokaci guda ramarshi ta fito, idanunshi a faɗe ga busassun hawaye a gefen idanunshi na hagu.
"Allah ya basu lafiya. Innarmu an sanarma Æ´an gida kuwa, ko in faÉ—a a zaurenmu?"
"Hmmm ana takai wa yake ta kaya. Duk da nasan Yahuza konfam ya faÉ—ama Uwarshi, nunawa dai zata yi bata sani ba. Ki sanar a zauren kawai. Baba sojanku kuma ya sanarma da iyayenku maza É—azu"
Yaya Saratu tace.
"To Allah ya kyauta. Yasa muji alkhairi. Gashi wayar mijinyawa bata shiga har zuwa wannan lokacin. Ni ca nayi ba mamaki ko tafiya jama'are suka yi shi da Sabiranne? "
Rayya tace.
"Nima nayi zargin hakan. Tunda sun taɓa tafiya tare lokacin waccan baƙar kadarar Asama'u na matsayin ƴar Hindu, da'ita aka haɗa aka tafi. Shine dalilin da yasa wayarshi bata shiga babu shakka. In ya samu nutsuwa zai kira, sai dai inje gidan in ɗakko wayar Yaya Hindun mu riƙe, Azgar dai wayarshi tana hannun Yaya Qazzafi."
Ajjiyar zuchiya Innarmu tayi. Duk da ma dai hankalinta bai kama hakan ba sam. Amman tana ji inama Allah yasa hakanne. To in ta tuno akwatuna da suka gani a tsakar gidan, da get da suka tadda a buɗe, tabbas wani abunne ya faru wanda bazai ma zukata daɗi ba. Tana fatan Allah yasa ba zaman bane ya ƙare ba. Dan in zamane ya ƙare shikenan magana ta ƙare, akwai masu zuba ruwa a ƙasa da yawa su sha.
To amman a lokacin da ya auri Asama'u da zafi zafi basu rabu ba, sai yanzu kwatsam, ko dai wani abunne ya kuma faruwa, ko kuma akan gidanta ne rikici ya haɗasune, ko dashi, ko da uwarmijin tunda dama taƙi jinin Hindu.
Muryar Yaya Saratu ce ta dawo da'ita cikin hayyacinta.
"Kuje Innarmu ni sai in zauna dashi, Rayya ta zauna da Hindu, Qazzafi ya kamata ya tafi shima, ya tafi daku ma ke da Baba Sojanmu, tunda duk an gaggama komai ku tafi gida kawai."
Shigowar Rayya da Baba Sojanmu ne yasa suka juyo shi dama a wajen Hindu yayi zamanshi, shi da Qazzafi, lokacin ne ya shigo duba Azgar É—in.
"Saratu mu zamu tafi akwai yaron da zai mayar damu gida. Nayi _nayi da Qazzafi yazo ya mayar damu gida. Yaronnan yaƙi, yace bazai iya tafiya ya bar Hindu a halin da take ciki ba. To yana da gaskiyarshi in akayi la'akari da irin shaƙuwar dake a tsakani. Bayan la'asar ma zo da iyayen naku duka. Kuci gaba da tirai ɗin lambar shi Gawata, nima zanci gaba da gwadawa, in bata shiga ba har yamma, to sai a tura Qazzafi yaje can tsohon gidan nasu, ya sanarma buyunshi halin duk da ake ciki, anan zamu ji labarin shi mijinyawan da Sabira suna inane.
Ibin do inaji a jikina akwai furobilem babba. Ruwayya muje ko?"
Tafiya suka yi suka barsu cike da alhini.
Rayya da Zubaina, da Qazzafi, suke wajen Hindu, Yaya Saratu tana wajen Azgar tana tubkewa da warwarewa, amman ta kasa tuno menene matsalar, ga dai matsala tana gani tasan akwai. Ga yaro ƙarami ya kamu da hawan jini.
"Hmmm Asama'u. Wai ka reni macijiya a gidanka, ya girma ya haɗiyeka kai da zuriyarka. Ta ina Asama'u zata samu farin ciki da nutsuwa a duk ma inda take. Ohh ni Saratu Azgar da hawan jini, yaro mai haƙuri da tausayi kamar ba Hindu ce uwarshi ba, tamkar ni na haifeshi. Allah ka kawoma wannan ahali taimako"
A É—akin Hindu kuwa, Qazzafi yana tsaye idanunshi akan Hindu, sai kallonta yake yi yana mayawa.
"Zubaida bana jin lafiya. Jikina yana bani tamkar Hindu lokacine yayi da zata zama tawa. Ina ji a jikina tamkar rabuwa suka yi da Mijinyawa gaskiya. Ga kuma a halin da muka je muka taddasu, ga akwati da jaka a yashe a ƙasa. Wayar Mijinyawa bata shiga, ga Sabira ba'a ganta ba.
Kai ina zuwa bari kawai inje tsohon gidan nasu, inji menene yake faruwa ai ba zasu rasa sani ba, kuma lallai inaso inga Mijinyawa."
Yana gama faÉ—in haka ya fice a mugun fusace.