← Book details Tsuron Tsirin Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 74 OF 84

Sashe 74

Tsuron Tsirin Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Haka dai naci gaba da gudanar da rayuwata ni da yarana a gidanmu.
Kullum Innarmu taza je aiki ta dawo ta iskeni.
Zaman gabaki ɗaya ya isheni, ya gama gundurata. Gashi ni bana zuwa ko'ina ina gida a ƙunce.
A gidanma iyakata falo, falonma saida Innarmu suka yi ta sosai da Innah Abidah.
Da inna fito sai ta hau labarin abinda ya faru, ita kaÉ—aifa taita dariya. Ko ta fita babban tsakar gida tasan yadda zata yi dai har sai ta sanarma jama'ar gidan ai gani a falo.
Su kuma suita gilmawa, ko su shigo wai tambayar wani abun, ko kuma sun zo wajen Innah Abidan dai, musamman Innah Mairamu.
Ita kam in ta shigo kai tsaye dani zata ta maida mun yadda akayi, da irin zanan da Mijinyawa ya sha. Rikicinnnan saida yaje har kunne iyayenmu maza, dan ba ƙaramin zazzaga innarmu tayi musu ba ranar, anyi ɗauki babu daɗi sosai, ta zazzagar da buhunhunan maganganu sosai.
Ina ya Allah babu ya Allah, lokaci yana ta shurawa dai, Asama'u ta saba a cikin gida, ta sake da Innarmu da Baba Sojanmu. Ita da Azgar ai ko muryarshi suka jiyo da gudu suke ficewa.
Gashi dama kullum zai shigo musu da Æ´ar tsaraba.
Watarana har dani za'ayoma tsarabar ɗan abun ci, ko abun sha haka. Wataran kaza ce zai miƙo mun gashasshiya da wata damammiyar fura mai lafiya.
Na yi ƙiba, kuma nayi haske sakamakon zaman waje ɗaya.
Kwatsam da daddare rannan sai ga Baba Sojanmu ya shigo. Lokacin ina zaune idar da sallata kenan, ina sauyama Asama'u kaya, zuwa masu sauƙi, bacci ya soma zuwa, tana ta ɗan kukakkakin rigima.
Ɗakinmu ya leƙo.
"Ruwayya mijin Hindu ne yazo. Nagoɗi ya buƙacemu ni dake a falonshi. Muje ko?"
Miƙewa Innarmu tayi bayan ta amsa.
Lafaya ta naÉ—a, ta É—auki Asama'u suka tafi tare.
Ajjiyar zuchiya na sauke.
Alhamdulillahi yau dai zan kwana a ɗakina. Nagaji, duk yadda gidanku ya kai da daɗi, ko muƙami. Gidan mijinki duk ƙasƙancinshi yafi miki. Ina nufin gidajen da akwai nutsuwa da fahimtar juna, soyyayya, tausayi mai ƙarfi, sadaukarwa a tsakankaninsu. Ba ko wanne gidan miji ke fin na ubaba, kafin kuce idanunane suka rufe da soyayyar mijinyawa ehe.
Dukkannin saƙwannin da Luba take turomun daga Mijinyawa, babu wanda ya sani, a tsakankaninmu mu huɗu ya tsaya kawai.
Kuma dangane da barin kayana a jama'are. Da kuma kamamun gidan haya, da zubamun wasu kayan da nace mijinyawa yayi salin alin.
Wannan sirrinmu ne, ƙila Qasimu ya sani. Amman ni ta ɓangarena ban kasance mai faɗan komai ba. Cikina na iya shanye abubuwa da yawa, bana jin wai saina fitar nake samun nutsuwa. Ƙirjina na da faɗin adana magana abadan, ko na wani lokaci mai tsayi gaskiya. Kuma ni na ɗauki rayuwar aurena sirri babba.
Innarmu babu abinda take sanarma danginta, na game da dukkan abinda ya taɓa rayuwar aurenta. Face abinda tasan na farin ciki ne zallah.
Hakan ya wanzar da girmamawa, farin ciki sosai.
Kusan halinta da kyau na É—ebo, komai shanye abunta take, ta nema ma kanta mafita da kanta, ta koya mana tsaiwa ma kanmu a gidan aure, ba kowa bane zai shigo rayuwar aurenki da sunan ya gyara miki gidanki, ko zamantakewar ba. Ta koya mana shanyewa da haÉ—iyewa sosai. Duk da ta kasance macen da bata barin takwana, amman ba komai take tankama ba.
Anan ni da ita hannun rigane, ni Hindu ba karta kwana ba. Tayi shekaru ma bana tankawa, haka kuma nake ni.
Su Yaya Saratu aka barma wannan halin, shiyasa ake yawan rikici dasu na famili. Kafin kuji muryar Hindu kam da wahala. Ni in tankawa kake so inyi, to bafa zan tanka ba, kome za'ayi.
Amman in kuma nayi ra'ayin tankawa babu É—ar a lamarina.
Bance ni da Innarmu akan daidai muke ba, sai dai kowanne É—an adam da yadda yake tafiyar da rayuwarshi. Ban kuma ce mu bama kuskure ba, bance abu baya shige mana duhu ba.
Aa a fahimci Hindu, a karɓeta da halinta.
In mutum ya kasance da tsaurin ra'ayi mutane ne suke kallonshi tamkar ya mayar da kanshi gwani na gwanaye, alhalin shi ba haka yake nufi ba.
Kawai abinda irin Hindu suka sani shine, zan iya samun mafita ba saina bayyana halin da nake ciki ba. In raina ya ɓaci nafi zaɓan in yi shiru, in na gama rufewa nake yi, bana kuma buɗewa.
Zan iya tunani in É—auki abinda ni nake ganin ya dace dani, ko da wasu zasu kalleshi a matsayin kuskurene. Baya damuna yawan cece kucen Hindu kaza, Hindu tayi kaza.
Miƙewa nayi da sauri_sauri na gyara fuskata na sauya kaya, na zauna ina jiran a kirani in fito.
Kunji wani ƙarfin hali ko?

Mijinyawa:.

Mijinyawa na gurfane a falo, Azgar na cinyarshi, yama cire mishi hularshi yana wasane da'ita.
Baba NagoÉ—i yana zaune a kujera.
Sai ga Baba Soja da innah sun shigo.
Asama'u ta sauke kusa da Mijinyawa, tayi saurin zuwa wajenshi.
A tsanake Mijinyawa ya sake shaishesu.
Sai kuma falon yayi tsit na wasu É—an lokuta.
Baba NagoÉ—ine ya katse shirun ta hanyar cewa.
"Sai kayi mana bayanin abunda ke tafe dakai, muna saurarenka"
Firit Innah Mariamu ta fito ta fita waje.
Baba NagoÉ—i ya girgiza kanshi.
Zata kuma shigowa yace.
"Mairo jeki can wajen Abidan ki zauna in mun gama kya dawo"
Zata yi magana ya É—aga mata hannu cikin rashin wargi, dole ta juya ta koma.
"Dama batun tarewarne nazo."
"Can gidan É—an uwan naka kenan ko? To yaushe ka tsayar ranar da za'aje a kwaso kayan nata, da kuma tariyar? "
Mijinyawa yayi gyaran murya yace.
"Ai komai ya kammala, kayanta duk suna gidan na kwaso, harma an jejjera mata. Sannan gidan É—an uwan nawa bai samu ba, sabida inda zamu zauna É—in ginin bai kammalu ba. Shine na kama haya nan kusa dashi"
Sai ya ja fasali a wajen.
Baba Soja yana ji baice uffan ba.
Innah tace.
"To masha Allah, Allah ya sanya alkhairi"
Falo ya É—auki shiru. Baba NagoÉ—i yace.
"To yaushe kake so a rakota?".
Kai ya kuma sunnewa kafin yace.
" Dama nazo ne in É—aukesu mu koma yanzu, tunda duk an gaggama komai"
Baba Soja yayi murmushi kawai.
"To Janaral kaji abinda yaro yace. Ke Ruwayya sai ki sanar da Hindu ta shirya ta fito ko?"
Innah tace.
"Inaga ya dai bari zuwa kamar jibi haka, in mun kammala kintse kintsenmu na mata, sai yazo ya É—auketa"
Baba Soja yace.
"Wa yace miki yanzu Hindu zata koma gidanshi wai? Ba zata koma yanzu ba wannan shine gaskiya"
Baba NagoÉ—i ya kalleshi yace.
"Kamar ƙaƙa kuma sai yaushe kenan? "
"Sai admishon ya fito an biya kuÉ—in rijistireshon in sha Allah, sannan zata koma, wannan shine dahir a wajena. Yanzu fom kawai fa aka siya, ko jamb É—in bata rubuta ba"
"Janaral nace ko boko ya taɓa maka kaine anya kuwa? Taya zaka riƙe mishi mata da yara har tsawon wannan lokacin? Bazai yiwu ba kaji na faɗa maka. Ruwayya a kirawo Hindu tazo su wuce. Dan Allah bana son wata magana."
Baba Soja yace.
"Ob kos boko ya taɓani kace ko? To shikenan ni dai Hindu ƴata ce. Duk wani uziri nayi mai shekaru sama da shida, sai kawai yanzu dan nace sai komai ya kankama, kafin in mayar mishi da matarshi sai ya zama furobulem a wajenka."
"To amman ayi haka dan Allah Janaral?"
Innah tace.
"Ni ina ganin NagoÉ—i a madadin ayi haka, a bar janaral akan abunda yace. Kamar yaune. Kai mijinyawa kaji abunda Babanku yace."
Baba NagoÉ—i zai yi magana Mijinyawa yace.
"Aa Baba, babu damuwa zan jira zuwa lokacin in sha Allah. Kuyi haƙuri ni zan tafi.
" Babu komai, ka kuma yi haƙuri kaji. A wacce unguwar gidan yake?"
"A kurna ne"
"A kurna wacce unguwar takamaimiya, ai Kurna da girma"?
"Kurna babban layi. A cikin unguwar bakin kasuwa"
"To faÉ—i lambar gidan, ko kuma bari kuje da Tasi'u yaga gidan. In lokacin biyan rijistireshon yayi, ba sai ka zo ba, ni zanzo"
Miƙewa yayi da hanzari, ya miƙama Innah su Azgar ya fita.
Baba NagoÉ—i ya sa aka kira Tasiu dan ya kai mijinyawa gida, ya gano gidan.
Nan Baba NagoÉ—i ya tayar da faÉ—a ta inda yake shiga ba tanan yake fita ba sam.
Mijinyawa dai haka Tasiu ya kaishi har ƙofar gida ya saukeshi, ya ga kuma gidan.
shirinshi ya rushe, yaso sau ɗayane asa Hindu ta leƙo su gana ma.
Washegari sassafe sai kawai ga Uwatale da Nawata.
Sukaita ƙwanƙwasa ƙofa, a mugun gajiye mijinyawa ya buɗe ƙofar tare da dogewa a ƙofar ɗakin.
"Bacci kake yi ne har yanzu. Dake Hindu ta dawo dole kaita bacci."
Mijinyawa ya É—an yi dariya kawai.
Uwatale tace.
"To ka bamu waje mu shiga a gaggaisa ko?
Jiya na ajjiye muku abincin dare, baka zo ka É—aukan muku ba. Gashinan an É—umama na tawo muku dashi, bansan ko Hindu zata yadda ta ci ba dai."
Ta ƙarashe maganar tana kallon girman gidan, da kyan tsaiwar ginin, sai dai ace tsohon gidane kawai. Amman gidan ya burgeta a ina ma ta taɓa ganin gida mai kyau irin wannan itakam.
Muryar mijinyawa da abinda yake cewa ne ya dawo da'ita hayyacinta.
"Ai bata dawowa ba. Sabida bata jin daÉ—in jikinta gaskiya. Shi yasa nace a barta, magani ma aketa mata"
Ya ƙarashe zancan yana sosa kai. Ji yake kamar zasu gane zahirin abinda ya faru.
"Allah sarki. Wannan makarai suna azabtar da'ita duk yadda akayi mazane a kanta shi yasa"
"Meye haka Uwatale kike yi? "
Nawata yai saurin katseta, ta ja bakinta tayi gum.
"To Allah ya bata lafiya. In ta samu sauƙi ta dawo ma zo mu ga wajen. Ni daga nanma kasuwa na nufa"
Nan suka yi sallama da juna.
Ina ya Allah babu ya Allah, lokaci akace alƙali.
Chapter 74 · 0% Book details