← Book details Tsuron Tsirin Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 84

Sashe 43

Tsuron Tsirin Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

mai diya konguratuleshon. Amman bakya jin ciwo ko?" Aa bana jin komai. Ya hanya, kun shawo tafiya" Idanu ya kanne yace. "beri bat hanya. Musamman hanyar shigowa wannan ƙauye naku, anyi ruwa ko ina mol. Motarmu ma mol sai riƙe mana take yi. Bot wi sobaib." Innarmu ya miƙama Azgar. "Ga sabon ango kin samu. Shikenan dai hankali ya kwanta ko?" Dariya kawai tayi mai, shima ya maida mata, yana ƙare mata kallo kuma fa na soyayya duk gamu a wajen. Innarmu ce ta soma shigo da abinci, sai Luba ta miƙe ta tayata kawo kwanuka, da ruwan sha. Baba Sojanmu sai ƙarema ɗakina kallo, damu kanmu yake. Mijinyawa yana gefe a takure, a ido a ido yake kallon Baba Sojanmu. Ajjiyar zuchiya Baba sojanmu yayi. Eni way inaga sai mun yi sallah kafin muci abincin ko, kai Magawata, moda ɗinka bata san munzo bane, ni banga kowa naka ba. A tsakar gidama naga sai kallonmu akeyi. Ko akwai furobilem ne? " Kafinma ya bashi amsa sai ga Nanno, labari ya isheta. Labulena yana hannunta, ganin fuskar Innarmu, da Baba Sojanmune yasa ta shigo, har tana ɗan washe baki. "Baƙi muka yi daga burni haka Hindu, ya jikin naki. Kinga ban shigo ba, bana jin daɗine zazzaɓi ya rabkeni" "Aa baki dai samu shigowar ba dai, ko da ma da zazzaɓin. Ai ke kinsan sauran" Cewar Innah Yahanasu. Nanno sai tayi kamar bata ji ba. "Bayin Allah sannunku da zuwa, ya hanya kuma?" Innarmu tace. "Hanya Alhamdulillahi. Ashe an samu ƙaruwa to Allah shi raya. Wannan shine mahaifin ita Hindun, wannan kuma babban wansu ne" Nanno ta dubi Baba Sojanmu, ta sake kallonshi da mamaki sosai bayyananne a fuskarta. Sai ta murmusa tace. "Allah sarki. Ai wannan yanzu shi ya haifi wannan, ya kuma haifi Hindu, shine ya sako ƙananun kaya harda hula kamar tubabbe? " Ƙur Baba Sojanmu yayi yana nazartar kalamanta, sai ya girgiza kanshi kawai, kallon tausayi ma naga yana ma Nanno. Mijinyawa yayi carab yace. "E ai kinsan tsohon sojane, sojoji saida ƙananun kaya" Nanno sai ta kame bakinta tayi shiru. Yaya Sojanmu da luba suka gaisheta ta amsa. Innarmu ta miƙo mata Azgar ta sa hannu ta amsheshi, har tana mai tofin da ita kaɗai tasan me take karantawa. Innar Yahanasu kafin ma ace Nanno ta gama tofinnan, saiji tayi ta zare Azgar a hannunta. Kallon_kallone ya wanzu a tsakaninsu. Idanunsu cike dam da son mayar da martani. Ƙuta dai Nanno tayi, ba tare da ta tanka ba. "Kai ashe kana nan, dakai ake karɓar barkar ne, dan rashin kunya, ko rashin tudun dafawane" Cewar Nanno bayan ta kasa tanka Innah, saita juye akan Mijinyawa. "Eskus me, lefine dan yazo ya gurfana a gaban illos ɗinshi o wat do yu min?" "Muje masallacin ko Yaya Sojanmu, an kusan shiga sallah" A tsaye su Baba Sojanmu suka wuce, suka bar Nanno itama tana tsaye. Baba Sojanmu sai turanci yake ma Mijinyawa. "Dis kwalli yu han to ridus is to muc." Baba Sojanmu da Mijinyawa kenan. Nanno tana tsaye ƙiƙam. Hannayenta ta tattafa. "To wata sabuwa, ana wata ga wata" "Magana kike yi ne? " Inji Innah Yahanasu. Da sauri Nanno tabi bayansu Baba Sojanmu. "Allah ya kyauta. Wai lafiyar uwar mijinnan naki ɗaya kuwa, jibi abubuwan da take yi. Duka fa baya wuce akan sunga janaral da ƙananun kayane. Shima nayi nayi dashi kar yayi zanzaronnan, yace baiga daliliba, haka ya saha haka zai yi. Ina jinsu da Nagoɗi ma suna yi kafin mu tawo. Yana ce mai baisan menene hamimmancin zanzaro a boko, da kuma gidan soji ba. Allah ya kyauta. Yaha Allah ya baki haƙuri, sai kin kauda kai akan abubuwa da yawa hmmm. Hindu ce duk taja mana komai, mai haɗawa haihuwa ta riga ta haɗamu dasu." "Wai kinsan Ya Ruwayya. Matarnan tunda Hindu ta fito asibiti sam bata zo ganin jikanta ba. Babu fa wanda yazo a cikin gidannan. Sai matar wan shi Magawatan itama gulma tazo yi. Ai sabida janaral ne wallahi kinsan Allah da bata isa ta ɗauki yaronnan ba, saina mata wankin babban bargo. Ɗazu ai na bisu ɗaya bayan ɗaya nai musu sul soso da sabulu, taci kukanta ta ƙoshi, nai mata wuji_wuji dan na fuskanci bata da mutumci, kuma gaskiya na faɗa mata. Gaskiyar da ba kowa zai iya faɗa mata ita ba. In jununta rashin mutumcine, ni wuta nake fitarwa." Baki Innarmu ta taɓe, ta dubi Luba. "Luba a bani ruwa zan yi alwala kinji. Bazan iya da wannan rigingimu na familin mijin Hindu ba." Miƙewa Luba tayi ta kaima Innarmu ruwa, wai bayan gidan waje zata shiga. Tana fa fita, sai ga gungun su Yaya Jamila, da ƴan ɗakin Innah Dubu sun tawo gulma, dan ba barka zance ba. Harda Uwatale itace akan gaba_gaba Miƙa musu ɗan Innah Yahanasu tayi. "Sai yanzu kuka zo barka bayin Allah. Tun jiya fa muka dawo cikin gidannan, ai ko baku zo dan ita Hindun ba, kwazo dan ɗan uwanku dashi jaririn ko. Hakan kuna ganin ya dace kenan. Ace sai naje na sulleku zaku kwaso tsofaffin zannuwa da sunan ganin jariri da uwarshi?" "Aa ayi haƙuri Mama. Dake yanayin ruwannan da akaita zugawa jiya da yau shi ya hanamu shigowa. Ni yanzune ma shigowata gidan, shine Nanno tace yanzu itama ta shigo, ashema har mahaifin Hindun shima yazo ganin sabon jini? Gashi tubarkallah shekarau kenan" Yaya Jamila ta ƙarashe da dariya, ta saki fuskarta ƙaƙas tamkar ba itaba. "Zakiya, gafa Shekarau" Ta miƙama Zakiya, nan aka shiga karɓan karɓa, sunata yabawa da girman Azgar. Shigowar Innarmu yasa suka tsayar da hirarsu suka gaggaisa. Shigewarta ciki tayi, Luba tabi bayanta, ga ƙaton cikinta a gaba tana tutturawa. Su Baba Sojanmu ne suka shigo, to ɗakin ba ɗaukarsu zai yi ba. Dole suka miƙama Innah yaron suka miƙe. "To bari muje, ga Baba sun dawo daga masallaci" Fita suka yi, a tsakar gidan na jiyo suna gaishe da Baba Sojanmu da Yaya Sojanmu. Buhu Mijinyawa ya shigo dashi, buhun bakko biyu ciccike da kaya ya dure a gefen kujera. Yana sa kai ya fita. Yaya Sojanmu shima ya shigo da wasu kayan. "To bari a saka muku abinci kuci kuma" Innah ta zuba musu jalof din shinkafa mai bushasshen kifi, harda farfesun ƙafar sa, sai turiri yake yi. Nima ta zubo mun cikin kwano ta dure mun. Innarmu da Luba ma ta zuba musu, suka fito duk muka haɗu anacin abinci ana ɗan hira haka sama_sama. "Ai da safe jinine ya ɓalle mata sosai, gaskiya mun tsorata da harma zamu je asibiti. To an karɓo maganin tsayuwar jini a wajen uwarmijinta. Matar abokin mijin ma ta kawo mata maganin ƙarin jini. Da naso ma muje asibiti dai to, amman naga jikin da sauƙi" "No no ai dole a kaita asibiti, jini fa kikace ta zubar fa Yaha? Yana da kyau a kaita asibiti. Ni duk wannan kokoshon ɗin bana yadda dasu, yarinya ta shirya in zamu wuce tunda A Bauchi zamu kwana, sai Yayanta ya kaita Asibiti, inma gado za'a bata a bata. An ma yi ai gaggawar sallamarta a asibitin gaskiya." Innah Yahanasu tace. "Ai ya tsaya. Kuma anayin hakan sosai. In dai tana cin lafiyayyen abinci shikenan, wannan farfesun zai taimaka mata. Gashi mijin ya kawo da yawa harma baza ragowar nayi a buhu, na sake gargasawa, zan soya sama sama sai in baza a wancan fallen ɗakin." Innarmu tace. "Eh Janaral tunda jinin ya daidaitu ba sai anje asibiti ba. Akwai abubuwan dana kawo mata waɗanda zasu taimaka ma jikin nata ma. Sannu kinji Hindu? Ko bakya jin daɗin bakinki ki daure romo romon ki dinga sha yana da matuƙar amfani gaya." Baba Sojanmu dai lallai yaso aje asibitinnan, da ƙyar aka tausheshi ya aminta. Ruwan samane ya dawo , a wannan ruwan sai ga Yaya Jamila an aiko da damammiyar fura tako ji nono. Sai kallon farfesun da Luba take ƙaramun take yi, ga lafiyayyar jalob taji manja da bushasshen kifi. Haka dai ta fice tana waige. A falo muka bar su Yaya Sojanmu da Baba Sojanmu Azgar na kan cinyarshi. Yajin daddawa a bokiti mai lita goma cike Innarmu tayo mun. Yajin daddawa mai kilishi, da nama a ciki yaji magi, da daddawa. Man shanu cikin kwano mai kamar bokiti kusan lita uku. Ga kayan mata na gyaran maijego cikin bakko guda. "Wannan gumbar kullum ki dama ki sha zata yi saurin ciko dake, a kunu zaki dinga dama mata Yaha. Ko a cikin madara mai ɗumi. Karfa tayi wasa dashi sam. (Ga yadda kuma zaku haɗa taku kumbar son so domin Allah) HAƊIN GUMBAR MADATA MAI DABINO (Ta mai Jego da Gyaran Mata na musamman) Wannan babban haɗi ne na musamman domin mata masu jego, amare, da ma duk matar da ke son dawo da ni'ima, matsi, da samun ƙari na kuzari da ƙarsashin na musamman. Abubuwan da Zaki Buƙata. Garin Madata (ko Geron Mata) Kofi 2 Dabino (Busasshe) Kofi 1 (a cire ƙwallon) Kwakwa da Aya Busasshiyar kwakwa da ayar da aka soya sama-sama Kayan Ƙamshi. Kanunfari (cokali 1) da Citta dakakkiya lokali ɗaya. Garin Asuwakin Mata (ko Gyadar Mata) Cokali 2 (domin matsi da samun farin ciki. Kuyi haƙuri in kalmar tayi tsauri)Zuma ko Mazarkwaila – Domin zaƙi da ƙarin inganci. Garin Madara – Kofi 1 babban kofi. Yadda Ake Haɗawa. Gyaran Kayan. Cire ƙwallon dabino. Daka dabinon, kwakwar, da ayar a haɗesu tare a niƙa, har su zama garin laushi. Haɗa Garikan waje guda A cikin kwanon haɗawa, juye garin madatarki, sannan ki zuba garin dabinon, kwakwar, da ayar da kika daka.Saka Magungunan, Sanya garin kanunfari, citta, garin asuwakin mata, da garin madararki duka a waje guda. Idan mazarkwaila ce, daka ta ki gauraya a ciki. Idan zuma ce, zaki zuba ta ne yayin da zaki kwaba gumban. Dakawa. Mayar da duka haɗin a turmi ki daka su sosai har su haɗe jikinsu ya zama guda, kirɓawa zaki yi tamkar kina dukan sakwara, wannan ba wai aikin wasa bane, ba ƙaramin aiki take yi ba, ba ta tuƙawa a wuta bace. (dabinon, da zuma, ko mazarƙwallar, zai sa gumban ta fara dunƙulewa da kanta) Shikenan sai ki soya riɗinki ki sake cakuɗawa a ciki shikenan kin haɗa gumbarki ta mata masu aji a cikin gidanki Hajiya. Yadda Ake Amfani Da Ita.
Chapter 43 · 0% Book details