Sashe 84
Tsuron Tsirin Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
BAYAN SHEKARU..:..
Tsaye nake a gaban madubina ina shafe jikina da man kamfanin Oriplame na madara da zuma.
Cikin sauri na zura doguwar rigata Abaya ja mai taushin yadi. Baƙin agogon fata na ɗaura, na saka takalmina baƙi, jakatama haka. Ɗakin na kalla komai na zaune a muhallinshi sai ƙamshi ɗakin ke zubawa.
Ga zanin gadona mai tsada, irin mai santsinnan, a wajen Anty Zee na siya tana shigo dasu daga Saudiyya, china, dama sauran ƙasashen.
Asama'uce ta shigo da sallamarta.
Anata rawar kai yau za'a soma jami'a ko?
To Ubangiji Allah ya dafa.
Asama'u kinsan ke macece dole ki ƙara kula da tarbiyyar dana baki. Jiya nasan mun daɗe daku, ina muku nasiha ke da Yayanki.
Asama'u ki riƙe kanki, ki dinga tuna in mu bama tare dake, babu idonmu Allah daya haliccemu yana ganinki. Ki riƙe mutumcinki, ki tsare matantakarki, shine darajarki, in kika rasa baki da wata daraja, a idon duk mai daraja.
Allah yayi muku albarka, duk wata nasiha ai nayi muku"
"Ammi in sha Allah bazan baki kunya ba.
Kinga kyan da rigarnan da kika siya mun tayi mun. Ammi takalmin ma da kika siya mun É—innan? Shi na ciro zansa. Komai dai sabo zansa.
Azgar ma naga kayan da Abba ya siya mishi ya saka."
Mijinyawane ya turo ƙofar.
"Kunanan anata nasiharne, Tutar so sai kace yarannan wata ƙasar zasu je karatunnan?"
Saye yake da baƙar sut, sai rigarshi ƴar cikin fara sol, da takalminshi sau ciki irinna ma'aikatan banki, da kwallinshi a idanunshi, amman shima kwallin ya zama ɗan boko gaskiya, zirarashi yake yi baya tusawa, ga ƙamshi yana zubawa ƙirjinnan hmmm, na faɗa ku sa mun gas hahaha.
"To fito mu ci abinci, in samu in sauke yarannan kar muyi latti fa Hindu, nima kusa in makara"
Asama'u ta suri turarena, ta feffesa na dunguri kanta.
Tare muka zauna a teburin cin abinci.
Ko'ina tsab, sai ƙamshin turaren wuta, cakuɗe da ƙamshin mai soyayye.
Azgar yana ganina ya hau zuba mun abincin.
Soyayyan dankalin turawane, da miyar ƙwaai, ga biredi mai laushi, shayi duk madara.
Rayuwa kenan, komai wucewa yake yi tabbas.
Muna cin abincinnan ina ƙara jaddada musu nasihata har dai , muka kammala muka fito tare.
Azgar tuwon shinkafa miyar kuɓewa ɗanya da bushasshen kifi zaka yi mun.
Asama'u ke kiyi mun wannan lemun na su abarba da lemo, Sabira ta ƙara share falo, tasa turaren wuta. Ke Asama'u sai kiyi wanke_wanke.
Ƴar motata na hau na fita, suka biyoni a baya.
Da gudu na wucesu da aka saki danja har ina latsa musu hon. Ina ganinsu, harda Baban a dariya. Shima haka yake mun, duk ranar ni zan kaisu makarantar.
A ciki na tadda Luba karyawa ma take yi. Taliya da miyar ƙwai take ci.
Ganina yasa tayi mun murmushi mai taushi, kafin in bata amsa Mijinyawa ya kira wayata.
"Ranki shi daÉ—e kin isa ofis lafiya ko?"
Idanuna na lumshe.
Lafiya lau, kaima ka'isa lafiya, ya sabon ofis, da sabuwar kujera to?"
Dariya yayi.
"Kin ganni inata jujjuyawa akai, ofishin yana da kyau.
In akayi birek zan zo in É—akkoki kizo ki gani, sai ki shirya zuwa sha biyun rana."
Agogon hannuna na kalla.
To shikenan Allah ya nuna mana, zan kasance cinin shiri. Yanzu dai kayi aikin ka, nima ka barni in yi nawa aikin"
Da haka mu kai sallama.
"Soyayya daɗi Hindu, irin wannan maƙale murya har ina"
Dariya muka saka, tare da tafawa.
Luba kenan iyayen sharri, to yama akayi kika rigani zuwa ne?"
"Au sabida kinsan na saba latti ko
Wallahi nasiharki naji, shine dai nace in dinga zuwa ina karyawa anan kawai"
Mu ka dai tattaɓa hira, kafin kuma kowa ya kama aikinshi.
Sha biyu nayi, sai ga kiran Mijinyawa wai ya fito.
Kafin ya ƙaraso, na buɗe mana alala da kunun gyaɗa dana tawo mana dashi, muka ci da Luba.
Yana ƙarasowa, na fita na sameshi, ya kaini sabon ofishinshi na matsayin Akawun cikin gidan, na sa albarka. Ga hotona da nashi a saman teburin, muna dariya.
Gaga_gaga_gaga
A kwai wani gagarumin rikici da'akayi a gida, wanda akaita gore _goren gida su Innah Mairamu. Wannan ya É—arsamun tunanin siyan gida da sunan su Innahrmu, sabida halin rayuwa, ban siya domin in zauna ba, ban siya dan ina tunanin watarana zan shiga ba.
Babu wanda yasan da gidannan sai Luba kawai
Wannan shine dalilin siyan gida danayi.
Ba zaman kaina naso yi ba, kuma ba fito na fito nayi ga maza, ko Aure ba. Ina tunanin nayi haƙurin da ba lallai ke da kikace ina da zuchiyar kafurci kiyi ba. Na kawar da kan da ke da kike kirana mara tausayi ba zata yi ba. Nayi sadaukarwar da ke da kike ganin inada tauri, jiji dakai, nuna ni nice wanda ke ba lallai kiyi ba.
In kece ni irin hukuncin dana yanke na haƙura da mijinyawa, ko da shine Autan maza zakiyi. Ko haƙuri zaki yi kuci gaba da zaman auren naku?
Inaga iyakar abunda ya sauwaƙa daga cikin waiwayen bayan kenan.
Amman kar ku mance Asama'u É—iyatace, haihuwarta ce kaÉ—ai banyi ba.
Ni an riga da an kawoni ƙarshen tuƙewa.
Dukkannin haƙurina, tunda ni ba Annabi bace, ƴar adamce, banzo kuma a sahabiya ba. Haƙurina dole yana da iyakarshi. Ba dan ni mai kawar da kai bace, ba dan ni na jure komai ba, sai yake nufin dole in zauna saina ƙarashe da mijinyawa bane, shine zan cika ba.
Ku fahimci wani abu guda, mai haƙuri, da kawaici, bai iya fishi ba, wanda yake miƙa rayuwarshi ga masoyinshi abokin rayuwarshi da zuchiya guda, irin wanda ni nayi, a ranar daya ce bayayi, to yana nufin bayayi.
Ban iya so ba, ban iya ƙiba.
Zuchiya zata iya shekara ɗari tana ƙunsan damuwa, ko tana ƙunshe da ciwo. Kuna da labarin abinda zai iya buga wannan zuchiyar ba dole sai mai girma ba, ba dole sai anyi babban abu ba ko? Abu kaɗanma da kika raina ƙanƙantarshi ka iya kai mutum maƙurar bango, har ya buga zuchiyar tashi baki ɗaya ma.
An yi ma zuchiyata irin turin da aka riga aka kaita bangon ƙarshen tuƙewa.
Amman me kuke gani?
A labarin ina da kusakuraina irin na cikar É—an adamtaka, irin naki kema, irin nasu suma.
Ni ba ma'asumiya bace, bare ince nice akan turbar gaskiya da gaskiya ba.
Dukkanin alkhairan mijinyawa ni na zaiyano muku da kaina, ban zama mai son zuchiyar da zan ɓoye alkhairanshi dan yayi mun budulci ba.
Wannan shine ɗan kaɗan ɗin haƙurin da nayi, kaɗanne bashi da irin girman da ku kuke tunani yana dashi, domin Allah nayi haƙurin. Yanzu ma da nace bazan iya biyayya ba a rabu dani, shima domin Allah ne. Akan mijinyawa bazan halaka kaina izuwa wuta ba. Muddin naƙi mishi biyayya, to Allah fa zai hukuntani tabbas. To a wajen Hindu rabuwar tamu itace mafi alkhairi. Kefa?
Na faÉ—a tun farkon labarina cewar son da nake ma mijinyawa, ya haÉ—iye wanda yakemun. Wabillahi, shima ya faÉ—a, kuma ya sani.
A ƙarshe nake cewa da duk waɗanda suka kirani da zuchiyar kafurci, da waɗanda suka ce kwangilar yahudawa muka karɓo ni da marubuciyar, da waɗanda suke cewa a rabu da Hindu, me take son koyama mata, tana son koya musu ko wacce ta fito daga gidan aurenta ne ta koma makaranta, ko ta kama sana'a Hindu bata da aiki sai cewa kuɗin kai duniyane.
To ku shaida, mala'ikun Allah su shaida na yafe muku, nasan rashin fahimtane da saurin yanke hukunci. Shi yasa babu kyau saurin yanke hukunci, da saurin faÉ—ar magana mai kaifi akan mutum.
Ni kam na yafe wallahi.
Sannan mu sani dukkan hukuncin da zamu yanke, muyi nazari sosai a kanshi.
Yawan magana bashi da kyau. Manzon Allah SAW yace akwai alkhairi a cikin yawan yin shiru. Ka faÉ—i alkhairi ko kayi shiru.
Na sani É—abi'ace ta É—an'adamtaka bazan burge kowa ba.
Ni bana yin komai dan in burge, asalima ni kushewar mai kushe taki yake zamema rayuwata.
Bana dariya da ƙaddarar kowa bana isgilanci akan ƙaddarar kowa.
wani zaiji duk duniya Hindu ya tsana, binciken laifinta ma yake yi idanu rufe.
Akwai waÉ—anda sunasan ganin Hindu, suna ji Hindu na burgesu. Nima ina sonku domin Allah
( yau a tayar mun da dibet mai zafi domin Allah. Yau ranar faɗan dukkan wani ra'ayine, tunda kun gama haɗa dukkan hujjojinsu da kuka riƙa)
Nima anan na naɗe tabarmar wannan littafin Harƙa ta Uku, biyoni a harƙa ta huɗu dan jin dawowa asalin turban labarinsu Hindu.
Na tsallake abubuwa da yawa, muka miƙa zuwa ga hamimman da fatan kun fahimta?
Kuskuren da nayi Ubangiji Allah ya yafe mun.
Daidai mai amfani dana rubuta mata suka amfana dashi, Allah ya bada lada.
Godiya ta tabbata ga sarkinnan Allah mai girma
Ƴan bati ina miƙo saƙon godiyata gareku.
Ina miƙa saƙon godiyata a gareku Ɗakin sharhi 1 Ɗakin sharhi 2 Ɗakin Sharhi 3
Da ace lokaci zai bani dama dana lissafo muku sunayen wasu daga cikin makaranta waɗanda kai tsaye zan miƙa musu lambar yabo.
Amman kash babu lokaci, sai dai inyi kuɗin goro wajen miƙa jinjinata ga dukkan masoyan labarina, masu bibiyar aikina na faɗin duk duniya.
Ku gyara zaman jiran Harƙa ta 4 domin yadda lamurannan zasu ci gaba da tafiya.
Me kika koya daga cikin labarinnan?
Wanne darasin rayuwa kuka É—auka.
Menene abu mafi ƙololuwa daya taɓa zuchiyarki.
Zaɓi team ɗaya tak
Team Hindu
Ko Team mijinyawa kike?
Faɗi dalilin zaɓen wanda kika zaɓa, da hujjojin da kika dogara dasu.
Lallai inason dukkan masoyana su tofa albarkacin bakinsu, kuce wani abu.
Sannan idan akwai inda na ɓata muku, ku yafemun.
Nima na yafe muku.
Ina godiya son so fisabilallahi.