Sashe 38
Tsuron Tsirin Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Ina zaune Harira ta sani gaba na sama Azgar umma a baki, yana tsotsa a hankali. Amman dai da dukkan halamu babu ruwa tukunna dai.
Karɓarshi tayi ta bashi ruwan zam_zam, ta miƙo mun dabino
"Tauna ki saka mishi a bakinshi da yawu yawunki maza"
Karɓan dabinon nayi na tauna na tura mishi da harshena a bakinshi ya hau tsotsa.
"To shikenan Allah ya raya, ni da zaran dangin mijinki mata sun zo sai in tafi in sha Allah ko? "
Hakane Harira, nagode sosai da dukkan taimakonki, dama ƙoƙarinki a gareni, Allah ya bar mana zumuncinmu, ya nuna mana ranar da zan aiko miki goron gayyatar Auren Azgar in sha Allah.
Dariya muka yi dukkanmu daidai shigowar Innah Yahanasu da Mijinyawa da abincinshi É—aure a É—ankwali.
"Allahu Akbar Hindu Duwab an zama uwa, Ubangiji Allah ya amince kai madallah.
Baiwar Allah sannu, kece kike zaune da'ita?"
"Nice Mama sannu da zuwa, ga angon naki nan fari sol dashi tubarkallah"
Harira ta miƙama Innah Yahanasu Azgar, ta rungumeshi tana dariya tace.
"Barka da shigowa duniya sabon mutum. Masha Allah, gashi ƙato tubarkallah masha Allah. Hindu sannu kinji, amman da kanta ta haihu ko? "
Innah Yahanasu ta ƙarashe zancan tana mai kallon Harira, fuskarta yalwace da fara'a.
"Eh da kanta ta haihu, ai zuwa yamma ma za'a sallameta da zaran likitanta tazo. Ni kam bari in tafi kuma, sai in nazo suna kuma"
Nagode Harira sai kin zo"
Harira tayi mana sallama ta fita.
"A zubo miki abinci ko? Tare da su Qasimu muke an hanasu shigowane suna waje amma, harda Baraka ita ta dafo abincin ma"
Zubomun abincin yayi shinkafa ce, ni kuma bana son ci dama tuwone gaskiya.
"Ahh wannan bushasshiyar shinkafar mai jego? Ai bazai mata kyau ba. Ai inaga gara a nemo mata tuwo ko Uwata?"
Eh Innah bakina babu daÉ—i sam, bazan ma iya cin shinkafa ba, dama tuwone"
Na ƙarashe ina yamutse fuskata"
"To shikenan ai sai a nemo miki tuwon yanzu, bayan tuwon dame kuma kike so Hindu? "
"Ka haÉ—o mata da farfesu in ya samu, in bai samu ba a kawo iyakar tuwon, amman yaji nama asa man shanu yaji, kayi maza"
Innah Yahanasu ta faÉ—a bisa Umarni.
Da sauri ya fice a ƙoƙarinshi na son cika wannan umarnin. Yana fita saiga Baraka an barta ta shigo, dama akace kar a wuce mutum biyu.
"Sannu Hinduwa, an sauka ashe? Allah ya raya me muka samu? "
Innah tana murmushi tace.
"Gashi namijine ɗaukeshi mana, ba ƙawarki bace Hindun ƴannan? "
Ta miƙa mata Azgar, ni dai sai bin yaron da kallo nake yi, inaji kamar mafarki ma nake yi. Innah Yahanasu inta kalli Baraka sai ta kalleni, kome take kallo ohon mata, amman dai naga tana ta girgiza kanta, harda ajjiyar zuchiya take yi na damuwa.
Lokacin sallar azahar ban samu nayi sallah ba, har saida ma'aikatan Jinya suka ce su ba da waje za'ayi goge_goge shine na samu da sauri na É—auro alwala nayi sallahta a gaggauce. Uwar biyu bacci take yi, ita da gani jiki take ji sosai. Ko É—azu tana ta kukan ciwon ciki sosai.
Har zuwa lokacin ba dangin mijinyawa, babu dalilinsu har ya dawo da tuwonshi lafiyayye tuwon shinkafa da miyar kuka ta ko ji nama da man shanu harda yajin daddawa.
"Yauwa maza zauna kici da kyau kinji ko? Kar ki barshi yayi sanyi. Bari in haÉ—a miki shayi tunda naga da madara."
Mijinyawa dai yana zaune da Azgar a hannunshi. Ita Baraka Qasimu ya maidata gida. Abdulƙadiri da Mijinyawa Babbane suke waje. Ƙarfe uku aka bada izinin shiga dubiya sai gasu sun shigo sun ga Azgar. Ni dai ina kwance idanuna a rufe, naci tuwo har wuya, ina baccin dole.
Wajajen biyar na Yamma Dakta AA nafaÉ—a na zuwa ta ce ta sallamemu, amman kafinnan akwai gwaje_gwaje da zata kaini aimun.
Innah Yahanasu tace.
"To kai rakata bari ni in haÉ—a kayan kafin ku dawo.
Nace ko ta wacce hanya su Ruwayya zasu san anyi haihuwar? "
"Na rubuta ma Shehulle takadda tun safe lokacin dana koma, ai yanzu ina mai kyautata zaton labari ya riga ya iskesu in sha Allah"
Bata ce uffan ba mu dai muka fita.
"Ba gwaji zan miki ba. Maza kije Hajiya Bara na jiranku kuje ku sa hannu sai ku zo ku kama hanya."
Ai kuwa cikin minti talatin muka je, muka dawo nan muka tattare kayanmu, mijinyawa yayi shatar mota har ƙofar gida.
Yana daga cikin babban abinda ke burgeni inga mace ta tafi haihuwa asibiti. An dawo da'ita har ƙofar gida, ga bebi, ga filas ga riyo maƙota na mata barka da dawowa, tazo ta shiga ɗakinta tsab dashi shima.
Sai dai mu motarmu na tsayawa ruwan sama ya ɓalle, dama garin ya riga da ya ɗinke yayi duhu sararin samaniya tayi baƙiƙƙirin sai rugugi take yi. Bismillah damuna ta sauka, rashin ƙyan hanya, da caɓewar gari salamu alaikum.
"To wannan ruwan fa dole sai ya ɗan sassauta kafin mu fita, ga jinjiri, gashi kema jikin naki ɗanyene, wannan jego a damuna caɓe_caɓe zamu yi shi ni Yahanasu a wannan jar ƙasa. Allah mai iko wai Hindu ce a cikin wannan rayuwar hmmm. Mamaki yasa na kasa haƙuri har saida na furta wani abu daga cikin zuchiyata, da yake damuna gaya"
Ni da mijinyawa tari wannan mun kasa yinshi, A gefena take, Mijinyawa na ɗaya gefen nawa. Mijinyawa Babba, da Abdulƙari suna gaban mota.
Babu wanda yace uffan sai mai mota da yace.
"Inaga a lulluɓe yaronnan kawai gaskiya ni zan koma. Allah kaɗai yasan yaushe ruwannan zai ɗauke Baba, ayi haƙuri ina da uziri gaskiya"
Da faÉ—a_faÉ—a yake magana.
"To shikenan bari in ɗakko leda babba a cikin gidan in yaso sai a lulluɓe Innah da jaririn, inna kaisu ciki sai inzo in ɗauki Hindun"
Cewar mijinyawa da yai saurin ɓalle murfin motar ya fita, mijinyawa babba ma ya bishi a guje zuwa ciki. Bai jima ba ya fito da ƙatuwar leda Innah Yahanasu ta fito da Azgar a hannunta suka shiga ya kaita. Kafin nima yazo ya ɗaukeni.
Baraka na barandar da murhuna yake ta girka tukunya ƙatuwa ta wankan jego, tana cikin barandar tana iza wuta, ga murhu ƙarami ta ƙara a gefe girki ma take yi.
"Mai jego irin albarka an dawo, ga ruwa ya tsuge kuma. Wannan jego a damuna ƙaƙas zaku yishi."
Saida na shiga daga ciki nace.
Sannu Baraka ashe kina ta aiki? "
"Wallahi kin ganni, ai tunda na baro asibiti inanan, ruwa na É—aura, da girki. ÆŠakinma naso in gyara saina ganshi tsab, turare kawai na kunna"
"Shige daga can ciki jikinki É—anyene, ki hau gado, in an juye ruwan wanka na miki magana. Yaronnan a bashi Umma yasha sai mutsu_mutsu yake. Ruwan umman ya kawo kuwa?"
A kunyace nace da'ita.
Aa bai kawo ba tukunna'
"Bashi a haka ya kama, zai zo ne. Bari in kunce kayan dana zo dashi akwai kifi bai ƙarashe bushewa ba sabuwar gashi ne, kar yazo yayi tsutsa"
Fita tayi a guje zuwa É—akin shirgi. Ni kuma na shiga ciki Azgar na kan gado sai mutsu_mutsu yake ta faman yi. Ina zama Mijinyawa ya shigo da riyo a hannunshi, da abincin Baraka daya kawo da safe.
Ina ba Azgar Umma, shi kuma yana zaune ya tanƙwashe ƙafarshi yana cin wannan abinci, idanunshi a kanmu, sai murmusawa yake yi.
Yanzu a ina zaka dinga kwana tunda nasan innah kam sai mun yi arba'in kafin ta tafi?, bansan ko zani wankan jego ba. Amman a nawa ra'ayin zuwa wankan jego baya burgeni, baya cikin tsarin rayuwata, da zaɓi za'a bani ko? Zan zaɓi in yi zamana a ɗakinane.
"Tutar so. A ɗakin kayan abinci zan dinga kwana. Ai har mun ɗakko katifar yayi ni da Qasimu, ya taya ni mun gyara, kafin dai su Yaya Saratu su ƙaraso. Sabida in Azgar ya farka zan dinga zuwa in taimaka muku. Um bari kiga in gama in fice kar a sani a bakin duniya"
Dariya nake mai Baraka tayo sallama da gaushi rigis a kasko ta dure mun ta fice.
"To ni kam na fita sai zuwa anjima zan leƙo. In akwai abinda kike so ki faɗama Baraka"
Yasa kai ya fice, ni kuma na sauke ajjiyar zuchiya daidai da zuwan umma ina ji Azgar ɗina yana zuƙa, take zuchiyata naji tayi wani irin harbawa da mugun ƙarfi saida na runtse idanuna. Sai naji bana iya gani. Da sauri na soma kiran Innah mutanenne suka motsa, ga jariri a jikina.
A guje ta ƙaraso, tunda taji kiran tasan bana lafiya bane.