Sashe 55
Tsuron Tsirin Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Aiki suke ta ta faman yi babu kama hannun yaro. Ko ina hada_hada akeyi, gwanin sha'awa. Baraka ce ta shigo da ƙatuwar fanteka "Yauwa Amaryar ƙarni, ga angon ƙarni can a waje, yace ki leƙa duk da wajen cike yake dam ta taron maza danƙam, ƴan raɗin suna. Duk da haka yace kizo zaku yi magana" Murmusawa nayi. Na dubi su Yalewa nace. To shikenan bari in leƙa." Ɗaki na koma na sako takalmi da mayafin da mijinyawa ya sako a cikin wannan kayan fitar suna. Na saka kaina na kutsa mata na fito tsakar gidan. Lungunmu danƙam da mata anata aikace_aikace. A tsakar gidanma matane gungu_gungu anata aikin yankan ganye, da wankin shinkafa kowa dai da aikin da yake gabanshi. Anata shewa, gidan suna ya ɗauki harami, suma da sassafe koma ince asuba suke aikin abincin suna a gidan gaskiya. Sannunku da aiki" Shine abinda nace dasu, ni kallo wannan basu isheni ba, nayi waje. Inaji anata ƙus_ƙus ƙasa_ƙasa, harda masu cewa. "Wannan mai gidan gilashi ce fa. Lallai Magawata yana ji da wannan mata tashi, tana tatse duk kuɗaɗenshi hiye" Babban mamakina a wannan wajen shine. Wai me yasa son zuchiya yake damunmu musamman mu mata? Ai kowa yasan mijinyawa bashi da hali, kuma fa ansan ina koyarwa. Wai an taɓa tambayar duk zaman da muke yi mijinyawa baya aiki, wake ci da shayar damu ma kuwa? Amman a hakan babu dama mace ta fito fes sai ace sai mijinta. Wata ma wannan fes ɗin zata kalla kwaɗayi yasa ta biyo, sai ta shigo gidan kana idanunta suyi kiliya. A zaure na tadda mijinyawa cikin farar shadda sabuwa kar, harda kularshi dara mai ruwan jinin kare mai kyau. Murmushi duk muka sakarma junanmu. "Kinyi kyau sosai Maman Azgar. Kinsan Allah jiya ko runtsawa banyi ba, sabida damuwa da irin yanayin yadda kika fito babu ko takalmi. Ga irin tsinkamun da su Nanno suka yi a taron jama'a, muna ƙoƙarin rufe kanmu da bargon sutura. Kiyi haƙuri Tutar so, nasan ke me haƙuri ce ki daɗa. Zamu girbe ribar haƙurinnan. Nayi alƙawarin ko da Nawata bai bar ƙauyannan ba, mu zamu bari, ba kuma zamu kai shekara huɗu ba. Zuwa wannan lokacin ina fatan zamu tattara mu bar jama'are sai ziyara." Ya dinga bani baki, ni ko nayi shiru ina saurarenshi kawai. Can na nisa. Babu komai ai. Ita rayuwa kowa da irin tashi. Sannan ni da kai muna zaune lafiya, kuma ina fatan duk runtsi mu riƙe amanar juna kamar yadda Yarda tasa muka mallakama junanmu amanar rayuwarmu, mu riƙe wannan amanar. Na yarda dakai irin yardar da ko wacce mace bace zata iya ma mijinta ba. Zuwa anjima za'a fito muku da abinci, da zaran an kammala. Ni zan shiga cikin gida, ana raɗin sunanne? " Ai kafinma ya bani amsa muka jiyo maroƙi yana shelar. "Allah ya raya Ɗan safiyo da Azgar. Ƴaƴa tagwaye, iyayensu ma tagwaye" Sai kiɗa ya biyo baya. Fuuu Yaya Salihu ya zo ya wuce mu. "Azgar kuma, menene to Azgar ɗin" A haka ya fice yana sambatunshi. Murmushi muka sake, na juya na koma ciki abuna. Ai nan naga anata surutai a tsakar gida. "Azgar kuma wannan wanne kuma irin sunane, wannan haka kamar sunan yare? " Inji wata zabiya daga dangin Nanno. Sai wata tace. "Ai yarenne ma, anfa ce babarbariyace, ga danginta sai yare suke yi, ga lafaya kina gani duk wannan aikin tana jikinsu fa. Shine ai sunan wani nasun aka saka ma yaron ai. Shi ko irin karar nan ma bazai iyaba. Matarnan in aka sake ta cika gida da ƴaƴa wallahi saita mulki kowa, yaranta ma haka zasu taso in uwatale ba ta yi da gaske ba sai sun mulki ɗiyoyinta. Nanno ta tabka kuskure da ta yarda da aurennan tun fil azal." Ni dai banma nuna nasan abinda suke cewa ba, na sake kutsawa. A bakin ɓarayinmu na tadda Yaya Jamila da Uwatale. Uwatale tana saye da atamparta mai kaza da ƴaƴa kun ganeta ai, mai ruwan jinin kare sai kaza da ƴaƴan nata kuma mai ruwan madara. Ƙafarta caɓe da lalle duk ya hauro mata. Yaya Jamila kuma fefa lesiri ne a jikinta. Mai ruwan bula ta yi lallenta a hannu da ƙafa shar dama dai bata rabo da lalle gaskiya. Kafeni da idanu suka yi, ga bakinta a kumbure harma an baɗa mata magani, ita Yaya jamila fa tsarabar rikicin jiya. Uwatale ma naga ciwo babba a wuyanta, babba sosai. "Hindu daga ina haka. Sai muka ji sunan yaro Azbar amman wannan suna bana hausawa bane ko? Ni ban taɓa jin irin wannan sunan ba, nace sunan wani yaren naku ne hakan, ko asalin sunan kenan azbar Allah da iko yake" Inji fa Uwatale wanda a yau dariyar munafurcin ya gagara. Fuskarnan tata a murtuke wallahi ƙwallace fal guraben idanunta. Sai kallon mai gidan gilashi take yi tana mayawa, ni kaina sai nasan nayi kyau. Ko kaɗan bana hausawa bane, kema ai bai miki kama da na hausawa ba ko. Zan wuce ko? " Na dubi Yaya Jamila da ta yi bankan_bankan a hanya" "In naƙi naki matsawa, tureni zaki yi ki wuce ne, koko Yayarki zaki turo mu daku, maras kunya kin shanye mana ɗan uwa jibi shadda mai gidan gilashi ya ɗinka miki, harma da gwal a kunnenki kina jin tsoron Allah kuwa?. Yaro an ƙaƙaba mishi sunan da bamu san wanne iri ne ba, ni bama zan iya kiran sunan ba sam" Sai na ƙare musu kallo tsab. Ina nazarin abinda zance kafin na yi murmushi. Hmmm Jamila kenan. To in ban mallake mijina ba, naki mijin kike son in mallake? Naga kema mulkinki kike yi a gidan aurenki, ance sai yadda kika yi da mijinki, a wata ruwayarma cewa akayi har talla kike ɗaura mishi. Yana kai miki duk ranar kasuwa, Ke akwai tsoron Allah a lamarinki ne. Ko kina jin cikar isarki ce tasa kike juya mijin naki? In isarce to nima da ita nake taƙama da gadara, in ba ba'ita bace hanyar duk da kika shanye mijinki kika dawo dashi jani talau, shine ake ramawa akan naki ɗan uwan. Ko rabuwa nayi da ƙaninki nayi mishi tasirin da abadan bazai samu irina ba, sai dai wata kalar daban" Ji nake kamar in rufeta da duka wallahi. "Amman Hindu baki da.... " Kina ƙarashewa zaki tare haƙoranki da hannunki dan wallahi saina zubar miki dasu, dan babbar abu ta kazan... Ina daidai da zamanin ko wacce shegiya a cikinku. A tunaninku zaku hanani kwanciyar hankaline a gidan mijinane, ƙarya kuke wallahi. Kunci ƙarya kun kwana da yinwa. Ƙyaleku kawai nake yi sabida bani da lokacin wannan shirmen naku. Karkacewa nayi ƙirjina da ƙirjin Yaya jamila suka gogi juna, na matseta a bango, a lokacin saranda tayi, ina ganin tsoro a idanunta. Nayi wucewata ina ji tana ƙungumama iyayena zagi, domin batasan darajar iyaye ba sam. Anata hada hadar girke_girke, kowa ya duƙufa a bakin aikinshi. Ɗakin kayan abinci na shiga, muka gaggaisa da ƴan uwa, anata wanka, wasu kuma bacci ma suke yi hankalinsu kwance. Ƴan gida sai ƙaremun kallo suke yi. Ga wannan haɗin sabulu ya murjemun fatata a cikin kwana bakwai nayi wani irin kyau shar shar dani. "Hindu kenan irin wannan zinare haka, kai ɗinkinnan ba damane gaskiya yayi kyau kin fito shar dake." Uwarɗaki na koma nanna tadda Luba da falmata suna kwalliya, ko wacce ta ƙure adakarta. Nan nayi zamana cikinsu, su Rayya, da Fannah suka shigo muna ta hirarmu gwanin sha'awa. Muryoyin su Qasimu na ke jiyowa a tsakar gida. Da Yaya ta shigone take faɗa mana rago suka zo ɗauka za'a yanka. "Wato Luba kuna gado ko, gara ke cikine dake ita kuma Falmata bata ƙaunar aiki sai son jiki. In aka kawo hanji ku zaku gyara ayi miya dashi ai. Ga tuwo can mun ɗaura daga shi mun gama komai. Zuwa sha ɗaya muna fatan mu kammala komai. Ga hadari harya soma haɗewa. Allah yasa kar ayi ruwannan dan caɓewa gidan sunan zai yi sosai" Luba tace. "Ai ni Yaya ji nake yi ma cikina na jujjiyawa tun jiya, Allah dai yasa a gama taronnan lafiya dani. Jibi zamu koma ko? " "Jibi kan uwar haka mun ma yi nisa, duk abinda zamu ƙarashe gobe zamu kammala komai da komai, jibi sai tafiya in sha Allah" Ƴan gida da suka kwana wajen Barakane suka soma tuttuɗowa. Ashe anko suka yi mai kyan gaske sun ko yi kyau, Babu laifi in dai wankane gidan aka tarar. wajajen goman safe shiru har lokacin ba'a aiko kayan ciki ba. Sai Innah Yahanasu ta tura Yaya da Fanna suje su karɓo, ko suji me ake ciki, shirun yayi yawa. Suna fita Innah Kulu da Innah Dubu suka shigo uwarɗakina. Da ganinsu neman magana ya kawosu. "Ke Hindu wannan wanne irin sunane kuka sanyama yaro, babu sanarwa ba komai, a cikin ƙauyannan wa zai iya kiran wannan suna sabida Allah fa. Sannan kuma tun asussuba muke ta jin ƙamshi abinci, mun shigo mun tadda anata girke_girke shin ba'a sanar muku a can ɓarayin Nanno za'ayi abincin suna haɗe dana Uwatale bane, ince akan wannan batun jiya akayi duk rikicin da akayi ko? Me yasa kuke da neman fitinane wai ni kam, ayi magana kuga kamar an matsa. Da Nanno da kanta taso zuwa, jama'a ne suka tausheta. Ji wani irin sunan yare da aka ɗauka aka sa ma yaro fa sabida Allah" Yaya ce tace. "Ai ba'a hana ku yin abincin acan ɓarayin Nannon ba. Muma ai ba zaku hanamu yin namu ba Baba. Batun suna kuma ai ba Hindu zaku tambaya ba ɗanku ya kamata ku tambaya. Wai me yasa komai sai Hindu ne ni kam itace ke Auren ko ita aka aurk ne?" "Kusan abinda kika faɗa hakane yarinya. Ai itace mijin, ɗanmu shine matar, shi yasa komai ake tunkararta aji ba'asi" Cewar Innah AKulu Innah Yahanasu wacce ta shigo yanzu yanzu, wacce saida tayi magana ma muka gane ta shigo tace. "Yanzu iyakar abinda ya kawoku kenan batun sunan yaro da batun girkin suna wai? To maza ku fice mun da gani marasa kai da tunani. Kafin in sa itace duk in doddoke muku kwanyarku. Ƴan masu ƙorafin tsiya" Wannan maganar itace wasila ta wanzuwar gagarumin faɗan da wallahi tsaiwa rubutashi ɓata