Sashe 2
Tsuron Tsirin Part 3 Complete Hausa Novel · about 10 min read
JAMA'ARE:.
Komawa Jama'are ainihin labarinsu na baya.
Mun tsaya a daidai lokacin da suka gurfana a gaban Nanno bisa wa'adin da aka yanka musu ya cika. Na ko ciki ko saki da fatan kun tuno ko? Yauwa.
HINDU:.
Bayan mun zauna, sai ga Uwatale, da Yaya Salihu, harma da Shafa, ita Uwatale wai tana wakiltan Mijinyawa babbane hmmm kuji wani abu.
"Yanzu wa'adi ya cika yau É—innan, da fatan ka tawo mun da takaddar Hindu ko? Dan wallahi babu gudu babu ja da baya matsawar batai ciki ba, saki ya tabbata a kanta babu kokonto. Kai kuma aure ya tabbata a gareka, kuma tabbas babu kome a tsakaninka da Hindu abadan, ko da kuwa bayan bana numfashi ne. Tunda dai kai baka da hankali baka sanma inda yake maka ciwon komai ba.
Ga Uwatale nan juna biyu gareta a yanzu haka fa, tana neman cika gida tabb da ƴaƴa. Amman kai ka ƙare a wannan mai ciwon, sai azaba makaranta suke gana maka. Bakwa wannan ƙauyen ba kwa wancan ƙauyen"
Yaya Salihu yace.
"Abi a hankali Nanno, tunda dai wa'adi aka basu, kuma lokacin ya cika. Duk wannan tashin tashinar bata taso ba, tana da ciki ko bata dashi, mu shine abinda ya zama maƙasudin haɗuwarmu anan. Hatta su iyayen ita Tsahare abinda suke jira kenan, ko jiya munyi taɗin da Balaji wanta akan batun Auren nasu, dama cikar wa'adin."
Yaya jamila tace.
"Ai bata da wani ciki ma, yaushe makaranta zasu barta ta haihu. Ai ya miƙo takaddar mu shaida kawai"
Harna buɗe baki zan yi magana tare da yinƙurin zan miƙe. Carab mijinyawa ya damƙe hannayena, na koma na zauna. Ajjiyar zuchiya ya sauke, tare da cewa.
" Nanno ina neman afuwarki, tare da ƴan uwana baki ɗaya. Ni da Hindu muna son junanmu sosai, ba zamu iya rabuwa ba, tayi mun halaccin da harshe da haƙori bazai iya faɗa ba.
Allah ya amsa adda'ar da mukai ta yi. Allah ya azurta Hindu da samun juna biyun, ma'ana tana da ciki."
Sai yai ƙasa da kanshi, yana sauke numfashi mai sanyi.
Idanuna na lumshe kawai, nayi guntun murmushi kawai. Ban taɓa zaton mijinyawa zai amince da ƙudirina ba, tunda har muka kwana muka tashi baice komai ba. Lallai ya yarda ya shirya rayuwa tare dani. Nima babu gudu babu ja da baya kuwa. Daga duniya har ƙiyama can cikin Aljanna maɗaukakiya"
"Me kace cikin haihuwa ita Hindu ta samu, bata samu tuntuni ba sai yanzu. Ya akayi kuka gane tana da cikin, asibiti kuka je ko yaya akayi, ko dai gidoga zaka yi mana?"
Cewar Shafa wacce take riƙe da haɓa. Surukai masu fada kenan a wajen dangin miji.
Ni a nazartarsu da nayi sam ba haka dukkansu suke so ba, sakin lallai suke so, rabuwar suka zaɓa muyi shi yasa suka ɓullo mana ta haka hmm. Uwatale kuwa har guntun tsaki ta ja, tare da ɗauke kanta zuwa gefe.
Yaya Jamila tace.
"To kunyi shiru, ku amsa mana wannan tambayar mana. Yaushe aka samu cikin ne, kuma ya akayi aka gane da gasken gaske cikin ne ba ƙaton kashi ba?"
Saina ƙwaceshi ta hanyar cewa.
Ni ai macece, kuma a bisa ƙa'ida mace na gane tana da juna biyune, daga lokacin da al'adarta bata zo ba, da kuma sauyi da zata ji a jikinta. To wata uku kenan banga al'adata ba"
Wannan maganar fuskata a sake, ta cikina kuma ina jin wani baƙin ciki, ga Yaya Salihu a zaune ana irin wannan maganar. Dashi da mijinyawa kunya tamkar zasu nitse a wajen.
ÆŠakin ya É—auki shiru na wasu lokuta kafin Nanno tace.
"Shikenan ciki dai watanshi uku, ko biyu kenan za'ace.
Munanan muna ƙirge daga yanzu har wata bakwai, ko takwas, inma shekaraune dai duk za'a haifa. Kuma nanda wata biyu ai ciki shi ɗan dumane zai fito ɓaro_ɓaro. Allah ya sauketa lafiya, kun haye wannan siraɗin.
Sai ki kiyaye aiyukan ƙarfi kinga dai da yadda kika samu cikin.
Sannan wannan koyarwar sai a haƙura da'ita zurga_ zurgar tayi yawa. In kika ji kina son wani abun ci ko sha sai ki mun magana, ko Uwatale"
Ta É—an sassauto muryarta, amman fa babu soyayya ko wani jin daÉ—i a yanayinta gaskiya.
Haka dai akace ni an sallameni in tafi.
Miƙewa nayi na fice na koma ɗakina.
Saina shiga zurga_ zurga a falo ina goye da hannayena.
Tabbas wannan lamarin akwai haÉ—ari a cikinshi, to in ba'a dace da jaririn ba kuma ya zamu yi, ga ciki ance akwai iyakar daÉ—ewarshi shekara gudane rak.
Saina ƙwarara kaina akan lallai za'a samu muddin muka je gidajen marayu, zamu samu in sha Allah.
Ajjiyar zuchiya na sauke, tare da lumshe idanuna ina hasaso da yanzu shikenan ni da mijinyawa ya ƙare fa kenan. Wannan kyakkyawan ginin soyayyan akeson a rushe mana hmm.
Amman batun dena zuwa koyarwa baima taso ba, babu abinda zai mun shamaki da aikina gaskiya, bazan ma soma wannan gangancin da kuskuren ba. To inna zauna muci me? Gashi nan da wata takwas za'a tawo suna daga gidanmu. Miƙewa nayi, naci gaba da zagaye, zuchiyata cike da taraddadi.
Ina tsaye mijinyawa ya shigo da sallamarshi.
Matsowa yayi ya jawoni jikinshi muka yi shiru a jikin juna, ajjiyar zuchiya kawai muke ta aikin saukewa.
Mun jima sosai a hakan kafin ya kamo hannuna muka zauna a kan kujera tare da fuskantar juna.
"Tutar so, bazan iya rabuwa dake ba. Kinga wannan hannun bazai taɓa iya rubuta miki wannan kalmar mai raba masoyaba abadan. Ni nakine abadan, bazan taɓa iya haɗa ko wacce mace dake a zuchiyata ba.
Halaccinki gareni babbane. Duk da nasan abinda kike so mu aikata haÉ—ari gareshi, bana ma tunanin yiyuwarshi, ina tsoron ranar tonon asirinmu. Ranar da zan bar duniya, ko ke ki bar duniya. Wannan rana itace ranar fallasa da tonon asirin da zamu fuskanta mai girma.
Da ace É—an da baka haifa ba yana iya gadarka da wannan asirin na har abada zai zama.
A hakanma Hindu kisan duk yadda zaki yi mu ɓoye wannan sirrin. Gadonma inta kama a raba da wannan yaron ko yarinyar.
Amman tukunna ke kin tabbatar zamu samu jariri ko jaririya a gidan marayu, suna bayarwa?"
Murmushi nayi, na kamo hannayenshi na riƙe.
Nagode da wannan rufin asirin da kayi mana. ÆŠakko jinjiri ko jinjira a gidan marayune kaÉ—ai zai bamu damar kasancewa tare. To tunda bamu san yaushe Allah zai bamu haihuwar ba. Amman ka daure muje asibiti gobe ayi mana gwaje_gwaje da kyau dan Allah. Sannan inaso in mun shiga garin mu nemi Harira muji duk matakin da akebi dan É—aukan yaro a gidan marayu. Sabida musan shirin da zamu yi tunda wuri ko?"
Hancina ya lakace mun muka yi dariya.
"To shikenan mai juna biyu. Sai ki bi komai a hankali. Kar ki mance da yin laulayi naku na mata, ni kuma duk zan sanar ma abokai.
Batun asibiti da dai kin bari ba sai munje ba. Tunda dai ke kinje ba É—aya ba, ba biyu ba ai shikenan."
Aa kaima yana da kyau muje tare. Ai ko a maganine zasu iya ɗauramu wata ƙila. In suka sake tabbatar mana bamu da matsala ai shikenan"
Shiru yayi na ɗan daƙiƙa kafin yace.
"Allah ya kaimu goben ya kuma fishshemu jin kunya. Yasa ba kuskure zamu aikata ba."
Shi ya tattayani muka maida kayayyakin da duk na hautsina, bamu muka gama ba sai azahar. Na gaji bazan iya girki ba. Garin rogo na jiƙa mana, ya shigo mana da soyayyan kifi gammo biyu Abdulƙadiri ne ya siya yace a kawo ma mai ciki. Har ya fesa musu ina da ciki.
Abun almara har mata daga maƙota wai suka shigo suna taya Nanno barka da samun arziki. Hmm ƙauye garinsu kare.
Iyayen yarinyar da aka ajjiye da sunan wa'adi ya cika. Suma suka zo ma su nanno da rikici akan su an ɓata musu lokaci ake nufi a banza.
Ina zaune mijinyawa na ɓare mun kifi, ina ci in kora da garin da babu sikari, ba ƙuli bare gyaɗa, mukai ta jiyo rikicin su nanno.
Uwatale ce ta leƙo wai kiran Mijinyawa.
"Wai baka ji anata rikici duk a kanka ne? Ohh mata tayi ciki kuma sabuwar tarairaya sai abinda ka mance, yanzu abincinne kake bata a baki."
Dariya kawai yayi mata. Itama a sigar zolaya ta nuna tayi maganar. Amman ni a zahiri nasan da gasken _gaske take.
Uwatale manyan magulmata kenan.
Miƙewa yayi zai fita nace.
Kayi zamanka me zaka yi musu to in kaje"
Na faɗa a shagwaɓe, ba shiri ya gyara zamanshi. Ba shiri uwatale ta fice haɓa a hannu baki a wangale.
Da daddare shi da kanshi ya dafa mana wata shinkafa da mun mance da'ita sanadiyyar tattare kayane ma na ganta, da guntun taliya.
Sabida son tabbatar da ina da ciki. Mijinyawa na ba kwano yaje wajen Baraka ya karɓo mun jallof ɗin taliyar manja tako ji kifi, harda daddawa a ciki.
Ita muka ajjiye akan da safe maci, sabida abinda zamu ci ma babu. ÆŠan kuÉ—in motar dana harhaÉ—a dashi zamu je Bauchi kuma zamu je asibiti. ÆŠan abinda ya rage sai mu É—an cefana cefane kafin ayi albashi.
Muna kwance muna hirarmu cikin soyayya.
Wai ni kam da mun rabu yanzu kana cikin wanne hali sai Allah. Ni kam uwar haka gidanmu ya É—auka, ko ince unguwa ta É—auka."
"Ai ni kam da yanzu kusan ina asibiti ma cikin rashin haiyaci rai kwakwai mutu kwakwai. Kinsan Allah bazan iya rayuwa in buɗe idanu ban ganki a kusa dani ba. Kuma wai kina raye, nima ina raye. Ƙila ma har kije ki auri wani in zama tarihi a cikin rayuwarki"
Dariya na saka na shige jikinshi. Haiƙan ya nuna kishinshi akan hakan, har muryarshi na sauyawa.
Daga haka labarin ya canja salo zuwa can_ can sama jannati.
Washegari da wurwuri muka shirya.
Kunsan Allah itacen da zamu yi ɗumame babu. A haka muka ci abincin Baraka. Taliyace duk ta danƙare a cikin romo, ta yi danƙo, a haka muka tuttura. Muka kakkaɓi ruwa muka fito.
Ni a bakin ƙofar fita na tsaya ina jiranshi.
Shi kuma yaje yi ma Nanno sallama.
Ya ko daɗe, daɗewar da har saida raina yayi mummunan ɓacin da ko da ya fito yazo inda nake, Bance dashi komai ba, kai har saida muka shiga motar Bauchi kafin yace.
"Wai Tutar so fishin daɗewar tawa kike yi ne? Haba Tutar so aimun afuwa kinsan sha'anin Nanno sai a hankali. Wallahi a hakanma saida na ɓata mata ranta sosai. Aimun afuwa"
Ya kafeni da idanunshi shaƙe da kwalli. Murmusawa kawai nayi, shi kuma ya sauke ajjiyar zuchiya.
Da muka isa Bauchi kai tsaye muka tare abun hawa zuwa gidan Harira da adireshin data bani.
Sai da mu ka É—an sha wuya kafin aka gane gidan da muke nema.
Ina shiga da sallama na tadda Harira a tsakar gida tana wanke gidan.
"Ahhh malama Hindu kece a tafe. Ashe da gaske kike zaki zo? "
Dariya nayi mata muka É—an rungume juna.
Wallahi Harira kin dai ganni. Tare muke da mijina. Ina wannan hirar da muka taɓa yi dake a makaranta akan ɗakko reno a gidan marayu? "
"Naji naji"
To itace ta kawoni, ina fatan zan dace? "
Hannuna ta ja muka shiga É—akinta.
Zama nayi a kujerar dake fuskantar nata.
Wani matashi dake taje kanshi ya gaisheni ya fita.
"Kin ganshi shine yaron da gidan marayu suka bani. Kinga ya girma shekara sha uku fa."
Harira tare nake da mijina a waje. Muna son É—aukar jariri sabuwar haihuwane. Sai dai namu ya bambanta da naki. Mu zamu É—auka ne mu nuna shi a matsayin É—ana dana haifa, ba kamar naki da kowa yasan a gidan marayu kika É—akko shi ba.
Amman Harira a rayuwarnan ciki ba dan tuwo kaÉ—ai.... '
Hannunta ta É—aga mun tace.
"Ya isa malama Hindu. Ai wannan babban sirrine da ya zame mun dolon doliya in rufe muku shi. Nafa san zafin rashin haihuwa. Na kuma san zafin gorin haihuwa kin manta ne? Banfa taɓa haihuwa ba, ko ɓari ban taɓa yi ba.
Nice nafi cancanta da in rufe miki wannan sirrin. Sai dai wannan abun yana da hatsari sosai Hindu.
Ki sake tunani da kyau tukunna. Amman kafinnan ki mai iso ya shigo sai mu tattauna baki É—aya, a tsayar da matsayar da za'a cimma nasara.
Jarirai sabuwar haihuwa baƙar wuya suke yi alal haƙiƙa"
Shiru nayi gabana na dokawa da jin tace jarirai na wuyar samu. A sanyaye na fita wajen mijinyawa, nai mishi iso muka shigo tare.
Bayan sun gaisa da Harira sai tace.
Mrs bukhari ce
To sai mun haÉ—u kuma gobe in mai duka ya amince. 💪ðŸ¼ðŸ’ªðŸ¼ðŸ’ªðŸ¼MRS BUKHARI