← Book details Tsuron Tsirin Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 80 OF 84

Sashe 80

Tsuron Tsirin Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ƙaƙas fa Nanno take faɗa da wani irin ɗaga murya. Ni wallahi baƙin ciki, takaici, sun hanani cewa uffan. Hannun yaran kawai na ja zuwa ƙofar ɗakina. Ina kiciniyar buɗewa Nanno ta ƙaraso, ko gani da kyau banayi. Baƙin ciki ya makanta ganina, jina nake yi tamkar in haɗiye zuchiyata in mutu kawai. "Sannu ƴar gidan ɗan boko, ubanki mai zanzaro da hula. Eh nace sannu ko, ɗiyar ƴar boko, ke ticha, uwarki ticha. Sannu shanshani" Kallonta muke yi dani da yaran dukka. "Ko zanji saukan aradune, naga irin kallon da kike yi mun, nasan saura duka tunda wuyanki ai ya riƙa, kin dawo binni, cikin gatanki, jibi a irin gidan da kike rayuwa shirgege ma malam. Wanda ko su Uwatale da suke rayuwa a gidan kansu albarka. Ke dai a komai sai fa kin nuna kinfi uban kowa" Ƙofata na buɗe ina jin juwa. Ina buɗewa ta wuce ciki da buhun kayanta. Uwatale na shirin ratsawa ta wuce ni, na damƙi kafaɗaarta, irin riƙon da yaro kema abun wasan da ake shirin ƙwace mishi. Baya na dawo da'ita idanuna sun riga sun sauya launi, sun juya. Kada ki sake ki shigarmun ɗaki, in kika shiga wallahil ƙudrat sai dai a fito dake ranga_ranga. Ke bama yanzu ba na rantse miki da Allah duk ranar da gigi, ko hauka yasa kika kuma shigarmun ɗaki, sai dai a ɗeboki a karairaye, ko in kakkaryaki in watsoki waje" Cillata nayi taje ta kusan faɗuwa, tayi taga_taga, nayi shigewata ciki, sai naga daga Uwarɗakina Nanno ta fito. "Ba shakka irin wannan dukiya da aka narka miki yayi. Ya ƙarar da kuɗin gadon nashi akan inganta rayuwarki, da ɗanki tilo, ga ɗan uwanshi ya sai babban fili da nashi kuɗin, ya gagganɗa da tarinshi da dama ya jima yanayi, tabkeken fili ya siya. Amman dake shi shanyayyene, shine ya ƙare a kashe miki nashi gadon haka" Ina wuni Nanno kinzo lafiya?". Na gaisheta, ai ita uwace, kuma ko wanne tsuntsu kukan gidansu yake yi, ta bani tsiya, ni kuma in maida mata da arziki, abinda kake dashi ai shi kake bayarwa. Ko bata ci albarkacin komai ba, taci na haihuwar Mijinyawa. "Ƴar nema, gidan asiri da ban wuni ba nace kya ganni ne? Kujera ta samu ta zauna. Ni ko ɗaki na shiga na ajjiye jakata, ina yinƙurin sauya kaya zuruf ta shigo. " Nace ba zaki kawo mun ruwa bane bare abinci? Dama ai Uwatale ta faɗamun ko ranar da suka soma zuwa wajenki, ɗaki kika shige kika barsu, su ga marasa amfani a wajenki ko, shine nima zaki mun wannan shariyar taki? " Zan zo, zan sauya kayane. Abinci kam babu sai in na girka tukunna" Labule ta sauke, ina jiyota tana kiran uwatale. Nayi saurin zura riga na fito. Wabillahi in kika shigo ɗakinnan saina karyaki ɓaras, sai dai ayi miki ɗori, in kin ɗauka wasane ki shigo kiga yadda zanyi wasan kura dake, ba kince bakya ji ba" Ƙafa ɗaya dama ta sako, ba shiri ta mayar da ƙafarta.. "Dama dake naga Nanno ce ta kirani. Naga ai ta'isa damu mu duka ko? Amman tunda haka kika ce shikenan. Zumunci kam Hindu bakya so, ina Matar wan mijinki ni kike jujjuyam.... " Nufarta nayi gadan_gadan batai wata wata ba ta arce. Naso in samu in dira a wuyanta in jijjigata in bugata da ƙasa, inga wacce za'ayi. Nanno na tsaye tana salati nayi ficewata waje. Ruwane dai na cika kofi na kai mata, na fito na tsaida sanwar abinci. Ina kan yin girkin Nanno ta fito da buhun kayanta. Uwatale na tsakar gida fa, tana ɓarin zance sai fi'ili data buɗe sabon shafi, wai ita ƴar abu ta.. "Ke zo Uwatale muje ki kaini gidanki. Ke kuma in ɗana yazo kice mishi yazo ya sameni a gidan Uwatale, na dai faɗa miki" To zan faɗa mishi." Iyakar kenan. Dafadukan shinkafa da kifi nayi, harna gama girkinnan hankalina baya tare dani sam, na rasa wanne irin tunani zanyi ni Hindu. Matan gida gulma suke ta faman yi, basu da laifi gaskiya. A haka dai nayi duk abinda na saba. Na saka ma yara abinci suna ci, ni kuma idar da sallah na Kennan inaso in kaima Nanno abincinta dana zuba. Sai gata ta shigo, in tayi sallama to banji ba, ina mai tabbatar muku banji bakinta ya motsa ba. Ai yanzu ma nake son in kai miki abincin sai gaki kuma" "Haka fa, to ai sai ki kawo mun inci, inanan har ya dawo." Abincin na ajjiye a gabanta, na kawo mata kwano da cokali. "Wannan turaren wutan mallakan daya turniƙe ko'ina, ɗaukeshi ki fita dashi. Ni bazan mallaku ba, na sha tabara, na sha yasin. Ɗana ma da kika mallake ina roƙon Allah ya kuɓutar dashi, a hannunki azzaluma" Ɗan murmushi nayi nace. To ameen, Allah ya kuɓutar dashi" Na ɗauki kaskon na fitar, na dawo na sameta tana magana akan kifin cikin abincin, da kuma yadda taji kayan miya. Ni dai gefe na koma na ɗauki Qur'ani na soma karatu. "Wannan abinci haka, ji kifi yadda aka ɓaɓɓareshi, ga kayan miya yaji yayi baja_baja, irin wannan almubazzaranci da yawa yake. Babu shakka ni inacan ƙauye, ku kunanan miji ya ƙare a kanki, dama danginki ko munasara" In kun tanka Hindu ma ta tanka. Ni da yarana muna ta karatunmu, nasu rabi da kwata wasa, kwata karatu, amman da zarrafe ake tashi. Uwatale ce tayo sallama tare da buɗe labule, daga wajen ta zuro langunanta biyu tuwo da miya. "Ki shigo mana tsoronta kike jine, ke da kike matar wan mijinta? ' " Hmmm ca tayi in na shigo saita ɓallani. Zata aika in Nawata ya dawo ma shigo tare ai. Ga tuwonnan" Ta saki labulen. Nanno ta ɗakko tuwon ta soma ci. Ina gani loma uku tayi ta rufe, taci gaba da cin shinkafar. Wajajen bayan isha sai ga Nawata ya shigo, ai Uwatale bata iya biyoshi ba, taji irin riƙon da naima kafaɗarta ai. Bayan sun gaisa, nima mun gaisa sama_sama. Saina ɗauki Asama'una data ɓingire tayi bacci. Azgar kuma gyangyaɗi yake ta yi. Azgar ɗin Ammi zo muje ka kwanta ko?" Tashi yayi ya biyo bayana na shinfiɗesu. Inaso zan siyama Azhar ƴar katifa da zai dinga kwanciya a kai gaskiya, ya ƙara girma yaci ace ba a gado yake kwana ba. Duk ranar da za'a zuba taki, sai dai mu kaisu falo mu shinfiɗesu. Ai gara ma in siya musu ƙananun katifa kawai in dinga musu shinkiɗar a falo. Shiru nayi da tunanin jin abinda Nawata yake cewa ƙasa_ ƙasa da murya. "To muma bamu san makaranta take zuwa ba wallahi nake faɗa miki. To da zanyi mai magana. Ita Hindunce tace ma Uwatale koyarwa take yi. Sai daga baya abun ya fito. Magawata baya kyautawa ya zama jani talau, sai yadda akayi dashi. Yanzu ya dace ace Hindu ta hana Uwatale shigowa kuma a gabanki fa ko ɗar bata ji. Shikenan zumunci take so ta raba mana, bazai yiwu ace Uwatale bata shigowa wajenta ba, ita ba shigo mana take yi ba dama. Yaronnan Azgar sam bai saba da su Zainaba ba sam." Zama nayi da kyau na shiga nazartar maganganun shi, ina jin yadda nanno ta sake buɗe ruwan faɗa tana mijinyawa zai zo ya sameta. Gaga gaga mijinyawa ba shi ya shigo ba sai sha ɗaya da mintina na dare. Bari kuji abinda ya faru, sai kawai ya shigo da ledar kayan shayi da biredinshi, gongonin madara ta pick ta gari fa, da furanto na leda, da sikari mai iyali mai zaki. Ga kuma kaza gashssshiya guda ƙatuwa, da abinda ya shigo kenan. Ku faɗamun wa zai fiddani ba sai Allah ba. Inajin sallamarshi sai na fito. Yana tsaye Nanno na ƙare mishi kallo, shima da mamaki yake kallonta, amman sai murmushi yake yi. "Ungo wannan ledar kai kicin Hindu" Yayi saurin miƙomun, kafin hannuna ya isa na Nanno ya isa, ta fisge. Ta buɗe taga wannan kayan da nima bansan daga ina bane. Tunda bawai siyowa yake yi ba, rayuwarma lallaɓawa muke yi, muna adana sirrinmu muna lulluɓe babunmu. Ni ban kasance mai roƙo, ko huda cikina ba. Shi kuma daidai ƙarfinshi yake yi, bazan iya haɗa karatuna da koyarwa ba, sabida yanayin lokaci, kuma munfi karatu da safe ma. "Babu shakka, madara ƙaton gongoni haka, ga kaza muƙeƙiya, shi kake kawo mata kullum, shi yasa kuka haɓaka ƙiba ji wani haske da Hindu tayi. Ni ina can ina sharɓar miyar kuka da wake. Kura da shan bugu gardi da ƙwace kuɗi fa kenan." Ai sai ta zauna ta soma huci, shi kuma ya gurfana gabanta kanshi a ƙasa. Juyawa nayi zan koma ciki. "Dawo dan gidanku, ai kece musabbabin zuwan nawa munafuka." Zamana nayi daga dokin ƙofar mukai shiru. "Wato kai mai mata shine ka sakata a makaranta tana karatu, ni da ƴan uwanka kace mana koyarwa take yi, tunda haka ta kitsa maka kace k0? To alkadarinku ya karye, asirinki ya tonu, kun kuma ji kunya, sabida haka dole a ajjiye karatunnan, ko kuma ka sallameta ta kama gabanta. Inaji ina gani surukata bazan bari tayi zurfin karatu a boko ba. Ƴan bokon da basu san addini ba, mu karatun muhammadiyya muka sani, sai ilimantiri da akeyi da can, in yarinya tayi sakandare mace ma mu bata cika auruwa ba, kuma a ƙauye da kuka gurgura kukai karatun a lokacin da kuke yi wanne surutune banji ba. Madadin ace ta sake haihuwa, yaro Asbar ya girma ga Ɗan safiyo mai gida ƙani za'a kuma mishi biyu fa kenan, amman ita tana ɗaya, ga boko zai kuma kangarar da'ita, haihuwarma taƙishi. To wallahi bazan yadda ba ta gama zuwa makaranta, kai koyarwanma ban yarda ba, ba kuma za'ayi ba. Wannnan kenan. Batu na biyu shine. Sai batun wannan uban gida, da uban kayan alatu daka ma Hindu irin wannan. Yanzu irin wannan gidan ka kama kake biyan hayanshi daga kai, sai ita, da ɗa ƙwalli ɗaya wanda dashi da babu kusan ɗayane, to menene marabar? bata da yawa kake wani buɗe baki nafaɗa. Wallahi sai kun bar gidannan, sai kun barshi ni dai na faɗa muku makaranta kuma dole ta daina, ji irin kayan alatun da kake kawo mata fa" "Kiyi haƙuri Nanno. Wallahi wannan kayan da kika gani bani akayi,
Chapter 80 · 0% Book details