← Book details Tsuron Tsirin Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 84

Sashe 40

Tsuron Tsirin Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hindu:.
Bani na farka ba sai bayan magriba, ko dana farka Innah bata ɗakin ina dai jiyo ɓuruntunta a tsakar gida, ga Azgar har an mai wanka an sake mashi seti sabo fil wanda ina kyautata zaton Innah ce tazo mana dashi, yayi kyau sai baccinshi yake yi. Ga tocila mai manyan batura taiga wannan tocilar ta ƙarfe nasan wacce ta haure shekaru talatin da biyar zuwa arba'in ta san wannan tocila, ko a hannun mahaifinta, ko a hannun dattijan anguwa.
ÆŠakin yayi É—umi ga iska bababa ana ta yi a waje.
A tsanake na tashi na shiga banÉ—aki na gyare jikina na É—auro alwala. Fitowa nayi na duba Innah bata falo, tana waje wajen Murhu kamar kifine take sake gasawa. Sallar magriba nayi, dana duba agogo isha tayi saina yi, ina sallamewa Innah ta shigo da sallamarta falo. A guje na cire mayafin nayi wurgi dashi gado.
"Kin tashi Hindu, ya jikin?"
Da sauƙi Innah ya gajiyar hanya? "
Kallona take yi cike da kulawa tace.
"Gajiya ta bi lafiya Hindu. Bari in zuba miki abincin ki samu kici, na dama miki kunun geroma ɗazu kafin Baraka take ko ta tafi. Gaskiya tana da ƙoƙari hatta kayan jinin da muka tawo dashi a asibiti taso ta wanke sai nace ta bari, shi irin wannan kayan jinin haihuwa na jikine sosai yake yi, sai dai in na jikin basa kusa suna nesa ne."
Kwanon da tuwon yake ciki ta jawo ta zuba mun.
"Innah ya'isa haka bakina babu daÉ—i"
"Ikon Allah irin jegon Ya Ruwayya zaki yi kenan, cikinta cunkushewa yake yi bata iya cin abinci. Kyanta ma ai kici gashasshen nama mai ruwa ruwa. Dan naga da yamma muka dawone ga ruwa. Shi yasa bance mijinki ya siyo ba, gobe dai ya siyo."
Miya ta zuba mun da bushasshen kifi guda guda, ta jawo wani kwanon muttala dogo mai kamar bokiti yana ma da hannu, ta É—aura a wuta cike yake fam da soyayye nama a cikin kakide.
Daya soma narkewa ta ɗebo namannan ta zuba mun, ta sake ɗaura irin kwanon, shi kuma cike fam da soyayyar miyar tumaturi da nama yake shaƙe, ta sake ɗebo naman miyarnan ta saka mun, ta miƙo mun tuwon.
"Maza kici, sai ki sha kunu, wanka kuma ko a bayinki na É—aki ki É—an gargasa jikin Allah bashi gobe mayi na ganye a bayan gidan tsakar gidanki ko? "
Saida na É—auki nama na tura a bakina kana nace.
To Innah"
Miƙewa tayi ta shinfiɗa dadduma, ta ta da kabbarar sallah. Ni dai ina cin tuwonnan ina kallon fuskar Azgar sai nake ji tamkar bani da wata damuwa a nan gidan duniya. Ga mijina ga ɗanmu, to me kuma zai damemu? .
Nan da nan na cinye tuwon tunda bashi da yawa kifi ne da nama ya cika kwanon, ina ɗan kurɓan kunun Azgar ya farka da kuka, Innah nake kallo, ita kuma carbi take ja.
"Ki ɗaukeshi ki bashi yanzu kam ya sha ya ƙoshi sosai, ɗazu ma da kukan ya tashi kina bacci."
Kunun na ajjiye na É—aukeshi na bashi Umma yana ta tsotso, Innah tana ta kallona, can dai tace.
"Yanzu Hindu ke naga ko a jikinki irin wannan rayuwar ƙauyanci da kike ciki. Dan Allah jibi ƙauyannan, da gidan, da mutanen gidan, da suke kewaye dake. Ke amman kinsan kin koma ƴar ƙauye futuk irinsu amman?"
Shiru nayi tare da sauke kaina.
"Ba magana nake miki bane dan abu ta kazan.. Kinga yadda kika koma baƙauya futuk kuwa, kinga takalmin da kika je asibiti dashi, da wani irin riyo zubin ƴan ƙauye da kuka je dashi, ke irin rayuwar da kika zaɓa kenan su Ya Ruwayya suna kallo sun zuba miki idanu ko? Shima yanzu wannan yaron a irin rayuwar da zai taso kenan haka kika zaɓa mishi ko?
Batun karatuma an yi magana yace har sai ɗan uwanshi ya gama gini. Amman a yadda naga uwarshi a tsaye ya maman maza, ba zata taɓa barinku ku koma birni har ta barki ki koma makaranta ba. In Janaral ya yadda da zaman ƙauye, kinsan bazai yadda da rashin komawa karatu ba. A cikin ƴan uwanki kin fita zakka, kece kaɗai kab gidanku ma kike rayuwa a ƙauye, yadda kika san asiri akayi miki. Ai shikenan tunda haka kika zaɓa. Shi ɗan uwanshi ba gashi har yayi tunanin ya koma kano da nashi iyalin ba, ya sai fili yana ginawa ba. Yanzu inma an barku kuje birnin tare dasu, a gidansu za'a raɓaku kenan. Ko shima ya sai nashi filinne zai gina yana fama da kwalli sai kace boka?"
Aa bai siya ba tukunna dai, amman in muka koma shima zai siya Innah. Kiyi haƙuri yayi alƙawarin zai sani makaranta kamar yadda akayi mishi sharaɗi. Kuma Innah bai ragamun da komai ba, yana bani dukkan kulawa, bai barni babu ci ba, bai barni babu sha ba, bai barni da rashin sutura ba. In banda lafiya yana tsayamun, bai gajiya da makaraina ba. Yana bani dukkan lokacin shi"
Wata uwar harara da tsaki ta ja duk a lokaci guda.
Murmushi nayi mata kawai, wani ƙududu ya tokaremun wuyana.
"A cikin gidannan babu wacce ta shigo barka ciki harda surukarki. Nayi tunanin ko ruwane ya hanata fitowa jikin tsufa. Sai dai kash ina kan shanyar zannuwan jinin biki sai gata a guje ta shige ɓarayin ɗayar mai jegon, mata a hakan suke ta shiga mata barka. Amman na zuba idanu mu gani zuwa gobe da safe zata shigo ko ba zata shigo ba. Wallahi babu abinda zai hana in farfaɗa mata magana ni da ita babu wanda zai iya rabamu. Duk yadda kakanni suke son jikoki, amman ace babu wanda ya biyomu asibiti, mun dawo ma babu wanda yazo, babu wanda ya kawo abinci ko dai ya nuna kulawa hmmmm"
Ni dai na kasa cewa komai. Sai dai naji wani irin ciwo dangane da abinda su Nanno suka yi. Shin wai ƙiyayyar da suke mun ashe har yarana ma ba tsira zasu yi ba kenan. To shikenan, bama zasu rayu a kusa da su ba, balle suma su ga ƙiyayya da mugunta.
A zuchiyata nake wannan batun. Saida Azgar ya ƙoshi yayi bacci, na zare Umman a hankali zan kwantar dashi Innah tace.
"A kafaɗa zaki sakashi, ki dinga shafar bayanshi har sai yayi gyatsa umman ya faɗa mishi kenan sai ki kwantar dashi. In kuma goyon ƴan ƙauyen zaki yi sai ki kwantar dashi, ya dinga kwaro miki tumbuɗi duk ku jagwale"
Kai Innah"
Na faÉ—a a hankali.
Ina kan shafar bayanshi Mijinyawa ya shigo da sallamarshi. Ya tsugunna har ƙasa ya gaishe da Innah, tare da tambayarta hanya"
"Bamu samu gaisawa da kyau mun tambayeki ya gajiyar hanya ba Innah."
"Gajiya tabi lafiya. Gobe naman ƙaurin ka kawo da wuri. Sannan inason ƙafar saniya da jelar sa zan mata farfesu ta sha, mu kasan a al'adarmu haka muke ma mai jego."
Ga manyan dalilan da yasa kanuri suka riƙe sirrin girka ma mai jego ƙafar saniya da jelar saniya, musamman a satin jegonta na farko.
Wannan daɗaɗɗiyar al'adace ta matan kanuri, wanda har yanzu da yawa basu yi watsi da'itaba. Kasancewar an san kanurai d riƙo, da girmama al'adunsu, wannan dalilin yasa sukai fice.
Sinadarin Collagen, da Sinadaran Gyaran Jiki. Kafar saniya da jelar sa suna É—auke da sinadarin collagen da kitse mai gina jiki.
Bayan haihuwa, gabobin mace da jijiyoyinta suna bukatar abubuwan da zasu dawo dasu yadda suke, sannan kafar saniya tana taimakawa wajen rage radadin ciwon gwiwoyi, da ƙashin baya, da mace ke ji saboda nauyin ciki.Kayan Yaji na Musamman da ake amfani dasu.
Ba a dafa ƙafar saniyar haka kawai, ana zuba mata kayan yaji masu zafi sosai kamar citta, masoro, kanumfari, da kimba, gyaɗar miya, tafarnuwa, habbahan, habbatussauda kaɗan, hulba kaɗan ƴaƴan. Wannan farfesu mai zafi yana taimakawa wajen gasa cikin maijego daga ciki, sannan yana sanya mata dumi domin fitar da dukkan gudan jinin dake cikinta, wanda ya rage a mahaifa.
Karin Jini da Kuzari.
Jelar saniya tana da nama mai dadi da taushi wanda ke cike da sinadarin iron (mai karin jini) Mace tana zubar da jini lokacin haihuwa, shan wannan romon yana dawo mata da kuzarinta a cikin sauƙi.
Karuwar Madarar umma.
Shan romo mai zafi na kafar saniya, da jelar sa, yana bude hanyoyin umma, kuma yana karawa uwa yawan madara domin ta shayar da jaririnta cikin sauki.
Wannan wata hikimace daga tsofaffi masani sirrin gyaran jikin mai jego.
Mijinyawa ya nisa kana yace.
"To to gobe za'a kawo in sha Allah. Ga wannan kaza ce, da balango nasa akai mata gashi na musamman ta samu taci kafin gobe. Sai da safenku"
Haka ya fita yana satar kallona.
Ni kaina hankalina yana kanshi.
Ni naman ma kaÉ—an naci, Innah ta zuba mun yajin daddawa ta sake zubo mun kunun gero dai, haka na samu dai nasha na kwanta.
A wannan daren, wani irin nutsattsen bacci nayi lafiyayye wanda rabona da yin irinshi dai na mance.
Sai da Asuba naji Ɓuruntun Innah tana hura itace, asubace, ina jiyo mijinyawa na jidan ruwa.
Jikina na kuma gyarawa na É—auro alwala nayi sallah.
Miƙewar da zanyi mai zai faru, ai sai jini ya ɓallemun, na soma ganin juwa ɗakin na jujjuyawa dani.
Jinine mai yawan gaske yake zuba kamar an buÉ—e fanfo, ga jiri na neman kayar dani, ina faÉ—uwa Azgar zan danne, in buÉ—e baki in yi magana na kasa.
Mrs BUKHARI
Mu kwana anan sai gobe in Allah ya kaimu💪🏼💪🏼💪🏼

*Ina mai farin cikin sanar daku basarakiyar dilkharmu ta matan sudan ta kammala* *Zan turo muku hotonta ku ganta, da nera dubu bakwai ɗinki zaki mallaki wannan basarakiyar Dilkha Hajiya, a haɗe take ruwan ɗumu da ƙwai kawai zaki saka mata ki kwaɓa ki shafe jikinki dashi, zaki dawo ki bani labari. Ga wani sirrin ƙamshi mai riƙe fata a tattare da wannan dilkha Hajiya* *siyan nagari maida kuɗi*💪🏼💪🏼MRS BUKHARI

...........

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/JVdGBW8N6iFFBHyPGYXdrF?s=sw&p=a&ilr=0
Chapter 40 · 0% Book details