Sashe 36
Tsuron Tsirin Part 3 Complete Hausa Novel · about 5 min read
A hankali na soma buɗe idanuna, ina jin kukan jariri a kunnuwana har zuwa cikin ƙwaƙwalwata, wani muhimmin saƙo sai isa cikin zuchiyata yake yi. A kan mijinyawa da jaririna na sauke idanuna. Na dubeshi, na dubi jaririn dake jikinshi yanata canyara kuka. Saman ɗakin na kalla, a hankali nace.
Ubangiji nagode, ka fiddani kunya, Allah Alhamdulillahi da wannan kyauta daka bamu. Ubangiji dama ina da yaƙinin ka amsa adda'armu, lokaci ne sai yanzu yayi."
Hannayena na miƙo daga kwancen da nake.
Miƙoshi inji ɗuminshi. Bani shi in rungume abuna"
"Hindu jikinki babu ƙarfi ba zaki iya ɗaukarshi ba, bara in kira ma'aikatan jinya"
Cewar Harira.
Murmushi nayi mata.
Zan iya, ai ciwo ya kau, farin ciki ya mamaye ƙuncin. Mijinyawa bani ɗana"
Harira ta fita kiran Dakta, shi kuma ya manna mun yaron a saman ƙirjina. Idanuna na lumshe, inajin ƙirjina na wani irin bugawa na ban mamaki. Kukan yaron yana ratsamun dukkan rassan jikina. Hannuna na saka a bayan yaron, mijinyawa yasa nashi hannun a saman nawa. Yaronnan wallahi kamar almara sai yayi shiru yanata ajjiyar zuchiya.
Ashe haka soyayyar uwa da É—a take, ashe haka uwa take ji game da É—anta, ashe haka É—a yake da daÉ—i? Madallah da ubangijin Halittu.
Take yaronnan ya samu kyakkyawan gurbi a cikin zuchiyata, ya kwanta yai lub, take naji tausayinshi mai ƙarfi ya shigeni.
Idanuna na buÉ—e na zubasu a cikin na mijinyawa.
Murmushi muka sakarma juna, a kunnena ya raÉ—amun.
"Shikenan hankalin iya rigima ya kwanta. Burina in faranta miki ranki ko da ni nawa zai yi baƙine"
A hankali na furta.
Raina fansane a gareka. Ina maka so irin wanda uwa take ma É—an data tsugunna ta haifa. Bana tunanin a duniyarnan zaka iya samun macen da zata soka rabin son da nake ma. Nagode da dukkan kyautatawarka gareni. Madallah da nagartarka"
Idanunshi sai suka kawo ruwa, ya ɗago inya kalleni sai ya kalli jaririn dake ƙirjina, ga hawaye fal guraben idanunshi.
Shigowar Harira da ma'aikaciyar jinyane yasa ya miƙe ya matsa.
Harira taso ɗauke yaron a jikina, amman ina naƙi yadda, dariya kawai tayi mun.
Wannan ma'aikaciyar jinya taimun tambayoyin duk daya dace dangane da yadda nake ji. Nifa jikina ma ya warware bana jin komai wallahi kumburi kuma dama a cikinshi nake.
Ruwan da ake ƙaramun ma ya ƙare, ta cire mun.
"A bata shayi mai madara ta sha ta warware hanjinta, kafin a bata abinci taci, zuwa anjima zata sha magani. Allah ya ƙara sauƙi"
Sallama tayi mana ta fita.
Mijinyawa ya ɗauki yaron a jikina ya zaunar dani tare da jingina mun bayana a fuskar gadon, fulo ya saka mun na jingina a jiki. Na miƙa hannu akan a dawo mun da ɗana jikina. Dariya duk suka yi. Mijinyawa ya saka mun yaronnan a cinyata na tallafeshi. Harira ta haɗamun shayi mai kauri. Ita ta dafo ruwan zafin, mijinyawa kuma ya siyo kayan shayin madara, sikari, furanto. Na kafa kai na shanye shayinnan. Ta sake kaɗo maganin jininnan ta bani na shanye.
"Sannu Hindu, yanzu dai asuba ta riga da tayi, in gari yayi haske sai a siyo miki abinci kici. Kinga tuwon Mijinyawa dana kawo mishi yaƙi ci fur, haka ya kwana yana zurga zurga tsakanin waje da cikin ɗakinnan. Shi bawan Allah ki kawoshi tunda ya samu bacci, kema ki kwanta nan da kamar awa guda wannan maganin zai soma aikinshi, ga tsumman ƙunzugu na tanadar miki"
Mijinyawane ya shinfiɗe jaririn a gefena kafin ya tafi masallaci. Ni a kan gadon nayi sallata ina tunanin yadda zan dinga zamewa in yi sallah in muka koma gida, wannan jinin kam nasam bazai hanani sallah ba, tunda gayyatoshi akayi. Amman duk da haka zanyi tambaya, to wama zan tambaya ni Hindu. Nasan dai jinin istihadha jinine na cuta, ko na magani, wanda wannan jinin dana gayyato yana cikin jinin da bazai hanani sallah ba. Tabbas nasan wannan, sai dai in da zan samu malamai inason a ƙaramun sani bisa ga ɗan sanin da nayi.
Ina daga kwance nake wannan tunanin, ina kallon matar da muke ɗaki ɗaya tana ba yaranta umma. Ɗayan ya gama sha an miƙo mata ɗayan. Naga sai runtse idanunta take yi, ko dai da zafine ba da umman?
"Ki daure, kinsan shan farkon akwai wuya, da zaran sun saba shikenan zaki dena jin zafin, in sun gama sha ga nan man kaÉ—anya sai ki shafa a saman umman. Sannu Balarabu"
Tamkar matar tayi ne dan inji amsar tambayata.
Mijinyawane ya shigo da tuwon shinkafa miyar taushe mai zafi, babu mamaki yanzu aka gama wannan tuwon.
"Ga tuwo da zafinshi yanzu ta gama. Inaso in kika gama cine, sai in je in sanar a gida halin da kike. Jiya bazan iya tafiya in barki ba tare da kin farfaÉ—oba. Amman yanzu da zaran na tabbatar kinci abincin sai inje, babu mamaki ma Innah Yahanasu ta iso tun jiyan"
Sai kaci malmala guda, sannan sai ka bani inci, amman infa kanaso inci"
Murmushi muka yi ma juna dukkanmu. Baiyi musu ba yaci malmala É—aya, ya dinga bani a baki naci malmala guda, da nama yanka uku, gashi miyar taji gyaÉ—a ga man shanu.
Wannan matar da ta haifi Æ´an biyu, sai kallonmu take yi, yadda mijinyawa ya zage yana bani, abinci a baki, yanata hilatata da hira.
Jakata ya buÉ—e ya ciri kuÉ—in ciki duka, ya mayar ajjihunshi.
Yasa hannu ya É—akko yaron.
"Wanne suna kike da sha'awar a sanya mishi Tutar so, zanyi mishi huÉ—uba? "
Azgar nake so ka sanya mishi, na jima ina dakon wannan suna mai Muhimmanci a Tarihin Musulunci
Suna ne na É—aya daga cikin Sahabban Manzon Allah (S.A.W) mai suna Asghar bin Qais
Haka kuma, ana yawan tunawa da sunan a tarihin Musulunci saboda jikan Manzon Allah (S.A.W), wato Ali al-Asghar (Ali mafi ƙankanta), wanda yake shi ne ɗan gullan Imam Husain (R.A) mafi ƙanƙanta, duk da akwai saɓanin malamai akan sunan, wasu sunce Abdullahi ne sunan.
Shi nake son ka sanya ma É—anmu"
"An gama Giwar mijinyawa, yaro zai amsa wannan suna mai daraja."
Huɗuba take yaima yaron da suna Asghar wanda hausawa suke kira da Azgar. Harira ya miƙama, yai mana sallama akan shi sai ya dawo.
Yana fita sai jini ya ɓallemun, magani ya soma aikinshi, tsumma Harira ta bani, na shige banɗaki cike da farin ciki nayi ƙunzugu na fito sai murna da zumuɗi nake yi.
Ban jima ba bacci mai lauyi lafiyayye mara fargaba a cikinshi ya kwasheni.