← Book details Tsuron Tsirin Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 84

Sashe 46

Tsuron Tsirin Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Innah ta sake zaro Ƴaƴan hulba shima tace ƙwaya ashirin kullum in haɗiya in bi da ruwan ɗumi. "Shikenan sauran kayan fitar suna, da gara suna tafe, su Saratu zasu zo miki da komai. Ina ganin da mun yi la'asar zamu kama hanya kuma. Gashi sai ruwa akeyi. Yaha ya batun wankan gida amman, girkannan za'ai mata ko? " "To naga kamar bata son batun wankan gidan gaskiya. Amman zamu tafi da'ita Maiduguri ko kwana gomane tayi, sai mu dawo mu ɗaura wanka. Dole kinsan ai mata gyara na musamman, jikinta ya rasa martabobin da gyarane kaɗai ka iya dawo mata dashi. Amman sai mu bari tayi talatin, sauran goman sai in tafi da'ita. Amman me kika ce?" "Aa ki dai tafi da'ita da zaran suna ya ƙare, a ƙalla itama za'a gane da gatanta, kar dangin mijin suga kamar ko neman kai akeyi da'ita. Zasu iya goranta mata tabbas. Kuma ai kinsan dole a girketa, hankalina ya kwanta sosai da kikace Maiduguri zaki tafi da'ita. Itama nasan gidanne can bata son zuwa. Akwai ƴan gutsiri tsoma sosai. Gulmace za'aitayi inta dawo. Bana son kowa ma yasan zaki tafi da'ita. Sai an watse kab, sannan ku tafi. " Ni dai ban iya cewa uffan ba. Azgar ne yayi kuka, innah ta karɓoshi, Luba na zaune sai ƙashi take ta faman gwagwuya ƙaƙas abunta. "Bashi Umma. Naga yaron yana da haƙuri kamarki. In ya biyoki ai zaki yi lafiyayyen goyo, kefa bakya kuka, ko a bacci kika tashi sabida haƙurinki, sai dai kisa hannunki a baki kawai kita tsotso. Bana mancewa har Asibiti Ya Ruwayya ta kaiki wai bakya kuka. Likitocin suka ce in dai kin yi kuka lokacin da aka haifeki shikenan, in daga lokacin ma anji kin kuma kuka babu damuwa. Wasu yaran haka Allah yayi su da kuka, wasu kuma masu dauriya" "Um ai wannan gashi yana ta canyarawa. Ai itafa irin wannan canyara kukan ban taɓa ganin tayi ba gaskiya. Yana dai da haƙuri shima irin nashi" Umma na bashi ya sha ya ƙoshi, muna ta hira da Luba, tana bani labarin irin nata zaman da falalolinta, da tafiyar karatunta da a yanzu ta dingine zuwa ta haihu kuma. Halima ce tayo sallama, ita da Baraka. Inajinsu a falo suna gaisawa da su Baba Sojanmu. Kafin daga bisani suka yo sallama suka shigo, Azgar na kafaɗar Luba tana shafar bayanshi. Gaisawa muka yi da Halima, ta yafo ɗan mayafinnan ƙarami irin na ƴan mata. Ta caɓa ado kanta da ƙarin gashi anyi mata kitso dashi. Da yayi gyatsa saita miƙa musu yaron. Bakara ta karɓa ta ba Halima. "Ya jikin Hindu? " Da sauƙi Baraka sai jiri da nake ji kaɗan. Yanzu ma wani irin sanyi nake ji duk da ga gaushi." "Ai hadarine ganga_ganga a garin. Halima na rako tayi barka inaso inje in zuba ma su Qasimu da mijinyawa abinci sun fito gona" Aa bari Luba ta zuba sai ki kai musu, tun tuni ma nake son magana da Mijinyawan fa. Ko dan Allah zaki mun Magana dashi, in yaso ma ya tafi da abinci? " Hakan ko akayi, sai ga mijinyawa amman a ɗakin kayan abinci ya tsaya, Luba ta miƙo mun kwanan abincin na fito. Allah ya soni basu kulani ba. A tsaye na shiga na sameshi, dana dure abincin saina faɗa banɗakin tsakar gida na gyara jikina da ruwan zafi, nayi alwala na shige da sauri. Hadarine sosai a garin. Sallar azahar da la'asar nayi. Yana zaune a saman katifar yayi yana kallona. A gurguje ina ka samo kuɗi haka, Innah tace ka jido ƙafar saniya da jela, ni kuma nasan kuɗin cikin jakarnan daka ɗiba ba zasu isa wannan hidimar ba. Ko bashi ka ciyo ne? " Murmushi yayi. "Banci bashi ba. Dama naje ne da zummar siyo ƙafafuwan saniya guda, kinga huɗu kenan ƙafafun, da jelar. To harma munyi ciniki yana daddatsawa dake Azare muka shiga mahauta. To sai Qasimu yace a ƙara kamar wanda na siyan. Shi kuma Abdulƙadiri ya sai naman ƙauri kinji yadda akayi kenan. Amman dama akwai ƴan wasu kudaɗen a jikina, in sha Allah ba zamu ji kunya ba. Kije kar aga kin daɗe ya zame mana magana, kyakkyawata kinga yadda kika yi wani kyau" Miƙewa nayi ina ƴar dariya. Ga abinci nan, ka dinga aikowa ana zuba maka naka, ai dakai akayi girkin, babu mai hanaka cin abinci. Dan Allah ka saki jikinka" "Ke tsoron Innah nake ji, kinsan Allah ko ganinta nayi sai naji faɗuwar gaba. Tana ganina take sake haɗe girar sama data ƙasa fa. Ke dai muje" Tare muka fito, yayi maza ya fice ni kuma na shiga ciki. "Ma firen inaga wi hab to go. Banason ruwannan ya taremu a ƙauyannan mol yazo ya sake riƙe mana mota. Allah ya raya ya ƙara lafiyar shayarwa ko? Tek gut kiya ob yo sef. Kinga yanzu kin zama uwa, dan Allah a dage. Kuma ya kamata yayi makaranta mai kyau, nasan bai den kun dawo Kano kema har kinyi nisa a karatunki, za mu tattauna da Magawatan. Ga wannan ki riƙe a hannunki" Ya bani kuɗi masu yawa. Yaya Sojanmu ma ya bani kuɗi, ya kira Luba itama ya bata kuɗi, Baba Sojanmu ya ƙara mata. Lafaya na naɗa, na sake lulluɓa da zani, Luba ta zauna da Azgar tare da su Halima. Mu kuma muka ɗunguma rakiyarsu Baba Sojanmu, gari sai sanyi mai ruwa_ ruwa halamun ruwa na daf da sakkowa. Muna fita Mijinyawa ya hangomu, abincima suke ci a ƙarƙashin bishiya. Ba shiri ya taso, shine harda gudu_gudunshi. Baba Sojanmu ya dafashi kanshi a ƙasa. "Ma firen wannan kwalli yu hab to ridus it is to muc filis" Murmushi kawai yayi, ya daddaki kafaɗarshi. "Ma diya mun tafi mu kam Allah ya raya" To Baba Sojanmu, Allah ya tsare hanya. Innarmu Yaya Sojanmu Allah ya kiyaye hanya. Anty zasu zo ne tare da su Yaya Saratu? " "Ameen Duwab zata zo. Ai masu zuwan da yawa. Gayyar da zasu yi bata wasa bace. Mun barosu anata rubuta sunayen masu tawowa aikin Khadija ne wannan kema kin sani" Kai kawai na jinjina ina yaƙe, ji nayi cikina ya ƙulle. Wallahi da yawa ba taya murna bace zata kawosu ba, gulmace da son ganin ƙwaƙwab. In sha Allah ba zamu wulaƙanta ba, masu son ganin gazawarmu da faɗuwarmu ba zasu gani ba. Rikici ne dai nasan sai wanda su Yaya Jamila suka mance. Har sukai nisa ban gaji da yi musu adabo ba. Sai da sukai nisan da yayi yawa, kana na sauke hannuna. Innace tayi gaba, na faki idanunta na damƙama mijinyawa kuɗin da Baba Sojanmu ya bani, tunda sunfi yawa suna da kauri sosai gaskiya, na wajen Yaya sojanmu kuma na soke su, suma da kaurinsu. Muna isa ƙofar gida, muka ga gilmawar Nanno da gudunta. "Ikon Allah. Wannan kamar fa surukarki ce take hangenmu, da taga mun juyo shine ta rufa da gudu" Saukar ruwan sama da ƙarfi shi ya katse mana bayanin, a guje muka shige. Ita a wajen ruwan zafi ma ta tsaya. "Ki shirya kizo ki sameni a banɗakin waje zamu yi wanka." To" Kawai nace da'ita ko dana shiga ciki, tsabar duhu har acibalbal suka kunna. Baraka nayi ma Azgar wanka, sai ga Innah Dubu nan ta shigo da sallama wai tazo itace zata dinga ma yaro wanka. Ita take ma na Uwatale ma. "Aa ki dai je kiyi ma na Uwatalen kika ce ko? Ya yaron da ko barkarshi baki zo bane, zaki ce wai wanka kika zo kiyi mishi. To bazai ma yiwu ba ehe" Cewar Innah daga falo muke jiyosu, mu muna daga ciki. "Aa baiwar Allah. Ai ba batun ƙin zuwa barka bane. Kuma in kika duba ai fishi dukkanmu muke yi da batun haihuwarnan da akayi a asibiti. Kuma shi mijinyawa yaje ya birne mahaifa mabiya a asibiti. Ai dole muyi fishi haƙuri ma ya dace a bamu" "Nace anƙi a baku haƙurin. Yarone dai Baraka na yi mai wanka ta wadatar. Ku je kuci baƙin halinku. Sabida na fahimci baƙin cikine kawai kuke ma yarannan. To ko ku so ko kar ku so, Hindu dai ta haihu da ɗanku babu abinda kuka isa kuyi. Wannan Auren damu daku ya zame mana TSURON TSIRIN TSANDAURI, ya gagaremu ba dai mutum ba sai dai Allah. To kinji wallahi. Haka kurum a baki yaron anaji ana gani ki dannamai kai a ruwa, ko ki shiɗa mishi sabulu a hanci. To kin ji" Innah ta dirarma mita, dan wallahi mita gareta, saita kwana ta wuni tana abu ɗaya. Dole ƙanwar naƙi Innah Dubu ta fita dan anfi ƙarfinta. Kuma ita ba mafaɗaciya bace sam. "Ke in zaki fito ki fito mu je wanka. Wannan abubuwan na gidannan ya fitarmun aka. Wallahi su bini a hankali kar su tunzurani rikicina babu kyau. Akanme suke ire iren wannan abun da girmansu da komai" Faɗa Innah take yi kamar me. Ni dai kaya na cire, na yafo zani na fito. Ai na shiga banɗaki, Innah na shirin shiga sai ga Nanno da Inna Kulu, da mahaifiyar Uwatale, sai Innah Dubu, sun shigo. Ƙugu Innah ta riƙe. "Ke dubu shiga ki karɓi jaririn a hannun Baraka ki mai wanka, jikanane ubanshi ma nawa ne, ita kanta Hindun bata isaba nafi ƙarfinta." Sai Innah Tine, mahaifiyar Uwaatale sunayene da'ita kusan uku amman mu ɗauki Tine ɗin tace. "To ma in banda kwaɓa ina wata Baraka da wankan jariri, nawa Barakan take. Mu a al'adance dattijaine ke ma jirajirai wanka. Kuma ta ɓangaren dangin miji a dattijanma. Alhakin wankan daya rataya a wuyan dangin mata wanke ɗiyarsu mai jegone kawai." Ai sai Innah ta cire ƙafarta ɗaya dake cikin banɗaki ta fito, a dokin ƙofar shiga ɗakina ta tokare. "In mata ta isa, tana jin tana da ƙarfi tazo, wallahi saina kwantar da'ita. Ke da kike maganar iko ke kika sanshi. Ke me al'adu shi yasa gaki kamar al'adarku ta neman magana da zuzuta ƙaramar magana ta zama babba. Kunsan Allah banga a cikin dangin Magawata daya isa yaima yaronnan wanka ba. An kaita asibiti babu ƙeyarku. An dawo da'itama haka har saida na wanke ƙafata naje jin ba'asin wa Hindu ta kashe muku a dangine. Ai kun riga ƙiyayyarku, da hassadarku, ta fito fili. Sai kawai dan bani
Chapter 46 · 0% Book details