Sashe 27
Tsuron Tsirin Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yau na wayi gari jikin nawa da ɗan dama babu laifi kam. Dan da kaina nayi share_share, mijinyawa lokacin yana ɗebo mun ruwa ya ciccika mun randunana. Nanno sai zazzaga faɗa take yi, amman yau abun nata akan su Shafa yake, wata gulmace Shafa ta jagoranta, shine abun ya zame musu matsala. Sarkine ma ya aiko ayi kiransu fa. Haka fa ake ƙyanƙyashe ƙwai tara tsinana a wannan gida namu. Gulma fa zaman daɓaro tayi ƙaƙas a gidan. Da ƙaton cikina a gaba na fito saye da mayafi a jikina. "Kin shirya zuwa wajen Barakan ne?" Wallahi kuwa, ƙafafuna duk sunyi nauyi amman inna tattaka zan ɗan warware, ai gara a wanke kayayyakinnan a adanasu ko?" Murmushi yayi mun yace. "Sosai kuwa. Dama inason zamu yi magana dake, ina sone inna gama ɗiban ruwan dama sai muyi. Nama mance da batun zuwa wankin kayan jarirai shab." To bari mu gama maganar ba sai inje ba. Ai ba sauri nake yi ba." Zama nayi saida ya kammala yazo ya zauna muna fuskantar juna yace. "Aiki Qasimu ya samo mana mu uku a cikin garin Bauchi. Na lura da gidan gonan wani babban mai muƙami. Kuma babu laifi akwai tsoka kuɗin. To kinga kuɗinnan muna da buƙatarsu ko ba gaskiya ba? Ga batun siyen rago, ga fita kunyar dangi, abincin suna duka dai, ga batun kayan fitan sunanki dole akwai buƙatar in fita aiki. Danma munyi dabara mun tara itace, ga abinci da kika tara duk dan kar a ji kunya. Tutar so dole in matsa duk da ina jin tsoron a yanayin da zan tafi in barki, sabida baki da lafiya, ga ƙullin da muke ɓoyewa. Amman me kika gani shawara. In tafi, ko in yi zamana dake? " Shiru nayi ina nazari. Ni kaina nayi tunanin hakan, amman duba da yadda ko bacci bana iya samu yasa ban mishi maganar fitan ba. Babu damuwa wannan shawarace mai kyau. Kaje Allah ya tsare, zan kula da kaina in sha Allah. Amman yaushe zaka dinga dawowa kenan?" "To Amin. Wannan dai tafiyar in muka yi Gombe zamu je kai tsaye, na tsawon wata guda. In muka gama da gidan gonarshi na Gombe, sai mu dawo Bauchi. To in muka dawo Bauchi kam ai duk sati ina gida. In kika ce kullum ma zan dawo sai in dawo ai mayyata" Ya faɗa cikin sigar zolaya mu kai dariya. To shikenan Allah Ubangiji ya dafa, ya baku abinda kuka je nema. Yaushe ne tafiyar to? " "Jibi ne in Allah ya kaimu cikin masu rai." To Ubangiji Allah ya nuna mana. Bari inje wajen Baraka. Ku sai yaushe zaku je Azaren ne? " "Yanzu dana kammala zamu wuce ai babu mamaki ni suke jira ma mu wuce. Zan wanke miki tsakar gidan kafin muje" Sallama mukaima juna, na fito zuwa babban tsakar gidan ina tattakawa a hankali. "Kaga mai ciki, ciki sai girmanshi yake yi. Kai zamu sha suna a gidannan, tsiranku da Uwatale babu nisa." Cewar Shafa kenan tana tsakiyar mata ana ɓarin gulmar da aka saba. Ita da kes ɗinta yana gaban sarki ya nemesu su zo gobe. Dariya kawai nayi, muka gaisa. "Sai ina haka Hinduwa? " "Wajen Baraka zani Tatsaure, kina da saƙone wajenta? " Na faɗa da gatse, sai ta ɗauki abun wasa. "Oo_oo bani da saƙo. Ai gara ki dinga miƙe ƙafar haka akeso. Haihuwar fari baka jaɓe waje ɗaya ba" A zaure ma na jiyo ƙarashen zancan ni kam. Ina sa ƙafa a gidansu Baraka na tarar da igiyoyin gidan shaƙe_shaƙe da kayan jarirai igiya biyar cike dam, da kayan jarirai da na yaro ko yarinya wacce ta ɗan tasa. Sun gama wanke komai safuna suke wanke wa. "Kaga Uwar biyu in sha Allah. Ai wallahi dama zamanki kikayi kinga Lamiso ta tayani mun wanke fes, safuna ya rage." Waje na nema a benci na zauna da ƙyar, ga goro ina ɗan ɓantara abu dai irin na masu dashi. Baraka Lamiso nagode shine baku jirani ba. Allah ya saka da alkhairi" "Laa ai babu komai Hinduwa yima kaine. Lallai wannan yaro ɗan gatan Baba da Mamane, irin wannan tulin Kayan wallahi ban taɓa ganin an yima wani jariri ko jaririya irinsu ba. Tubarkalla ji kaya fa reras." Dariya kawai nayi, ina daga zaune muna ta hirarmu, da haka muka jiyo muryar Mijinyawa yazo wajen Qasimu amman ba zama suka yi ba waje suka yi ficewarsu. Na jima a wajen Baraka sosai, saida ta kammala abincin rana shinkafa da wake da manja da yaji. Zuba mun tayi cikin kula. Nan nace ba sai ta yi na dare damu ba wannan ya ishemu, da ƙyar ta amince. Gaga gaga gaga gaga. Ranar dasu Mijinyawa zasu tafi nice rakiya har ƙofar gida, Uwatale bakinta a washe sai farin ciki take ta faman yi. Ni kuma makaraina tamkar jira dama suke yi Mijinyawa yasa ƙafarshi a gidan ya tafi. Sai ya zamana bana iya baccin dare sam idanuna a soye, ga faɗuwar gaba, ga matsanancin ciwon kai subhanallahi. Gashi da safe ne nake jin bacci, inna kwanta makarantar fa? . Haka dole nake lallaɓawa inje makarantar in bada ilimi. Kafin in iso gida ji zanyi kamar in yi bacci a hanya. Inna dawo ko abinci bana iya ci, sai bacci, bana sake sanin kaina sai daf magriba, kuma idanuna sai kuma soyewa suke yi. Sai inji kamar babu ruwa sam a cikinsu. Shi yasa yanzu duk ɗan abinda zan iyayi da daddare nake yi. Ina riƙe da kaina, ko in ɗaure jiƙaƙƙen tsumma a kaina tamau. Wani irin tafasa kullum kaina yake yi. Tsumman fa ɗumi yake yi inna ɗaura, gishina in kuka luma yatsa kwatan yatsanku zai iya lumewa, in kika cire yatsan a haka wajen zai tsaya tamkar an huda sakwara, yadda kukasan babu ƙashi. Duk yadda bana son hayaƙi sai gashi da kaina nake yi. Cikin sati biyu nayi wata iriyar rama ta ban mamaki, a sati na uku zuwa na huɗu nayi wani irin kumburin da wallahi idanuna rufewa suka yi ruf, saina ɗan ɗaga girata kafin nake iya gani. Allah ya raba kowa da ciwon makarai. Sun wuce tunanin masu tunani. Baraka hankalinta ya tashi ranar da ta kawo mun abinci da kanta. A guje ta kirawo Nanno. Ita kanta taji tsoro a karo na farko. "Wai wannan Hindun ce Baraka? Ciki kenan masu gari jibi yarinyar mutane yadda ta koma abun tsoro ni ƴasu, kuma haihuwar da shingen kusan wata biyu inaga. Nace ke Hindu shi Magawatan yayo miki aike ne ko yaya, duk da wannan makon ake sa rai da dawowar tasu? Ga juyin ɗaki kinyi kina da ciki irin haka menene na juyin ɗaki. Da kin bari ma ƙawayenki su Uwatale ai zasu yi miki" Kunji wai ƙawayena su Uwatale fa hmm. Bai yi aike ba. Wannan satinne satin dawowar tasu, an shiga sati huɗu." "Umm nace wannan fantimotin kuma na waye. Kaddai kice ke Magawata ya kuma siyama na haihuwa? Dan wallahi nasan ba hankali bane dashi ba tsab zai aikata." Aa na Abdulƙadiri ne ajjiyace ya kawo mun, yana tara kayan Aure ne" "Ita Gwamma kuma ta barshi ya ɗebo uba uban kaya ya kawo miki. Allah mai iko. Ke dai kece uwar kowa, hatta abokan miji sai yadda kikai dasu? To bikinma ai ya riga ya zo, suna dawowa bikin za'ayi ta faru ta ƙare" Tana girgiza kai harta fice. Da haka su Uwatale sukaita tururuwar zuwa dubiya. Da ɗaya biyu suka zo saina dawo tsakar gida nayi kwanciyata. Duk wanda ya shigo ina tsakar gida a kwance. Wannan kenan. Washegari asabar ne, tun asuba nayi bacci, bani na farka ba sai sha biyun rana. Kumburin ya ɗan saɓe tunda ina gani ba saina ɗaga girata sama ba. Taliyar hausa nake jin sha'awar ci, ta manja da bushasshen kifi. Ina da kifina tun wanda Innarmu taimun aikenshi kafin inje biki, da naje bikinma na kuma tawo da wani kusan cikin leda mai zane. Adanashi nayi tare da shinkafa karolin dana tawo dashi daga gida ta kusan rabin buhu, wake, maggi, farin mai, garin tuwo sabida dai batun haihuwarnan ne, in fita kunyar masu son in gaza. A ciki na ɗakko kifi babba na wanke, nayi jajjagen kayan miya na tsaida sanwata. Ashe da rabon jarumin maza, jan gwarzo na Hindu ba da kanka a sare. Ina ƙoƙarin zare itace in samu gaushi zan yi turaren wuta kafin in kashe, naga ƴan tsaka tsakin matasa sun dure buhu a ƙofar ɓarayina. Leƙawa nayi na tadda Uwatale a tsaye a ƙofa itama tana kallon kayan. "Ba mamaki ɓatan kai suka yi Nawata ne ya dawo kenan, shine suka jingine buhun a bangonki" Baki na taɓe nayi komawata ciki, har ta janye buhu ta shige dashi ɓarayinta. Saiga Qasimu da Mijinyawa jaye da babban rago ƙaton gaske mai murɗaɗɗun ƙaho. Ciki na koma na zaro mayafi na fito. Qasimu ashe kuna tafe?" "Hindu Subhananallahi cikinne du ya mayar dake haka, kina shan magungunan zaƙi da duk wanda ya dace, Baraka ta dafo miki kuma kina sha? " Ɗan murmushi nayi. Goga naku kuwa sakan igiyar ragon yayi ya nufoni yana taɓa fuskanta. Hanlalinshi in yai dubu ya tashi gaya. Musamman da yaga shatin hannayenshi sun zauna akan fuskar tawa basu baje ba. "Tutar so lafiya kika koma haka, shi yasa jikina duk bai bani ba, wallahi kaga abinda nake faɗa maka ko? Ni dai ku barni har Hindu ta haihu nanne zanfi gane kaina, har in tafi neman kuɗi" Uwatalece ta shiga da sauri taji kukan rago. Nanno kuwa anci gagarumar sa'a batanan taje Azare akan batun bikin Abdulƙari, daga can zata biya har misau wata guda zata yi. Bata nan ma za'ayi bikin tunda mun shiga satin bikin ma. "Aa_aa wannan ƙatoton ragon ai ko ni Nawata bai yankamun lokacin haihuwar Zainab ba. Mijinyawa yanzu kaine da wannan rago hoɗijan" "To ai Nawata kika ce, shi daban ni daban. Ke da baki da aiki sai neman Sababin tsiya. Na fahimci Uwatale baki da kirki sam. Ayi magana ki kwashi jiki ki sanarma Nanno. Tutar so ina buhun kaya da yara suka shigo dashi? " "Laaa ai wallahi nayi zaton Nawata ne ya dawo. Kaga fa harna soma buɗewa. Kukan ragone ma ya zaburo dani ka ganni nazo." "Har kin soma buɗewa fa