← Book details Tsuron Tsirin Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 84

Sashe 51

Tsuron Tsirin Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ana wannan ruwa muka jiyo sallamarsu Innah Mairamu, dasu Innah Abidah, da ƴan gida harma da waɗanda in ba dole ba bama magana, amman duk sun harhaɗo sun zo. Wallahi kuma nayi farin cikin ganinsu, baka sanin yawan dangi na da amfani sai kayi aure, sai kaji kana alfahari da yawan danginka. "Ahh sannunku Abidah kun ƙaraso, anata ruwa haka dai muke ta aiki a ruwan ma. Sannun ku da zuwa kun riga ƴan Borno isowa su da sukace asubar fari zasu tawo, a hanya ma zasu yi sallah Asuba" Innah Abidah dake ta faman kalle_ kalle ko magana ma ta kasa yi, sai da Innah mairamu tace. "Magana fa akeyi. Ai Yaha mun sha hanya. Ga hanyar shigowa nan ɗin bata da kyau sam. Ga laka motarmu sai cijewa take yi. Ai dake lokacin da muka kawo ita Hindun da ranine hanyar bata kai haka lalacewa ba. Hindu ina sabon maigida?" Sannunku Innah Mairamu. Kun shawo hanya ga ruwa." "Ke Halima ku shige ɗakin can na gaba, nan ɗin duk ya cike. Hindu sai fa an nemo musu matsugunin kwana, amman a yanzu dai haka duk zamu zauna." Cewar Innah Yahanasu Nan aka rabu, duk ɗakunan an cikesu maƙil da jama'a. Gida ya kaure da hira da abubuwa dai na ƴan uwa. Tunda na miƙa Azgar na fito zuwa barandar da su Yaya suke suna ta zuba abinci tire _tire ga nama nashasha. "Hindu za dai a samu masauki ko a wajen Baraka ko? Kinsan ba zasu so su yi nisa ba?" Za'a samu duk a maƙota da za'a saƙasu. Su innah Mairamu su anan zasu zauna ne?" Kafin inyi magana Innah Abida ta fito. "Zanje direba ya shigo da kayan kawai in an samu matasa sai su kawo mai. Hindu ashe kayan ɗaki kika sauya haka uban ubansu? Gaskiya mijinki yayi ƙoƙari gaya irin wannan kaya a ƙauyennan ai ko a birni sai haka. Nace amman a Bauchi aka siya ko, ko dai daga Kano ne?" Ta kakkafeni da idanunta. A Bauchine" Na faɗa a taƙaice. "Ai ashe Bauchi za'a iya samun irin wannan kaya na zamani haka, gaskiya ya gwangwajeki, ai da gani zasu yi tsada dai. Ta ƙarashe tare da ficewa a guje. Ni dai cikin ƴan uwa na koma ni da Luba muna gado, Azgar dai yau zai sha ciwon jiki gaskiya. Ga hayaniya yau dai yasan yazo duniya, ya faɗo a ɗan dangi. Anti matar Yaya Sojanmu ce tace. "A miƙa yaronnan haka Fatima yasha ɗauka" Fatima tace. "Ai da su Murja zan kaima shi suna ɗayan ɗakin" "Ana ruwannanne zaki fita da jinjiri ai bazai ma yiwu ba" Inji Rayya" "To rasa kunya. Gashi Hindu kwantar dashi" Sai Luba ce ta karɓeshi, na kalleta na watsar, ni dama tun tasowarmu Fatiman Lungun Baba Doraga bama shiri sam. Ficewa tayi a ɗakin. "Ai gara kije, ni banso ma ta biyomu ba wallahi" "Zainab ɗin Baba Lukumanu tace. " Maza ki bari uwarta Innah Yabi ta jiyoki wallahi" Ni dai kallonsu kawai nake yi. Yaya Zubaina ce ta shiga miƙo turen abinci. "Saura ɗaya Zubaina anan ciki" Cewar Anti, saima ta tashi ta fita kawai karɓowa. Can sai muka jiyo sallamar Su Yaburra dasu Falmatan Innah Yalewa, dasu Fannah, da Yakura. Sai sabon murna da yaren Kanuri kake ji yana tashi. Falmata ƙawatace ai tana shigowa ta haye gado da goyonta. Hamshaƙi mai kuɗi take aure, tana zaune a Chard. Ita dai tsiyarta bata hausa sai yare. Inajin komai, amman amsar bana iyayinta zur zur inta yi, sai dai ingausa dai. Amman nafi Mrs BUKHARI, ita iyakarta gaisuwa da yaren Kanuri. Nan aka shiga hirar zumunci ta rungumeni sai ƙamshin kabbasa take yi, ta ci lallen gargajiya ga kitsonta na gaɓa yis_yis_yis. Kiran Innah Yahanasu naji, na fito da sauri Tana tsaye ita da Innah Yalewa kamarsu ɗaya sak tamkar ƴan biyu. Rungumeni tayi tace. "Kajinya" Kalmace ta nuna tsananin ƙauna. Annuri kawai nake yi, naga dangin Innarmu cikin ummansu sunyo tattaki domin nuna ƙauna da ƙarfafa zumunci. "Yauwa uwar ɗakinnan naki dole mu za'a barma, kinga iyayen gidanku sun haɗu a can ɗakin, su Yabi da Abidah, yaran matan aka bari a naki ɗakin. To uwar ɗakinnan mu zamu mamayeta sabida tattaunawa ta musamman. Ga niƙan sunasun ɗinnan wa zai kai. Da niƙan kayan miya, ko bari zanma Baraka magana ta shiga gaishe da su Abidah. Kó dúa ganyí, Yaya ( ko ba haka ba Yaya) Ta tambayi Innah Yalewa. Kai ta gyaɗa tace "Hárúgú tà vás ( hakane tabbas) "Fáto adə́ sáwábe kárgá-bé-rSync kózə́ndé shíoró landányé. (Su bar mana ɗakin ko dan mu yi hirarmu ta zumunci) Muna cikin wannan magana, ni ina daga dokin ƙofa, su Innah Yahanasu suna daga waje. Sai ga Yaya jamila ta shigo. " Baraka kinga niƙannan na bokatannan uku muke son akai a niƙo mana yanzu. Sai kuma inda za'a aro tukwanen girki manya manya" Cewar Innah Yahanasu data watsar da Yaya Jamila. "To Innah, bari a kira yara su zo su ɗauka. Hindu ni kam na tafi, gobe da asussuba sai in dawo. Masu zuwa kwana kuma zuwa dare Qasimu zai zo ya tawo dasu in sun gama hirarsu" Tana sa kai ta fita sai Yaya Jamila tace. "Ke Hinduwa shiga ki kwasomun kayan da Magawata ya kawo miki na barka. Da cefanen da aka baku kuɗi kuka yi na fitar suna. Wannan ragunan kuma zan wuce dasu. Kai Nawata shigo mana kake tsaye kazo ka sunce mun ragunannan du biyun" Cike da hadara da taƙama irin ta dangin miji, isar rashin isa kenan, har wani daddaƙile wuya takeyi. "Wacece wannan haka take magana da isa da gadara? " Cewar Yalewa. Ni mamaki ma yasa motsi wannan na kasa, har Nawata ya shigo ƙebe_ ƙebe ya kama igiyar rago. Aiko farantin dake hannun Innah yahanasu ji kuke ƙwal a hannun Nawata. Ba shiri ya saki igiyarnan, yana yarfe hannunshi. "Ubanwa ya aiko ki maras kunya fitsararriya? Ke na lura baki da kunya baki da mutumci, hala dai bazawarace ko, kin kasa zaman naki gidan shine kike baza mulkinki a kan matan ƙanne? Ke Hindu wannan ba mijinki bane? Duk da naga ba kwalli a idanunshi" "Yayanshi ne, shi yana waje. Sannan mahaifiyarmu ce ta aikomu mu kai mata komai da komai" "Tunda ita take aurenta ai dole ta aikoku, to kuje ku faɗa mata babu mahalukin da a wannan duniyar ta maliki yaumuldin daya isa ya kwashe ragunannan ya kai mata. Ko shi Magawatan yake ko magarana ne bai isa ba. Na fiku tauri da zafi wallahi" Ni dai ina tsaye ina waige. Aiko sai gasu Innah Abidah, da Innah Mairamu, da Innah Yabi, sun fito. Idanu na lumshe kawai na buɗesu akan Yaya Jamila dake cewa. "Ai kuwa dole mu ɗauka wallahi. Nanno ta isa da ɗanta, kuma ta isa da kayanshi. Ke baki haihu bane ko baki san yadda uwa tak.... " Tas Yaya Saratu ta ɗauke Yaya Jamila da mari. Marin da ya zama, wasila ta janyo hankalin ɗaukacin ƴan gidanmu. Su Innah Yalewa dama su suna tsaye. Dasu Yakura, da Fannah Innah Abidah tayi saurin shiga tsakanin Yaya Jamila da Yaya Saratu. "Kinmun daidai. Kai kuma ƙaton banza zo ka wuce kafin insa a tuɓemun kai wallahi, aita dukanka kamar kwarto" Ai ba shiri ya tsallake ya fita. "Menene yake faruwa baiwar Allah yi mun bayani. Ke kuma Saratu haka akeyi zaki zo ki haddasama ƴar uwarki fitina a dangin mijinta." "Haka fa, ai dama zaki aika Abidah dole kice haka ai. Munafuka kawai mai hassadar tsiya. Kema maza kizo ki fice kafin in saka wannan yaran su miki na jaki. Maras kunya kawai. Yanzu in saka Yanuna tai miki duka" "Ai wallahi sai an bamu kayannan. Ke kuma zaki san kin daki jamil... " Ai bata ƙarasaba Yaya ta dira a wuyanta ta ruƙunƙumeta, Falmata ma ta mara mata baya. Dambe ya kaure ya kacame. Aka hautsine, kowa ya firfito daga masu taɓe baki, sai masu murna, da masu alhini. Ni dai ina tsaye kawai kamar dutse. "Kai subhanallahi. Yalewa ke kizo mu saka hannu. Fanna kuyi mata magana ko zata ji karta kashe ƴar mutane fa, kunfa san Saratu sarai akan batun dambe, dama ita bata cacar baki tun da can" Ai kafin kace kwabo an cika ɓarayinnan maƙil da ƙyar su Nanno suka kutso kai suka shigo tsabar cikowa. Da ƙyar su Khadija da Anti suka raba faɗannan. Duk su Yaya sun farfasama Yaya jamila baki, Yaya ta kusan cire mata kitso ɗaya. Dan janshi tayi ya ɓanɓaroshi. "Ya salam ke Nanno menene yake faruwane yara sunce ke kika aikosu menene kiyi mana bayani dallah_dallah" "Wanda zaku ɗauki rahoto ba. Ai sai tayi miki bayani ki bata amsar daya dace Abidah. Uwargidan janaral. Ai batun ayi bayani kike yi, to ke Nanno yi mata bayani." Innah Abidah dai bata ce komai ba, sai Innah Kulu ce tayi mata bayanin raguna, da cefanen suna aka aiko su Jamila su karɓo, da kayan barka da mijinyawa ya ba Hindu. "Haba dai an taɓa yin haka ne ace baza'a barmu muyi abincin suna da kanmu ba. To menene amfanin yawanmu. Shin ko al'adarku ce ta baku wannan damar ai sai mu sani ko Mairamu? " Cewar Innah Abidah. Yalewa ce ta karɓe duk da hausarta bata da kyau tana mayar da mace namiji, namiji ya koma mace. "Ai ko al'adarsu ce ta basu wannan damar, wallahi bama za'ayi wannan aikin ba. Mun yi musu kala da waɗanda zasu ma girki har muci? jibesu ƙazamai gidadawa dasu, tama ina za'ayi haka. Ke tsohuwa kuje dai yaro ya baku kuɗin cefanen abinda zaku dafa, ba dai wanda zaku dafa mana ba" Innah Yahanasu zata yi magana. Yalewa tayi mata yare ta yi yare, sai ta ja ta riƙe ƙugunta bata ce uffan ba. Sai hura hancinta take yi. Uwatale a guje ta shigo, tana dube_ dube. "Shin wannan ragon da aka ƙaro da cefanen da aka shigo dashi Mijinyawa ne yayi ko bashi yayi ba? " Cewar Innah Kulu. "Shi yayi mana wa zai mai. Kuma in kuna tunanin wata gwanintace, mu kam mun raina. Kune matsiyata da har kuke ganin ɗanku wata bajintar yayi, wanda har kuke jin hassadarku ta motsa ku bama zaku iya haƙuri ba. Kuma Munci kayannan sai dai ku
Chapter 51 · 0% Book details