Sashe 41
Tsuron Tsirin Part 3 Complete Hausa Novel · about 5 min read
*Kin Dade kina neman Adashin gatan da zaki shiga ki rika Tara kudi kadan kadan ki kwashi idan nace Miki kaya hajiya ta ina nufin komai ga Anty zee nazo muku da Tsarin adashi ki rika Tara kudin ki kadan kadan ki kwashi duk abunda kike so, akwai bangaren kayan sawa na Yara Dana manya, akwai kayan kitchen, akwai sarkoki ,takalma , jakuku Nan Yan gayu, mayafai dadai sauran su me kuke jira maza ku shigo ku fara tari tun yanzu* 💃💃
Jininnan zuba yake yi sosai, gabaki ɗaya sai naji na rasa dukkan kuzarina. In kira Innah ma na kasa, jirine yake neman kaini ƙasa
Kukan Azgar ne ya shigo da mijinyawa da sauri.
Ganin jini a ƙasan kafet yana zuba kamar bawali daga jikin asalin ƙunzugun dake jikina.
Faɗuwa nazo yi akan kuma Azgar dake kwance yana kuka, daidai shigowar Innah Mijinyawa yai saurin tareni muka faɗi ƙasa.
Innah tayi ihu ganin na kusa faÉ—awa kan bawan Allah, har idanu saida ta runtse tasa hannunta bisa kanta.
"Subhanallahi ai jinine ya ɓalle mata. Hindu sannu, kai yi maza nemo maganin tsayar da jini na gaggawa tasha kafin mu kaita asibiti. Subhanallahi sannu Hindu"
A guje mijinyawa ya fita, ni dai da ƙyar nake nishi sabida yadda jini ke bulbula a jikina. Inaso ma ince akwai maganin tsaida jini, ina dashi amman harshena yayi mun wani irin nauyi. Dama Harira tace akwai yiyuwar ɓallewar jini tabbas.
Ai kuwa bai jima ba sai gashi da ruwan ganyen gwanda da tsamiya, da manda wanda aka dafama Uwatale Shafa ta kamfato mishi.
"Kafa kai kisha maza."
Cewar Mijinyawa wanda ya saka mun kofin a bakina, Innah tana riƙe da Azgar sai kuka yake yi. Runtse idanuna nayi na shanye duka.
Banfi minti biyar ba, Allah cikin ikonshi jinin sai ya daidaita. Amman ko iya tashi zaune bazan yi ba.
"Jeka tunda jinin ya tsaya zan gyara wajen"
"Innah kije daga falo zan taimaka mata, kiji da jaririn"
Ni dai da ƙyar nake numfashi sai naji mijinyawa yayi sama dani zuwa bayi, ya ajjiyeni a kan kujerar wankana da nake zama.
Kuma fa wallahi nauyine dani sosai. Ƙarfin haline, da kuma sabon ɗaganin a duk lokacin da makaraina suka rabkeni. Ai Anty Badiat ta rarrage muku abubbuwa da yawa, na dangane da ciwon makaraina. Tace kanta sara mata yake yi in tana rubuta waje.
Shi ya ciremun kayan jikina, ya fita ya É—ebo ruwan zafi sirkakke cikin bokiti yaita kwaramun yana wankeni.
Tsumma da ɗan diras ya kawomun nayi sabon ƙunzugu ya dawo dani gado. Jina nake yi sakayau, sai jiri.
Ya saka tsumma ya dinga aikin jininnan, wallahi babu ƙyama sam a fuskarshi, da kuma yadda yake dama hannunshi a jininnan. Yasa sabulu da soso ya dirje wajen tas. Kana ya ɗauki bokitin ya fitarma da Innah dashi.
Azgar tazo ta shinfiÉ—e tanai mun sannu, gaushi ta fita ta É—akko a kasko, ta ajjiye ta kuma fita sai gata da bawo na wankan jariri da ruwan zafi.
Sabulun salonta ta É—akko dashi tazo cikin roba na jariri daban, nawa ma daban anyi mishi haÉ—e haÉ—enmu sirrinmu sosai a ciki.
Lita biyar haka ta kawo mun a farin bokiti mai murfi. Sai ƙamshi yake zubawa.
Ta cicciro manya manyan kwalaben turarukan wuta wasu lita biyar, wani lita uku, humrorin lita uku uku gasunan kusan kala bakwai. Wannan kayan ƙamshin jegone, shima daɗaɗɗiyar al'adace har a garar abincin da ake kawowa daga gidansu maijego, tare da suturu ana saka turarukan wuta bokiti bokiti manya manya sosai. Haka humrorinma ake sakasu.
Innah ta harhaÉ—a itacen turare ta watsa a wuta, tare da farcen turare, turare mai dogon tarihi, turare mai sirri wanda ya kamata ace ko wacce mace ta mallakeshi. ( kizo in baki Farce Hajiya sunanan hawa uku nake dashi masu kyau da inganci, mai daÉ—aÉ—É—en tarihi)
Take ƙarnin jininnan ya gushe, ƙamshi ya maye gurbinshi.
Baraka ce ta shigo da sallamarta.
"Innah dama wankan nazo yi mai, kya ji da maijego ke kam"
"Allah sarki ƴannan, ai ko nagode sosai. Kinga yanzunnan jini ya ɓallema Hindunma. Inaga sai mun koma asibiti zuwa anjima, amman tasha magani jinin ya daidaita"
"Ashsha sannu Hinduwa, ai Innah ba sai anje asibiti ba. Bari in ɗakko mata wani jiƙo na ƙarin jinine sadidan. Sai taci abinci ta ƙoshi zata sha, jinin data zubar zai dawo. Ai ko jiya an dafama Uwatale irinshi, domin itama ta samu wannan ɓallewar jinin harma ake tunanin kamar ba zata kai ba. Amman ko yanzu na ganta a ƙafafunta zata shiga wanka. Bari in ɗakko mata. Haka sittin ma in mace ta haihu ko jini bai ɓalle mata ba, ana bata tasha. Nanno ce ya kamata ace ta aiko mata"
"To shikenan. Ai sannunki da ƙoƙari Baraka. Wannan yarinya ba dai kirki ba. Ita Nannon da kika ce, jira nake in gama ma Hindu wanka, zanje ɓarayin nata inji mutum nawa Hindu ta kashe mata da ta kasa zuwa ganin jikinta. Na fahimci bata da mutumci, inda mutumci yake ma ba saninshi tayi ba sam."
Baraka dai ta rasa ta cewa.
Fita tayi, ita kuma Innah saita fita kwashe ruwan wankana, ni dai gabana sai faÉ—uwa yake yi.
Baraka na dawowa na yafa zane muka shiga wanka.
"Bansa miki ruwan da zafi ba, sabida jinin da kika zubar yanzu, in ruwan yayi zafi zai iya ɓalle miki sabon jini. In jikinki yayi sauƙi kika samu kuzari ma dinga yi dana zafin, tsumma zansa in gargasa miki jikin"
Ai ko tsummane take tsomawa inta ciro sai a gadon bayana, ko ƙasan marata.
Amman dake ba tafashasshe bane, kuma jikin babu inda baya mun ciwo, babu inda baiyi tsami, da kumburi ba, sai naji wannan gashi na mugun mun daÉ—i, yana shigata sosai.
Ta jima tana yi mun.
"To ga sabulu kiyi wankan soso, zan kawo miki ruwan da zaki shiga ki zauna na magani yanzu."
Fita tayi ta bani waje, na saɓi haɗin sabulun salonnan na sille jikina tas dashi, har wani santsi fatata take yi.