Sashe 24
Tsuron Tsirin Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
miya a saman gaushi ki karɓo shinkafa a wajen Abidah sai ki haɗa mishi. Miyar Innarku Abidah bata ciyuwa ɗanyar miyar tumaturi take yi duk tsami ga ruwa." Dariya muka yi dukanmu, na ɗauki kwano na fita ta zubo mun farar shinkafa, ga miyar nan ta ɗaura a wuta tsululu tumaturinnan. A babban tire na haɗa mishi komai, na aika aka siyo mun lemun kwalba na limca na saka mishi. Da sallama na shiga na taddashi ya ɗauki tagumi ya ɗaura a kumatunshi. Bayan na dure abincin saina zauna daf dashi, nasa hannuna saina cire tagumin ina mai murmushi mai sanyi. Bani labarin zuchiyarka. Ka tsorata ko? " "Ai dole in tsorata kina jin Abinda Baba sojanmu da Baba Alƙali suka ce fa. Ke kinji ƙirjina kuwa sanda Baba Sojanmu ya miƙo biro da takaddarnan kuwa? . Sannan batun dawowa birni tare da su Nawata. Wannan tunaninane kawai bani da tabbaci in Nanno zata amince mun, ko kuma akwai sarari a cikin gidan ma da zamu iya zama. Wallahi na faɗane domin in kuɓuta kawai" Ai sai nazo wuya, inaji har makaraina na neman su dokeni, dalilin daya hanani cewa uffan kenan na lokaci mai tsayi. Shi yaga canji a tattare dani, dan take idanuna sukai luɓu_luɓu suka zama jawur. Ga abinci bismillah kaci, sai ka huta ni zan shiga daga ciki." Miƙewa nayi, yayi carab ya miƙe tare da shan gabana. "Hinduna me na faɗa wanda ya sosa ranki haka har kika kasa zama in ci abinci dan Allah? " Sai naji na sakko ganin yadda ya tashi hankulanshi. Komawa nayi na zauna tare da zuba mishi abincin. Zauna da kyau kaci ka ƙoshi sai ka huta ka shawo hanya. Ya jikin Nanno naji kace ba lafiya kuma cuta mai tsanani ko?" "Ke dai ki bari Nanno na kwance ana jinyarta baki ganta ba, abun tausayi. Ai bayan tafiyarki da kwana biyu ta soma ciwon. Abu kamar wasa daga ciwon kai, sai jiri, sai kawai ta faɗi bata san ina kanta yake ba. Akaita magani dai har zuwa yanzu bata iya tantaceni tsakanina da Nawata in faɗa miki" Shiru nayi ina jinjina lamarin Ubangiji. Mutum fa ba'a bakin komai yake ba. Allah yaso nuna mishi iyakarshi, yanzune kawai kafin ƙiftawar idanu. "Hmm Ubangiji Allah ya bata lafiya. Amman anje asibiti ko ko dai a gida aka barta? " "Ba'aje ko'ina ba. Kawu dai yana rubuto mata rubutu cikin jarka ana aikowa duk sati. Yaya Salihu yaƙi amincewa aje asibiti. Shima Kawu yace ciwon bana asibiti bane. Ana zaton jifanta akayi, ta taɓa samun haka a lokacin tana da cikin Autarmu. Tunda dai ta kwanta ciwonnan sai da ta haifeta Allah ya kawo yankewar abun. Jujjuyata akeyi fa kamar jinjira. Yaya Jamila da Yaya Zakiya duk suna gidan suke jinyarta. Magunguna kuwa baki gani ba, duk inda muka ji labari tafiya muke yi mu karɓo. Har yanzu dai babu makari." Shiru nayi ina nazarin wannan wanne irin ciwone haka. Gashi sun canfa wai jifane to wa zai jefi Nanno ni naga bata da komai. To Ubangiji Allah ya tashi kafaɗarta kawai zamu ce. Amman ai da an jarraba na asibiti sai kaga an dace" Dariya yayi ya girgiza kanshi kawai. Saida yaci shinkafa loma biyu kafin yace. "Hindu sha'anin mutan ƙauye sai haƙuri, kedai ki bari kawai. Shi Yaya Salihu yasan tarihin ciwon na Nanno. Kuma ance yana da asaline da kishiyoyinta tunma mahaifinmu yana da rai haka ake jiƙawa a matse. Sabida Nanno macece mai rikici sosai. Hatta mahaifinmu yana shakkarta. Kuma ta kasance silar arzikinshi. A lokacin mahaifinta mai garine mai darajar gaske. Ya tallafama mahaifinmu sosai a bisa aikin Safiyo ɗinshi, kuma gonakan da duk muka gada ya samesu ne sanadin mahaifin Nanno. To hakan yasa sai Babanmu ya fifita, ya ɗaga darajar Nanno a cikin sauran kishiyoyinta. Kuma tana taƙamar ita ɗiyar mai garice. Mai gari a lokacin darajarshi ta kusan ta sarki gaskiya. Kuma mai gari zaki ganshi da tulin dukiya. Suna kiran ragowar gama garin jama'a da bayinsu. To a wannan gaɓarne kishiyoyi akace sun jefeta. Ciwon yana tashi mata lokaci zuwa lokaci. Sanda aka haifemu Nanno kusan hauka tayi fa tuburan, sabida ta haifi ƴan biyu kuma du maza, ke dai Allah ya kiyaye kinji tarihin da tsayi sosai. Mu kanmu Allah ne ya rayamu har muka zama mutane kawai. Amman menene abinda ya sosa miki ranki ɗazu? " Batun da kace wai baka san ko Nanno zata barmu, mu dawo birni bane ya sosani. Ai wallahi muddin Nawata ya ɗauko Uwatale suka dawo birni. To na rantse maka da wabillahillahi la'ilaha illahhuwa, ni Hindu zamana nima a Jama'are ya ƙare. Ko an ƙi ko anso, shine kawai" Shiru yayi yana kallona, yadda yaga na ɗaure fuskata tamau. Sama da ƙasa Allah bai bashi ikon tankawa ba. Shigowar Luba da Sunusi ce ta katse mana wannan zance. "Sunusi ashe dai rai kan ga rai. Hajiya Luba ikon Allah alƙawari ya cika" Cewar mijinyawa dake yashare baki. Zama suka yi nan aka shiga gaishe_gaishe da tambayar yaushe gamo. Mun jima a ɗakin ana hira sosai kafin Sunusi yace. "To mu kam zamu wuce in kaita gida, kafin in wuce wajen aiki" "Sunusi kayi babur ne?" "Inafa Mijinyawa a ƙafa ma zamu murza, ai rayuwar watarana dai sai labari. Muna sa rai inta kammala karatu ta soma aiki al'amuran zasu ɗan sassauta. Kasan fa ta koma makaranta. To wallahi kuɗi ya zauna a hannuna ina ba dama. Ga ƙaramin juna a tattare da'ita lamarin dai sai godiyar Ubangiji nake faɗa maka kawai" Miƙewa muka yi muka tattaka musu har titi. Kafin mukai sallama da juna. Muna tafe mijinyawa yace. "Kin sake yin kyau sosai. Kuma har ƙiba naga kinyi, sai kikai zubin masu cikin sak. Ga idanunki duk sun kumbura." Murmushi nayi kana nace. Kuma kullum a ɗarare nake kar a gano shirinmu, inka ganni kullum da hijabi hatta bacci dashi nake yi. In ana kallona sai inta tsarguwa kamar za'a bugo jirginmu" Ajjiyar zuchiya ya sauke yace. "Ai kuwa a gaskiya da mun shiga uku. Ta Nanno mai sauƙine tunda bata da lafiya. Amman Baba Sojanmu ƙila sai ya sa bindiga ya harbemu, yai fata_fata da namanmu" Dariya muka kwashe dashi kawai. Gaga_ gaga_gaga washegari motarmu ta ɗaga sai garin Badariyya. Da yamma lis sakaliya muka isa garin. Abdulƙadiri da Qasimu su suka taimaka mana wajen shigar mun da kayana ciki. Ni kuma na wuce kai tsaye ɓarayin su Nanno. Nan na taddata babu yadda take. Su Yaya Jamila duk suna cikin ɗakin da ƙanwarta Akulu ma tazo. Gaishesu nayi da mai jikin. "Matar Magawata ko? Tubarkallah gatanan kuwa yanayinta duk yayi na masu juna biyu, naga ta kumbura ta ɗanyance." Kai kawai na sauke ƙasa, jiyane na tashi da wannan kumburin. Sakamakon maganganun da Innarmu ta cunkusamun wanda yai sanadiyyar motsawar makaraina. "Ai kuwa gata nan fa. Da cikinnan tayi tafiya mai tsayi irin wannan bata ko tsoro ma" Cewar Yaya Jamila. Mijinyawa na shigowa na miƙe ina tafe irin na masu ciki harna fice. Matan gida sai wani hararata suke yi. Ni kuwa Hindu ko in kula. Zaman dirshan nayi a gaban buhunhunan da muka tawo dasu har saida Mijinyawa ya shigo. Nan ya shiga sunce kaya, yana jujjuyewa a mazubin kayan hatsinmu. Kayayyakin jarirai dana siyo, da wanda Innarmu ta bani duk na tura jakar cikin ɗaki, shi wannan sai dare ya raba zamu buɗe. Danma nazo na iske Uwatale bata nan, wai sunje Birni ita da Nawata gano gini. To haka na kasance kullum jikina babu daɗi, yau ciwo gobe lafiya. Makaraina suna kusa daf dani, mijinyawa ya shiga sunturin maganina. A haka na lallaɓa muka koma asibiti. Na ƙundume ƴan kuɗaɗen dana riƙo muka koma ma likita. Nan ya bamu magani na tsawon wata biyu tukunna, itama Allurar ta wata biyu ce, in aka gama, sai a dawo a sake gwaje_gwaje, kafin a sake ɗauramu akan magani da allurai. Sai dai zuwa ɗaya, biyu sai likitan ya bamu shawarar in dinga yi mishi a gida in dai zan iya, ya nuna mun inda zanyi tunda a hannuce, yace allurar kan jijiya itace tafi ko wacce haɗari. In kuma bazan iyaba, to mu nemi wani kemis mafi kusa damu a dinga yi mishi, alluran kuma sam basason zafi, mu ajjiyesu a waje mai sanyi. Haka akayi mai allura muka dawo gida. Muna zaune Mijinyawa ya ɗaurama ranshi damuwar duniya. Gani yake rayuwarshi ma ta ƙarene baki ɗaya. Haba mijinyawa yana da kyau ka dangana. Ka sani in Allah ya nufi zaka samu lafiya, to zaka samu ko da baka so. In Allah bai ƙaddari zaka ga ɗanka a duniya ba, wallahi ko kanaso, ko baka so ba zaka gani ba. Na sha faɗama ka riƙe istigifari, da tsayuwar dare, da karatun Qur'ani. To bayan wannan sai ka dangana, ka barma Allah kayanshi. Amman bana son wannan haɗa kai da guiwar da kake yi, dubi har ka soma ramewa fa." Kanshi ya ɗaga sama, sai naga hawaye na shatata ta gefe da gefen kuncinshi. Ƙanƙameshi nayi mukai shiru na lokaci mai tsayi. Kafin na zame jikina, muka haɗa idanu. Na dinga bashi kalma, ina ƙarfafashi, tare da tausarshi. "Hindu nayi miki alƙawarin rayuwa a birnin zuchiya, filin gidana ke kaɗai daga ke sai yaran da zamu ɗebo a gidan marayu. Raina fansane a kanki. Ki ji daɗinki babu ke babu kishiya, kuma zan sake ƙara kyautatawar da nake yi miki bisa wanda nake yi miki. Zan so duk abinda kike so, zan miki duk abinda kike so. Ke matar rufin asirice sosai. Kin sadaukar da duk jin daɗinki kin biyoni ƙauye, kin jure tsangwama da takurar dangina, duk dan mu rayu tare. Na kasance juyi, amman duk da haka kika sake sadaukar da duniyarki domin kawai ni Mijinyawa ki zauna ki rayu dani. Kuma kina da damar da zaki iya neman saki, dan kije ki auri mai haihuwa ku rayu tare. Ni ko naso ace Nanno tasan da zaman wannan al'amarin tattare danine ba tattare dake bane. Sai dai kash, muna son rungumar yaran da zamu dinga ganinsu muna jin daɗi. Hindu wallahi a yanzu nafi ki son a karɓo jaririnnan, na fiki sonshi wallahi. Sabida gara ma ke, ko yau inna mutu zaki iya aure ki rungumi naki. Nifa, in