Sashe 82
Tsuron Tsirin Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read
da Jamila, suna raye. kuma suna amsa sunan dangin mijinki, to tabbas babu ranar da zaki samu sauƙi. Amman mijinki yana sonki, kuma yana kyautata miki, yana miki adalci tsakaninki da danginshi. Kuma in kikai la'akari shi kowa ya juya mishi baya, amman ke duk rintsi danginki suna tare dake. Soyayyarku abar sha'awace, da abar kwatance. Zamun miji mai irin nagartar mijinyawa sai an tona, kamar yadda samun mace mai irin, haƙuri, da nagartarki sai an tona. Ajjiyar zuchiya na sauke, tare da lumshe idanuna da nake jinsu tamkar zasu tsaye tsabar rashin ruwa a cikinsu. Zama nayi a bakin gado ina jin hayaniyar matan unguwa, su Maman Zailani da suka mayar da gidan tamkar yadda uwatale take yi a lokacin da nake can. Adashe ma Uwatale ta kafa musu kamar yadda Shafa take uwar Adashe a ƙauye. Wannan adashe shi yai silar da yasa kullum mata cike da tsakar gida, acan jama'are, aita gulma ana faɗa. To irinshine Uwatale ta biyomu dashi kuma. Wannan ja'iba da mai tayi kama. Hayaniyarsu ta hana ƙwaƙwalwata hutawa sam. Turmi na ja zuwa falo, da wuƙa. Kafin in zauna zaman jajjage na ɗaura tafashen namana. Daga zaune na jajjage kayan miyana tsab. Saida na tsayar da sanwa, kana na fita tsakar gida na ɗauro alwala. Su Maman Zailani na mun sannu nayi kamar banji ba, sabida ina gani akan idona Maman Zailani na ma sauran matan zunɗena kafin ta gaisheni. Na gani, na kuma ji, sai na mayar da ganin nawa, da jin tamkar ma banji ba. Har saida na zo zan koma ɗakine Uwatale tace. "Hindu ƙawayena suna ta gaisheki baki ji ba" Na dubesu na watsar tare da cewa. Ayya" Nayi shigewata ciki. Sai gidan duk ya ɗauki shiru ji kake ƙus_ƙus. Duk wannan abun fa Nanno tana cikin gidan, tana falon Uwatale a zaune labule a rataye a ƙofa, koni da zan wuce na ganta yi nayi tamkar ban ganta ba. Bayan nayi sallah, na tsaida sanwar shinkafa ga magriba ta gabato, ni da yara mukai wanka fes, na sauya musu kaya. Ai ina fitowa ɗiban ruwa a randa sai naga Uwatale na ma yaranta itama wanka. Su kansu abun ya ɗaure musu kai, sai Zainab cewa take yi. "Mama mai yasa kike mana wanka da daddare yau? " Uwatale sai rufe ma yarinyar baki take yi, ni dai na ɗebi ruwana nayi shigewata. Da daddare da mijinyawa ya dawo, nanno ta kuma riƙeshi sai kusan sha biyun dare ta sakeshi ya shigo, anata artabu akan lallai ita tana kan bakarta saina dena karatu, shi Kuma mijinyawa sai haƙuri yake bata, yana ta kwatanta mata abubuwa. "Nonno ke fa kika ce tunda zata ci gaba da karatu sharaɗine mu dawo gidannan, to mun dawo kuma naga kinci gaba da batun Hindu ta ajjiye karatu, kefa kika ce ko mu dawo gidannan, ko Hindu ta ajjiye karatu, ko mu rabu. Na zaɓi mu zauna anan ɗin, kuma kika ce dokace baki yadda mu raba gida da Nawata ba, mu zauna a gida ɗaya duk runtsi, shima nace na yarda. Nanno me yasa abubuwa in akaina da Hindu ne kika fi zafafawa? Hindu fa bata ƙinki, bata ƙin kab dangina, me yasa kowa yake ƙinta ne. Da kince rashin haihuwane, an haihu tsugunne bata ƙare ba. Nawata kace wani abu, wallahi kaina ji nake kamar zai fashe, inaga ma mutuwa zanyi" Nawata yace. "Hakane duk abinda yace. Kuma nima inata baki haƙuri ki barta tayi karatunta Nanno. Kuma sharaɗi kika bashi na abu uku ya zaɓi ɗaya. Kuma ya zaɓa dan Allah ki bar maganarnan hakanan." Sai shiru ya ratsa tsakar gidan kafin tace. "Shikenan na bari, kar ka mutu, amman ba dan ina so ba wallahi. Da kake cewa da nace haihuwa ne yanzu an haihu. Ai har yanzu Hindu fa bata da maraba da juya in faɗa maka. Kaga matan arziki nan, yanzu haka da kake ganinta cikine a jikinta, Ɗan safiyo ƙani na biyu kenan za'a haifa mishi. Kake wani batun haihuwa. Yaro ɗaya rak ya girma baki raɗau har ya shiga makaranta, amman ko halamun ciki tattare da Hindu babu. Wannan baƙaƙen makaran nata zasu bari ne ta tara yara" Ni da nake jiyosu illahirin kunya sai da naji tamkar in nitse, ace uwace ke faɗama yaranta maza irin wannan magana mai nauyi da kunya, ita ko a jikinta. "To naga sabida munafurci a uwarɗaki fa Hindu take girkinta. To ban yarda ba, ta fito ta kafa dutse a tsakar gida kamar yarda matar mai gidan ta kafa nata. Ban yarda ba, ban lamunci aiki da kalanzir ba, dole da itace zata yi aiki wallahi ban amince ba. Ko data kawo mun abincinta sau biyu, Uwatale ce gata taci, da ƴan jikokina. Ni bana cin abincin risho ance cuta yake sakawa. To bazai yiwu ta kashemun jikana da ɗana ba, kaji na faɗa maka" Idanu na kuma lumshewa, na miƙe na koma uwarɗaki na gaji dajin wannan maganganun. Da ƙyar aka sallameshi ya taso ya shigo. Yana cin abinci yana son mun bayani, na katseshi. Naji komai, kar ka damu zan dinga yi a tsakar gidan, amman ba'a itace ba, a gawayi. Duk na ɗauka zamu mata biyayya. Abu ɗayane shine zanci gaba da karatu, kuma zanyi aiki wannan kam babu abunda zai canjashi sau ƙudurar Allah." Ajjiyar zuchiya kawai ya sauke, yayi magana ma ya kasa sam. Gobe su Innarmu zasu zo, tare dasu Yaya su ga waje, tunda babu aiki asabar ne." Ai sai ya ƙware harda tari. Da sauri na tsiyaya mishi ruwa ya sha. "To fa gashi Nanno tananan, Ubangiji Allah yasa a rabu lafiya. Nasan abune ma mai matuƙar wahala a wanye lafiya" Haka dai mukaita jimantama juna. Da Allah ya taimakemu, mun wayi garin asabar sassafe sai bugun ƙofa. Ina buɗewa naga Nanno da shirinta tsab harda buhunta. Ta kalleni ta harareni yarda take so, taƙi ma amsa gaisuwata. "Maza je ki kirawomun wannan maras kunyan, ya ƙule ɗaki da safennen bazai fito ya fice ba, ɗan uwanshi tuni ya fice. Shi yana ciki kina mai Zizizi da zazaza" Ni dai komawa nayi na tasheshi, da ƙyar ya buɗe idanunshi da suka rune sabida tsantsar gajiya. Nanno na nemanka, kamar ma tafiya zata yi" Jawoni yayi na faɗa mishi. "Ba shakka, tabbatattu" Cewar Nanno data ɗage mana labule yana hannunta. Da sauri na sakeshi kaina a ƙasa. Shi kuma ya miƙe da sauri ya bita. Ashe tafiya tayi. Ni kuma suna tafiya na fito da teburina dake ɗakin shirgina na jama'are, da mijinyawa ya tawo mun dashi. Na fito dashi waje, gefen randunana na ajjiye. Akai na ajjiye kurfona mai rami biyu, na saka gawayi na kunna, kana na shige ciki. Na dawo da tukunyane, Uwatale ta fito da tuwonta tana yankawa. Ban kalleta ba, bata kalleni ba sam, ni daɗi hakan yayimun. Yau da iskanci ta tashi, cika take tana babbatsewa. Shayi da ƙwai na soya nayi shigewata bayan na ɗaura ruwan shinkafa. Ƴar lisuwa kamar zata halaka Uwatale. Wajajen goman safe Mijinyawa ya aiko yaro da kayan miya da kifi jela huɗu manya. Na soya su, nayi miya gidan ya kaure da ƙamshi Uwatale ta rasa sukuni sai zurga_zurga take yi haka ma yaranta. Ni dai na gama komai na, har wanka da sa turaren wuta, da wanke kayan kwanuka dana ɓata. Su Innarmu sai bayan Azahar suka samu shigowa. Sunga waje dai, innarmu da ma ƴan uwana sake ƙarfafani suka yi, Innarmu harda tsaraba cikin bako. Uwatale kam, ai tun kafin su Innarmu su zo ta zari mayafinta suka fice ita da yara yawon barbaɗa. To yawon barbaɗa mana, wa take dashi a ƙwaryar kano da kewayenta? Gaga_gaga_gaga_gaga. Abubuwa da yawa sukaita cukumurɗawa, makirci, munafurci, ƙarya, sharri. Yau kwatsam na fito zanje gidan abokin Baba Sojanmu shima janaral ne, inama yaranshi karatun boko a gida, ranakun asabar da lahadi. Baba Sojanmu yaje gidanne yaji suna neman malamin turanci, da lissafi, shine yace zan iya. Duk ran asabar da lahadi nake zuwa, wata a bani ƴan canjin da yake mugun sauƙaƙe mana rayuwa. Na shirya tsab zan fita, harna kulle ƙofata na jiyo ihu da nishin Uwatale a ɗakinta. "Hindu! Ki taimakamun naƙuda nake yi haihuwa zanyi, wayyo Hindu zan mutu ki taimakamun na tuba" Na jiyo Uwatale sai maimaicin sunana take yi, haihuwa tazo. Mrs BukhariMRS BUKHARI