Sashe 4
Tsuron Tsirin Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Naji abinda duk yake tafe daku, amman sai dai akwai wani hanzari ba gudu ba. Æoye wannan sirrin abune mai É—an karen wahala. Kasan yawancin mata a jama'are a gida suke haihuwarsu, suna dai shiga asibitin azare a duba lafiyarsu, shima ba kowa ba. To ya zata yi da batun bayyanar ciki, da canjawar da masu ciki suke yi na yanayi, gara ma laulayi zata iyayi, wannan bazai zama abu mai wahala ba. Gaku a gidan gandu, har mahaifiyarka da kishiyoyinta duk suna cikin gidan, ga facaloli. Duk ba wannan ba, in É—aya a cikinku ya mutu ya za'ayi da batun gado, wannan shine babbar matsalar, wannan ranar itace ranar tonon silili, ranar kuka kuma. Akwai wanda na sani shekaru matsu tsayi a baya, a lokacin ilimi bai yawaita ba. Wata mahaukaciyace ta haifi yaron a rumfar gidan cikin dare, su kuma ita da mijinta su suka karÉ“i haihuwar, mahaukaciyar a wajen ta rasu suka riÆ™e yaron. Shi dai wannan yaron yaci gadonsu, tare da Æ™annenshi wanda Allah yaba iyayen goyon nashi daga baya. Har gobe bashi da masaniyar basu bane iyayenshi ba. To ku ya zaku yi duk kun shirya?. Duk da nasan in sha Allah kafin wannan lokacin iyaye da manyan masu faÉ—e aji sun mutu, sai dai in Allah yaso gwada Æ™udurarshi sai kai ka mutu, ko ita ta mutu ku riga iyayen. A wajen tashin hankali da tonon asirin yake fa" Kallona yayi, nima shi É—in nake kallo ina nazari. "To ke Hindu kinji duk abinda akace. Kusan duk nima na jajjero mata wannan jawabin da kika yi. Musamman na mutuwar. Amman duk da haka ta nuna tana so. Ina ganin in abu ne mai yiwuwa samun jaririn, babu damuwa mun É—auki hatsarin, matsawar zai faranta mata rai hakan, to ni babu wata matsala, ni kaina bani da burin daya wuce inga ranar da zamu karÉ“o É—a a gidan marayun da sunan mu muka haifi abinmu" "To shikenan ke Hindu kinji fa abinda yace" Naji Harira, saida muka amince kafin muka zo. Dama munsan samun É—an mutum sukun da guda abune da yake da girman gaske. Ban yi tunanin abune mai sauÆ™i ba gaskiya" Murmushi tayi tace. "To yanzu dai in sha Allah zan yi Æ™oÆ™ari in samu Hajiya Bara Æ™anwar wacce ta bani wannan yaron Hannafi. Zan mata bayani in sha Allah sai ku dawo zuwa rana ita yau. Allah bashi In tayi mana iso sai in kai ku, in kunje sauran maganar sai ayi tsari da dokokin É—aukar yaron abune mai yawa, kinsan yanayin duniyar sai a hankali, dokokin suna da tsauri. Ina zuwa to" Fita tayi ta bamu waje. Ni dai wallahi babu wani tsoro ko fargaba a raina sam. Mijinyawane ma ya sare, duk ya shiga ruÉ—u sai nazari kawai yake yi. "Kina ganin wannan hanyar zata É“ulle kuwa Tutar so? Kada mu aikata abinda asirinmu zai tonu. Kada kiyi tunanin ko bana son a É—akko É—a ko Æ´ar ne, wallahi aa ni kaina zuchiya ta kwaÉ—aita gaya da ganin jariri a kan kafaÉ—ata ina jijjigawa. Wannan shine kaÉ—ai dalili babba da zai riÆ™e igiyoyin aurenmu abadan" Zata É“ulle ai tsayuwar dare zamu dage dayi. Sai kaga Allah ya bamu namu kafinma lokacin wancan É—in yayi. Ai komai na Allah ne. Shi ke da tasarrafi akan komai. Maji roÆ™on bawane, majiÉ“ancin al'amuran bayine. Ina da yaÆ™inin Allah zai lamince mana, tunda ba saÉ“a mishi muka yi ba, ba kuskure zamu aikataba. Balma taimakone" Harira ce ta shigo da É—umame da ruwan bunu ta dure a gabanmu. "Gashi kuci bamu É—aura sabo ba. Nima dama Allah_Allah nake yi in gama in wuce wajen aiki sai gaku" Godiya nayi mata, ta fita ta bamu waje. A gaskiya bamu tsaya fulako ba, cinye abincinmu muka yi muka kora da ruwan bunu. Bamu jima ba mukai ma Harira sallama, kai tsaye muka wuce babban asibiti janaral. Muka tadda layi, zani ba zani ba har layi ya kawo kanmu, lokacin biyu harta gota, dan mijinyawa yaje yayo sallah ma ya dawo. Mun shiga muka tadda likitan macece, bayani nayi mata abinda ya kawo mu. Sannan mun taÉ“a zuwa asibitin sau É—aya an bincikamu, amman mijinyawa dai bai kuma biyoni ba bare yaji ba'asin sakamakon nashi ba, duk da aikine babba ba wai zuwa É—aya za'ayi a sanar dakai matsala ko akasinta ba. To itama dai gwaje_gwajen ta sake yi mana. Ta haÉ—a mijinyawa da likitan maza, akace in zamu dawo ya tawo da samfurin abinda ya dace a auna, aka bashi kwalba tsabtatacciya da zai sako a ciki. Rana ita yau mu dawo, a sake wani gwajin. Haka kurum wannan karon sai naji faÉ—uwar gaba kuma, tsorona Allah tsorona ace bazan taÉ“a haihuwa ba, gashi Allah ya jarabceni sosai. Sai dai ina kai kukana gareshi. Kafin mu shigo gida ragowar Æ´an kuÉ—aÉ—en nawa haka na Æ™undume muka yo jefane, nice harda siyan nama. A lokacin jama'are ta samu wutar nefa Alhamdulillahi, sai dai ba duka unguwanni ba, kuma ba wani kawo wutar akeyi ba, sai ayi sati babu, dake mu unguwarmu garine sosai muma akwai wuta. Kuma Yaya Salihu ya ja mana a cikin gidan namu. Sai mu kwan goma ba'a kawo ba wallahi. Amman dai babu laifi motsi yafi laÉ“ewa. Ina kai ku, mun dawo mun tadda matan gida dana maÆ™ota duk a gidan. Suna ganinmu aka shiga yima mijinyawa barka da samun arziki, harda masu kuma habaici da caÉ“a muggan magana. Ciki nayi babu wacce tama isheni kallo, balle in tanka mata. Uwatale na Æ™ofar É“arayinta a zaune ta dasa kujera, ta É—auki tagumi ta dasa. "Kun dawo, ashe bakya gidan? " Wallahi" Iyakata da'ita kenan. Ina kan buÉ—e Æ™ofar É“arayina mijinyawa ya shigo, uwatale na ta faman bin ledoji da kallo. "Tsaya Tutar so, kinsan fa bake kaÉ—ai bace. Bari inzo in buÉ—e miki mana." "Ahhh lallai Mijinyawa kace Hindu ita sai dai taci ta kwanta kawai. BuÉ—e Æ™ofarne ba zata iyaba. Sai kace a kanta aka soma ciki. Ai saina soma kakarin amai na shige da gudu, zuwa bayin tsakar gidana. Da gudu uwatale ta biyoni, mijinyawa ya watsar da kayan hannunshi ya biyoni yana ta faman sannu sannu. Kallonshi nayi muka yi murmushi, na rungumeshi. A kunnena ya raÉ—amun. "Kin ko kyauta kin aiki moÉ—a randa saÆ™on zai isa" "Sannu Hindu ko in shigo in taimaka miki ne? " "Aa uwatale kije kawai, ni aikin me nake yi da bazan taimaka mata ba" Ni dai buta ya miÆ™o mun na wanke fuskata na fito. Shi kuma ya cika bokiti da ruwa ya shaÆ™ema banÉ—akin. "Sannu, uhmmm nace wani abun kika ci ne. Kinsan masu juna biyu ba komai suke iya ci ba. Ni wallahi nama yi tunanin duk burgace ba wani ciki, ashe dai tabbas akwaishi. Haha Allah ya inganta. Dan ko Nanno bata yadda akwai cikin ba. Ashe dai akwaishi, dan ban taÉ“a ganin kin yi amai ba" Ta saka kai. Ta fice. Hannun mijinyawa na ja muka shiga ciki, saida muka zauna nace. Uwatale fa sai mun san yadda zamu zauna da'ita. Duk wata maganar data danganshi cikinnan da batun asibiti, da batun gidan marayu daga yanzu ba zamu sake yinshi a cikin gida haka ba. Sai in mun fita, a hanyarka ta rakani makaranta sai mu yi" Hannayena ya damÆ™e yace dani. "Duk yadda kike so haka za'ayi Tutar so. Yanzu muje mu É—aura girki, bari in karÉ“o itace" Nera hamsin na danÆ™a mishi ya fice, ni kuma ina tsakar gida ina jujjuye É—an kayan abincin da muka siyo, ga nama na juye a tukunya, ina kan juye kayan miya É—anye a basket Nanno ta shigo. "Haka aka koya miki a gidanku? Ya da ciki Æ™arami jikinki zaki dinga durÆ™uso irin wannan. Alhalin yanzu uwatale tace kin gama amai? Abincin ma in kikai haÆ™uri sai su Shafa su dinga dafawa ana zuba miki, nan da wata biyu ko uku, zuwa lokacin cikin ki yayi wata biyar ko hudu yayi Æ™wari, sai kici gaba da yin girkin ai. Amman fa sai abinda kuka ce" Har a fuska Uwatale bata ji daÉ—in wannan magana ta Nanno ba. Nima kuma har a cikin raina banso wai a dinga zubo mun abinci daga cikin gida ba, wannan Æ™azaman ne ni zanci abincinsu. Aa zan dinga yi da kaina ko da a zaunane. Sabida ba ko wanne abinci nake iya ci ba. Zan dinga yi" "Au Allah. Kenan bakya so a dinga zuba miki, sabida dai kina mana kallon Æ™azanta ko? " Uwatale ce tace haka. Ƙwarai da gaske hakane. Zan dinga girkawa da kaina" Na bata amsa sam ba hargowa, babu tsoro dan ba yankani za'ayi ba. Nanno tace. "Ba shakka. Ishasshiya, to kiji ki kuma ji, ni dama nayi hakanne dan in taimaka miki ke da kika samu ciki da Æ™yar, kar yazo ya zube. Cikinnan na zubewa zaki tattara komatsanki ki kama hanyarki. Dan ni wallahi banso ma kika samu cikin ba. Ke uwatale wuce muje" Kundai ji da kunnenku abinda tace. Ita bata so ma na samu cikin ba. Ma'ana bata so haÉ—a zuriya dani ba fa kenan. Wanke nama na nayi, na jajjaga tafarnuwa da citta na zuba, na yanka albasa, na zuba dunÆ™ule guda biyu na rufe. Ina aikina, ina jujjuya maganganun Nanno, da irin girman Æ™iyayyarta gareni. Da ba dan mijinyawa na mun son da baya bashi da misalin musaltuwa ba, kuma nima ina sonshi, a zamanmu baya cutar dani, balma sai kyautatawa da tattalina. Wallahi da yanzu wata maganar akeyi ba wannan ba. Amman bazan hukuntashi da laifin danginshi ba. Mijinyawa da kanshi daya shigo ya haÉ—amun wutar na É—aura tafashen nama. Na zauna kusa dashi da tiren tsintar shinkafa ya sa hannu ya karÉ“a" "Kije ki É—akko takadda da biro ki rubutama su Innarmu wasiÆ™a Shehulle zai tafi kano gobe sassafe" Da murnata naje na yago takadda da biro. Shehulle wani maÆ™ocinmune kuma abokin Mijinyawa Babbane. Direbane har gidanmu ya sani, in zai shiga kano ina bashi takadda yakai gidanmu, in zai dawo Innarmu takan haÉ—oshi da takadda da rigi_rigin kayan tsaraba. Tanan muke isar da saÆ™on junanmu. Wannan karon batun samun ciki shine yazo a layin farko bayan buÉ—ewa da dubun gaisuwa, tare da fatan aikhairi maras yankewa. Saina labarta musu batun ciki, na kuma Æ™arashe da gaishe_gaishen dana saba tare da tambayar Baba