← Book details Tsuron Tsirin Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 84

Sashe 48

Tsuron Tsirin Part 3 Complete Hausa Novel · about 6 min read

muka yi ciki. Na buɗe nan in ciro kuɗi, in buɗe can in ciro haka na harhaɗa harda ƴan kuɗaɗen adashen dana ɗauka dama na hidimar sunanne. Na gagganɗa kuɗaɗe dubu hamsin ta wancan lokacin fa. Ni da kaina na fita na kirawo Innah, suna ta aiki ita dasu Baraka. Falo ta shigo ta zauna na damƙa mata kuɗinnan. Kuɗin cefanen abincin sunane. Yace ayi amfani da shinkafar karolai dake jingine a wancan ɗakin dama sabida sunan ya siyo. Wannan na cefanene" Ta juya kuɗin ta ƙirga ta ƙirga tace. "To gaskiya sun yi kaɗan wannan fa sai dai ayi girki ɗaya. Tunda kinsan dai ba za'ayi gajiyayyen abinci ba. Abinci za'ayi na fita kunya yaji nama yaji kayan lambu ko?" Shiru nayi daman nasan za'a rina wallahi, ko nawa aka ba innah ko ya kai dubu ɗarine saita raina. Mu hidimar sha'aninmu na Kanuri muna cin nama da abinci masu kyau sosai. Amman nasan ai in su Yaya Saratu suka iso, za'asan duk yadda za'ayi abinci dai na fita raini za'ayi kala biyu. "To shikenan dai bari su Saratu suzo sai mu yanke abinda ya dace." Miƙewa tayi ta fita ta soke kuɗinnan a mararta ta fice. Shadda na koma na samu Luba na buɗewa abun mamaki shadda mai tsada, kuma wallahi ta sha surfani na zamanin, ɗinkinma riga da zanine, rigar ɗinkin hannun fanka, Allah yasa kunsan ɗinkin? har a zanin an yi surfani mai kyau, kuma sabon samfurine na surfani dan gaskiya ban taɓa ganin irinshi ba. Shaddar mai ruwan baƙin bulu ce, sai akayi mata surfani da zare mai kamar ja, kamar kalar hoda dai gashinan. Harda takalmi na ƴan burni baƙi, da mayafinshi na yayi shima baƙi. Sai sarƙa da ɗankunne mai ruwan gwal, sai ɗan diras guda shida, rigar umma guda shida. Sai atampa dinkin riga da siket, kuma koddibuwa atampar mai ruwan ganye, da ruwan madara. Sai kayan jarirai na hanga masu tsada kala biyar, harda takalmin yara. Murmushi nayi, nayi farin ciki nayi mamaki, mijinyawa ya sammaceni, kaya yayimun masu daraja. Madallah da mijinyawa. "Gaskiya surfanin shaddarnan yayi kyau sosai Hindu. Sosai gashi shaddar mai tsadace mai gidan kashe kalace fa." Wata nau'in shaddace mai wannan sunan, wadda aka buga yayinta a shekara ta dubu biyu, ko dubu biyu da ɗaya. Nasan wasu sun santa. Mai Gidan Canza Kala" (ko wacce wasu ke kira da Mai Gidan Kashe Kala) tana daya daga cikin shaddodi mafi ban mamaki da kayatarwa a wancan lokacin. Ga yadda take da kuma abubuwan da suka sa ta shahara. Sauya Launi, Babban abun da ya ba ta wannan sunan shi ne, yadda take sauya launi dangane da haske. Misali, idan kana cikin daki ko inuwa tana iya nuna kalar kore amma da zaran ka fita zuwa cikin rana ko karkashin wutar lantarki mai haske, sai ta koma kalar shudi, ko ruwan gwal. Tayi zamani sosai wannan shaddar. Mamakin inda har aka samu kuɗin wannan shaddar nake yi gaskiya. Amman koma yayane nasan daga baya zaimun bayani. Iyakar kunya ya fiddani, ni bamma sa aka zaimun kayan fitar suna ba, sabida bashi dashi na kuma sani. Zuwa la'asar sai muka jiyo tsayuwar mota ta bayan tagar ɗakina. Can kuwa sai yara suka soma shigo da kayayyaki a buhu, buhu suna durewa a tsakar gida. A lokacin duk muna ciki an kammala aikin Baraka nayi ma Azgar wanka ma lokacin. Su Yaya Saratune muka jiyosu ana gaisawa dasu Shafa a tsakar gida. Can sai gasu da sallamarsu sun shigo. Murna da jin daɗi ya kaure, akaita raha, ana dariya. Baraka na kammala wankan jariri ta miƙa musu, sukai mana sallama ita da Halima. Dama nace Baraka ta Ɗibi abinci ta tafi dashi, Innah da kanta ta zuba mata da nama zuƙu zuƙu. Saida su Yaya sukai sallah, suna cin abinci ana zuba hirar yaushe gamo da yadda suna zai kasance. Yaya Zunaiba ce ta jawo babban buhu ƙato shaƙe da kayan maijego atampopi da kayan jariri, su omo da sabulu kuwa suma buhunsu daban tare da tawul ɗin nabkin da ledar nabkin kun tunota mai ruwan hoda, wata mai ruwan madara ko? Rayuwa kenan. Atampopi, shaddajo, materiyal, leshi sunfi kala talatin wane talatin shi kanshi Azgar ya sami riguna masu tsada ni dai bansan guda nawa ba. Harda su takalmi da jaka fa. Sai kuma kayan cin suna Yaya Sojanmu da Akaramine sukaimun. Shadda biyu, lesiri biyu, atampa biyu, komai mai tsada fa. Shaddar ta gida ita kuma wagambari ce irin ta da mai tsada. Dan a wannan lokacin wagambari sai masu kuɗi, ko mulki ke sakata me kyan kenan. To mu dama kanuri har gobe wagambari tunƙawo da darajarmu ce, hatta a bukukuwanmu na al'adu. Du biyun itace. Ga lafayu masu kyau guda uku. Atampar daya holan daya hitaget ce manyan sosai. Leshin kuma mai gidan kwamfuta da mai wuri da azurfa wanda a wannan lokacin sune abun tunƙawo da alfahari. Sun yo cefanen girkin suna da duk abinda zasu buƙata hatta da man girkin da zasu yi sun tawo dashi. Su albasa, attaruhu duka dai, Sun tawo da lemukan kwalba kiret kiret. Harda hofuna mai ɗauke da sitika a jiki dake an faɗama su Innah sunan yaron ga sunanshi nan ɓaro ɓaro a jiki, wanda za'a rabama mutane, guda ɗari da hamsin akayi. Wacce aka rubuta tayi Rayya ce. Kayan gara da ragowar sauran gudunmawowin ƴan gidanmu, da abokan arziki Innah Abidah itace zata tawo dashi. Wannan da suka tawo dashi iyakar na ƴan ɗakinmu ne, dana Innarmu, da jama'arta na makaranta. Ga zanin gado mai bargo babba sun tawo mun dashi ja wanda zan saka ranar suna in sha Allah. Su Yaya Jamila saida Nanno ta turota ganin ƙwab, uwatale ma saida ta shigo wai gaida baƙi, Nanno dai wannan karon bata shigo ba dai anci sa'a. Kuma rikici sosai take ji, sau nawa suka yi da Innah akan batun wankan jariri da ake turo Innah Dubu, ita kuma Innah ta kafe tayi rantsuwa harda dukan ƙasa ta lashe. Kusan raba dare akayi anata shirye_shiryen yadda suna zai kasance cikin daraja. A lokacin ni kuma Innah tana yarfamun kitso ƙananu namu na al'ada, ga lalle lallaɓe an ƙunsamun a ƙafafuna da hannayena. Washegari akaci gaba da hada hada. Su Yaya Saratu suka tafi kasuwar cikin Bauchi da wannan nera dubu Hamsin ɗin, Innah ta ƙara dubu talatin a kai, su Yaya sunce zasu cika ashirin ɗin ya zama dubu ɗarin. Jama'a mu riƙe zumunci gam gam wallahi. Ƴan uwa abun wuyane. Ai ko rago sukutum suka siyo da ranshi tiƙeƙen gaske, da uba uban cefane rigijib. Gabaki ɗaya matan gidan sukai cirko_cirko a tsakar gida cike da illahirin mamaki. sai yamma sakaliya motoci ƴan gida suka ƙaraso bus biyu sukayi na masu ruwa suna. A lokacin ko minti ashirin su Yaya basu yi da dawowa daga cefsne ba. Ana wani irin ruwa kamar da bakin ƙwarya suka ƙaraso. Dama tun rana ake wannan ruwan ko abincin da za'a tarbesu dashi a ruwa su Yaya Saratu suka girka. Shinkafa ce dafa duka taji naman rago. Dan sun tawo da ɗanyen naman rago him, tun jiyan suka tafasashi sama_ sama aka barshi a tukunna, ko ɗazu da suka gama girkin ƴan gida sun kuma tafasa naman gudun kar yayi tsami.
Chapter 48 · 0% Book details