← Book details Tsuron Tsirin Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 84

Sashe 33

Tsuron Tsirin Part 3 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Mijinyawa:.
Jin jikin Hindu ya saki ne yasa ya juyo da sauri, taɓatan da yayi sai yaga ta koma baya halamun babu numfashi a tattare da'ita.
"Hindu! Hindu?".
Shiru babu Hindu babu ɗan dalilinta. Riƙeta gam yayi. Ya shiga yi mata karatu a kunnenta yaji shiru.
Jikinshi take ya soma rawa daidai tsayuwarsu a cikin tasha, harma an soma sauka.
" Baiwar Allah ki taimaka mun mu sauka da'ita. Iyalinace ta suma ne, asibiti kuma zamu je dan Allah"
Wata mata dake kusa da Hindu yaima magana.
A motar ya barsu ma, ya fita ya nemo mota ƙarama aka sa Hindu a ciki, yana riƙe da jakarta.
"Magawata lafiya Hindun ce babu lafiya ne?"
Juyowar da Mijiyawa zai yi sai yaga Harira ce.
"Harira Hindu babu lafiya bata ma san inda kanta yake ba. Dama wajenki muke son zuwa ki mana jagora wajen Hajiya Bara"
"To ai ni É—inma ganinnan da kayi mun, wajen naku zani. To ai sai mu shiga mota mu je asibitin"
Harira ta shiga gaban mota, mijinyawa yana baya tare da Hindu, kanta na bisa cinyarshi.

Jama'are:.

Da magriba Inna Yahanasu tayi sallama ta shigo cikin gidan. Matan gidan duk suna tsakar gidan.
"Ahuwanku dai masu gida, da fatan mun same ku lafiya? "
"Yauwa maraba lale baƙuwa."
"Wajen Hindu nazo, ni ƙanwar mahaifiyarta ce"
Shafa ta washere baki tace.
"Ayya, to Tatsaure kaita ɗakin Inna, Nanno tana wajen mai naƙuda bara a kirawo miki ita"
"Subhanallahi, naƙudar tazo ne. To Allah ya buɗi idanunta lafiya"
"To Ameen, amman ba Hindu bace matar Abokin tagwaitakanshi ne ke naƙuda. Muje in kai ki ciki"
Cewar Tatsaure. Kayanta suka kinkima jaka uku zuwa ciki.
"Baƙuwace da daddare haka Tatsaure? "
"Hmm ai ko dai Innah. Ƙanwar mahaifiyar Hindu ce tazo. Shine Yaya Shafa tace in kawota wajenki kafin a kira Nanno"
"Ayya, to ku shiga, baƙuwa maraba"
Shiga da Inna Yahanasu ciki akayi. Tana zaune ta jima, itace har bayan isha, kafin Nanno ta shigo.
"Hi haƙuri baƙuwa, ina wajen mai haihuwane, tun rana sai yanzu ta sauka, an samu ɗa namiji. Ance wai wajen Hindu kika zo ko? "
"Eh wajenta nazo"
"To basanan. Tun ɗazu muka fahimci basa gidan, kuma ɓarayinsu a kulle yake. Amman babu mamaki gidan Abdulƙadiri suka je. Zan aika yara su yo kiransu. Yauwa ai gara da Allah yasa kika zo. Gobe zan ɗauketa zuwa Toro akwai wani mai maganin gargajiya, to wajenshi zamu je ko za'a dace. Abunka da mai makarai babu mamaki su suka riƙe cikin. To kinji"
Innah Yahanasu tace.
"Wanne irin maganin gargajiya ne kuma? Ai asibiti gobe zan É—auketa in kaita. Babu wani maganin gargajiya da za'ayi."
"Au Allah ishasshiya, a matsayinki na wa kenan? Ashe ba da arziki kika zo ba kenan? "
"A matsayina na uwarta, banzo da arziki ba. Duk abinda kike ji dashi kin tara kin samu, alo tsiya alo danja. Kano ma zan tafi da Hindu kuma ko mijinta baida fawa, balle ke"

To mu kwana anan sai in Allah ya kaimu Monday kuma in sha Allah
Son so💪🏼💪🏼💪🏼MRS BUKHARI

.........

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/JVdGBW8N6iFFBHyPGYXdrF?s=sw&p=a&ilr=0

*Kin Dade kina neman Adashin gatan da zaki shiga ki rika Tara kudi kadan kadan ki kwashi idan nace Miki kaya hajiya ta ina nufin komai ga Anty zee nazo muku da Tsarin adashi ki rika Tara kudin ki kadan kadan ki kwashi duk abunda kike so, akwai bangaren kayan sawa na Yara Dana manya, akwai kayan kitchen, akwai sarkoki ,takalma , jakuku Nan Yan gayu, mayafai dadai sauran su me kuke jira maza ku shigo ku fara tari tun yanzu* 💃💃

"In mijinta bai isaba, ni uwarshi na isa har nayi yawa ma. Babu inda za'a ɗauke mishi mata a kaita wallahi. Kinsan Allah ko wankan jego bata isa taje ba. Asibiti dai bama zuwa akan Hindu kuma ba za'aje ba to kinji. In sama da ƙasa haɗewa zata yi, to sai dai ta haɗe babu asibiti a gidannan"
Innah Yahanasu ta dubi Nanno tace.
"Zaki ga inda ake mulkar mutum har fadarshi kuwa. Hindu ɗiyata ce, ƙafata ƙafarta zan tafi da'ita Kano, ke Maiduguri ma zan wuce da'ita inga ta tsiya. Tunda ke kam baki da mutumci tabbatacciyar maras ɗa'a"
Innah Dubu ce ta shigo da sauri tace.
"Haba baƙuwa, haba Yaya ku yi haƙuri. Mufa surukan junane, ai bai kamata ma ace ana wannan hatsaniyar ba. Baiwar Allah Hindu dai sun fita zansa Tsalha yanzunnan yaje ya kirawosu su dawo. A yi haƙuri wannan faɗace_faɗacen a watsar dashi"
Kafin Nanno tayi magana Yaya Jamila ta leƙo.
"Nanno jini ya ɓallema Uwatale fa, sai kin zo."
Fita tayi da sauri tana
"Ina kofi a jiƙa manda, a ɗebi ganyen gwanda dana dafa da tsamiya, ha haɗa da mandan, ta kafa kai tasha maza kafin jininta ya ƙare. Wannan yarinya taji jiki."
Nan Nanno ta wuce ta bar Innah Yahanasu.
Innah Dubu kuma ta tura Tsalha kiransu Hindu a gidan Abdulƙadiri, duk tunaninsu can suka tafi.
Tuwo ta kawo ma baƙuwa, tuwon masara miyar bushasshiyar kuɓewa da naman rago a ciki yanka ɗaya jol, sai kakide da aka sa mata da yajin daddawa.
"Ga abinci dan Allah kici. Duk abinda ya faru kiyi haƙuri. Yaya ce bata da haƙuri sam"
"Babu komai nagode, ni ɗinnan da kika ganni na fita rashin haƙuri, nata ai wasane. Da Allah inaso zan yi alwala in yi sallah kafin ita Hindun tazo"
Innah Dubu ta nuna mata wajen alwala, ta dawo ta shinfiÉ—a mata tabarma ta fita zuwa bakin murhu tana raba tuwon dare.

Asibiti:.
Chapter 33 · 0% Book details