Sashe 83
Tsuron Tsirin Part 3 Complete Hausa Novel · about 9 min read
Mun jima sosai a haka kafin yayi shiru.
"Me yasa kike ta wahalar da kanki a kaina ne?"
Ba wahala bace, ai duk abinda zanyi na alkhairi ma wani, ko wata zan samu lada mai yawan gaske. Ballantana abinda zan yi maka kai da kake uban Æ´aÆ´ana. Babu asara a yin alkhairi, ko da kai akasin hakan aka baka. Baya nufin naka alkhairin ya zube, yananan yadda yake a wajen Allah"
"Uban Æ´aÆ´anki? "
Sai yayi murmushi ya sauke kanshi kawai.
A wannan daren, mun tattauna abubuwa masu yawan gaske, da ƙyar ma bacci ɓarawo ya sacemu. Daren ya kasance mana wani irin dare mai cike da gurika, gami da yaƙini akan Allah zai shiga cikin lamarin karatun mijinyawa ya taɓa.
Da safe dai na ɗumama mana wannan masa, da naman kan saniya, sai shayi mai kayan ƙamshi dana dafa, Iya Halima kawai, sikarin ta ashirin ce aka siyo.
Mu kuma ruwa muka sha abunmu, sai mijinyawa dana É—an tsiyayama shayin.
"To ni kam mijinyawa zan tafi, naga Hindu ta kintsa zata tafi aiki, ga yara duk sun shirya suma. Am Magawata nace in Asama'u suka samu hutu, inaso in zo in É—auketa, ina wannan barar"
"Aa Halima ai basa samun hutun da har zata yi wata tafiya, kana suna karatun Islamiyya sosai, yarannan basu da wani hutun da har zaki ɗauki Asama'u. Kuma in taje Azgar irin shaƙuwar dake tsakaninsu, bazai ji daɗi ba. Kamar dai yadda aka saba kya dinga zuwa ganinta"
Murmushi tayi mai fassara, ni naso ma ya amince kar Halima taga kamar an tauyeta.
"Ka duba dai dan Allah"
"To zan duba zuwa lokacin da kika yi Aure. Kinsan ai bazan baki yarinya bakya gidan iyayenki ba, bakya gidan mijinki ba. Wannan ganganci kenan Halima"
Ai kamar an sosa mata inda ke mata ƙaiƙayi sai ta miƙe.
"To inason ganinka a waje kafin in tafi, akan batun aurenne. Hindu ni zan tafi"
Ki gaida gida Halima"
Mijinyawa yaso ƙin zuwa, ni nace mai yaje yaji koma menene. Nayi mai ishara da idanuna.
Saida ya gallamun harara kana ya fice.
Zancan na aurenne dai, dan rai a ɓace ya shigo yana ta faɗa. Ni ko sai dariya nake yi mishi.
Gaga_gaga_gaga
Haka akaita bugawa, rayuwa taci gaba da tafiya.
Har Allah ya kawomu ranar da mijinyawa ya zauna a ajin jama'a ranar farko.
Ya samu bizines admistireshon, na mance ban faÉ—a muku fannin da yake ba.
Nan aka soma buga karatu.
Ranar farko haka ya dawo daga makaranta idanunshi jawur.
Na tambayeshi ya karatu.
"Karatu ko wahala, kinji wani turanci wai da malaminnan yake mana, itama wata mace da bata wuceki ba, baki ji turanci ba. Ni bana ma gane komai"
Mijinyawa hoo wato yanzu turancin yafi karatun wahala kenan?"
Idanunshi ya zare.
"Ina gara ma turancin ina ɗan gane ƙanana, amman karatun, bama zan iya ce miki dame_dame akayi ba. Ɗan ƙarfin guiwar dana samu ma ɗayane. Bani kaɗaine babba a ajin ba, akwai kamata, harma da wani magidanci wanda gaskiya babbane"
Dariya na fashe dashi, shi kuma sai hararata yake yi.
Kace da sauƙi tunda kaga wanda ya fika. Jami'ace fa, ai sai kaga tsoho ma"
"Woo ba zaki gane bane Hindu, su sun iya turanci fa. Harma gabatar da kanshi wani yayi a gaban duka ajin. Ke kinji turanci? Wallahi yayi masifar burgeni. Ƙiris yarage in yi tafi fa"
Dariyace taci ƙarfina. Ai sai ya ɗauki jakarshi ya shige ciki, a guje na bishi ina ci gaba da dariyata.
"Haka fa Qasimu yake mun. Duk bala'in da zan shiga, wallahi duk masifa sai yayi dariya"
Ni naita ƙarfafashi ina nusar dashi.
Nan muka shiga yin lesin, darasi sosai muke yi, zan iya cewa kusan tare muke karatun, wani digirin nima nake haÉ—awa kuma hakan ya taimakeni gaya.
Ƴan gidanmu babu mahalukin da bai yi mamakin komawarshi makaranta ba.
Haka danginshi da abun ya iskesu, Yaya Jamila ce tazo tai ta zazzaga, Nanno dai wai tana ƙauye zazzaɓi ya lulluɓeta, tana ta kuka wai za'a kafurta mata ɗa.
Saida yaje ƙauyen Kawu ya shawo kan lamarin.
Uwatale kuwa irin ruɗun data shiga yana da girma, wallahi bazai rubutu ba. Zazzaɓine ya bigeta, jikinta yaita rawa kakakar_kakakar.
Ranar asabar na ƙarshen satin Mijinyawa na farko a makaranta. Da yamma muna zaune muka jiyo sallamar Baba Sojanmu da Innarmu, sun zo ta ya mijinyawa murna.
Rungumeshi Baba Sojanmu yayi, yana ta bubbuga bayanshi.
Ni dai farin ciki tamkar ya halakani wallahi. Yau ga Baba Sojanmu rungume da mijinyawa suna cikin aminci.
Fita damu Baba Soja yayi, zuwa wani gidan cin abinci. Yayi mana odar abinci, muna ci yana ƙarama mijinyawa bayani akan amfanin ilimi, da ribar auren mace mai ilimi. Yace dashi da ba dan ya auri mace mai ilimi ba, ba lallai ne yayi tunanin inganta rayuwarshi ba, babu lallai yayi tunanin komawa karatu.
Baba Sojanmu harda kyauta ya kawo mai na agogo, da turare.
Gaga_gaga_gaga
Nike riƙe da komai kamar yadda nayi alƙawari, da daɗi babu daɗi dai haka aketa gurgurawa, kamar yadda na alƙarwanta. Wataran naje aiki a ƙafa, shima mijinyawa yaje makaranta a ƙafa, haka dai.
Ganin wahalar da muke sha, da irin dariyar da Uwatale ke yi da habaici, shi ya tura mijinyawa ya dage akan karatun haiƙa. Nawata ma cewa yayi asarar kuɗi da lokaci. Wannan kalmar ta dakeni sosai.
Shigarsu mataki na biyu ke da wuya na samu aiki a wani gidan rediyo buri ya cika.
Albashin dai babu yawa, amman yafi na koyarwa.
Watana shida da wannan gidan Rediyon Baba Sojanmu ya sama mana wani gidan rediyon ni da Luba.
Sai abubuwa suka soma mun sauƙi, suna warwarewa a hankali. Rayuwa kenan shirin Allah.
Sabira ta girma, ga surutu sai ta shiga Islamiyya da wuri, da'ita su Azgar ke tafiya su ajjiyeta gidan Yaya.
Rayuwa tai ta haske, wahala tana raguwa.
Allah cikin ikonshi da Amincewarshi har mijinyawa ya kammala karatunshi, munci kwakws tabbas.
Sai yawon neman kuma aiki, ga yara sun girma suna taimakona sosai, musamman Azgar dake da karanbanin son girki, a hankali a hankali ya dinga koya, yana maida hankali.
To kwatsam sai ciwon makarai suka dawo sabo ta yarda har saida na rasa aikina. Ciwo magashiyyan nake yi.
A lokacin na sake sanin daɗin ƴaƴa, mijinyawa ya samu wata makaranta yana ɗan riƙon aji, dole zai fita sabida ni bani da aiki, yaranne zasu yi mun komai Sabira na biye dasu, shi kuma in ya dawo daga koyarwa, zai mana wanki, da abincin dare. Inajin daɗin irin haɗin kansu, da irin yadda suke son junansu a kusa.
Ina ba matan da basu taɓa haihuwa ba shawarar, ko ƴaƴan ƴan uwa, ta roƙa a bata ƙarami sosai. Ko ta sanarma danginta da mijinta, ta ɗakko a gidan marayu da yardarsu, bance dole sai kinyi irin na Hindu, dama ire _iren mata irina da suka zaɓi ɓoyewa ba.
Irinmu sunanan suna rayuwa a cikinku, ba tare da kunsan ƴaƴansu daga gidan marayu suka ɗakko ba. Ƴaƴa rahamane sosai, kar ki zauna kita tunani, ki kashe rayuwarki akan abinda Allah kaɗai ke yi. Ɗakko riƙo ki riƙe da zuchiya ɗaya. Ina mai ba ki shawara in zaki ɗakko ki ɗakko namiji, kada ki sake ki karɓi mace, ni dai na faɗa miki ne bes ob esfiriyans.
Haka dai nayi kusan wata huÉ—u yau lafiya, gobe ciwo. Ko kuma dare nayi ba bacci, gari na wayewa kamar bani ba.
Duk na kumbura na fita hayyacina, hankalin su Baba Sojanmu da mijinyawa duk a kaina.
Bamu nan, bamu can gidajen magani.
Gaga_gaga_gaga
Rayuwa ta shura, mijinyawa ya samu aiki a bankin farko, ta dalilin wani abokin Baba Sojanmu.
Ni kuma Baba Sojanmu, ya sake nema mun aiki a gidan rediyo Kano tare da Luba.
Wannan samuwar aikin shine warwarewar komai na rayuwarmu, silar shiga sabuwar matsala. Haka fa Ubangiji yake ikonshi.
Da sannu, muna ta samun ƙarin albashi, da sannu munata adashe, da sannu rayuwa nata shurawa.
Mijinyawa yana siyo komai na hatsi ya ajjiye, cefanen kayan miya, kifi nama yawanci nafi yi ni. Sai in abu ya ƙare ni zan yi saurin siyowa.
Ya sauyamun komai na É—akina a wani adashe daya soma yi, tare da abokan aikinshi.
Yasan nawane tarina, nasan nawane tarinshi.
Zan iya cire kuɗi a asusunshi, in yi abinda zanyi. Bai taɓa jin menene dalili ba. Haka zalika nima, haka zai cire kuɗi, me yayi, mai zai yi? Bana tambaya.
Mun yarda da juna, mun gamsu da juna, sam_sam bana tunanin akwai abinda a duniya zai sauyamun mijinyawa ba. Amman sai dai kash, kaico.
Mijinyawa Shine siyan man injin babba daya siya, kowa na gidan in an kunna yana amfana, sabida yace Nawata shima yayi nashi ƙoƙarin, na bamu wajen zama, ruwan famfo, wutar lantarki.
To a wannan gaɓar da muke zuwa aiki dukkanmu ne, Uwatale mutuniyarku, naga masoya gareta ko? wata dai tace tana hangota a mai sakakken baki.
Ta samu aikin asibiti a wani asibiti mai zaman kanshi a matsayin. Ward atendans, masu tura gadajen marasa lafiya, masu kai gwajin jini lab, masu shinfiɗa zanin gado, duk dai sune ward atendans ɗin. Wannan shine aikin uwatale a wani katafaren asibiti mai zaman kanshi, wanda an ɗauketane sanadin shi Nawata yasan mijin mai Asibitin, asibitin na mace ne, kuma itama Uwatalen ya kaita gidan matar, sai aka bata aikin sabida sanayya, tunda aikine wanda ba dole sai da kwalin karatu ba akeyi. Kuma suma suna yin tsarin karɓi in karɓa wannan yasa take aikin dare.
Tunda muna fita aiki, tofa itama shine dole sai tayi. Dakta ma wani sa'in Nawata ke kiranta in iskancinshi ya motsa. Dan mugun bugun ƙirji yake yi da wannan aiki.
Uwatale kab unguwa ƙarya take musu a matsayin wani aikin take yi babba, ba irin wanda ake tunani ba. Tana sa fararen kaya, da guntun hijab irinna sistas ɗin asibiti, tamkar nos haka zaku ɗauka, in kuka ganta.
Hatta su Nanno tunaninsu kawai uwatale malamar jinyace. Wannan kenan, yau dai kunji hankalinku ya kwanta dai ko? Hahahhh...
To tun kafin al'amura su gama warwaremun da kyau, na ɗan soma yin gajerun bidiyoyi na ba mata shawarwari, akan yadda zasu inganta rayuwarsu, da yadda zata kula da kanta ma ita macen. Sabida a aikina da nayi na gidan jarida, ai ina zuwa hotu ɗakko rahoto, na ƙara sanin Allah da girma yake, na ƙara sanin mata na buƙatar mai taimaka musu ko da shawarane.
Da haka na soma, ina ɗan watsawa shafukan sadarwa, sannan akwai wani shiri na zamantakewa dana yi riƙon ƙwaryarshi, shima yayi mun ido, ta yadda nafi tattauna matsalolin mata akan abubuwa biyar da suka fi dakushe ma da yawan mata rayuwa. ( zaku ji a gaba)
Wani bidiyo da muka yi da mijinyawa shima ya tofa albarkacin bakinshi, wannan bidiyo ya taɓa zukata. Akan wata ce da mijin ya maidata kamar injin ɗin buga kuɗinshi. Haɗata yake yi da maza manyan masu muƙami, taje ta kwanta dasu, a bata kuɗin sai ta kawo mai. Data gaji sai ta neme ni ta kirani a waya ta labartamun.
A dalilin wannan kes ɗinne, muka yi bidiyo muna masu jan hankalin iyaye akan mahimmancin bama yara ilimi, da mahimmancin jan yara a jiki su shaƙu da ku. Dan wannan harda ƙarancin ilimin addini, da rashin sanin madafar rayuwa.
Wannan bidiyo shine mabuÉ—i, ko ince matattakalar dana tattaka na shiga lamarin mata sosai.
Wasu shawara kawai suke so, wata rarrashinta kawai take so in yi. Wata so take kawai ta bani labarinta inji, dan ko na bata shawara ba É—auka zata yi, labarin kawai take so ta bayar.
Mun yi bidiyo biyu uku da mijinyawa.
To bidiyo har jama'are aka kaima Nanno ta gani.
Da muka je zo kuga rikici da cin kashin da Nanno tayi mun, abun ba'a cewa dai komai.
Saina dawo bidiyona ni kaÉ—ai. Bidiyonma sai na daina sai É—an rubutu dai haka. Da haka na dinga tara mata ina sakasu a zaurena dana buÉ—e.
Wannan shine tarihin aikina na agajin mata da nake yi.