Sashe 81
Tsuron Tsirin Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
babu sisin kwabona a ciki. Sannan dan Allah kiyi haƙuri ki dena batun barin makaranta alƙawarine na ɗauka nake ƙoƙarin saukewa. Sharaɗine a kaina" Ai ina wuta tasa Mijinyawa, ta dinga surfa faɗa harfa da kukanta. Ta jima tana faɗannan, wallahi data gama faɗanta fes, sai ta mimmiƙe a saman kujera wai anan tare damu zata kwana. Mijinyawa ya kalleni nima shi nake kallo kawai babu baki sai idanu. Yafitoni yayi muka fita waje. "Yanzu ya zamu yi ko in je in nemi wajen kwana in bar muku nan ɗin?" Hmm aa ka shiga kayi kwanciyarka da yara a ciki, ni zan kwanta a falon, dare yayi, ai gara ka shiga, ga gajiya ka kwaso. Amman fa zanje makaranta kasan jarabawa nake yi, kuma zan iya juran komai banda batun daƙile karatuna, ko aikina wallahi kaji na faɗa da manyan baƙi" Ina faɗin haka nayi shigowata, ciki na shiga na ɗakko fulo da bargo na shinfiɗa, Asama'una na ɗakko, na shinfiɗe a gefena shi da Azgar kuma suka kwanta a ciki. Munsharin Nanno bai barni na runtsaba, da nayi karatu sai na dinga nafila kawai sai wajajen daf asuba na kwanta. Safiya nayi na haɗa duk wani abun kari na ajjiye a falo, Nanno na zaune tana kallona. Na shirya ƴan makaranta. Ni dai ficewata nayi na barsu ita da ɗanta nayi shigewata makaranta. Nasan dai cinyeshi ne kawai ba zata yi ba. Me akayi, ya suka ƙare? Ban sani ba sam. Ku tambayeni mai ya faru to bayan dawowata. Ina dawowa na shiga gida da sallamata, sai naci karo da bokitina na wanka a fashe, a kuma yashe a tsakar gida. "Hala baki san kun tashi a gidan bane ko Maman Asama'u? Ai kun koma gidansu Maman Zainab tun safe" Cewar Maman Zailani ƙawar uwar gulma. Sai naji abun yana jujjuyamun a kaina, mun koma gidansu Uwatale, sabida me, me yasa to? Bani da amsar wannan tambayar, saida na shiga na tabbatar da zancanta kafin na juya, su Azgar na biye dani. Ina fita naci karo da Mijinyawa idanunshi sun kaɗa sunyi jawur kuma tabbas yayi kuka, ganin irin matsanancin tashin hankalin da yake ciki, sai na sake fuskata sawai, sabida ya samu sanyi, salama daga gareni, duk da ni ɗin bai sanyayashin, nima fa a cikin zafi da zugi nake. Barka yallaɓai daga ina, yau babu aikinne? " Sai ya ɗan murmusa. "Yaushe zanje aiki Hindu, ai tun fitarki ake ɗauki babu daɗi. Harma dai yanzu mun koma gidan Nawata bisa umarnin ko in koma ko Nanno ta ɗaga mun nono. Kuma sharaɗine ta bani akan ko mu rabu, ko ki dena makaranta, ko kuma mu koma gidan Nawata. Shine na zaɓi komawa can ɗin. Nasan zaman gidan ƙuncine, takurane a garemu bai ɗaya. Amman me? Allah yana ji, Hindu yana ganin komai" Ba zamu ga haka ba. Allah yasa haka shine mafi alkhairi. Amman wallahi bazan ajjiye karatuna ba, kuma zanyi aiki inata jaddadawa" "Har yanzu roƙon da nake ta faman yima Nanno kenan. Amman wallahi ta kafe a wannan karon tace babu gudu babu ja da baya. Amman ina kan lallaɓata kafin ta koma dan jimawa tace zata yi. Kinsan mun fa gama magana ta ban sharaɗi. Tana komawa gidan Nawata, sai kawai tace ita bata yarda da wannan sharaɗin ba, kawai karatun take so a ajjiye. Mujenku yaran Abba" Ya kama hannun su Azgar ina gaba suna bani kariya. Kunsan menene? Bana wani iya kallon gabana, ƙafata nake jefawa kawai, kana ko wacce adda'a na tuna yinta nake yi kawai har muka isa ƙofar gidan. "Hindu" Juyowa nayi na dubeshi, sai muka yi murmushi kawai, ya haɗiye abunda zaice, ni kuma bance mishi me yake son cewa ba. Babu abunda nake buƙata face in yi sallah in kwanta kaina tsagewa yake shirin yi. Ga karatun jarabawa dake jirana. Da sallama na shiga gidan fuskata sawai sawai tamkar ba'a gumamun ba. Nanno na tsakar gida tana tankaɗema Uwatale garin tuwo, ita kuma mandiyar wanke_wanke take yi. Gidan kaca_kaca da tsummokarai, da tarkace kona menene oho. "Ahh kin dawo ashe, kinje can gidanku na da kika tarar kun dawo nan ko?" Eh naje, kai nayi murna sosai gidan haya ai sai dole, kinga nan ko hankalinmu kwance, mutum bashi da fargabar notis, ko na kuɗin haya. Sannu Nanno da aiki" Uwatale sai tayi turus, ba haka taso ba, so tayi in nuna ɓacin raina, ko inyi faɗa ita dai ta kai Hindu ƙasa, batasan ba wajen bane. Nanno dai bata tanka mun ba, ina tsaye mijinyawa ya shigo ya buɗe mun ɗakina na shiga da ƙafar dama bakina da adda'a ta neman tsari. Ɗakin na ƙarema kallo, kayan kujeruna duk sun zauna, sai dai babu filin tsakar ɗaki baifi mutum uku suyi sallah ba, iyakar filin kenan. Uwarɗakina na wuce kayan kicin ɗina suna zazzaune da ƙafafunsu, gadonma ba'a ko kafa ba. Ga sib mai ƙofa shida suturu duk a gefe dai. Inaso in yi alwala, kuma kamar ba ruwa ko?" Na dubi mijinyawa dake ta wasa da yara. "Akwai a bokiti a falo dana ɗebo kaɗanne" A bawo nayi alwalata na kabbara sallah, na daɗe sosai goshina a ƙasa. Wallahi kafinma in sallame Ubangijina maji roƙon bayinshi, ya yayemun duk wani damuwa, da ƙuncin zuchiya. Da ƙarfina na shiga aikace_aikacena. Mijinyawa kam kafin in idar Nanno ta doka mai kira ya fita a guje. Inaji tana farfaɗamai magana. Haka naita aikinnan kayan Kicin wasu a ƙarƙashin gado, ragowar duk na ɗura a sib ƙofa biyu cike da kayan kicin ɗina, sai kurfo ɗina na ajjiyeshi a gefe can wajen sib. Saida na share ko'ina dako ina, kana na fito da wannan bawo na zubar da ruwan alwalar a magudana. Ba kowa a tsakar gidan, ga abinci dai a murhu garin tuwo kaca _kaca a kan duwatsun murhun, dama bakin tukunyar. Ƙaramar randata na buɗe sai naga cike take tab da ruwa. Ciki na koma na ɗakko bokiti ina zuba ruwa Zainab ta fito. Ke inane bayan gidanku? Ta nuna mun da yatsa. Toka da omo na ɗauka na shiga banɗakin, a wanke dai yake babu laifi, sai zarni da ƙarni da yake yi. Zagewa nayi na wanke tas, na ɗebi ruwa nayi wanka tare da alwala. Na fito kenan Uwatale itama ta fito daga bayin ba haya, dake a rabe suke. "Ashe kece kike ta wanke banɗaki, ai a wanke yake tas Nawata yasa na wanke sabida ku" Funfurunfus nayi mata, nayi shigewata ɗaki, lokacin magriba ma tayi, ga wuta ma an kawo. Risho na kunna na rura gawayi na kunna turaren wuta. Ban ko shafa mai ba, na nemi rigar yadi mai sauƙi kwatin na saka, tare da gabatar da sallah. Ina ƙoƙarin rufe taga dake a layi tagar take ba irin ta cikin gida bane, tagar falo ne take cikin tsakar gidan. Mijinyawa na gani a wajen tagar da ledojin cefanenshi. "Yauwa inata adda'ar Allah yasa baki rufe tagarnan ba. Ungo kayan cefanennan ga kalanzir a gora ma na siyo, ɗan abinda ya samu ki girka zanje in taɓa aikin dare ni saina dawo kawai" Karɓa nayi, tare da mai adda'a. Ina tsaye a jikin tagar ina kallonshi yana tafe a tsanake. Rufewa nayi kawai na shiga aiki. Shinkafa da wake na ɗaura, bana jin zan iya jajjage kaina ciwo yake yi sosai. A uwar ɗakina na kunna rushona dan wannan datti bazan iya dashi ba, ko babu datti bazan iya girki a tsakar wannan gidan ba, uwatale na leƙamun tukunya, tana kallon abunda zata tattara ta kai rahoto ba. Sai bayan isha na kammala girkina, na toya mai. Saida na zuba ma yara nasu, kana na ɗauki kwanon dana zuba ma Nanno na fita. Suna tsakar gida, sai tuwo suke ci, a faranti ɗaya dukkansu suke cin abincin harda Nanno. Kwanan na ajjiye. Ga abinci Nanno" Bata ko kalleni ba, dama na ayyana hakan tabbas. Shigewata ciki nayi, na samu Asama'u taƙi cin abinci. Zo uwata mu ci tare to" Sai ta soma murna, tare muka ci abincin inayi ina ɗan karatuna. Yara sun yi bacci wajajen takwas da kaɗan bayan sun gama aikin da aka basu na makatanta. Ni kuma karatu nake ta faman ci, har zuwa wannan lokacin ina jiyo hirarsu Nanno a tsakar gida, harma da Nawata duk ina jiyosu, dan sosai suke ɗaga murya harma na saba nikam. Sai wajen sha biyu saura naji an ƙwanƙwasa mun taga, da sauri na isa wajen. Waye" "Mijinyawa ne" Da sauri na buɗe. Leda ya miƙo mun, baice uffan ba ya zagayo zuwa ciki. Ai kuwa Nanno na jiranshi, ashe a tsakar gidan ta soma bacci ita dai sai taga shigowarshi taga mai ya tawo dashi. Falo na dawo na zauna. Ina jiyo bambaminta amman bana gane abunda take cewa. Da ƙyar ya yakice ya shigo, idonshi kawai na kalla nasan ya galabaita gaya. Tarbanshi nayi da ledar hannunshi na zaunar dashi, tare da yi mai hidima. Naso ya soma wanka, amman yace mun rabonshi da abinci tun karin safe, yako ci abinci sosai na zuba mishi tsiren daya kawo akan abincinshi, nawa na bari sai da safe sai muci da yara. Na tambayeshi shin ya ba nanno nata tsiren.? "Kaza ma na sai mata rabi, wannan tsiren nasan inta gani duka zata haɗa shiyasa. Muita haƙuri har Allah yasa a rabu lafiya. Nace dashi. Watarana ai sai labari. Wanka yaje yayo, mun jima sosai muna tattaunawa kana mukai baccinmu. Washegari ma sassafe nayi ficewata, na barshi akan ya kullemun ƙofata in zai fita, na ɗauki sifiya ki. Ai ina fitowa Nanno ta riƙeni carab wai babu inda zani harda kukanta. Aka buga, aka buga, aka kaɗa, aka raya taƙi, ga lokaci na ta tafiya, kuma jarabawa garemu. A ranar da ni mai kukace, da kuka zanci wallahi harda birgima, amman dake ba mai kukan bace, sai ido kawai. Uwatalece ta saka baki ta dinga lallaɓa Nanno, kana ta sakeni, na ja hannun yara muka fita ko tari ban ba. Har naje makaranta na dawo, inata tubkewa da warwarewa. Wai shikenan ni Hindu babu wani ƙwanciyar hankali da zan iya samu ko da na ɗan ƙanƙanin lokaci ne daga dangin mijinyawa? To yaushe wannan ƙoyayyar zata zo ƙarshene? Yaushe zasu gane Hindu bata nufin kowa da sharri? Wata zuchiyar tace. Muddin Uwatale,