← Book details Tsuron Tsirin Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 84

Sashe 29

Tsuron Tsirin Part 3 Complete Hausa Novel · about 2 min read

kawai yace. "Hmm Allah fidda A'i daga roro. Akwai kwantaccen rikicin da bansan a ina zai tsaya ba Tutar so. Allah ya bani ikon cinye wannan jarabawar. Nanno ba zata ɗauki haihuwa a asibiti da sauƙi ba. Sannan mahaifa ya zamu yi da batun buso, jinin da ake buƙatar a gani a zani wanda nake ganin in su Shafa sun haihu ana wauwankewa a tsakar gida duk ya za'ayi dasu Hindu?" Idanuna na lumshe, ƙirjina da zuchiyata suna ta kokawa. Ni duk babu wannan a tunanina. Tunanina shine a samu yaron tukunna shine mai mahimmanci. Kai dai muci gaba da adda'a. Allah zai mana mafita" Haka muka kwana da zulumi, ni kam akan sallaya na kwana cur, idanuna a kangare, a soye, a bubbushe, ƙayau_ƙauyau. Ƙarfe takwas Nanno na fita maƙota karɓan haihuwa, muka fice cikin hanzari, da leda a hannun Mijinyawa, kayan jira jiraine a ciki wanda zamu kaima Harira. Kasuwa muka soma zuwa muka sai setin bahun na wankan yara, da riyo babba mai murfi daban, sai ƙarami mai murfi biyu dake manne gefe da gefe, me ruwan omo muka samu. A wajen na sai tawul ɗin nabkin, ledar labkin, da kayayyakin da muka samu. Kai tsaye sai gidan Harira, fita ma take shirin yi, ganinmu ne ya kawo mata tsaiko. "Allah gwanin hikima. Nace ko wata hikimar kika yi ne, har kika rikiɗe sak mai cikin gaske, irin wannan kumburin ma ai yayi yawa. Allah sarki Ubangiji Allah ya rufa asirinku a samu wannan jariri a baku, wallahi tunda aka shiga wata tarannan ni kaina sai faɗuwar gaba nake yi." Hmmm Harira, ciwone ke sani wannan kumburin, wannan yafi ƙarfin na masu ciki ai." "To Ubangiji Allah ya sauwaƙe. Yanzu dai muje gidan marayun mu samu Hajiya Bara mu san halin da ake ciki" Muka ɗunguma zuwa gidan marayu, Hajiya Bara na zaune a ofishinta ta gammu kwatsam. Itama ta jinjina halin data ganni a ciki sosai. "Toh labari marar daɗi, har zuwa yanzu ba'a samu jarirai sabuwar haihuwa ba. Ke ko sati ɗaya da haihuwa ko biyu, ba'a samu ba. Dama ban rufe muku ba ba'a fiye samu ba. Mata da yawa sunyi irin naku daga ƙarshe sai cewa suka yi an haihu ɗan babu rai kawai. Wasu kuma da haka asirinsu ya tonu. Abinda zance daku ku ƙara wata guda wata goma kenan, in ba'a samu ba shikenan zan taimaka muku a samu gawa a asibiti wanda suke mutuwa iyayensu su gudu su bar gawar a asibiti, asibiti kuma ta adana a mutuware. Inaga sai dai ayi hakan. Kuyi haƙuri"
Chapter 29 · 0% Book details