← Book details Tabarmar Kashi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 84 OF 171

Sashe 84

Tabarmar Kashi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zuzzurfan tunani nadeeya ta shiga,daya bayan daya qwaqwalwarta ke mata bitar maganganun da sukayi da afifa,akwai abubuwa da suka bata mamaki tausayi da kuma daure kai,ashe already yaa toufeeq da anty N din sunsan juna?,but itafa laifin yayanta take gani to be frankly,a nan bataga laifin sãahar ba,cikar diya macen kenan ko ita ba zata dauki izzar d'a namiji ba. Amma abinda yafi gigitata rayuwar da säahar din ta fuskanta,wadda ta tilastata sauyawa daga ainihin dabi'unta. Abu mafi ban mamakin shine daya zamana wai ta taba aure,babu abinda zai nuna maka alamun hakan tattare da ita tafi miliyoyin 'yammata cikar haiba da komai na halitta. Sake juya kanta tayi wata shawara me girma na tsargawa cikin ranta,sai ta kira sunan
Dr da

"Abbana"

"'Ya akayi?" Ya tambayi nadeeyan yana qoqarin ajiye wayarsa bayan ya gama duba wani abu.
Idanunta suka dan kai kan wayar,sai taga kamar hoton MAJI dinta

"Abba dama kana da hoton maji ne?" Bakinta ya subuce ta jefa masa tambayar,don basu taba magana makamanciyar irin wannan baidanunta a kansa tana kallonsa. Harara ya watsa mata

"Yau nine na koma abokin wasanki?" Janye dubanta tayi zuciyarta da gwiwarta tana karyewa

"Kayi haquri" ta fada a sanyaye,sai yaji tausayinta ya kamashi

"Me ya faru kika kira sunana?" Gara zamanta tayi

"Ka taba sanin wani abu akan anty säahar?"
Shuru ya danyi sannan ya girgiza kai

"A'ah,akwai wani abunne?,mahaifinta Dr mamman munyi karatu dashi tsahon shekara biyar,sanann musan juna sosai a wancan lokacin,yanayi da lokaci ya jefa kowa inda yaso sai kuma aka rabu,sai bayan dogon lokaci bayan mun hadu da muhyiddeen na
fahimci dansa ne,shekaru masu yawa kuma
sai yau Allah ya gaddara ganawarmu" kai ta
jinjina,sannan ta warwarewa dr jarma din
kome data ji daga afifa.

Tsahon lokaci yana jinjina kai ba tare da
yace komai ba

"Amma abba ni ina da shawara" juyawa yayi ya
dubeta
"Wacce irin shawara ce?"

******Tun daren ranar da aka kawota take
magale da sãahar,duk inda ta motsa sai ta
bita gafarta qafartaji takeyi kamar zata gudu
ta barta. Ko da sukazo kwanciya sai data
rungumeta sosai,a haka bacci yayi awon gaba da ita.
Afifa na gefe tana kallonsu,dariya tayi lokacin da take zare jikinta daga na nadeeyan a hankali

"Ah kin hadu fa da chewing gum" murmushi sãahar tayi,tana shafa kan fadeela gami da maida mata gashinta da ya ya mutse baya

"Ta saba aiko a gida sai tayi bacci kafin na koma dakina" kai afifa ta gyada tana kallon fuskar fadeelan cikin tausayawa,farat daya taji yarinyar ta shiga ranta.

Kwana uku cakal amma sai ka dauka fadeelan ta shekara a gidan,ta sake sosai tana ta walwalarta da harkokinta,zuwanta sau ya sake raya gidan,baya rabo da motsinsu da kai kawonsu ita da saahar,maama dai 'yar kallo ce,amma ita kanta yarinyar ta shiga zuciyarta,idan ka gansu zaka dauka itama daya ce daga cikin jikokinta,hadda da dr girema fadeelan ta shiga zuciyarsa,yana kallonta kamar su Aleena,idan ka shigo gidan zakayi tunanin itama jikar gidan ce kamar su khalifa.

Fadeelan bata taba jin rayuwa tayi mata dadi ba kamar wannan lokacin,saahar ce komai nata,yadda take kula da ita a gida haka a nan,harna sama da gidan,saboda a nan din a sake take fiye da can da take ganin bata da wani hurumi da can din. Batun ciwo kuwa tun randa aka kawota babushi ya tafi,gefa guda kuma kullum sai sunyi waya da nadeeya da kuma dr Jarma,wanda ya dauke nadeeyan ya maidata gidansa,yace itama ta zauna a can na wani lokaci.

*****Duk yadda yakai ga son ya dauke kai ya bar musu fadeelan yaga iya gudun ruwansu amma ya gaza. A yau yana tsaka da aiki ya kashe system din ya mige gafafunsa saman table din hadi da relaxing bayansa jikin couch din da yake kai yana lumshe idanunsa,jiya ya kira nadeeya yayi mata titsiye,ta kuma tabbatar masa fadeelan tana can. Yaso qwarai ya tattara ya zuba musu idanu,to amma zuciyarsa ta kasa dauka,gidan gaba daya shuru,babu kowa,dr din ya dauke nadeeya kamar yadda ya dauke fadeela.

Miqewa ya sakeyi yana kaiwa bakin corridor din dab da wasu flowers dake fidda sanyi me qamshi,ransa yana zafi sosai game da yarinyar. A baya yana lallaba rayuwarsa,yana yinta hankali kwance ba tare da wata baquwar fuska ta kutso musu ba.
Amma daga bayyanarta cikin watanni kacal tana neman ta zame musu qarfen gafa

"Idan kabar mata fadeela tayi winning a kanka" daga can tsakiyar zuciyarsa ake gaya masa,kamar an zaburar dashi ya dawo da baya ya dauki wayarsa yayi kiran number dr jarma.

Bugu biyu ya daga ya koma ya zauna sosai yana gaidashi cikin girmamawa. Kadaran kadaham ya amsa masa,cikin kamewar nan tasa yace

"Abba idan babu damuwa zan qarasa na dauki fadeela, kusan hutunsu nex week zai qare,ya kamata ta dawo ta shirya a nutsr kafin lokacin" gyara zamansa dr jarma yayi

"Eh to ai babu laifi.
..ummm... babu laifi,amma
idan kaje ka tano harda yarinyar khadijatu me kula da ita din kenan" hannunsa ya dunqule guri daya yana shigar da tafin hannunsa ciki

"Okay abba" ya fadi yana jin kamar dr jarma din yayi masa wata mummunar bushara

"Ka dauki saiiad kuma ku tafi tare" dr jarma ya gara fada,saboda yanason ya samu me masa monitoring abubuwa "In sha Allah" ya fada sanann ya gimtse wayar.

Iska me zafi ya furzar daga bakinsa zuciyarsa na sake soyewa da bacin rai da kuma damuwa,dr yana girmamawa al'amuranta da yawa,ya bata wani matsayi me girma,ya bata kuma yarda dari bisa dari

"Ya Allah, ya rabb,kada ka sanya yarinyar nan ta zame mana sharri cikii rayuwarmu,dukka abinda ya qulla ya Allah ga wargazashi" ya samu kansa da furtawa.

Lokaci ya duba yaga akwai sauran lokaci da zai isheshi yaje ya dawo,sai ya fada toilet ba tare da ya kira sajjad ba,nufinsa idan ya gama shiryawa sai ya kirashi,idan yace baya cikin gidan shikenan sai yayi tafiyarsa,ya tabbatar aikin Sanya Ido zaije yayi,shi kuwa sam sam bazai iya wani tsaiwa lallabata ko neman alfarma daga gareta ba.

Tsaf ya shirya cikin kamala da wani ajiyayyen kyau da kwarininsa cikin wani lallausan vadin boyel me garancin kauri,fari ne qal kamar yadda kake iya hango fara tas din singlet dinsa daga ciki,rufaffen takalmi ya saka charcoal color na kamfanin Stuart Weizmann me asalin kvau da tsada. Kansa sai dake dauke sassalkar sumar daya gada daga bangare biyu,dr girema asalin shuwa dan qasar borno,da kuma maji balarabiyar
Algeria ta kwanta luf saman kansa tana sheqi da fidda tattausan qamshi. Lafiyayyar fatarsa yake daurawa agogo,dai dai lokacin sajjad ya tura gofar ya shigo sanye da wata abaya ta maza,da alama yana cikin gidan yana hutawa,idanunsa akan TOUFEEQ da yayi wani mugun kyau

"Yanzu nake shirin kiranka ka fito zaka yimin
rakiya"

"Amma dai my man.....
.Wannan kwalliyar
zance zakaje?" Ya jefa masa tambayar cikin shakku. Kyawawan fararen idanunsa ya dago ya watsa masa,bayan ya dakata daga sanya agogon,wani abu yayi masa tsaye a wuya,kamar zaiyi magana sai ya maida bakinsa ya rufe yaci gaba da daura agogonsa,don yiwa sajjad magana ma bata bakine,kome zai fada bazai fasa jansa da magana ba,kuma gobe sai ya qara. Shi kuma a yadda yanzun yakejin zuciyarsa ko doguwar magana bayason yi. Gaban dressing table dinsa ya qarasa,ya dauki turarukansa ya fara feshe jikinsa daga wuyansa zuwa qirji,sannan ya sauya wani ya feshe sauran sassan jikinsa dashi,ya ciri key din mota guda daya daga inda yake ajiyesu yayi gaba yana fadin

"Kada ka wuce minti uku,ina parking lot" ya garasa fita ba tare daya waiwayoshi ba.
Qaramar dariya sajjad ya saki yana dan buga qafansa, already yasan da fitar,tuni Dr ya sanar masa,amma baisan da wurwuri haka zasuje ba

"Ko second daya ka bani sai fa na rakaka" yayi zancan shi daya,sai ya juya ya fita daga dakin.bava iin zai canza komai a jikinsa,don dakin,baya jin zai canza komal a jikinsa,don haka takalmi kawai ya sanya ya biyo bayanshi.
*HUGUMA*

* TABARMAR KASHI_*

Book 02 Page 04

Sosai take zaune gaban dr girema gafafunta a tanqwashe kamar zata maidasu cikinta,ko cikakken motso batayi tun zamanta a wajen

"Sati guda suka rage miki,har yanzu bazan hanaki damarki ba,ki bawa Mahmud dama,ko kuma ki gabatar da wanda kikeso ban hanaki ba,bance lallai sai mahmud ba,shikenan maganar,kina iya tafiya" kamar qafafunta ba zasu iya daukar gangar jikinta ba haka ta miqe tana hada hanya,tun jiya kanta yake mata ciwo kadan kadan tunda taji abban nata yana nemanta,ta sani dama tatsuniyar gizo ba zata wuce ta qoqi ba. Sannu sannu takai kanta daki,Allah yasa yau din afifa ta dauki fadeela sun fita yawonsu,itama meson fita guraren shan iska ne kaman afifa,sai biyu ta hadu sukayi tafiyarsu suka barta.

Ba irin saqe saqen da zuciyarta
batayi mata ba a sanda take kwance saman gadon,tana hasaso yadda yau za'a daura mata igiyar wani,wanda dukka wani nauyi nasa da haqgin aure zai rataya a wuyanta,duk wata kebantacciyar mu alama ta maaurata zata hadasu?, Saita runtse idanunta gabanta na tsananta faduwa. Bata shiryawa wannan al'amarin ba sam cikin rayuwarta,ta sake mallakawa wani namiji zuciyarta da gangar jikinta?,wani abu ne me wahala da ko cikin mafarki batason ganinsa bare a zahiri. Kuka takeson yi amma a yau din zuciyarta gaba daya ta ida qeqashewa,sai faman zafi da radadi da zuciyar keyi.

Baaba rabi ce ta shigo dauke da wayarta data wuce ta bari a falo

"Alhaji yana kiranki" tana daga kwancen ba tare data cire kanta daga cikin duvet ba ta miga hannu ta karba wayar ta kara a kunnenta

"Kina ina?" Dr girema ya tambayeta

"Ina dakina"

"To yayi,ki duba nan veranda dake baya kina da bago" wayar ta saki ta sulale cikin duvet din. Wai me yasa mahmud bazai haqura ya sakar mata mara tayi fitsari ba? yafison suvi zama mara alfanu?,zaman da ba zai qaru da ita da komai ba?,tabbas yau zata sake jaddada masa da babbar murya,don bata shirya wani rayuwar aure da kowa ba,dole idan abba yaga ya janye kuma bata kawo kowa ba ya haqura ya ayaleta. Da wannan qudurin ta sauko daga saman gadon cikin bacin rai,Adire boubou ce a jikinta,saita yafa mayafinta zalla saman kanta ba tare data nema babban mayafi ba ta zura takalmanta ta fice.
Chapter 84 · 0% Book details