← Book details Tabarmar Kashi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 73 OF 171

Sashe 73

Tabarmar Kashi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jikinta ta kalla babu buqatar sai ta koma ta canza kaya,doguwar riga ce da hijab dinta madaidaici duka golden yellow,sai wani adon wani abu me kama da lace da akayi daga qasan hijab da rigar sai slippers dake qafafunta.

Juya muqullin tayi tana duban
motar,qirar motar ba baquwarta bace duk da tana da tsada,ta saki boyayyen murmushi,tana rige da hannun fadeela daketa tsallen murna sukayi gaba,labiba dake cika tana batsewa ta biyo bayansu.

Kafin labiban ta iso tuni ta bude front seat ta sanya fadeela,ta zagaya sashen driver ta bude ta shige,dole da tazo back seat ta bude ta shigan tana qwafar raina mata wayon da sãahar din tayi

"Ko ba komai yau mun samu new driver" ta fadi don ta baiwa sãahar din haushi

Sarai ta jita,amma saitagi nuna hakan,murmushin da ya subuce mata ma kauda kanta tavi gefe don kada ta gani

"Zakiga new driver gain idonki" ta furta gasan zuciyarta.

Hira sukeyi da fadeela irin wadda suka saba,daga yadda suke hiran kadai zai gaya maka zallar shaquwar dake tsakaninsu da kuma gaunar juna,labiba na zaune a baya kamar zata fashe,ita taso samun wannan damar, amma kuma bata sameta ba koda quater dinta,yanzun ga wata banzan nanny daga sama tazo ta mamaye rayuwar yarinyar.

Sai data tabbatar fadeela ta shiga class,ta kuma sanya hannu akan kawota sannan ta fito. Zata tada motar mrs sadeega ta sanvo kan tata,dole ta tsaya suka gaisa "Kina aiki me kyau miss säahar, kowa ya kalli fadeela yasan tana samun canji garara,hatta da performance dinta a class ya qaru,tiny baby ta fara komawa chubby ma sha Allah"

"Alhamdulillah" sãahar ta fada,ita kanta tana jin dadi ko yaushe yadda yarinyar ke wayar gari da goshin lafiyarta da kuxarinta suna garuwa,basu jima ba sukayi sallama,mrs sadeega ta wuce su kuma suka fice.

Ta cikin mirror ta dubi labiba dake zaune a bayan ta toshe kunnuwanta da earpiece tana bin waqoqin turawa tana gyada kai,murmushin mugunta ta saki, saita take motar ta qara mata gudu. Da sauri labiban ta daga kai,ta zare earpiece din daga kunnenta

"Ke meye haka? ki rage gudu da Allah" tana kaiwa nan ta maida earpiece din. Da kadan kadan ta sake garawa motar gudu fiye da dazun,tuni labiba ta cire earpiece din harma da wayar duka ta ajjiye,cikin fada da tashin hankali take magana

"'Wai bakya gani ne,wanne irin gudu ne
wannan?,kashemu zakiyi ne,dake fa nake
magana!" Kunnen uwar shegu tayi da ita,salma
sake qara gudun da tayi,ta shiga kurdawa
tsakanin motoci tana overtaking,ta tuna
da tsohuwar dabi'arta na mugun gudu a
hanya,don a baya saida yaa Saifullahi yasa aka hanata mota na wasu watanni sannan ta bari.
Tun labiba na hayaniya har ta fuskanci
hayaniyar ba zata kaita ba,ta koma lallashi
da kwantar da murya,amma sãahar kam ko
a jikinta,ta dinga shimfida gudu da ita,sai ga
labiban tana sakin hawaye,kowanne sashe a
jikinta rawa yakeyi,don babu abinda ta tsana a
mota irin gudu.

Daga bakin gate din gidan ta tsaida motarta bude ta fice abinta tare da bar mata
key din a jikin motar,tayi knocking gofar gate
din,daya daga cikin security din ya taso ya duba wacece sannan ya bude mata. Baya yaja cikin rusunawa,saboda sosai Allah ya sanya ma ma'aikatan gidan gaba daya gain wani irin girmanta. Yadda suke mu'alama da masu aikin gidansu haka ta dauki kowa cikin gidan,tana girmamasu qwarai, irin girman da duka cikin gidan ba wanda ke basu irinsa,bugu da qari me hannun kyauta ce ita,a hakanma afifa tace mata saita rage,don kada su lura da ita din wace,su sanya ayar tambaya a kanta.

"Madam ya na ganki a qasa?" Ya fada da 'yaf gaurayayyiyar hausarsa da bata fita tarr
"Daga waje na sauka"

"Welcome" ya sake fadi yana dage gate din don yasan yana jinkirin budewa labiban yau shine mutum na farko da zata fara saukewa kwandon rashin mutuncinta na safe.

65
*HUGUMA*

* TABARMAR KASHI_*8

DON MARTABAR MANZAN ALLAH ME
FITARWA KIYI HAKURI KIYI HAKURI.

Hankalinta kwance tama manta da wani abu da ta yiwa labiban,ta gama shirinta tsaf ta canza kava,tana duba saqon afifa a waya da take gaya mata mahmud nason a bashi dama yazo ganinta,sai taji sallamar hajiya qarama cikin matsakaicin parlor din da daga shi sai hallway na dakunansu,don ba kasafai take fita babban falonsu ba indai ba kitchen zata ta shiryama fadeela abinci ba.

A nutse ta daga kai tana amsa
sallamar,kamar kullum hajiya qaraman cikin shigar alfarma dake nuna zallar alfaharinta take,labiba ce da tayi firgai firgai ke take mata baya,ta zamu daya daga cikin kujerun ta zauna idanunta akan sãahar tana karantar yadda yarinyar sam wani abu baya mata kwarjini ko va tsoratata

"Barka da safiya" ta gaidata cikin salon data saba gaisuwa,sai data gyara zamanta sannan tace

"'Barkanki,ya kwanan uktie?"

"Alhamdulillah ta amsa mata tana qogarin katse kiran dake shigo mata waya.

"Ya akayi kikayi gudun wuce sa'a haka da labiba.har kina shirin hallakata?" A nutse ta sake kallon labiba sannan ta maida kan hajiya garama

"Ni din?"

"Kefa" ta amsa kai tsaye tana kallonta,tare da mamakin yadda take bada amsa lokuta da dama kanta tsaye,kamar ba wadda ke aiki a qarqashinsu ba,ita din kuma sai ta gaza daukan kowanne hukunci koda da zazzafar magana ne,abinda bai taba faruwa ba tsakaninta da duk wani me hidima dake qarqashin ikonta.
Ajiye wayarta sãahar din tayi sannan tace

"To bansan sanda akavi haka ba,don normal driving nayi yadda na saba,saidai ko a idonta ne ya zamana gudun daya wuce qaida,asalima a waie na sauka nabar mata motarta ta qarasa shigowa da ita,kina iya tambayarsu idrith dake bakin gate" yadda tayi maganar a miqe kai tsaye yasa hajiya qarama duban labiba

"Wallahi qarya takeyi,jini na saura kadan ya hau" labiban ta furta kamar zata saki kuka

"Bansan waye me gaskiya a tsakaninku ba,sai kiyi haquri, tunda bakison hudu next time karku sake hada mota" baqinciki kamar zai kashe labiban haka ta juya ta fita, sãahar kuwa ko daga kai ta kalleta bata sake yi ba.

"Ina fatan magungunan nan sun qare kamar yadda na irgasu?" Hajiya garama ta fada bavan ficewar labiba,wayar ta kuma ajiyewa,ta dora idanunta duka cikin na hajiyan. Wani abu me qarfi hajiyan taji tattare dasu,sai ta zame ganinta tana cewa

"Kin zubamin ido baki amsamin tambayata ba"

"Sun qare‚na yau kawai ya rage"

"Kin tabbatar?" Saita jinina kanta kawai ba tare data ce komai ba. Tsam hajiyan ta miqe tana mata wani kallo

"Yayi kyau,cikin satin nan ganwar mahaifin fadeela zata dawo rayuwa damu cikin gidan nan,banason komai ya canza daga cikin sharudan dana gindaya miki,and then....magungunanta duka zasu dawo hannuna,duk lokacin da zata sha ki kaimin ita tasha sannan ta taho,wasu lokutan tafiye tafiye na kasuwanci na suna kamani,idan hakan ta taso zan damqa su a hannunki ta yanayin daya dace" daga haka ta juva tana fita daga falon.
Kasa dauke kallonta sãahar tayi daga kanta,haka kawai a yau din wani qaqqarfan zargi ya taba zuciyarta,sai taji gaba daya zuciyarta tayi mugun matsewa da takurar son jin wanne matsayi hajiya qaraman ke dashi a gurin fadeelan.

Kusan zaman banza tayi a gurin,ta kasa tabuka komai,zuciyarta da kwanyarta nata jujjuya mata al'amura masu dama game da rayuwa,hango kanta ta dinga yi shekarun baya,lokacin da adam ya maidata mahaukaciya tuburan,ya dinga shayar da ita gubar allurai da magungunan da suka kusa sanyata amsa sunan mahaukaciyar me license ma,tsoro ya shigeta bayan wata zuciyar ta ayyana mata.
.. hajiya garama na
daya daga cikin masu wanna hali da dabiar.
Wani gumi ne ya karyo mata,ta yaya zata bari hakan ya faru da zuciya da ruhin da suke da rauni,salihar zuciya da kyakkyawan ruhin da basusan sabo ko cuta ba,sam sam....ba zata taba bada wannan damar ba,zata yi dukkan me yiwuwa ta katange fadeela daga dukkan wata cuta muddin ranta matugar ta samu kuma tabbaci da yaqinin abinda take zato din,sai inda qarfinta ya qare.

Sau uku baaba ramatu na wuceta,tun batayi magana ba harta tambaya

"Antyn fadeela lafiya kike yau kuwa?" Dan garamin murmushi ta saki tana gyara kwanciyarta cikin sofa

"Lafiya lau nake baaba, kasala kawai nakeji"

"Jiki da jini dama,to Allah ya garemu da lafiya"

"Ameen ya hayyu ya gayyumu" ta amsa mata tana maida idanunta ta lumshesu

Dawowar fadeela daga makaranta ne ya tasheta a wajen,yau gaba daya zancanta na dawowar sister nadeeya ne(haka take kiranta kamar yadda taji abby dinta wani lokaci yana kiranta da shi),ta hana sãahar yau sakat,alamu sun nuna akwai qaqqarfar shaquwa a tsakaninsu,bata samu hutu ba sai da suka kammala komai,ta hau google meet ta kira mata abby dinta,ta ja mata qofar dakin ta barta a ciki. Tun wancan ranar bata sake bari nasu take barin parlor din ko gurin,har sai ta
kammala sannan ta biyota tana bata labarin hirar da sukayi da abby dinta.

Tana kitchen tana hada mata abinci ta
shigo da gudu da tab din a hannun ta

"'aunty,don Allah sister nadeeya zaki kiramin" ta
fada a marairaice,murmushi ta saka ta ajjiye
wuqar hannunta,ta goge ruwan hannun nata
jikin towel,ta koma ta watsapp din da aka
budeshi saboda ita kadai ta kira matan,cikin
sa' a tana online sai ta miga mata ta koma aikin
nata,ita kuma ta juya da gudu ta fice.

Tun daga kitchen din take jiyo hirarsu da
dariyarsu,allai nadeeyan uwa ce da fadeela keyi da ita sosai. Har ta gama abincin ta
baro zuwaira hirar bata qare ba,sai ta wuce
dakinta ta daura alwalar sallar la'asar. Tana
idarwa fadeelan na shigowa rungume da tab
din,murya qasa qasa tace

"Sister nadeeya tace na kawomiki ku gaisa,nace abby ya hana sai an fara tambayar mutum tukunna,don Allah aunty nanny zaki gaisa da ita?" Murmushi ya subuce mata, fadeelan badai jin magana ba,saita miqa hannu ta kamota jikinta,ta karba tab din ta ajjiye a gabansu,fuskar nadeeya ta fito sosai a screen din.
Murmushi ya wadaci fuskar nadeeya, okaci daya da idanunsu suka gauraya waje daya kowa yaji wani abu game da dan uwansa

"Barkaaa" nadeeva ta fada tana waving hannayenta wa sãahar

"Barka kadai" sãahar ta maida mata itama cikin murmushi

"Yamma ne nan ko? to kin yini lafiya auntynmu?" Murmushi ya sake subucewa
Chapter 73 · 0% Book details